Showing 57001 words to 60000 words out of 154779 words
ya yi sanyi tsananin tausayinta ya kama su .
Sanin haka ya saka na yanke shawarar kawo Adam wajen dangin mahaifina, saboda anan ne kawai nake da tabbacin ko bayan raina ba zai rayuwar da yake yi a can ba, na san zai samu canjin rayuwa in sha Allah."
Sun tausaya mata tare da yi mata addu'a.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Adam na aiki a ƙarƙashin Yayansa in da suke cigaba da kula kamfanin Asadullah.
A wannan lokaci Allah ya yi wa Inna wuro rasuwa a can ƙasar Chadi.
Mutuwar ta daki Adam sosai, don har ya kai ga suma.
Abba, Ahmad, Adam sune suka je ƙasar Chadi a tare.
Kwana biyu suka yi suka bar Adam a can, wanda shi sai da ya yi sati biyu ya dawo Nigeria.
Na'ima na kula da Asadullah ɗanta ya yi kyau gwanin sha'awa.
Duk wanda ya kalli yaron sai ya yi sha'awar ɗaukar sa.
Tun yana watanni bakwai ya fara tafiyarsa ko ina.
Wata rana sun je siyayya yayin da Na'ima ke goye da Asadullahi kasancewar yana barci.
Tana zagayawa tana duba abin da take buƙata Ahmad na tsaye yana jiranta.
Wata budurwar ta ƙaraso wajen yana kallonsa tana murmushi ga hawaye dake tsiyaya a fuskar ta.
Kallo ɗaya ya yi mata ya gane ta ƙawar Na'ima ce ta school, yakan gan su lokuta da yawa a tare idan ya ya je ɗaukar Na'ima.
Kallonta yake yi har ta karaso wajen da yake tsaye ta durkusa a gabansa tana kuka.,
Sautin kukan ne ya janyo hankalin Na'ima ta tsaya daga nesa tana kallonsu.
"Don Allah Yayan Na'ima ka taimake ni wallahi son ka ya yi wa zuciyata illah. Tun da kake kawo ƙanwarka na kamu da mahaukacin soyayyarka. A yanzu na kasa auren kowa addu'a ta ita ce Allah ya haɗa ni da kai, ga shi ban san gidan Na'ima ba ballantana na bincike ta ko za ta taimake ni. Na yi jinyar zuciyata akan sonka ko ba za ka so ni ba ka aure ni zan kasance ne mai yi maka hidima.
Tana juyawa ta ga Na'ima ta mike da sauri ta rike ƙafarta tana mata magiya . Ganin yadda take kuka akan son da take yi wa Ahmad ya sa ta yi kuka ita ma ta rungume ta.
"Kin yi Mani alkawarin za ki taimaka Mani na aure shi?"
Kai kawai ta gyada mata tare da share mata hawaye.
"Wallahi tun da yake zuwa daularki da kawo ki na tamabaye ki kika ce Yayanki ne nake neman hanyar da zan sanar da ke. Ranar da muka bar makarantar ko da na fito ban hanku ba can ina nesa na hangi tafiyarku na yi kuka, amma ban fasa addu'a ba sai ga shi yau Allah ya amsa Mani."
"Ki yi shiru zan baki adireshin gidana za mu tattauna kin ga yanzu ana Kallon mu ne."
"Da gaske zai sure ni?"
"In sha Allah zai aure ki. "
"Kin yi aure ne ba ganki da goyo?"
"Eh yarona ne sunansa Asadullahi."
Addu'a ta yi mata tare da mata godiya bayan ta bata adireshin gidan nata ta tafi.
Bayan tafiyarta ne Ahmad ya ce .
"Ban san baki da hankali ba sai yau, anya kina so na kwai tun da baku kishi na?"
Murmushi kawai ta yi aka ɗaukar masu kaya suka biya aka loda masa a bayan motar.
A cikin mota ba wsnds ya iya magana a cikinsu har suka karasa gidan, nan ma sa ma'iaktan gidan ya yi suka shiga da kayan. Ko kallonta bai yi ba ya shige don ta ɓata masa rai.
Zubaida kuwa komawa gida ta yi ba tare da ta siye komai ba, zuciyarta fara tas. Don ta san tun da Na'ima ta yi mata alkawarin aurensa ba makawa sai ta cika mata.
