Showing 54001 words to 57000 words out of 154779 words

Chapter 19 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6297

a yau ne saboda Sir Asadullah, ko ka mance a halin da muka kai ta asibiti za'ayi mata aiki ba ka da kuɗi, na yi yawo ban samu ba, ka yi buga-buga ba ka samu ba na bika kasuwa ba ja da shi, ka nemi taimakon ubannin gidanka ba su taimake ka ba, sai da ja je kamfanin Asadullah ya taimaka mana da kuɗi wanda lokacin matarka tana gaɓar rayuwa da mutuwa . Don Allah ka taimaka masa ko don taimakawa da ya yi wa iayakinka duk d bai san waye ba "

Ajiyar zuciya Isah ya sauke tare da cewa.

"Kin saka jikina yin sanyi. Bari na shiga na fito sai mu san yadda zaj ɓullo wa lamarin."

Murmushi ta yi tare da jinjina masa kai.



*Waye Sir Asadullah?*

Asadullah Ahmad Abubakar shine cikakken sunansa. Asalinsu mutanen jihar Yola ne a garin Adamawa, Asalinsu Fulani ne, makiyaya.

Ahmad wato Mahaifin Asadullahi Ya taso shi kaɗai ne a wajen mahaifinsa Abubakar. Abubakar yana da ƙani mai suna Sale Ko da ya taso bai san Mahaifiyarsa ba. Don ta rasu yana da shekaru biyar a duniya. Sale lokacin da matar Yayarsa ta rasu bai yi aure ba saurayi ne shi.

Mahaifinsa ke kula da shi su biyu ne suke rayuwa a cikin wannan gidan. Sai dai ƙanin mahaifinsa wato Sale shi yake masa komai na larura da ya shafi kuɗi. Saboda yana da rufin asiri da ƙoƙarin neman na kai. Ganin Yayan nasa ya daina fita ko ina saboda ɗawainiyar yaro ne ya saka yake masu komai na ci da sha har da sutura. Kullun idan
Zai dawo sai ya siya masa ƙosai da biredi.

Ana cikin wannan lokacin ne Saleh y yi aure, in da ya auro matarsa ƙyakyatawar Bafulatana mai suna Joɗa nan gidansa dake jikin gidan Yayansa ya ajiye ta .

Shawara ya yanke tun da shi ya yi aure ga Yayansa tin mutuwar matarsa ya kasa ƙara aure.

A wata ranar Juma'a ne y shiga gidan Yayansa bakinsa ɗauke da sallama. Hannunsa ɗauke da bakin leda.

"Assalamu alaikum"

Mallam Abubakar ya amsa yana sakin murmushi ya ce.

"Saleh har ka dawo?"

"Eh na dawo."

Ya karaso ciki yana mikawa Ahmad ledar biredi da tsire da ya siyo masa . Karba ya yi cike da murna yana nuna wa mahaifinsa.

Bayan sun gaisa ne Abubakar ke tamabaye shi kasuwa. Ya amsa masa da Alhamdulillah.

Shiru ne ya biyo baya kafin Sale ya yi magana ya ce.

"Yaya na ce me zai hana ka kawo Ahmad Gidana ya zauna, tun da ka gajara ƙara aure."

Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa

"Ban hana ka ɗaukar Ahmad ba sobida kai ma uba ne a wajensa kamar yadda nake uba. Abu ɗaya ya yi mu da ni da kai uwa ɗaya uba ɗaya, to akan ne zan maka iko da shi.

Cikin farin ciki duk suka yi sallama tare da cewa Gobe zai ya ɗauke shi.


Washegari kuwa bayan ya sanar wa da Matarsa Joɗa ta yi farin ciki, don tana son Ahmad sosai.

Da safe kafin ya fita ya shiga gidan Yayansa ya dauko Ahmad da Kayansa.

Kafin ya yi tafiyarsa don yana zuwa Lagos kai shanu ne.

Joɗa tana matukar don Ahmad sosai ba wanda zai ce ba ita ta haife shi ba. Duk da ba kowa yake kai yara ba

Koda Joɗa ta sanar wa mijinta shawarar kai Ahmad makarantar boko. Bai yanke hukunci ba sai da ya sanarwa Mahaifin Ahmad, ya nuna duk masa duk hukuncin da ya yanke ka akan Ahmad daidai ne domin ɗan sa ne shi ma .


