Showing 3001 words to 6000 words out of 154779 words
B,AMMA TABBAS ALƘALAMINA NA DA KAIFI KUMA NA MUSAMMAN NE. KUN GWADA KARANTA LITTAFAI NA KUN GA SALON RUBUTUNA KUN GANI KUN YABA MANI, NI KUMA IN SHA ALLAH NA ZA KU YI NADAMAR BIBIYATA BA. NA GODE DA YABO DA KUMA ADDU'AN KU A GARE NI, ALLAH YA BAR ƘAUNA.*
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
.*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page2️⃣
"Yaya da ruwana kuma sai inda ƙarfjna ya ƙare."
"Au haka kika ce?"
"Ko na rasa rayuwata akansa ban damu ba in dai shi zai rayu. Saboda shi bango ne da al'umma da yawa suka jingina da shi, rashin rayuwarsa zai zama sanadiyar shigar wasu cikin wani hali, ceton rayuwarsa tamkar ceton al'umma ne. Wannan ma kaɗai ya ishe ni abun alfahari."
Ajiyar zuciya Umma ta sauke tare da kallon Isah ta ce.
"Ka rabu da ita kawai je ka shirya ka tafi wajen aikinka."
Ba musu ya bar wajen ya nufi ɗakinsa.
_Fatima Zahrah_
Tana shiga ɗakinta ta gan shi a yamutse alamar an yi mata bincike. Drawar da take zuba magungunanta ta bude ta zuba su sannan ta fara gyara ɗakin da aka hargitsa mata.
Bayan ta gama ta karkaɗe gadon ta kwanta bakinta ɗauke da addu'a.
Wayarta da ta ajiye gefen filo ta soma ruri. Ganin lambar ya saka ta ɗaga tare da cewa.
"Ummina barka da warhaka."
"Barka dai Zahrah tawa ya kike?"
"Ina lafiya Ummina."
Ta yi maganar cikin raunin murya.
"Na san ba za ki taba jin dadin zaman gidan nan ke kadai ba, kuyi haƙuri in sha Allah next week za mu dawo?"
"To Allah ya dawo da ku lafiya ya karɓi ibada."
"Amin ya Allah, kin ci abinci Kuwa?"
"A'a."
"Ki je ki ɗebi abinci ki ci na San yanzu masu girkin sun gama ."
"To Ummi ina su Abi da su granny?"
"Suna can suna ibada, na ji hankalina bai kwanta da har mafarkinki na yi shi ne n kira na ji lafiyarki."
Mumrmushi ta yi tare da cewa
"Ina lafiya Ummina."
Sallama suka yi sai ta ajiye wayar tare da miƙewa tsaye ta nufi ƙofar fita.
Tana zuwa babban falon gidan ta nufi hanyar kitchen kai tsaye. Tsawar da aka daka mata ne ya sa ta juyo tana kallon Hajiya Maimuna matar wan Babanta.
"Gidan uban waye za ki je a wajen?"
"Dama yunwa nake ji shi ne zan ke na ɗebi abunci na ci."
"To yau dai ba za ki samu cin abinci a gidan ba. Domin masu aikin da ke girka abincin kina ci yau mun hutar da su. Saboda zuwan Babban yaronmu, kasancewar Hilal baya son abincin masu aiki. Don haka wannan abincin haramiyarki tunda ba da uwarki aka shiga kitchen ɗin ba."
Cikin sanyi jiki ta juyo ta kalle kowa da ke wajen, duk suna nan sai dai wannan karon ba ta ga Yaa Hilal ɗin ba.
Cikin sanyin jiki ta koma part ɗin Umminta.
Hijabinta ta saka har ƙasa kamar yadda shine shigar da take yi idan za ta fita. Ta ɗauki handbag ɗin ta da makullin motarta.
Fitowa ta yi sanye da hijabi a hankali take tafiya zuwa lokacin kowa ya watse a babban falon gidan.
Taku ta ji daga upstair ɗin tana juya wa idanunta suka sauka akan Yaa Hilal yana sanye cikin wando na uniform ɗin su sau sai farar T-shirt mai dogon hannu.
Cikin takunsa na isa da ƙasaita da kaga idanunsa ka ga zarra ƙirar jikinsa irin na jarumam mazan nan ƙarfafa saboda yawan motsa jiki da yake yi .