Har dare Ahmad bai shiga ɗakin Na'ima ba, bayan ta kwantar da Asadullahi akan gadonsa ta shirya ta nufi ɗakin mijinta.
Yana kwance ya yi rigimgine ta yi sallama, amsa wa ya yi ba tare da ya kalle ta ba.
Ta karasa ta zauna bakin gadon.
"Yaya Barka da dare."
"Barka."
Ya amsa a gajarce .
"Fushi kake da ni?"
Shiru ba amsa mata ba ta yi magana sau biyar kafin ya ce.
"Anya kuwa Na'ima kina so na?"
"Eh mana ko ka manta cewa ba haɗa mu aka yi ba mu muka hada kanmu kafin iyayenmu suka fahimci soyayya muke?"
"Idan har kina so na dole ki yi kishi na."
"Ina kishinka sosai saboda sai da so ake kishi, sai dai ban taɓa sakawa a raina cewa ni kadai zan rayu da kai ba, domin kai mijin mace huɗu ne, idan na yi jayayya da hakan tamkar ba bijire wa dokokin Allah ne. Tana matukar ƙaunarka kuma na tabbatar da ta san kai nake aure ba za ta roki Wannan alfarma a wajena ba. Ta ɗauka ciki ɗaya muka fito. Don Allah ka aure ta."
Tashi zaune ya yi yana Kallon ta fuskarsa dauke da zallar takaici da mamaki.
*Ba na da lafiya ina barar addu'arku my fans*😢
*Maman Ihsan ce*✍️
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
*Maman Ihsan ce*✍️
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page2️⃣9️⃣
Tashi zaune ya yi yana kallon ta fuskarsa dauke da takaici da zallar mamaki.
Haka ta dinga roƙonsa da magiya akan ya amince da wannan aure. Wanda ƙarshe ma fada ya so ya zame masu.
Washegari bayan ya fita zuwa office da rana sai ga Zubaida ta zo. Da fara'a Na'ima t karɓe ta hannu bibbiyu, bayan sun gaisa ta kawo mata ruwa da abinci, ta kasa ci cikin zaƙuwa ta ce.
"Ya amince da ni kuwa?"
Murmushin karfin hali ta yi tare da cewa.
"Ki sha ko ruwa mana sai mu yi magana ."
Ta dauki kofin da ta zuba mata ruwa ta kai baki ta fara sha, idanunta suka sauka akan babba frame na hoton Ahmad da Na'ima suna rungume-rungume da yarinsu Asadullahi. Kallo ɗaya za ka masu gane cewa. Ma'aurata ne .
Ruwan da take sha ya sarƙe mata a wuya ta fara tari cikin firgici. Na'ima sai bubbuga bayanta take yi tana jera mata sannu
Sai da ta tsagaita sannan ta ce.
"Dama mijinki ne shi ba Yayanki ba?"
"Yayana ne kuma mijina ne."
"Na shiga uku."
"Zubaida ta fada tana ɗora hannu akai."
"Karki damu hakan ba zai hana ya aure ki ba, fatana da kyakkyawar zuciya kike son shigowa cikin rayuwarmu ba don wata manufa ba, idan Allah ya ƙaddara ke matarsa ce ban isa na yi jayayya da hukuncin Allah ba."
Nan Zubaida ta dinga mata rantsuwa ba komai tsakanin ta Allah take sonsa.
Ta yi mata alkawarin zai zo gidan su in sha Allah, kada ta sake zuwa nan gidan "
Sallama ta yi mata suka fita ta raka ta har bakin gate.
Tsawon kwanaki uku tana ta kokarin ta shawo kan Ahmad ya amince da zancen aurensa da Zubaida. Har fada suka yi magana ta yi nisa Ahmad ya kai karar ta wajen iyayensu.
Faɗa sosai Mahaifiyarta ta yi masu, sannan ta nuna mata kuskure da take kokarin yi. Amma ta kasa fahimta karshe sai ta saka kuka wai ta yi alkawari kuma yarinyar ba ta da matsala za su zauna lafiya, za ta samu abokiyar fira .
Ganin haka ya sa Abba ya ce a barta Allah ya tabbatar da alkahiri.
