Showing 63001 words to 66000 words out of 154779 words

Chapter 22 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6279

so sai mun aura maka ita. Idan ba mu isa ba sai ka nuna mana iyakarmu."

A fusace uncle Adam ya ce.

"Ke Zubaida tsaya matsayinki. Ke kin isa ki ce za ki zaɓawa Asad matar da zai aura?"

Mumrmushi ta yi tare da cewa.

"Ga shi ko kana gani a matsayina na uwa a gare shi."

"Ƙarya ne wallahi ai kama da wane ba ta wane."

Dad ya kalli Uncle Adam ya ce.

"Me kake yi haka ne?"

"Ya me nake yi ko me matarka take yi, bayan na shaida maka cewa na bawa Asad auren ƴata, shi ne take shirin tura shi tura shi zance wajen ƴar ƙawarta ko ƙanwarta ce oho."

"Ni ce dau uwarsa Ni nake da ikon zaɓa masa matar da ta dace da shi."

Ƙarya ne, ƙarya ne wallahi. Ba ki haɗa komai da Asad ba face ki ce kina auren mahaifinsa ke matar ubansa ce bayan nan kuma fa? Yanzu idan ya sake ki wani iko kike da shi akan Asad.? Ni kuma nan ni ne maɗaurin auren Asad ko a lahira ni ne ubansa jini ɗaya Muke daga tsatsona Abubakar muka fito kin ga kuwa idan aka tsaga jinina za'a ga na Yaya."

Kallomsa ya maida kan Asadullah ya ce.

"Asad ɗana, ga ƴar uwarka can tana jiranka. Na baka ita a matsayin matar aurenka kuma uwar ƴaƴanka in sha Allah. Ko Na baka zaɓi ko Maryam ko Abida duk wacce kake so ka zaɓa a cikin su biyu."

"Ba zai yiwu ba Adam ta yaya kake neman mayar da ni ƙaramar mutum ce. Tun yaushe nake kokarin ganin na zaba masa matar aure ta gari. Ƙawayena da dangi na bi na zakulo yana watsa Mani kasa idanu, sai yanzu da na shawo kansa kake so ya bijire Man? Shi su ƴaƴan naka ai bai ce yana son su ba ."

"Ai ba zai taɓa kin nasa ya zaɓi bare ba."

"Ai soyayyar ƴan uwantaka daban da..."

"To ba ki isa ba na fi ki iko da Asad kuma idan na zartar da hukunci ya zauna ko Yaya ba zai yi jayayya da Magana ta ba."

Sa'insa suka fara yi a tsakaninsu har ran Dad ya ɓaci ya daka masu tsawa.

"Ya isa!"

Sai da lokacin suka nutsu kowa ya yi shiru.

Asadullah kallonsu yake yi da mamaki akan macen da zai aura suka wannan jijiyar wuya.

Juyawa ya yi zai koma amma ganin kiran bodyguard ɗin sa Sulaiman ya saka ya nufi ƙofar fita .

Jin muryar Mahaifinsa ya yi ya ce .

"Asad."

Juyowa ya yi sannan ya ce.

"Na'am Dad."

"Zo nan."

Cikin sanyin jiki ya karaso bai kalli Mom ko Uncle Adam ba dan haushi suka bashi.

"A cikin yaran kawunka da yarinyar da Mom ɗin ka ta zaɓa maka wacce kake so a cikinsu.?"

Shiru ya yi ya ma rasa mai zai ce.

"Dole za ka sanar da ni a gaban kowa kuma yanzu, saboda hakan ne mafita."

Kowa ya zuba masa idanu suna jin faɗuwar gaba don tsoron abin da Asad zai ce.


*Maman Ihsan ce*✍️


09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z




*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page3️⃣2️⃣

Kowa ya zuba masa idanu sana jin jin faɗiwar gaba don tsoron abinda Asad zai ce.

"Ba wacce nake so a cikinsu ko da na aure su sai dai idan biyayya zan yi. A zahirin gaskiya ba wata macen da na ji ta kwanta Mani a rai."

Dam dam haka ƙirjin Uncle Adam da Mom yake bugawa, sakamakon jin zancen da Asad ɗin ke faɗa.