Cigaba ta yi da tafiya yayin da yake bayanta. Tunawa ta yi da wata rana ƙanwarsa Maryan ta shiga gabansa tana tafiya kawai sai ya janyo ta tare da hankaɗa ta ta fadi a saman tiyel ta fasa goshi.
Tunawa da hakan Fatima Zahrah ta yi ƙanwarsa da suka fito ciki ɗaya ya ji mata haka ballantana ita da ta zamo kamar mujiya a wajensu.
Da sauri ta matsa jikin bango don bashi hanya. Ko kallonta bai yi ba ya wuce abinda ya barta da ƙamshin turarensa.
Bayan ta fito ne ta hangi ficewarsa gidan shi da sojojinsa.
Parking lot ta nufa ta shiga motarta har ta yi mata key kenan sai ga kira ya shigo wayarta . A'isha ce ƙawarta ke kira bayan ta isa gida.
"Assalamu alaikum."
Daga can ɓangaren A'isha dake zaune a falon mahaifiyarta ce ta ce.
"Wa'alaiki salam, ya jikin naki?"
"Alhamdulillah."
"Kin ci abinci kin sha magana kamar yadda Dr ya faɗa?"
"No yanzu dai zan je restaurant na siyo."
"Akan me ba kuna da masu girki har mutane uku ba?"
Mumrmushin takaici ta yi tare da cewa.
"Kin san ɗan gatan gidan ya dawo, kuma baya son girkin masu aiki aiki, shine suka ce masu aikin su bari su ne za su girka. Na je zan ɗebi abinci shi ne mahaifiyarsa ta hana ni saboda ɗanta aka girka."
Cikin fusata A'isha ta ce.
"Ji wani maganar banza, yadda fa suka takama da gidan kema dole ki yi, shi ɗangatan na su ai gidan kakansa da ya haifi ubansa ne kema haka gidan kakanki da ya haifi Babanki matsayinku ɗaya akan me za su nuna maki wariya?"
"Kada ki damu da Ummina na nan da dole za ta bani abincin da zan ci."
'kin ga ki koma gida kawai bari yanzu zan kawo maki abinci, kin ga ba ki da lafiya Please kada kuyi driving a cikin wanna hali ."
Godiya ta yi mata sannan ta fice daga motar ta kashe ta cire key.
_Jidderh_
Gabaɗaya ranar ba ta yi barcin kirki ba saboda halin da ta ga Sir Asadullah a ciki. Kamar kullum bayan ta yi sallar asuba ba ta koma barci ba, ayyukan gidan ta yi kamar yadda ta saba yi. Bayan ta kammala ta yi wa Mahifiyarta sallama ta nufi hanyar titi don yau da ƙafa za ta tafi saboda ba ta da kudin abun hawa. Hakan ya sa ta bar gidan da wuri yau.
Tana tafiya hankalinta na ga wajen uban gidanta, sai jinjina lamarin take yi a zuciyarta.
*SHEKARU BIYU DA SUKA WUCE*
Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe motocin sir Asadullah suka shigo harabar kamfaninsa. Kai tsaye motocin suka nufi parking space, motoci ne guda biyar biyu a gabansa biyu a bayansa sai wata hadaddiyar mota dake tsakiya, ita ce wacce Sir Asadullah ke ciki. Security ne tsaye ƙikam a parking space ɗin. Bude masa murfin bayan motar direbansa ya yi ya fito yana gyara zaman rigar suit ɗin da ke jikinsa.
Ya wuce ciki yayin da amintaccen bodyguard ɗin sa wato Sulaiman ya take masa baya har zuwa hanyar da za ta sada shi da office ɗinsa.
Secretary ɗin sa ta miƙe ta ce.
"Good morning welcome sir, your friend is here to see you ilet him in as per your request anytime your friend are around I should always let them in."
"Okay."
Ya faɗa yayin da ya shiga office dinsa bayan bodyguard ɗinsa Sulaiman ya bude masa ƙofar office ɗin ya shiga. In da ya samu abokinsa Sagir zaune a office ɗin yana jiransa. Bayan sun shiga ne Sulaiman ya tura ƙofar office ɗin. Sir Asadullah ya wuce wajen hanger ya cire jacket ɗin dake jikinsa ya yi hanging ɗin jacket ya bar shert dake jikinsa. Zama ya yi a mazauninsa ya zauna yana kallon Abokin nasa ya ce
"Sagir ya aka yi ne daga ina haka da safe? Okay sorry ba mu gaisa ba ko?"