Ba yadda Ahmad ya iya haka ya fara zuwa zance wajen Zubaida. Duk da ba wani sakar mata fuska ya yi ba.
Aka saka ranar bikinsu rana ɗaya da na Adam ƙaninsa. Don shi ma ya samu wacce yake so.
Kwanci tashi ba wuya Lokacin da aka saka na bikin ya zo. Wata ranar juma'a aka daura auren Ahmad da Zubaida sannan aka daura na Adam da Hauwa'u.
Amare suka tare a gidajensu. Yayin da Zubaida suke zaune gida ɗaya da uwargidanta Na'ima. Sai Hauwa'u Amaryar Adam kuma suna zaune a gidan da Abba ya ba shi. Babu nisa a tsakanin gidajen na su.
Ranar da aka kawo Amarya ranar Ahmad bai dawo ba sai ƙarfe goma na dare. Amarya na zaune a ɗakinta Na'ima na zaune a falo. Tana jiran dawowarsa.
Tana ganinsa ta yi masa sannu da zuwa. Ya amsa mata fuskarsa babu walwala sosai.
Cikin tsokana ta fara magana.
"Ango ka sha ƙamshi, ina kazar amarcin da ka siyo?"
"Ni na fada maki na siyo kaza?"
"Na san kowane ango abun da yake tanada kenan."
"To ban da wannan angon."
Kai tsaye ya nufi ɗakinsa ta biahi cikin sanyin jiki.
Kwanciya ya yi ba tare da ya rage kayan jikinsa ba.
"Yaya."
Ya ji muryarsa ta kira shi, a hankali ya bude idanunsa da ya lumshe su ya bude akan kyakkyawar fuskarta.
"Ka sani fa yanzu ne lokacin da za ka fara gwada adalci a tsakanin matayenka, aure an riga an daura ba abinda ya rage illa mu yi fatan zaman lafiya a tsakanin mu da kuma fatan ka zama adalin miji a tsakaninmu."
Haka ta dinga lallaɓa shi da maganganu masu dadi da kwantar da hankali har ya tashi. Da kanta ta taya shi rage kayan jinkinsa. Ya shiga don yin wanka .
Da sauri ta fice ta nufi kitchen, kaza guda ɗaya ta fito daga cikin fridge, ta wanke ta ta shafa magi da kayan ƙamshi a jikin kazar, sai da ta tabbatar ko ina ya ji sannan ta bude Ovon ta kunna dan gasa kazar.
Ko da ta koma ya fito daga wanka ƙaramin towel ta ta ɗauka ta taya shi goge jiki.
Ta bashi kayan barci don ya saka. Ya muna mata cewa jallabiya zai saka.
Fita ta yi zuwa lokacin kazar ta gasu sai ƙamshi take yi, leda mai kyau da tsafta ta saka kazar a ciki, sannan ta bude fridge da suke ajiye kayan sha, ta ciri fresh milk mai sanyi da hollandia youghurt ta saka a wata ledar ta fito daga kitchen ɗin.
Yana tsaye ta shigo ɗakin.
"Na ga ba ka shigo da komai ba ga shi mai yiwuwa yinwa take ji na san za ta ci."
Kallonta kawai yake yi har Lokacin bai daina mamakin Na'ima ba.
Ba yadda ya iya haka ya karɓa ta raka shi har kofar part ɗin Zubaida. Sau da ta ga ya shiga bedroom ɗin ta sannan ta bar wajen. Ɗakinta ta koma ta tura ƙofa ta shiga, jingina bayanta ta yi da bayan ƙofar tare da fashewa da kuka. Ba ta taɓa tunanin za ta ji haka a zuciyarta ba.
Zuciyarta na mata zafi sai kuka take mai tsuma zuciyar mai saurare.
Ganin kukan ba mafita ba ne ya saka ta tashi ta nufi toilet ta dauro alwala ta zo ta fara gabatar da sallolin nafila. Tare da addu'ar Allah ya sanyaya mata zuciya ya zaunar da su lafiya cikin aminci.
Daga nan ta dauki alƙu'ani mai girma tana karantawa. Soi karfe biyu da rabi na dare ta kwanta.
Ɓangaren Ahmad kuwa yana shiga dakin sallama ya yi mata. Tana zaune bakin gado, tana ganinsa ta saki ajiyar zuciya.