"Ki yi haƙuri Mom wallahi biyayyar uwa ce kawai za ta ni zuwa wajen yarinyar da kika zaɓa mani, ga Uncle shi ma ya bijiro da zancen auren ƴarsa. Kin ga idan na bi ra'ayin ki na zaɓi yarinyar da kika zaɓa mani zai ji ba dad'i ganin ga ƴar uwata ƴarsa na ƙi ta. Kamar yadda idan na zaɓi ƴarsa na san ke ma za ki ji ba dad'i ne ki ce n watsa maki ƙasa a idanu. So ku yi hakuri Please."

Ya karasa maganar yana haɗe hannayensa alamar roƙo.

Dad ya kalle shi ya ce.

"Ba zai yiwu ba dole ka zaɓi ɗaya daga cikinsu."

Ɗan jim ya yi kafin ya ce.

"To Dad ka bani lokaci kadan zan yi nazari kafin na zaɓi daya daga cikinsu."

Mom ta yi saurin cewa

"Ka je ka ga waccen saboda ka san ta don yaran kawun naka ba ɓoyayyu ba ne."

Jinjina kai ya yi sannan ya fice daga falon. Sulaiman bodyguard ɗin sa ya tarar a ƙofar yana jiransa.

Gaba yayin da s shik kuka take masa bayan fitarsa ne Uncle Adam kalli Mom ya ce.

'Yar bakin ciki hankalin ki ya kwanta burinki ya cika , hankali ki ya kwanta wato bai auri ɗaya daga ɗaya daga cikin ƴaƴana ba. To bari na fada maki kamar yadda bai sure ki ba Hakazalika ba zai auri kowace yarinya da kika kawo ba idan kuma kika matsa to mutuwar kasko zamu yi, dan Wallahi sai dai kowa ya rasa."

Yana gama fadar haka ya fita fuu yana cika kar ɗanwaken da zai yi juyin farko a wuta.

Dad kam gabaɗaya sun daure masa kai, yadda kowa ke nuna cewa sai ta hanyarsa Ajmal zai samu mata .


Jidderh ce ta yi sallama ta shigo cikin falon, cikin girmamawa ta durkusa ta gaida Dad, ya amsa cikin sakin fuskar tare da tambayar ta mutanen gidan, ta amsa da Alhamdulillah.

Nan ta gaida Mom ta amsa mata ba walwala, har ta mike ta nufi kitchen dai ta ji Mom ta ce
" Jidder?"

"Na'am gani nan zuwa."

Ta fadada tana dawowa in ga Mom take.

"Mom ga ni."

"Ki fara shga cikin ɗakina ki ɗauko Maganin da zan sha."


"To Hajiya."

Ta fada tana tashi daga Wajen.



_Asadullahi_

Yana zaune. Bayan motar yana kallon Togo da jama'ar sai dai hmhanafaya hankalinsa na wani wajen can daban, don a zahiri ba titin yake kallo ba ya lula can duniyar tunani.

Al'amarin Uncle Adam da Mom.

Fitowa ya yi daga cikin motar, ƙamshin tutarensa kawai ya tabbatar wa ma'aikatan kamfanin ya ya iso.


Wunin ranar da na dai Asadullah ya yji shi gabaɗaya ya kada gane meke damuwa.


Da wuri ranar ya dawo gida .


Ƙofar Sualaima ne ya yi saurib fitowa daga motar ya zo ya buɗewa Asadullah . Yana fitowa ya nufi cikin gida.

Ba kowa a falon ƙasa, don haka kai tsaye ya nufi upstairs. Direct ɗakinsa. Bayan ya shiga ne ya ji kamar motsi.


Yana juyowa kafin ya samu damar ganin ko waye ya ji an fesa masa abu a fuska. Daga ranar bai sake gane komai ba, sai dai ya farka ya ga ne a in da yake. Sai dai an ɗaure shi da sarƙa.




*Cigaban labari*



_Hilal_

Shaƙo Idanunta ya yi ta fara zaro idsnu tana kakari.

"Waye ya maki ciki?"

Daidai lokacin ne Dr ya shigo yana ganin abunda an Hilal ke ƙoƙarin aikatawa. Da ƙurar ya kwace Zahra daga hannunsa.

