Showing 1 words to 3000 words out of 154779 words

Chapter 1 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6263

[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug







*GABAR CIKIN GIDA*



*ƊANƊANO ƊANƊANO*


Mama Ihsan ce✍️




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️





Numfashinta ne yake barazanar ɗauke wa, tana ta fafutuka da rayuwarta yayin da ƙafarta ɗaya ke duniya ɗaya ke lahira. Maganinta take nema ba ta ganshi a cikin ɗakin ba, drawar da ta san tana zuba magungunan a ciki ba. Ta duba ba komai a ciki, dakyar ta iya miƙewa ta ƙarasa bakin ƙofar ta buɗe ƙofar,tana buɗe wa ta ji numfashinta ya ɗauke ta zube a wajen.

Numfashinta ta janyo da ƙarfi tana kwance wajen ta sauke idanunta akan wan mahaifinta wanda suke kira da Abba da ƙanwar mahaifinta da ƙasar mahaifinta wacce suke kira da Aunty Lailai. Da 'ya'yansu suna kallonta suna murmushi. Can ta hangi maganinta a saman Centre carpet, da rarrafe tana jan jiki ta ƙarasa wurin maganin, ta miƙa hannu za ta ɗauka sai ƙanwar mahaifinta ta take hannun tare da cilla maganin ƙasar kujera.

Hawaye ne ke zuba daga idanunta ta kalli ƙanwar mahaifinta da ta take mata hannu ta yi mata alamar da ta yi haƙuri ta bari ta ɗauki maganin. Ba tare da tausaya wa ta cilla maganin ƙarƙashin kujera. Sanin cewa za ta iya dauko maganin ne ya saka ta tura hannu ta fito da maganin tare da watsa mata kallon tsana, tana bin ta da ido har ta haura upstair hannunta rike da maganin, yaranta biyu Kausar da Nabeela suka mara mata baya.

Zafafan hawaye ne suka fito mata da idanunta ta mayar da kallonta ga wan mahaifinta kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai ya nufi part ɗin sa.

Numfashinta ke sama da ƙasa sai ya yi kamar zai dauke sai ya dawo kamar tana janyo shi suna kokawa da shi. Ga ƙirjinta dake sama da ƙasa. Kwanciya ta yi sa saman tiyel ɗin falon duk da ciwon baya son sanyi a haka tana jan jiki ta ƙarasa ƙodar ɗakinta ta na shiga ta tuna wayarta na falo tare da maganinta ta barshi, a haka ta koma tana jin numfashinta kamar zai bar gangar jiminta gabaɗaya. Tana zuwa ta ga Yaa Mansur yana shigowa falon, kallonsa ta yi da idanunta da suka zubar da hawaye tana mika masa hannu alamar taimako take nema, kau da kansa ya yi tare da cewa.

"Shegiya dama ki mutu kowa ya huta, ko za mu yi farin ciki a gidan."

Sanin cewa ciwon baya son sanyi amma sai ya ƙure gudun A.C dake falon wanda hakan ya sa ciwon mata ƙara tsananta. Haurawa ya yi sama yana cewa.

"Ina jiran jin daddaɗan labarin mutuwarki, duk wanda ya far sanar da mu sai na masa kyauta mai tsoka."

Wayarta ta hango a ƙasan center tables inda ta ajiye tare da maganin. Tana jan jiki ta ƙarasa wajen tare da ɗaukar wayar. Lambar ƙawarta A'isha ta lalubo daƙyau ta danna kira har ta yi mata 3 missed calls ba ta ɗaga ba daga nan daga nan ta ajiye wayar tana kwance tana kallon wayar ƙirjinta na sama ƙasa numfashin na yi kamar zai dauke gaba ɗaya saboda sanyin A.C ya yi yawa.

Wayar ce ta kawo haske alamar kira ya shigo, duk da ba ta duba ko waye ba ta danna ɗaukar kiran, ta kasa magana sai sautin numfashinta. Cikin wayar ta ji muryarsa yana cewa.

"Assalamu alaikum, Fatima Zahrah kin manta yau muna da lecture ƙarfe tara ba ki zo ba ga shi har loka..."

Ƙasa ƙarasa wa ya yi da maganar sakamakon jim sautin numfashinta tare da ajiyar zuciya.

"Subhanallah ciwon ne ya tashi?"

Ba ta iya magana ballantana ta masa masa.

"Ya Salam kuma na san Umminki ba ta dawo ba ko, kin ga ina zuwa."

Katse kiran wayar ya yi yayin da numfashinta ya tsaya cak, ba ta motsi kwata-kwata.