Amsa sallamar ta yi tare da cewa.
"Sannu da zuwa makararren ango."
"Ayi Mani afuwa."
Ya faɗa tare da ajiye ladar kazar ya zauna a bakin gadon.
Kallonta ya yi tana sakar masa murmushi, ido ya zuba mata don bai san haka da kyau ba, don bai ma taɓa tsayawa ya yi mata kallon arziki ba.
"Na san a gajiya kike bisimillah ki samu abinda kika ci."
Taso wa ta yi ta nufi kitchen ta dauko faranti da kofuna ta ajiye.
Duk yadda ta so ya ci abincin ba ci ba, ko dandana kazar ya kasa yi, da ya ga kamar ta damu ne ya saka ya ɗan sha fresh milk kaɗan.
Ita ma ba ta wani ci ba ta bar shi. Ta kwashe sauran ta kai kitchen ɗin ta.
Kwanciya ta yi bayan ta yi wanka ta sauya kaya.
Shi kam ya dade a zaune kafin ya tashi ya zo ya yi sallar nafila ya kwanta.
Haka zamansu ya kasance har ya gama kwanakin da zai yi ba abinda ya shiga tsakaninsu har ya koma ɗakin Na'ima.
Da Na'ima ta fahimci haka sai da ta bata rai kafin Ahmad ya kusanci Zubaida.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Allah ya azurta Zubaida da samun ciki. Suna zaman lafiya sosai komai tare suke yi. Hatta girki tare suke yi. Unguwa ma tare suke zuwa ko daga ɓangaren Na'ima ko Zubaida.
Laulayin ta Zubaida ke yi kusan tare suke renon cikin ita da Na'ima, Asadullah na zuwa makaranta.
Lokacin da Zubaida ta haifi yarinya namiji lokacin Asadullah na da shekaru biyar.
Ranar suna yaro ya ci suna Kamal ansha Shagali sosai, kusan ma Na'ima ce ta dauki nauyin kayan sawarsu.
Kowane kaya tare suka saka iri ɗaya hatta sarƙa da ɗan kunne.
Haka suka cigaba da zama kusan raunon yaron Na'ima ke yi, wacce Asadullahi ke kiranta da Ammi, ita kuma Zubaida yana kiranta da Mom.
Bayan shekaru biyu aka yaye Kamal wanda a watan da aka yaye shi a watan Zubaida ta sake samun ciki.
Sai dai har wannan lokaci Na'ima ba ta samu ciki ba, tun bayan haihuwar Asadullah ba ta samu ciki ba. Sai dai a watan da aka yi auren Zubaida aka kawo ta gidan Na'ima ta riga ta samun ciki sai dai nan da nan ya ɓare. Daga nan ta samu sau biyu yana fita, har yau Allah bai sake ba ta ba.
Ɓangaren Adam kuwa shi ma matarsa ta hafi ɗa namiji yaron ya ci suna Nasir. Tsakanin Nasir da Kamal watanni uku ne tsakaninsu.
Kuma suna zunuban da juna kasancewar mazajensu wa da ƙani ne, sai sai a wajen Na'ima wuce haka saboda Adam din shi ma Yaya ne a wajenta tun da ɗan wan mahaifinta ne.
Zubaida ma cikin ya zo mata da laulayi ne haka Na'ima ke ɗawainiya da ita har Allah ya sa sauke ta lafiya ta haifi ƴa mace.
Ranar suna yarinya ta ci suna Fauziyya, anyi Shagali sosai. An ci an sha kowa sai farin ciki. Na'ima ma a wannan sunan ta yi rawar gani. Kuma yarinyar ta shiga ranta sosai don tana son ƴa mace.
Ammi da Abba ma ba'a barsu a baya ba sun bada kyaututtuka wa mai jego da jaririyar.
Ammi ma da ta tayar da hankali lokacin da za'ayi auren ganin ƴarta Na'ima ba ta taɓa ƙorafin zaman nasu ba hakan ya tabbatar mata da zaman jin dadi suke da juna.
Matar Adam ma ta sake haihuwa in da ta haifi ƴa mace mai suna Abida.
Asadullah ya yi wayau sosai don ko Kamal ya yi wayau sosai. Tun da ya ga Asad na kiran mahaifiyarsa da Ammi shima haka yake kiran Na'ima. Sai Zubaida wacce suke kira da Mom.