Take ta zube a wajen tana ta faman tari.

"Za ki fara fadi ko sai na illata rayuwar ki?"

Ita dai sam ta kasa gane me yake nufi da wai tun yaushe ta fara harka, sannan kuma wani ciki yake magana akai, sam ta kasa gane manufarsa.

Doctor ne ya yi magana yana cewa

Ka duba halin halin da take ciki mana, ka bari ta huta abi komai a sannu."

Tashi ta yi ta zauna bakin gadon tana mayar da numfashi.

Babu abinda Hilal ke aika mata da shi sai mugun kallo, bakin ciki ne a a cikin zuciyarsa.

Zuwa ya yi ya samu Dr akan ya basu sallama. Tsoronsa da Doctor ya ji ne ya saka ya basu sallama.


Yana shiga ɗakin ya tsuke fuska .

"Tashi mu tafi kafin na ɓalla ki a wajen nan."

Haka ta dinga rawar jiki tana ɗaukar dankwalinta da takalmi ta saka.

A tare suka fice kowa zuciyarsa ba dad'i. Wajen parking motocin da aka tanada a asibitin suka nufa. Mazaunin direba ya shiga yayin da ya shiga ta zauna a gefensa.

"Wa ya yi maki ciki? Kuma yaushe kika fara mu'amalar banza da maza?"

Hawayen da take riƙrwa ne suka samu nasarar zubowa daga idanunta.

Ita tun da take a rayuwarta babu wani ɗa namiji da ya taɓa rike ko da hannunta ballantana suka kai ga mu'amalar banza da shi. Amma wai yake mata zancen ciki har da ma tambaya wai yaushe ta fara

Tsawar da ya daka mata ne ya saka ta sakin wani marayan kuka.

Bai ce mata komai ba, ta cigaba da kukan nata, kasancewar baya son hayaniya da kuka ya saka shi yin parking a gefen hanya.

Kallon gefen fuskanta ya yi ya ga shatin yatsunsa biyar a fuskarta sakamakon marin da ya yi mata a asibitin. Tsawa ya daka mata tare da cewa

"Za ki rufe Mani baki ne ko dai na sauya maki kamanni a wajen nan, wallahi idan ba ki kiyaye ni ba sai na ɓallaki a wajen nan."

Tana jin haka ta san muguntarsa don haka ta haɗiye kukan da take yi. Sai dai zuciyar ta mata zugi bisa kalamansa gare ta na cewa yaushe ta fara mu'amala da maza."


A haka suka ƙarasa gidan ran kowa a jagule, bayan ya yi parking a parking space ne ta kai hannu dan buɗe murfin motar, amma sai ta ji ta a gam alamar ya yi lucking ɗin motar ta juyo ta lalle shi da niyyar yi masa magana ya bude mata sai ta kasa sakamakon zuba mata Mayun idanunsa da ya yi masu masu matukar kwarjini da ya yi. Sai ta sunkuyar da kanta tana Wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle. Tsabar kwarjinin da ya yi mata ne ta kasa yi masa magana .

"Tambaya ta ƙarshe zan yi maki kada ki ce mani baki sani ba. Waye ya yi maki ciki.?"

Tura baki ta yi tare da cewa

"Wai kai kana ta Mani maganar ciki ya za'ayi ma ace wai ina fa ci..."

Kafin ta kai aya ta ji saukar yatsunsa biyar a gefen fuskarta wanda sai da ta ji wani shuu a kunnen nata, ga wani duhu da take ganin ya gifta, jin ta da ganin ta sau da suka ɗauke na wucen gadi, ba ta gama farfaɗo wa da azabtar marin da ya yi mata ba ta ji ya kai mata duka a baki, nan ma wani azaba ta ji wanda ya saka ta sakin ƙarar azabtar da ta sha har ta rintse Idanunta.

Wani gishiri ta ji a cikin bakin nata, alamar jini ne bakinta ya fashe.

"Get out in my car ƴar iska mai fuska biyu. Zan yi maganin ki ne."

Tana buɗe kofar ta ji ya buɗu. Hakan ya saka ta fita a guje tana kuka.

