Showing 24001 words to 27000 words out of 154779 words

Chapter 9 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6294

Nadiya sukan shigo domin wasa da su duk da haka shi baya shiga kum Mansur ne sa'an Hilal don ko watanni biyar ne a tsakanin Hilal da Mansur.

Yaran Salisu kuwa Mahmud da Sadik ba da zuwa ko ina daga part ɗin su sai kuma na kakanninsu don ko sun je sai an koro su wata rana ma s haɗa masu da duka don Maimuna matar Abubakar ba ta da mutumci ko kaɗan. Da Mahmud suka fahimci tsanar da aka masu sai suka daina shiga wajan su sai dai wakan kakanninsu. Ita fama ƙanwarsu Fatima Zahrah ba ta zuwa ko ina kullun tana maƙale da Dada ballantana ba isashshiyar lafiya ce da ita ba tana da ciwon athma kuma mai tsanani da tari ya fara mata daga nan idan tana tari sai ta ce wa Ummi tana jin numfadhinta sama-sama ita Umminta ta ɗauka mura da tarin da take yi ne ya sa take numfashi sama-sama don haka dai ta faɗa wa Abbi ya siyo mata maganin tari suka fara ba ta amma bai daina ba. Don haka suka yanke shawarar kai ta asibiti. A ranar da suke da niyyar kai ta asibiti ne Ummi ta shirya ta tana kirasa girki kafin su tafi.

Ta ɗora manja a tukunya ta ɗora a wuta sai ta ji ƙarar kiran wayarta, fita ta yi daga kitchen ɗin ta nufi falo don ta san Abbi ne ke kiran wayarta.

Tana falo tana amsa wayar da Abba ya kira ta sai Fatima Zahrah ta nufi kitchen lokacin manja da Ummin ya ɗora a wuta ya ƙone yana hayaƙi. Fatima Zahrah na shiga ta shaƙi wannan hayaƙin sai ta fara tari numfashinta ya fara fita sama-sama ta fadi a wajen daidai lokacin da Ummin ta dawo kitchen da sauri ta lashe wutar tare da ɗaukar Zahrah ta nufi Falo don ba kowa Mahmud da Sadik suna school ita ma saboda asibitin da za su ne ya sa ta zauna gida Abbi na office.

Ɗaukarta ta yi ta nufi harabar gidan tana ƙwalawa direba kira. Dada ce ta fito don ɓangaren su yana kusa da nata. Ganin Ummin rike da Zahra hankalin Dada ya tashi da sauri ya ƙaraso tana tambayar abinda ya same ta. Shiga motar tayi bayan Ummin ta saka Zahrah a bayan motar sannan ta koma sauri-sauri ta dauko Hijabinta.

Koda suka karasa asibitin ganin halin da Zahrah ke ciki aka amshe su cikin gaggawa.


Bayan wani lokaci tana kwance tana barci Dr ya fito ya basu izinin su zo yana son ganinsu s office dinsa.

Nan yake sanar da su cewa Fatima Zahrah na ɗauke da cutar Athma. Cikin tashin hankali Dada ke mamakin wai ƙaramar yarinya mai shekaru goma ce ke da wannan cuta. Nan ya sanar da su cewa ciwon baya son sanyi zai iya tashi idan sanyi ya shiga jinkinta Kum ta kiyayi wanka da ruwan shayi da shiga cikin ƙura ko hayaƙi ya dai kafa masu dokokin da za su kiyaye tare da magunguna da kuma Inhelar da za ta dinga shaƙa.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a cikin gidan ba abinda ya sauya akan zaman da suke yi, ana cikin wannan halin Laila ta dawo da yaranta wai mijinta ya sake ta. Ta kwaso yaran wai ba za ta bar su a wajen kishiya ba.

Tun da Laila ta dawo ta fahimci soyayyar da Dada da Papa ke yi wa yaran Abbi musamman Fatima Zahrah ya sa ita ma ta fara jin haushin hakan.

Don ba su ma damu da yaranta yadda suka damu da Zahrah ba da yadda suke kula da ita ya ƙaru saboda laruran da take da shi . Ta so ace Dada za ta fifits Nabeela da Kausar me amma ta ga ba haka ba.