Matar Adam kuwa Hauwa'u suna kiranta da Mamy kamar yadda suka ji yaransu na kiransu.
Zama mai daɗi suke da ba tashin hankali a ciki. Matar Uncle Adam ma ta sake haihuwa ranar suka yarinya ta ci suna Maryam. Yaransu uku Nasir, Abida, da Maryam.
Na'ima haihuwa dama tun da ta haifi Asadullah ba ta sake yi ba, sai bari. Sun yi yawon asibiti shiru. Daga karshe Dad sunan da yaran ke kiransa kenan ya ce su tafi ƙasar waje don a duba mahaifarta. Ita kam ta ce Allah ne bai kawo ba, tun da Nam kasar Nigeriya sun ce lafiya lau ba za ta je ko ina ba. Dole ya barta don har ga Allah ya so a ce sun tarar zuri'a shi da Ita.
Mom ta nuna ita ma ya kai ta tun da ita ma haihuwar daga biyu shiru ya ce Allah ne bai kawo ba. Ta ji ba dad'i amma ta share.
Lokacin da Asadullah ya kammala secondry school Dad ya kai shi ƙasar waje karatun digiri ɗinsa.
Lokacin da Kamal ya kammala karatun secondry school ɗin Ne Mom ta yi tunanin shi ma zai kai shi ƙasar waje ne, sai ta ji yana zancen zai kai shi A.B.U Zaria Mom ta nemi da ya fita da shi shima ko da ƙasar Turkey ne ya kai shi mana, amma Dad ya ki amincewa.
A nan kasar Nigeriya suka yi karantun su yayin da Asadullah ke can U.S yana karantunsa akan ilimin kasuwanci.
Bayan tafiyarsa da kwana biyu Ammi ta shirya don zuwa gidan wata ƙawarta wacce ta samu accident. Duk da cewa a ƙauye take sai sai ba wani nisa duk da sai an bar gari.
Tun da ta shirya don zuwa dubiya ƙauyaen jikinta ya yi matukar sanyi. Ji take kamar kada ta yi tafiyar.
Ɓangaren Dad ma haka don sai da ya ce ta fasa tafiyar nan, ta ce ba damuwa ko ba yau ba dole za ta tafi, don haka ta fita yana biye da ita a baya. Don ya bari sai ta tafi sannan ya wuce kamfani.
Ɗakin Mom ta shiga ta same ta kwance ba ta da lafiya.
"Ya kamata ki je Asibiti Mom ɗin yara."
"Eh yanzu zan lallaɓa na yi wanka sai mu tafi asibitin, Alhaji idan zai tafi office sai ya sauke ni."
Sallama ta yi mata tare da addu'ar Allah ya ƙara Lafiya, ita ma addu'ar sauka lafiya ta yi mata suka ta fice.
Har wajen Dad ya raka ta in da Direba ya ja motar suka tafi. Suna ɗagawa juna hannu ita da Dad.
Daƙyar ya ja ƙafarsa ya koma cikin gidan cikin sanyin jiki wanda ya kasa gane me yake ji ne.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page3️⃣0️⃣
Daƙyar ya ja ƙafarsa ya koma cikin gidan cikin sanyin jiki wanda ya kasa gane me yake ji ne.
Bayan kamar awanni biyu da tafiyarta har lokacin Dad bai fita ba, Mom kam har ta je ta ga likita ta dawo.
Ganin Dad a gidan ne ya saka ta yi mamaki. Wayar Dad ce aka kira, jin ringing ɗin wayar ya saka shi faduwar gaba, don ya yi ta kiran wayar Ammi ba'a ɗaga ba. Cikin sanyin jiki ya ɗaga tare da yin sallama.
Muryar da ya Abba ya ji ya yana tamabayarsa yana ina, bayan ya sanar da shi yana gida ne Abban ya ce ya zo ya same shi a wani wajen hanyar fita garin.
Fita ya yi da sauri gabansa na faɗuwa ya kira direba ya ja su.
Tun daga nesa suka ga jama'a an taru a gefen hanya, ga jami'an tsaro a wajen.
Suna parking ya fito daga motar ya karasa wajen.
Mota