Lumshe idanu ya yi ransa na masa zafi. A hankali ya fito daga cikin motar cikin sanyin jiki kamar an jefi kaza da gishiri.

Ba kowa a main falo, kai tsaye ta nufi part ɗin na su. Tana zuwa ta ga gabaɗaya suna falon. Abbi Ummi, Yaa Mahmud da Yaa Sadik.

Cikin tashin hankali suke tambayar ta daga ina take suna ta kiran wayar ba ta shiga, sannan kuma wannan fuskar da ta kumbura da ga baki ya fashe.

Ƙasa ba su amsa ta yi sai faɗa wa jikin Ummi ta yi tana sakin kuka mai cike da raɗaɗin zuciya da ƙunci.

"Abbi me y saka ƴan uwanka suka tsane mu, me ka saka ba sa ƙaunar su ga nuna farin ciki da walwala. Dangin Ummi kawai suke ƙaunarmu ba sa son ganin kukan mu, amma danginka ba sa son su ga nuna farin ciki."

Ummi ce ta ce .

"Ya na ga fuskar ki a kumbura ga baki shi ma ya kumbura ya fashe, daga ina kika mun dawo ba ku nan ga wayarki a gida. Ballantana a kira .

"Mom kin san lokacin period ɗina ne yanzu ko?"

"Eh na sani me ya faru?"

"Daga cikinsu da marata na ciwo na kwanta kin san wani lokacin ina zubar da jini sosai daga gani shi ne su Sunyi Laila da Mummy suka ce wai ciki ne da Ni na zubar..'

Dukkansu salati duka hau yi.

"Kada ki damu Allah yana tare da ke."

Cewar Abbi yana mata kallon tausaya wa.

"Me ya saka naga kamar kin sha duka ga fuska ta kumbura ga baki ya fashe?"

"Yaa Hilal ne ya mare ni ya kuma duke ni a baki wai sai na fada masa wanda ya Mani ciki ."

A fusace Yaa Sadik ya mike don zuwa ya samu Hilal.

Yaa Mahmud ne ya rike shi tare da cewa.

"Ka kiyaye Yaa Hilal domin ba Mansur ba ne ko Faisal da ka saba faɗa da su. Wannan Hilal ne karo da shi ba za ka ci riba ba, kai ma ka san waye shi ba sai na baka labari ba."

Dawowa ya yi don shi ma ya san ba zai iya ja da shi ba.

" A gaskiya wannan rayuwar cikin waɗan nan mutanen ba dad'i, gara mu bar masu gidan gabaɗaya mu koma wani wajen.,"

Sadik ta yi maganar cikin ɓacn rai, Ummi ne ya ce.

Sai dai ku yi hakuri domin kuwa domin Kakanku haka ya tsara cewa ba wanda zai bar gidan nan."

Hannun Zahrah Ummu ta kama suka shiga ciki n ɗakinta ganin yadda bakin ma ya kumbura. Wanka ta saka ga yi da ruwan ɗumi sannan ta fito ta sauya kaya ta sanya pad a jikin panta ta shafa miski a ƙasan wajen ta shirya cikin doguwar riga.

Tea Ummi ta haɗa mata sannan ta ɗauko mata magani ta kawo mata.

Amsa ta yi ta kafa kai bayan ta yi bisimillah ta sha, maganin ma ta sha sannan ta kwanta.


_Hilal_

Yana shigo wa kai tsaye ya nufi upstairs. Jin Muryar Mummy ya yi tana cewa.

"Yanzu da ka kai ta asibitin ka yarda ciki ne da ita ba sharri aka yi mata ba ko? Wai ina ruwanka ne ma da ka kai ta asibiti?"

Na yi abinda zan yi wa kowa ne ko da a hanya na ga mutum haka zan taimaka masa ba wai don ita na yi ba ."

"To Meye na ka na shiga damuwa ?'

Daniwata ita ce yadda za ta zubar da kimar ahalinmu ta ɓata mana sunan family yadda aka san wannan family ya ji suna idan mutane suka ji daya daya cikin familyn ga abinda take aikatawa ai ta ɓata mana suna don. Sai ya shafi kowa da ke cikin gidan nan. Bayan haka Meye damuwata ita ta ne can ga ƙararta."