Don haka sai ga haɗa kai da sauran matan gidan suna ƙuntatawa Ummi.


Papa ya samu buɗi sosai ya canza masu gidan wani ƙaton gida na Alfarma ya siya mai part da yawa sama da ƙasa. An gyara gidan sosai ba kowane iyali part nasu. Iyaye mata part ɗin su hudu har da Aunty Laila kenan kowacce part ɗin ta da ɗakunan hudu da falo bayan babban falon na kowa a gidan dai samarin gidan kowanne part ɗin sa na upstair. Zuwa lokacin Hilal mahaifinsa ya kai shi karatu ƙasan waje.


Sai da ya yi shekaru biyar bai dawo ƙasar ba, sai dai su dinga waya da iyayensa. Yana can zaune a ƙasar America yana gudanar da aikinsa a can.

A yanzu yana da matsayin Chief of staff of the army Tamim Walton.

Yana gudanar da aikinsa a can ƙasar America saida mahaifinsa Dady ya matsa masa Sannan akan ya dawo, baya haka ma mahifiyarsa Mummy ma ta damu da dawowarsa.

Yaa Mahmud kuma aikin banki yake yi, yayin da Yaa Sadik kuma lauya ne, sai Yaa Mansur kuma ɗan jarida ne, sai Yaa Faisal dake shaƙar ƙarshe a jami'a.

Hakan ya saka shi ya dawo ƙasar in da suka shirya liyafa ana shagailin dawowarsa.

Bayan kwana biyu da dawowarsa ne Dada ta dafa masa zogale wanda ta aika Fatima Zahrah ta kai masa har ta yi masa ɓarna ya saka ta punishment ciwonta ya tashi ta kwana a ɗakinsa wanda ya kawo hargitsi a cikin gidan. Har sandiyar fitar Zahara zuwa makaranta da Mansur ya ce a kai shi Wajan aiki har aka yi dambe da Yaa Sadik da Yaa Mansur har Papa ya kira kowa ya zo.



*Cigaban labari*

Gabaɗaya ilahirin jama'ar gidan kowa ya hallara a falo. Ga fuskar Sadik da Mansur duk sun ji wa juna rauni.

Kallo ɗaya za ka yi wa Papa ka gani ɓacin ran da yake ciki.

"Ban san ya kuke so na yi ba, so kuke ku kashe ni da baƙin cikinku ko? Yaushe za ku so juna? Yaushe za ku saka ni farin ciki kuma ku zauna cikin farin ciki?"

Kallon Munsur ya yi tare da cewa.

"Kai a matsayinka na Yaya a wajen Zahra don ko kana so ko ba ka so ita ɗin jininka ce ba ka isa ka canza ta ba. Shin akwai wanda baya da motar kansa ne a cikin samarin gidan nan? Sauran motocin gidan na tanade su ne saboda ƴan mata idan za su je makaranta da iyayenku mata idan za su fita unguwa. Amma saboda neman fitina da tashin hankali ya sa ka hana ya kai ta bayan ta makara da zuwa makaranta ko?"

Kallo sa ya mai da kan Nabeela ya ce.

"Kema ranar har ta shiga Mota kika ce sai dai ta fito akai ki a dawo da ke kafin a kai ta ko? Shin motar mutum ɗaya yake zama a ciki ne ba na za ku iya zama a tare a kai kowacce makarantarta ba?"

Budar bakin Nabeela ta ce.

"To Papa ta yaya zan shiga motar da ita ta saka mani cutar da take da ita, ai ana ɗaukar cuta ta shaƙar numfashi."

Kausar ta yi saurin cewa.

"Wallahi ni ma ba zan iya zama waje daya da ita ba."

Sadik ya yunƙura zai yi magana Abbi ya ɗaga masa hannu. Hakan ya saka ya danne zuciyarsa.

Zahra kan hawaye ne ke fita daga idanunta ganin yadda ƴan uwanta ke gudun ta saboda wata larura da Allah ya jarabe ta da shi.

A fusace Papa ya ce daka masu tasowa tare da cewa.