Wani babban Mention mai matukar girma da tsaruwa, girmansa ya kai unguwa guda. Tun kafin ki ƙarasa Mention din za ki ga symbol inda aka rubuta *ASADULLAH MENTION* zagaye yake da security dake kula da wajen.

Mai daidaita sahu ne ya ƙara so mention tun daga nesa take ce masa ya tsaya amma bai saurare ta ba yake ƙoƙarin ƙarasawa bakin gate ɗin. Hannu da ya ga wani security ya ɗaga masa alamar ya dakata daga can ne ya sa ya dakata.

"Haba Mallam ina ce maka ka dakata ina za ka ke haka, ka san ba'a bari a ƙarasa wajen ko?"

"Yarinya meye alaƙar ki za Mention ɗin?"

"Aikatau nake yi."

Ta bashi amsa a takaice, ya sake ce mata

"Ina son shiga cikin wajen nan ne ko Allah zai sa na yi ido hudu da ɗan albarka, duk da na ji an ce baya ƙasar.

"Wa kake nema."

"Sir Asadullah nake so na gani ido da ido ko..."

Tsawa suka ji an daka masu wani security dake ƙarasowa wajen yana cewa.

"Who is there!?"

Da sauri ta mika masa kudin tana cewa.

"Baba ka tafi."

Ta fito daga cikin napep ɗin yayin da mai napep ɗin ya juya, ganin ta ya sa security ɗin komawa.

Gaishe su ta yi ba wanda ya amsa mata kamar dai kullum, gate suka bude mata ta shige.

Gidajen dake cikin Mention ɗin suna da yawa kuma kowanne ya hadu iya haduwa, kana ganin wajen ka san an narka dukiya a wajen.

Wanda ya fi kowanne tsaruwa ta nufa, ɗaga kai ta yi tana kallon upstair na gidan tun kafin ta shiga. Alhaji Ahmad ta hanga yana sanye da medical glass, hannunsa rike da jarida yana karantawa.

Sauke kanta ta yi ya nufi main falo, kasancewar safiya ne masu gidan ba su tashi da wuri don haka ba ta yi mamakin ganin ba kowa a falon ba. Sai sanyin A.C da ƙamshi dake tashi a falon.

Kai tsaye ta nufi sashen da take aiki, kamar an ce ta juya sai ta hangi Doctor da wanda yana yawan ganinsa ya zo ɓangaren Sir Asadullah.

Sai dai yau ta ga ya nufi wani ɓangare wanda tunda ta zo gidan ba ta taɓa zuwa wajen ba, don ba ta ma ganin ko masu gidan na zuwa ɓangaren. Ganin da ta yi Doctor ɗin na waige-waige alamar rashin gaskiya ne ya sa ta yi tunanin bin bayansa.

A hankali take sanɗa tana bin bayansa har ya ɓacewa ganinta, ko da ta ƙarasa wajen ta kasa gane wane ƙofar ya shiga. Sai ta lura da ƙofa ɗaya dake buɗe. Don haka ta ƙarasa a hankali jikin ƙofar tana leƙe.

Gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa sakamakon ganin Sir Asadullah a cikin ɗakin an ɗaure masa hannaye da ƙafarsa da wata doguwar sarƙa.

Toshe bakinta ta yi da hannayenta biyu tana kallonsa. Da ba don ƙwayar idanunsa da suka kasance ruwan ash kamar na mage ba da ba za ta yi saurin gane shi ba, don ganin yadda ya canza mutum mai tsantsar kyau, kwarjini da cikar haiba.Yadda ya dawo.

Wayar Doctor ɗin ne ya yi ruri, ya ciro daga Aljihun suit na rigarsa, ƙara wayar ya yi a kunne.


*Prison/Gidan yari*

Zaune yake a saman gadonsa kasancewar a gidan yarin ma shi yana V.I.P ne komai nasa shi kaɗai aka ware masa, ƙaramin falon da wasu kujeru ga bedroom a ciki. Sabanin sauran wadanda ba vip suke ba da suke ɗaki ɗaya a cakuɗe da juna. Don shi hatta abincinsa ma siyo masa ake yi baya cin abincin da sauran prisoners ke ci.

Zaune yake a bakin gadon kare da waya a kunnensa ya danna kira. Ana ɗagawa ya fara magana cikin fusata yana cewa.

"Wai Doctor meye amfanin aikinka, kullun sai na sa an kawo mani jarida ina jiran na ci karo da labarin wanann matashin ɗan kasuwa Asadullah ya mutu amma shiru nake ji me ye haka!?"

Doctor dake kallon Sir Asadullah ya ce.

"Wai gaggawan mene ne kake yi?"

Jidderh dake laɓe jikin ƙofar tana kallon Dr amma ba ta jin maganar da na cikin wayar ke faɗa.