Ya yi maganar yana murmushi , shi ma Sagir ɗin murmushi ya yi tare da cewa.
"Ban sani ba."
_Fatima Zahrah_
Fitowar ta kenan daga cikin ɗakinta tana sanye da hijabi hannunta rike da waya ta kara a kunne tana cewa.
"Okay ga ni nan fitowa ba bari na zo na shigo da ke."
Ko da ta ƙaraso falon gidan gaba ɗaya ilahirin jama'ar gidan suna falo, sai dai kowa ya yi shiri kamar ruwa ya ci su.
Hajiya Dada ce ta kalli Fatima Zahrah ta ce.
"Ina za ki je hak cikin ranar nan?"
Mumrmushi ta yi tare da cewa.
"Kakus kin manta na faɗa maki cewa tun da muka shiga s.s ce ɗin nan an kawo sabuwar student tana so na?"
Kai Dada ta jinjina alamar gamsuwa sannan ta ce.
" Eh na tuna har kika ce A'isha sunan ta ko?"
"Yauwa to ita ce ta ce na yi mata kwatancen gidanmu ta zo tana waje."
Bayan kamar mintinan bakwai suka shigo rike da hannun juna murmushi bakinsu dauke da sallama.
A'isha ta durkusa ta gaida jama'ar gidan suka amsa gabaɗaya sakamakon tsofaffin gidan na falon.
Har Fatima Zahrah ta ja hannunta suka wuce cikin part ɗin su.
Suna zuwa falon A'isha ta kalle ta tare da cewa.
"Zahrah duk wadannan nan ahalin gidan nan ne?"
"Eh me kika gani?"
"Kun yi yawa na gani."
Zahrah ta yi murmushi ta ce .
Shi Wannan tsohon da kika gani wanda yake sanye da medical glass yana karanta jarida , shi ne Kakanmu wato Alhaji Muhammad Tafarki kenan, amma muna kiransa da Papa. Sai matarsa wacce ke zaune a gefensa wato Hajiya Jummai muna kiranta da Dada. Ƴaƴa guda hudu suka haifa cikinsu har da Abbi na. Babban ɗan su shi ne Alhaji Abubakar Tafarki, muna kiransa da Abba nan gidan yake zaune tare da matarsa Hajiya Maimuna muna kiranta da Umma. Suna da yara uku Yaya Hilal da Yaa Aminu sai Aunty Maryam. Bayan Abba sai ƙanin Abba wato Alhaji Adam Tafarki muna kiransa da Dady, shi ma nan yake zaune tare da matarsa Hajiya Amina muna kiranta da Mummy suna da yara biyu mace da namiji Yaa Mansur sai Aunty Nadiya. Daga Dady sai mahaifina wato Alhaji Salis Tafarki muna kiransa da Abbi sai matarsa Hajiya Zainab muna kiranta da Ummi ina da yayyu maza biyu wato Yaa Mahmud da Yaa Sadik sai ni auta. Daga Abbina sai autarsu wato Hajiya Laila muna kiranta da Aunty aurenta ya mutu nan take zaune da yaranta mata biyu wato Aunty Nabila da Aunty Kausar."
"Ma sha Allah shi ya sa na ga kuna da yawa."
Ai idan kin kira Babban gida ne, don Papa ya ce ba wanda zai tashi ya koma wani gida cikin ƴaƴansu, kowa ya zauna a family house, sai dai Aunty dake mace ce ta yi aure a wani gidan, Kafin auren ya mutu ta dawo ya yaranta."
"To me ya saka Papa ya hana sosai tashi sai dai su zauna family house?"
"Ba jituwa ne a tsakanin alhakin namu, tamkar maƙiyan juna haka muke."
"Ta yi maganar cikin takaici."
Ganin ranta ya ɓaci ya sa A'isha kawar da zancen, don da alama abun na ƙona mata zuciya.
Fatima Zahrah ta tashi ta je ta kawo wa A'isha ruwa da lemu. Daga nan suka fara firan school ka asancewar suna shekaran ƙarshe a a secondry school, suna shirin zana waec da neco.
_Asadullah_
Kwance yake yana saman tangamemen gadonsa yana barci, da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana. Kiran wayarsa ce ta farkar da shi daga barcin da yake yi. My Mom shi ne sunan da ya bayyana a kan fuskar wayarsa.