"Kuna da hankali kuwa? Me take da shi da kuma gudunta? Ko cutar ƙanjamau da hanta da suke da illa ana ɗaukarsu ta hanayar shaƙar iska ne? Ballantana ciwon asma meye illarsa?"

Kallon Aunty Laila ya yi tare da cewa.

"A gabanki yaran nan suke fadin irin wannan magana kina kallonsu ko?"

"Papa ka yi hakuri yara ne ba su san komai ba."

"Irin tarbiyyar da kike yi wa yaranki kenan ko? To na gaji haka nan, dama ina fama da iyalan gidan nan amma tunda kika rabu da mijinki kika dawo da yaranki komai ya ƙara lalacewa. Ki kwashe su ki mayar da su gidan uban su ba. Zan iya ba."

"Papa don Allah ka yi hakuri Wallahi mahaifinsu baya ƙaunarsu yanzu haka ma baya ƙasar amma da zaran ya dawo zan mayar da su."

Wayarsa ce ta soma ruri ya duba ya ga abokinsa ne Dr Ibrahim. Hakan ya saka ya ɗaga.

Bayan ya saurare maganar ne ya katse kiran wayar tare da ɗaukar sandarsa ya fara tafiya yana cewa.

"Fita na gaggawa ta kama ni, za ku iya tafiya sai na dawo."

Daga nan ya fice daga gidan kowa ya watse Mahmud ya kai Sadik asibiti yayin da shi ma Mansur Faisal ya ɗauke shi don kai shi a yi masa diresin Wajen.

Daga nan kowa ya watse washegari tafiyar gaggawa ya kama Hilal ya koma America.

Papa da kansa ya saka aka kawo masa sabuwar mota ya mallaka wa Zahrah, ya ce duk in da za ta ke ta tafi da ita ta bar masu wadancan motocin. Ta yi farin ciki da godiya ta ce ba ta son direba za ta dinga driving da kanta. Don haka Yaa Mahmud ne idan yana free yake koya mata.


Sai da Hilal ya dauki lokaci bai dawo ƙasar ba don har sai da Mom ta matsa masa akan rashin dawowarsa.



Hakan ya saka rana ya dawo kasar tare da yaransa sojoji, wanda saboda murnar dawowarsa ne Mummy da Umma da Aunty Laila suka ce da masu girkin gidan kowacce kada ta shiga kitchen su za su shiga su girka masa girki na musamman.

Ranar da ya dawo ne Zahrah tana kwance a asibiti da ciwonta ya tashi ta zo ɗaukar magani Aunty Laila ta cilla maganin ƙasan kujera har ƙawarta da abokinta suka ɗauke ta zuwa asibiti.



*Cigaban labarin*


Bayan Fatima Zahrah ta gama waya da ƙawarta akan cewa akan za ta kawo mata abincin da za ta ci ne ya sa koma cikin ɗakinta tana zaman jiran zuwan A'isha.

Bayan kamar mintuna talatin aka tura kofar dakin aka shigo da sallama.

Tashi zaune ta yi tana amsa sallama tana kallon A'isha.

"Sannu ya jikin?"

"Da sauki na gode."

Miƙa mata abincin ta yi ta cire cokali ta bude ta fara ci. Aisha ta tashi ta karasa ta dauki mata ruwa a fridge.

Bayan ta gama cin abincin ne A'isha ta kalle ta ta ce.

"Don Allah ki daina sakaci har ciwon ya yi tsanani. Ba ki da magani ne?"

"Ina da magani na je zan ɗauki maganin shi ne a falo shi ne Aunty Laila ta jefa su ƙasan kujera suna kallona suka tafi suka bar ni. Sai ga Yaa Mansur ya sake buɗe gudun A.C hakan ya saka ciwon nawa ya yi tsanani. Sai ga kiran wayar abokin kwara ya kira ni a waya ya ji halin da nake ciki maybe shi ya saka ya kira ki, farka wa na ji na ganni tare da ku a asibitin. Bare sun Y Mani abin da jini na suka kasa yi mani. Kun cece rayuwata yayin da dangina suka nemi kashe ni."



*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page1️⃣3️⃣


Bare sun yi mani abun da jinina suka kasa yi mani. Kun ceci rayuwarta yayin da dangina suka nemi kashe ni."