Ya ji maganar yana haurawa upstair.


*Kuyi hakuri na ji na shiru ina da uzuri ne don ba na ma gari na yi tafiya ne. Am very busy almost all the time*


*Maman ihsan ce*✍️

09065357995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page3️⃣3️⃣

"Damuwa ta ita ce yadda za ta zubar da kimar ahalinmu ta ɓata mana sunan family yadda aka san wannan family ya yi suna, idan mutane suka ji daya daga cikin familyn ga abinda take aikatawa ai ta ɓata masa suna don ya shafi kowa dake cikin nan. Bayan haka ta je can ta ƙarara."

Ya yi maganar yana haurawa upstair .

Ummi na fitowa daga cikin ɗakin Fatima Zahrah bayan ya ba ta magani ta yi barci ne sai ta nufi ɗakin Abbi.

Zaune ta same shi akan gadonsa da alama tuninin yake yi.

"Hannunsa ta rike a cikin nasa wanda hakan ya saka ya juyo ya kalle ta yana mata murmushin yaƙe .

"Ya jikin Zahra?"

"Ta yi barci."

",Allah ya sauwake."

"Abban Mahmud."

Juyowa ya yi ya kalle ta da alama yadda ta kira sunan maganar na da mahimmanci.

"Yanzu haka za mu cigaba da rayuwa a cikin wannan gidan. Na gaji. Kusan shekaru talatin muna abu ɗaya. Na sha yi maka maganar mu tashi mu bar wannan gidan, ka ce Papa ya hana bayan ƙiyayyar da ake yi maka ya shafi matarka da ƴaƴanka, idan muka yi wasa sai ya shafi jikokinnu. To ba zan bari hakan ya faru ba, akan me za su saka mu a gaba. Musamman Fatima Zahrah tsanar da suke yi mata ya fi na kowa yawa a cikin gidan nan. Zan je na samu Papa idan har kai ba za ka bar gidan nan ba to ni zan bar gidan nan ni da yarana."

Tana shirin tashi ta ji ya rike hannunta.

"Kin ga don Allah ki sake hakuri in sha Allah wata rana komai zai dawo daidai. "

Mumrmushin takaici ta yi tare da cewa.

"Haƙuri na nawa kuma ai tun da ba yi haƙirin kusan shekaru talatin to wani hakuri ya rage kuma?"

Da kike maganar tashi a cikin gidan nan kin san cewa ba na da in da yafi nan ko? Saboda nan gidan ubana ne kuma ya mallaka Mani wannan ɓangaren halak malak, ba wanda ya isa ya tashe ni a nan, kamar yadda suma suke takama gidan ubansu ne to haka ni ma, kamar yadda ya mallaka masu ɓangarorin da suke zaune haka ni ma ya mallaka mani na wa. Kuma sanin kanki ne cewa ya haramtawa ƴaƴansa barin gidan nan dole kowa ya zauna a cikinsa. So kike na saɓa umarnin mahaifina ne?"

Tun da ya fara magana ba ta katse shi ba sai da ya kai aya ta ce .

"Ba so nake ka tsallake umarnin mahaifin ka ba, ka zauna amma gaskiya ni da ƴaƴana abun ya ishe mu haka. Sun saka mu gaba musamman Zahra kullum cikin matsalarsu take. Har ya kai ga an yi mata ƙazafin ciki. Ba'a bar ta hakan ba sai da aka haɗa mata da suka akan laifin da ba ta aikata ba. Wallahi, summa tallahi ba zan bar maganar nan ba sai na sanar da Papa wannan zancen idan bai ɗauki mataki ba ni na san matakin da zan ɗauka akan hakan."

Tana gama fadar haka ta nufi kofar fita duk yadda Abbi ke kiranta ba ta saurare shi ba ta fice abun ta, don ranta ya gama ɓaci akan zancen."



_Asadullah_

Yana zaune a wata kujerar roba dake ɗakin da aka ajiye shi . Har lokacin hannunsa da ƙafarsa ɗaure suke da wani sarƙa. Sai dai wannan karon da alama yana cikin hayyacinsa.

Wani mutum ne ya turo ƙofar ya shigo cikin ɗakin, sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login