Cikin Muryar wanda ke barci ya ce
"Mom."
"Wai har yanzu barci kake yi ne, bayan na fada maka yau za'a kawo maka matar da za ka aura ko ka mance?"
"Mom don Allah ki daina wahalar da kanka wajen nema mani matar aure, shi aure lokaci ne da shi idan lokacin ya zo zan yi."
"Ba na son gardama, ga ta nan tana jiranka ka shirya ka fito."
Ba ta jira cewarsa ba ta katse kiran wayar .
"Oh Mom ke baki gajiya kin kawo mani ƴan mata sama da sau biyar na ce ba su yi mani ba, amma ba ki gaji da aikin nemo matan ba. Wannan ma haka za ta koma don ba wata ƴa mace a gabana."
Tashi ya yi ya shiga bathroom ya sakarwa kansa 🚿 shower kusan mintuna talatin yana wanka, fitowa ya yi sanye da white bathrobe a jikinsa sai ƙamshin turaren wanka da sabulunsa yake yi. Hand dryer ya sa busar da gashin kansa.
Man shafawarsa mai tsada ya shafa a jikinsa. Ya shirya cikin ƙananan kaya riga J.C na kamfanin ƙwallon ƙafan Manchester united. Sai baƙin wando 3quater da ya sanya. Ya fesa turarensa mai daɗin ƙamshi da tsada. Tsadadden agogonsa na kamfanin GUCCI ya ɗaura a tsinysiyar hannunsa. Sai takalmi shi ma na kamfanin GUCCI ya saka a ƙafarsa.
Wayoyi guda biyu ya ɗauka ya fice daga ɗakin.
Downstairs ya nufa inda ƙamshin turarensa ya riga shi isa gare su.
Suna zaune a main falon gidan. Alhaji Ahmad da matansa biyu Hajiya Hajiya Zubaida da Hajiya Zulaihat suna zaune samun kujera. Yayin da Kamal da Fauziyya da Suhaila na ke zaune a ƙasan carpert. Can gefe kuwa budurwar da aka kawo masa ya gani ko ta yi masa ne.
Tunda budurwar ta ji ƙamshin turarensa ta juya zuwa in da ƙamshim ke fitowa . Idani ta zubawa Asadullah tana ganin tsantsar kyau da Allah ya masa.
Kallo ɗaya za ki masa kin san ya haɗa jinsi da Fulani. Dogo fari ne yana da kayan siffa da nagarta kyakkyawa ne yana da zagayayyen fuska mai ɗauke da manyan idanu ƙwayar cikin idanun ba baki ba ne Ash color ne ruwan toka kamar dai idanun mage.hancinsa dogo wanda ya dace da fuksar sai ƙaramin bakinsa wanda ya yi kasance pink color.
'Wow'
Ta furta tana kallonsa wanda shi ko kollonta bai yi ba idanunsa na kan Mom da take masa kallon sai yanzu ka ga damar fitowa.
Murmushi ya sakarwa Mom tare da mata alamar ta yi haƙuri.
Bayan ya ƙaraso ne ya ya kalli Mahaifinsa tare da cewa.
"Barka da safiya Dad."
"Barka dai Son ka fito, ya aiki?'
"Alhamdulillah."
Kallon Mom ya yi tare da cewa.
"Barka da safiya my Mom."
"Barka my son ya kake?"
"Alhamdulillah."
Kallon Hajiya Zulaihat ya ce.
"Barka da safiya Aunty."
"Barkanka."
Ta fada a takaice. Taɓe baki Mom ta yi tare da kau da mai daga kallon kishiyar ta ta.
"Barka da safiya Babban Yaya.?"
Cewar Kamal yana murmushi, shima mumrmushin ya mayar masa da martanin tare da cewa ƙanina ya kake?"
Fauziyya ta ce.
"Morning big bros."
"Morning my dear ya kike?"
"Am fine."
Suhaila dake maƙale jikin Hajiya Zulaihat ta kalle shi ta ce.
"Ina kwana Yaya."
"Ƙanwata ya kike?"
"Lafiya lau."
"Ma sha Allah."
Mom ta yi gyaran murya ya kalle ta sai ta yi masa nuni da budurwar da aka kawo masa.
Bai kalle ta ba ya ce.