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page2️⃣7️⃣

Ko da Koda ta sanar wa mijinta shawarar kai kai Ahmad makarantar boko, bai yanke hukunci ba sai da ya sanarwa Mahaifin Ahmad, ya nuna masa duk hukuncin da ya yanke akan Ahmad daidai ne, domin ɗansa ne shi ma. Haka aka kammala masa komai ya fara karatu. Komai Sale ne ke yi masa. Don dama ya fi mahaifin Ahmad rufin asiri.


A daidai wannan lokacin Joɗa ta fara laulayin ciki. Kuma cikin na wahalar da ita. Abubuwa suka yi wa Sale yawa, ya ɗan dakatar da wasu tafiye-tafiye da zai yi.

Abubakar ne ya tashi da zazzaɓi mai zafi sosai hankalin Sale ya tashi sosai. Ya ɗauke shi zuwa asibiti. Shi ya dinga jinyarsa. Ahmad ya dinga kuka don ya yi wayau ya san abun da ke faruwa.

Kwanansu biyu a asibiti Allah ya yi masa cikawa. Sale ya sha kuka Sosa don har sai da ya suma, Kasancewa Abubakar kadai ne ɗan uwansa Wanda ya rage masa. Ahmad ma ya sha kuka sosai da sosai don ya san mutuwa ya san mahaifinsa ya tafi kenan, ba uwa ba uba.

Joɗa kuwa Ita ma sai da ta yi rashin lafiya don dama ga laulayin ciki da take yi.

Bayan kwana arba'in suna zaune a tsakar gidan kan tabarma, Sale na shan fura da Joɗa ta dama masa. Ahmad ya yi sallama ya dawo daga makaranta.

Gaishe su ya yi Joɗa ta masa alama da yazo gare ta. A hankali ya taka bayan ya cire Sandals din makarantarsa, kwantar da shi ta yi saman cinyar ta tana shafa kansa. Ganin kamar yana cikin damuwa ta ce.

"Me yake damunka?"

"Yanzu ni ma na zama Maraya ban da mama da Ba..."

Hannu ta sa ta toshe masa baki ta ce.

"Ka da ka sake kiran kanka maraya, domin kai ba Maraya ba ne tun da kana da mu ni ce mahaifiyarka ga kuma mahaifinka."

Ta ƙarasa maganar tana nuna Sale dake kallonsu yana murmushi. Sannan ta ɗora da cewa.

"Nan da watanni kadan zan haifa maka ƙani ko ƙanwa."

Murmushi ya yi har sai da ƙananan haƙoransa suka bayyana.


*Bayan watanni Bakwai*

Wata ranar Litinin Joɗa ta tashi da naƙuda, wata maƙociyarsu ce Saleh ya kira. Dattijuwa ce da taimakon Allah da taimakon ta Joɗa ta haihu.

Ta haifi ƴa mace fara kyakkyawar gaske, son kowa ƙin wanda ya rasa.

Ranar suna aka saka wa yarinya suna Na'ima, murna da farin ciki a wajan su ba'a magana. Ahmad ya na matukar kaunar ƙanwar ta sa sosai. Ko kukanta ya ji ya yi yawa shi ma zai yi kamar zai yi kuka.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka yaye Na'ima. Shakuwa mai karfi ce ta shiga tsakanin Ahmad da Na'ima. Kullum yana ɗauke da ita inda sun rabu sai dai idan makaranta ce zai tafi, nan ma har kuka take yi za ta je. Idan ya tafi ya barta daƙyar take yin shiru sai Joɗa da Sale sun sha aikin rarrashi.

Lokacin da ta cika shekaru uku aka saka ta makaranta ita ma, lokacin Ahmad na ajin karshe a primary school.

Tare suke zuwa kamu na su gwanin sha'awa ba wanda zai ce ba su ne suka haifi Ahmad ba.

Ɗan ƙaramin gidan da Mahaifin Ahmad ya rasu a ciki shi ne kawai mallakinsa, don dama shi ba mai shi ba ne, hakan ya saka Sale yake taimaka masa, har yakarbi Ahmad ya saka shi a makaranta.

Zuwa lokacin kuwa dukiyar Sale sai bunƙasa take yi. Don shanu ne da shi sosai, ga filayen da ya siya ya ajiye a matsayin ƙadarori.