Ta yi maganar tana goge ƙwallar da ya gangaro daga Idanunta.

"Gaskiya zamanki ke kaɗai a cikin wannan gidan ba zai yiwu ba, saboda ba ki da isashshiyar lafiya ga Umminki da Abbinki ba sa gari, dama a ce ko su Papa da Dada suna nan ne da sauƙi. To dukkansu huɗu tare da tafi Saudiya aikin umara to ya za ki yi?"

"Ba yadda zan yi A'isha."

"Ko za mu je ki cigaba da zama a gidanmu kafin su Umminki su dawo?"

"Rufa mani asiri kafin a ƙalla mani wani sharrin, a haka ma kwana ɗaya da muka yi asibiti sai da suka ce wai yawon karuwanci na tafi."

"Subhanallah!, To Allah ya kyauta."

Da amin Zahrah ta amsa yayin da wayarta ke ruri.

"Wai ina Yaa Mahmud da Yaa Sadik ne?"

"Sun bi su Abbi Ni ma saboda exams na ce ba zan je ba."

"Okay Allah ya dawo da su lafiya."


Bayan sun taɓa fira A'isha ta yi mata sallama, miƙewa ta yi suka nufi ƙofar fita.

A ƙofar falon suka hadu da Yaa Hilal yana ƙoƙarin shigowa falon, tsaya wa suka yi ya fara shigowa A'isha ta kalle shi ta ce.

"Sannu ina wuni?"

Ko kallonsu bai yi ba ballantana ta saka zan zai amsa mata, da kallo ta bishi ya haura upstairs har yana tsallake steps. Sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta mai da dubanta ga Zahra ta ce.

"Shi wannan guy ɗin kullum idan aka gaishe shi baya amsawa mutane gaisuwa, dai ya yi kamar kurma don ko kallon mutum baya yi ballantana a san cewa yana ji baya amsawa ne."

"Hmm to dole ne sai kin gaishe shi ballantana idan bai amsa ba ki yi ta damuwa da mita?"

"Ke ma kin san ban cika gaida mutane ba, ban san me ya saka ba shi duk na hadu da shi ba na iya haƙura sai na yi masa magana ba, so nake ko sau ɗaya ya kalle ni ya amsa mani"

"Saboda me?"

"Kawai dai ban taɓa ganin namijin da ya cika duk wasu qualities da ake buƙata a wajen ɗa namiji ba sai shi."

Taɓe baki Zahrah ta yi tare da cewa.

"A ganinki kenan, shi ɗin wasali ne da shi da za ku ce baki taba ganin ɗa namijin da ya kai shi ko yafi shi ba?"

Murmushi A'isha ta yi tare da cewa.

"Zahra kenan, ke ai baki san komai ba akan nagarta ɗa namiji, amma bari na fada maki duk in da ake neman cikakken ɗa namiji aka zo kan wannan guy ɗin an gama. Yana da ƙira da ƙira da da cikar halitta da zati irin na cikakken ɗa namiji. Yana da wani irin kwarjini da zarra wan da ba kowane irin mutum zai iya tunkararsa ba, ni kai na nikan so na yi masa magana wanda zai sa ya kalle ni amma sai na ji na kasa saboda kwarjinin dake cikin idanunsa, wallahi yana da jini mai gudu a jikinsa."

Cikin takaici Zahra ta ce.

"Kema sai ki shiga sahu tun da kin zama ƴar wahala."

Cikin rashin gane in da zancen ta ya dosa ta ce

"Sahun me zan shiga?"

"Sahun masu sonsa mana, ga Aunty Nabeela nan da Aunty Kausar. Bayan su ma wasu ƴan matan ni kan ga sun biyo shi har gida. Kada ki ga haushinsa da nake ji wallahi namiji ya yi ta masu wulakanci amma suna bin sa don rashin zuciya. Kada ki ga wata fa ranar na dawo daga Islamiyya har tana kuka akan ya ƙi sauraron ta ta biyo shi tana masa magiya tare da roƙonsa, kamar shi kadai ne ɗa namiji a duniyar nan."