"Ka ga ka kwantar da hankalinka ba kai kaɗai ke son ganin bayan Asadullah ba a cikin gidan nan ma maƙiyansa ne zagaye da shi. Kuma sun yi mani tayin makudan kuɗaɗe idan na kashe shi, so ka bi komai a hankali, yanzu haka allurai da magungunan da nake bashi a hankali suke raunana jinsa da ganinsa za su yi masa illar da zai yi rayuwar da gwamna mutuwaraa ma akan rayuwarsa domin rayuwa ce mara amfani. Ka jira lokaci."

A fusace ya ce.

"Ba zan iya ba! Ka san cewa Asadullah shine mutumin da ya saka aka kama ni ƙarshe gani a gidan yari duk sanadinsa. Ya yi fatali da dangantaka dake tsakani na da shi, ina kiransa da sunan Yayana shi ma ƙaninsa yake kira na ko sunana baya kira amma dan na aikata wani laifi wanda zai iya yafe mani amma ya haɗa ni da hukuma ya mance dangantaka dama ɗan uwa zai iya tura ɗan uwansa prison? Wallahi sai na ɗauka fansa kuma rayuwarsa ce fansa a gare ni."

"Ka kwantar da hankalinka yallaɓai."

"Wane kwantar da hankalin zan yi ka san yadda rayuwar gidan yari yake rayuwar ƙaskanci da rashin 'yamcin da ya saka ni abu ne mai sauki? Idan har ba ka yi masa alluran guba ya mutu nan da kwana biyu ba to za ka ga abinda zan aikata maka duk da ina rufe kuwa."

"Na sani in sha Allah za ka ji kyakkyawar labari, ka san sai mun iya takun mu, kasancewarsa babban mutum sananne kuma idan ba ku da kuka saka ni aikin ba babu wanda ya san yana ƙasar nan, kowa ya ɗauka yana waya ƙasar wajen harkokinsa. Hatta bodyguards ɗin sa na ji suna magana kan cewa wai Sir Asadullah bai taba tafiya shi kadai ba sai ya je da na hannun damansa, kuma sauran guard ɗin ma sai ya samary da su zai yi tafiya. Amma wannan karon ace ya yi tafiya shi kadai kuka ba wanda ya ga fitansa su ba su yarda ba. Ka ga dole mu bi a sannu , na fada wa Hajiya haka ita ma ta damu akan kashe shi."

"To ni dai ina jiran jin labari mai daɗi ne kawai."

Yana gama fadar haka ya katse kiran wayar tare da shafa gemunsa yana dariya.

Bayan Dr ya mayar da wayarsa a Aljihu ne ya kalli Asadullah ya ce

"Ka yi mani alkhairi da dama a rayuwata kai mutumin kirki ne matashin da al'umma ke bukatar irin ka, amma ke bukatarka, ama dole na aiwatar da aikin da aka saka ni don tseratar da rayuwata da iyalina."

Sir Asadullah kallon Dr yake yi kuma yana kallon Jidderh dake laɓe, kasancewar Dr ya bawa ƙofar baya ya sa baya ganinsa, sai dai da alama baya fahimtar komai baya cikin hayyacinsa sai lumshe idanu yake yi kamar mai maye.


Wani allura ta ga Dr ya ciro sirinjin da ruwan alluran a ciki ya ciro. Yana soka masa a jijiyar hannu sai ya wani zabura ya miƙar da jikinsa sai jikin ya fara rawa kamarazari kafin kuka ya saki jiki ya kumshe idanu.

Ganin Dr yana hada kaya alamar zai tafi ya sa Jidderh ta yi saurin barin wajen a guje ta nufi ɓangaren da take aiki.

Hawaye ne kawai ke bin fuskarta na tausayin wannan bawan Allah.



Mansur tunda ya katse kiran wayar ya tabbatar ciwon Fatima Zahrah ne ya tashi. Don haka hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba don yana tausayin yarinyar.

Department ɗin ƙasar Fatima Zahrah ya nufa. Wato A'isha, daidai lokacin take ƙarasowa da motar ta a wajen.

Bayan ta yi parking ne ta fito daga cikin motar yayin da Mansur ya fito daga cikin motar.

Ganin yanayinsa ya sa ta ce.

"Lafiya ya na ganka a firgice?"

"Ba lafiya na kira wayar Fatima Zahrah ta daga amma ta kasa magana da alama ciwonta ne ya tashi don dai..."

"Ba lokacin dogon bayani zo mu tafi gidan nasu."

Shiga suka yi cikin motar da sauri ta ja motar suka bar jami'ar.

Dama ke nake so na gani saboda na san baki da shamaki da gidan,don dai idan ni ne ba bari za'ayi na shiga cikin gidan ba. Musamman idan wannan Yayan nata sojan yana gari sai ki ga gidan zagaye da sojojinsa.