Don ya tashi a gidan da yake ya siye babban gida ya koma, ga ɓangaren kiwo ta bayan gidan, sai dai akwai ƙofa daga cikin gidan da za ta sada ka da filin da ake kiwon.



*Bayan shekaru goma sha biyar*


Wata ƙyakyatawar yarinya ce tsaye a bakin titin a gaban wani makaranta, kallo ɗaya za ka yi wa makarnata ka san cewa makaranta ce ta ƴaƴan masu hannu da shuni. Sanye take da uniform ɗin makarantar riga da wando sai ƙaramin hijabi iya wuyanta.

Wata lokaci-lokaci take kallon agogon hannunta yana ware Idanunta tare da tura baki gaba.

Wata baƙar mota ce ta tsaya a gabanta tura baki ta yi tana kau da kai .

Murmushi ya yi tare da cewa.

"Tuba nake."

Shiga ta yi tare da buga marfin motar da ƙarfi.

"Ai sai ki ɓalla Mani marfin motar."

"Wallahi Yaya Ahmad ka ɓata Mani lokaci ga shi na gaji."

"Sorry ƙanwata ka da ki damu tun da yazu kin kammala zana waec da neco ai sintirin nan ya ƙare ko?"

Banza ya masa kamar ba ta ji me yake cewa ba, don haka ya ce

"Amaryar duk gajiyar ne?"

"Wallahi na gaji ni kam Yaya kana damuna."

"Kin ga ni kam ina cikin farin ciki, don daga yau ki fada ƙirga kwanakin aurenmu."

Jin ta yi shiru ne ya saka shi cewa.

"Na'ima."

"Yaya."

Ita ma ta kira shi. A hankali ta bude Idanunta ta sauke akansa .

"Ina son fa na ci gaba da karatuna kafin na yi aure sai na shiga University."

Dariya ya yi tare da cewa.

"Ai kin san cewa ba za'a bari ba ko?"

"To bayan mun yi aure za ka bar ni ko?"

"Ban sani ba amma sai yadda ta kasance."

A wani katafaren gida motarsa ta tsaya, horn suka danna aka buɗe masu gate.

Shiga suka yi ya yi parking din motar, kusan a tare suka fito daga cikin motar. Hajiya Joɗa na zaune a kan kujera mai zaman mutum uku.

Na'ima na shiga ta yi kira da jakarta ta karasa ta kwanta jikin Joɗa.

"Wash na gaji."

Ahmad ya gaida Joɗa ya shiga ɗakinsa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka tsaida ranar auren Ahmad da Na'ima.

Don saura sati biyu bikin ya rage, Ahmad yana koyarwa a wata makarantar secondry ta Gwamnati ce. Saleh wanda suke kira da Bappa ya siya wa Ahmad gidan da za su zauna. Joɗa wacce suke kira da Inna ta yi wa ƴarta kayan kitchen na gani na faɗa.


Wata ranar Asabar ne aka daura auren Ahmad da Na'ima. In da suka tare da gilashi gidan da Bappa ya siya masa.

Kuma an zuba masu komai a cikin gidan. Duk aikin Bappa ne ya yi wa Ɗan Yayansa.

Kasancewar zuwa lokacin Bappa ya daina kiwo sai dai ya siye kadarori ya tara. Sannan kuma akwai manyan shagunansa da suke kasuwa ana siyar da kayayyaki a ciki.

Zaman lafiya da kwanciyar hankali suke yi a cikin rayuwar aurensu. Tana samun kulawa sosai a wajen mijinta.

Auren ba jimawa Allah ya nufe Na'ima da samun ciki. Sun yi farin ciki sosai da wannan kyautar da Allah ya basu.

Bayan watanni tara ta haifi ɗa namiji santalele kyakkyawan gaske mai kama da mahaifiyarsa. Fari tas kamar yaron larabawa.

Murna a wajen Bappa da Inna ba'a magana, sun samu jika, dama tun bayan haihuwar Na'ima Allah bai sake bata haihuwa ba.

Gida aka dawo da ita tana samun gata da kulawa wajen iyayenta. Ranar suna aka sakawa yaro suna ASADULLAH.

Ranar da suna cika sati biyu ne Bappa ya mallaka wa jikansa wato Asadullah manya-manyan kadarorinsa. Don sai da ya tara su Joɗa Ahmad da Na'ima. Sannan ya mallaka wa Asadullah takardun a ta hannun Na'ima. Takardar farko ta plaza ce da ya siya, ta biyu kuka na wani kamfani ne dake garin Kano. Takarda ta gaba kuma ta wani kamfanin ne dake garin Lagos.