Ganin A'isha na kokarin cigaba da na ƙoƙari na cigaba da zancen sa ne ya saka ta ce mata.

"Ke Mallama zanensa ya ishe ni haka nan, ba ki san mugun hali da muguntarsa ba ne shi ya saka kike yabonsa wallahi bai da imani."

"Ya taba maki abu na rashin imani ne?'

"Zan baki labarin amma ba yau ba, kin san ba na da lafiya ."

Sallama suka yi A'isha ta ja motarta ta fice yayin da Zahra ta koma cikin gidan.


_Sir Asadullah_

Kwance yake a ƙasar ɗakin an rufe masa baki da salatef, ƙafarsa ƙafarsa ma an ɗaure ta da da wani sarƙa an ɗaure masa sarkaa sarƙa a ƙafarsa.

Juyi kawai yake yi a ƙasan ɗakin sam tiyes ɗin ga kansa dake sara masa. Hatta hannayensa ɗauke suke waje guda an haɗe su waje guda. Kwance yake .yana fuskarsa na fuskantar ƙofar amma da alama baya cikin hayyacinsa. Manyan idanunsa sun yi jajir kamar wanda ya yi shaye-shaye.

Cije baki kawai yake yi don cikinsa da kansa ba karamin ciwo suke yi masa ba. Ga zazzaɓi ga yunwa rabin da aba shi abunci tun juya da safe ga shi yanzu yammaci ne.

Yana cikin wannan halin sai aka turo ƙofar ɗakin yake ciki aka yi, wata mace ce sanye da da hijabi da kuka niƙab wanda ya rufe mata fuskarta ko ƙwayar idanunta ba'a gani, bayanta wani namiji ne yana sanye da facemask da baƙin glass a fuskarsa. Daga ganin yanayin shigar da suka yi ka san sun yi shi ne saboda ɓadda kama, ta yadda ba wanda zai gane ko su waye su.

Suna shiga suka same shi a halin da yake ciki. Bayan sun kalle shi ne sai suka kalli junansu.

Body language suke yi daga gani ba sa so su yi magana ne don kada a ce yana cikin hayyacinsa ya gane ko su waye ta hanyar muryoyinsu.



_Jidderh_

Tun da ta ido Asadullah Mantson ɗin hankalinta na wajen Asadullah. Ta so ta duba yau ma ta ga halin da yake ciki don tana son sanin waye ke son ganin bayansa. Mutumin kirki mai nagarta da taimakon al'umma. Kitchen ta fara shiga ta gaida ma'aikatan gidan dake ta aikace-aikace. Ta gushe su don masu gidan suna ciki.

Haɗa idanu suka yi da wata budurwa wacce za su iya zamowa sa'annan juna. Kallonta ta yi tare da mata alama ta zo da hannu.

Ganin haka Bahijja ta fito tana cewa Mama shugaban masu aikin gidan cewa.

"Mana ina zuwa yanzu."

Ba ta jira cewarta ba ta fito ta samu Jidderh a corridor da zai sada ka da kitchen ɗin.

"Ke lafiya kika kira ni?"

"Tambayarki zan yi don Allah."

"Ina jin ki Allah ya sa na sani."

"Ina Sir Asadullah yake ne kwana nan ba na ganinsa."

'Eh to na ji an ce wai baya ƙasar wai ya tafi wata ƙasar, sai dai ban san wace kasa ba ce ya tafi. Sai dai abin da yake bawa mutane mamaki bai taɓa tafiya shi kadai ba tare da amintaccen bodyguard ɗinsa Sulaiman ba. Don shi ma Sulaiman ɗin yana maganar hankalinsa bai kwanta ba, don duk ƙasar da Sir Asadullah yake tafiya a fadin duniyar nan yana da lambarsa na ƙasar amma abin da ya bashi Imamaki wai wannan karon lambarsa ta kowace ƙasa ba ta tafiya."

Jinjina kai Jidderh ta yi tare da cewa.

Wa ke sanar da ke haka?"

"Muna jera masu abinci a dinning table ne sai Sulaiam din ya shigo ya sanar wa Dadyn sir Asadullah."

Jinjina kai Jidderh ta yi tare da cewa.

"Na gode sosai na tsayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login