"Ita ma wannan kamar sauran dai a sallame ta kawai, idan na tashi zan nema da kaina ."
Ɓata fuska Mom ta yi tana kallonsa. Kamal ya ce .
"Babban Yaya wannan fa tafi sauran wadanda aka kawo maka a baya. Ba ka kalle ta ba ne ta hadu."
Suhailat dake jikin Hajiya Zulaihat ta ce
"Yaya kam wannan kyakkya..."
Hajiya Zulaihat ta kai mata duka a baki, cikin ɓacin rai ta ce
"Ina ruwanki ban fada maki ki daina shiga sabgar mutanen nan ba, Ina ruwanki?"
Dad ne ya kalle ta yace.
"Haba mana Zulaihat me ya sa kike haka, ko da ba kece kika haifi Asadullah ai ɗan ki ne, tunda ɗana ne, kamar yadda Suhaila take ƴata, ki daina raba Mani kan yara ba na so."
Ba ta ce komai ba ta ja hannun Suhailat suka wuce cikin.
Asadullah ya ce.
"Na rasa me na yi wa Aunty."
"Kada ka damu wani shawara ka yanke akan yarinyar nan, tana da tarbiyya ƴar ƙawata ce."
Shiru ya yi yana kallon budurwar da ta sunkuyar da kai kafin ta ɗago ta kalle shi suka haɗa idanu.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page0️⃣3️⃣
Shiru ya yi yana kallon budurwar da ta sunkuyar da kai kafin ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido.
Ɗauke kansa ya yi daga kallonta yayin da ita kuma sai kallonsa take yi. Yamutse fuska ya yi tare da kallon Mom ya ce.
"Mom ba ta da wani banbanci da sauran matan da kika kawo mun fa, kuma duk na ce ba su yi ba kika hakura wannan karon ma ina so ki hakura Mom zan nemo mace da nake gani ta dace da rayuwata."
"Son wannan karon fa ba zan saurara maka ba, don haka ko me za ka ce sai ka auri Fadeela."
Kallon Dad ya yi zai yi magana Dad ya ce.
"Ba ruwana tsakanin ku da Mom ɗin ka ce, duk abinda ta fada ya zauna, idan aka biye maka a tuzuru za ka yi ta zama. Shekarunka talatin amma a ce ba ka da budurwa, sai ka ce wacce aljani ta aura?"
Bai ce komai ba ya nufi upstair a abin sa, don ya lura yau kam Mom ta gama da shi ba za ta saurare shi ba .
Ita kam Fadeela duk da ta lura ko kallon arziki bai yi mata ba, kuma da alama baya son ta amma hakan bai son ta amma hakan bai sa ta ji za ta iya haƙura da shi ba.
Mom ta kalle ta tare da cewa.
"Kada fa wannan ya dame ki, ki kwantar da hankulinki ki faɗa wa Mamanki ina na nan zuwa za mu tsara komai."
Cike da farin ciki ta yi godiya ta fice daga gidan.
"Oh Allah zamani ne ya kawo mu da mata ke tallan kansu a wajen namiji haka, ni kam Mom Wallahi ba'ayi namijin da zan je tallan kaina har gidansu ba. Ko da ya fi Yaa Asad kyawu da kuɗi kuwa."
Cewar Fauziyya tana tashi wajen. Kamal ya bi ta da kallo tare da cewa.
"To ke meye naki a ciki, da ba don yayanki ba ne zan iya cewa kishi kike yi yi. "
"Yaa Kamal kenan."
Ta fada tana barin wajen.
_Fatima Zahrah_
Gajiya ta yi da zaman ɗakin nata, don haka sai ta yanke shawarar zuwa part ɗin Kakanninta. Don idan kewar ta ishe ta an nan take zuwa ta ɗebe kewa.
Ko da ta ido main falo Aunty Laila ce da ƴaƴanta, Kausar da Nabeela. Tun kafin da ta ƙara so ta ji Muryar Nabeela na cewa.
"Wallahi ba zan yarda ba sai dai ita ta hakura ta bar mani Yaa Hilal ɗin don ba zan iya haƙura da sonsa ba."
Kausar ma ta ce.
"Kamar yadda ni ma ba zan iya haƙura da sonsa ba, ai na girme...."
Sallamar Zahrah ya sa ta yi shiru kuma ba wacce ta amsa sallamar daga uwar