Ya mallaka masa su akan cewa da zaran ya kai shekaru ashirin da biyar za'a mallaka masa a hannunsa. Farin ciki mamaki ne duk suka mamaye Na'ima da Ahmad.

Sai da ya ce Ahmad ya dakatar da koyarwa da yake yi ya koma ya fara juya kadarorin da aka mallaka wa jikansa kafin ya girma a mallaka masa.

Haka suka cigaba da zama a gidan ana kula da ita da kuma yaronta

Ahmad ma ya dawo gidan ya tare wai tare suka san a su zauna shi ma


Wata rana an dukkansu suka shirya ɗin zuwa kasuwa. Bappa, Joɗa, Ahmad da Na'ima.

Bayan sun gama siyayya Joɗa na rungume da jikanta Asadullahi dake cikib towel Bappa na gaba suka ji wata murya daga bayansu ta kira sunan Bappa .

"Sale!"

Dukkansu suka juya har da Na'ima da Ahmad suna kallon wannan mai kiran sunan. Baki duka saki da tsanin mamaki wanda har sai da firgici ya bayyana akan fuskarsu.



*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page2️⃣8️⃣

Dukkansu suka juya har da Na'ima da Ahmad suna kallon wannan mai kiran sunan. Baki suka saki da tsanin mamaki wanda har sai da firgici ya bayyana akan fuskarsu.

"Inna wuro?"

Mamaki ya kama su Na'ima ba na ganin tsohuwar ba sai na ganin saurayin da suke tare da shi mai tsananin kama da Ahmad.

"Dama kina nan?"

Abba ya mata tamabayar cike da mamaki.

"Ina ƙasar Chadi garin dangin mahaifiyata"

Jinjina kai ya yi tare da cewa.

"Ikon Allah"

Kallon Ahmad ta yi wanda ke tsananin kama da saurayin dake bayanta.

"Wannan Amadu ne ko?"

Abba ya yi murnushi tare da cewa.

"Eh shi ne."

Yana kallon Saurayin dake bayanta wanda ya zuba wa Ahmad idanu kamar ya ga sabon halitta.

"Wannan fa wane ne?"

"Ƙanin Ahmadu ne wanda na tafi ina dauke da cikinsa, wanda ni kaina ban san da shigar cikin ba sai bayan mun rabu da mahaifinsa."

"Ikon Allah."

Ya faɗa yana kallon Ahmad ya ce.

"Ahmad wannan matar mahaifinka ce, a baya mata biyu yake da su duk da zaman nata da mahaifinka bai yi nisa zaman watanni uku suka yi, suka rabu lokacin ba za ka wuce shekaru uku ba. Ashe sun rabu tana da ciki. Lallai jini ba ƙarya ba, duk wanda ya kalle ka ta kalle shi ya san tsatso ɗaya kuka fito."

Cikin so da ƙuna Ahmad yake kallon Adam, kafin ya bude masa hannunsa alamar ya zo gare shi.

Shi ma cikin so da ya ji ya shige shi lokaci guda ya ƙara da gare shi suka rungume-rungume juna cikin so da ƙauna.

"Ahmad ya ce Alhamdulillah ashe ina da ɗan uwa ban sani ba."

Murmushi Adam ya yi tare da cewa.

"Ni ma ban sani ba, ko da na girma mahaifiyata ba ta bani labarin mahaifina ba, ko da na yashi na ga mahaifiyata a gidan wani mutum matsayin matarsa, na ɗauka shi ne mahaifina. Sai da na ga ya rabuwa ƴaƴansa dukiyarsa kafin ya mutu ban da ni, da na tamabaye shi kai tsayeya faɗa Mani dukiyar ubansu ne ni ma na je ubana ya bani. Hankalinsa ya matukar tashi na tambaye mahaifiyata amma ba t sanar da ni komai ba. Dai bayan rasuwar mijinta na tashi hankali akan sai na ga ubana take sanar da ni ta yi aure ba ta wuce watanni uku na ta fito saboda ba sa jituwa da uwar gidan ta bukaci saki. Sai bayan ta koma ƙasar Chadi ta fahimci tana da ciki.

Ba ta sanar da dangin mahaifina ba sai da lokacin da aka nuna Mani wariya na gane, sai kwanan nan take faɗa Mani ta ji labarin rasuwar mahaifina, da matarsa wacce ta riga shi rasuwa. A cikin kabarin take faɗa Mani ta bar su da yaro ɗan shekaru uku. Na damu shi ne ta kawo ni gidan mahaifina. Muka tarar wasu ne a ciki suka ce an basu aron gidan su zauna ne, daga nan suka Mana kwatancen gidan da kuke, kafin mu je shi ne muka biya kasuwa ashe da rabon nan za mu haɗu.

Daga nan Abba ya ce su ɗinguma zuwa gida. Su ƙarasa tattaunawa a can.

Haka kuwa aka yi bayan an loda siyayyar da suka yi a mota suka ɗunguma zuwa gida.

Bayan na kai mahaifiyar Adam wato Inna wuro ɗaki, Joɗa ta kai ta nan ta ce ta yi wanka za'a kawo mata abincin.

Ahmad ma ya kai Ɗan uwansa Adam ɗakin da ya zauna lokacin yana saurayi. Ya ce ya yi wanka kafin su ci abinci.


Bayan awanni biyu suka hadu a falon suna tattaunawa, Abba yake sanar da su cewa

"Gidan da wansa mahaifin Ahmad ya rasu ciki shi kadai ne ya bari gadonsa, don dama baya kiwo. Inna wuro dama ta san bai da komai don haka ba ta yi mamaki ba.

Sau ya ɗuara da cewa .

"Ahmad kuma kasancewar na saka shi a makaranta ya yi karatu har matakin digiri shi ya saka ya samu aikin Gwamnati. Amma yanzu dole aikin ya tsaya haka nan, saboda dukiyata da na mallaka da ya kamata a ce Na'ima ce ƴata za ta yi gadon komai na wa , amma kasancewar ta mace ya saka na mallaka komi na wa da sunan ɗanta Asadullah. A mallaka masa dukiyar idan ya mallaki hankalin kansa. Amma yanzu haka mahaifinsa zai cigaba da kula da kamfanonin kafin lokacin da Allah zai raya shi. Namiji ne shi kuma babba a cikin ƴaƴan ku ina fa yaƙinin cewa zai dauki nauyin ku da na ƙannensa.


Kallon Adam ya yi tare da ya.

"Zan baka ɗaya daga cikin gidaje na da kuma mota kamar yadda na bawa Yayanka."

Daga shi har mahaifiyarsa farin ciki suka yi tare da mika godiya gare su.

Kallon Adam ya yi tare da cewa.

"Ka yi karatun boko ko?"

Jinjina kai ya yi tare da cewa.

"Na yi Abba har matakin diploma."

"Alhamdulillah."

Abba ya faɗa yana kallon Ahmad ya ce

"Sai a samu wani gurbin a cikin kamfanin a bashi ya fara aiki."

Jinjina kai ya yi cike da godiya ya ce

"An gama Abba."

Dubansa ya mayar kan Inna wuro ya ce.

"Kin dawo Nigeria da zama kenan ko kin kawo sa ne ki koma?"

"Na kawo sa ne na koma ."

'Umma ta yi saurin cewa.

"Ai da kin zauna a gidansa tun da yanzu an bashi gida, ga mota kuma ga aiki ai ina ganin zamanki a nan zai fi."

Cikin rauni ta fara magana ta ce

"Zama na a can shi zai fi mani, domin kuwa ina son..."


Sai kuma ta kasa ƙarasa wa.

"Kina cikin wata matsala ne?'

Girgiza kai ta yi alamar ba komai.

Kallon Adam take yi alamar saboda shi ta kasa maganar, lura da haka ya saka Abba cewa.

"Ahmad a kai shi wajan Alhaji Usman Isma'il ya zaɓi motar da yake so."

Cikin girmamawa ya amsa tare suka mike suka fice. Abba ya kalli Na'ima ya ce ta karbi yaron hannun Inna wuro ta kwantar da shi tun da tana barci.

Bayan tafiyarsu ne Inna wuro ta goge hawayenta ta ce.

"Sale Ina ɗauke da muguwar cutar jeji a yanzu haka likitoci sun fada mani ba zan wuce Wata uku a raye ba."

Daga Abba har Umma jikinsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login