"Okay Yaa Hilal kake nufi ko?"

"Eh shi nake nufi ko ba Yayanta ba ne?"

"Eh cousin brother nata ne, mahaifinsa shi ne wan mahaifinta ne."

Gudu take yi akan titi har suka iso katafaren gidan . Kasancewar security sun santa sosai kuma Alhaji Babba ya basu damar indai ta zo a barta ta shigo kai tsaye babu shamaki ya sa suka bude mata gate ta shigar da motarta ciki.

Ko parking space ba ga nufa ba saboda ta san halin da aminiyarta ke ciki. Har can wajen main door ta yi parking, a tare da Mansur suka fito.

Knocking take yi ta ji shiru, zuwa lokacin ma Fatima Zahrah ma ta suma ita kadai ce yashe falon kamar gawa.

A'isha ta bude kofar sannan ta leƙa ganin ganin ba kowa sai Zahrah dake kwance ba ga motsi ne ya saka ta juya cikin tashin hankali ta kira sunan Mansur tare da masa alamar ya ƙaraso.

Da hanzari ya ƙaraso wajen suka shiga taimaka mata ya yi suka dauke ta suka sanya ta a bayan motar.

Key A'isha ta yi wa motar suka bar gidan a guje.

Cikin damuwa Mansur ya ce.

"To ina mahaifiyarta take ne?"

"Ka mance ta fada mana sun tafi Saudiya aikin umara ita da mahaifinta."

"Okay na mance sai yanzu na tuna fa, amma yadda Zahrah take ba isashshiyar lafiya ba ai bai dace ta zauna a wannan gidan ba. Gidan da suka kamar maƙiyan juna suyi ta gaba da juna ko wani na bukatar taimako sai dai ya mutu ba wanda zai kalle shi. Kuma babu bare a gidan duk ƴan uwan juna ne dangin juna jini ɗaya. Wanan al'amarin wannan ahalin yana ɗaure mani kai."

Haka dai suke ta jimama lamarin har suka ƙarasa wani asibitin kudi dake kusa da su.

Taimakon gaggawa aka fara ba ta bayan sun yi nasarar farfaɗo da ita ne aka sanya mata oxygen. Mansur ma da A'isha suna asibitin sun manta da wani school ma saboda hankalinsu na ga ƙawarsu.


Har yamma suna tare da ita ba tare da sun leƙa school ba.

A'isha ce ta kwana da a asibitin bayan ta kira iyayenta ta sanar da su. Washegari aka sallame su tare da ba ta magunguna bayan an yi mata allurai.

A'isha ta yi driving ɗin ta har gidansu ta yi horn. Ganin sojoji da yawa ne ya sa suka gane cewa. Yaa Hilal ne ya dawo.

Parking ta yi a parking lot tare da kallon Fatima Zahrah ta ce.

"Besty zan barki a nan don wadannan murɗa-murɗan sojojin ba na son ganinsu, na San yanzu ma ogan na su na ciki."

Godiya ta yi mata sannan ya fice daga motar, ita kuma ta motar ta tafi.

Cikin yanayin sanyin jiki irin nata take tafiya. Ta nufi main door. Tana rike handle ɗin ƙofar ta ji hayaniya na tashi daga falon, Hango su ta yi sun hallara a babban dinning area, Yaa Hilal ne suka zagaye ƴan matan kowacce na cewa ita ta girka masa na ta zai ci. Har suna kokawa kowacce so take ya karbi plate da ya zuba masa abincin da ta girka masa. Musamman Aunty Nabeela wacce kowa ya san irin son da yake masa, shi ne bai bayar da fuska ba amma soyayyar ta gare shi ya kasa ɓoyuwa, duk da cewar A Kausar ma tana son sa amma ta iya ɓoye nata.

Da sallama ɗauke a bakinta ta shigo falon, dukkansu suka juya suna kallonta ba wanda ya amsa mata sallamar sai Yaa Hilal. Sauran kallon tsana ne suke jifanta da shi tare da mamakin yadda aka yi t warware Haka alhalin ba ta iya fita.

Jin muryar Yaa Hilal ya amsa mata sallamar ne ya saka ta kalle shi tare da cewa.

"Yaa Hilal ina wuni ka dawo lafiya?"

Bai amsa mata ba ballantana ya kalle ta. Ba ta yi mamaki ba don ba yau ya fara ba, kuma halinsa ne.

Tafiya take a hankali ta nufi part ɗin mahaifiyarta hannunta rike da jakar magungunan da aka bata. Da

_Jidderh_

Yau daƙayar ta iya aikinta tun da ta ji ana shirin kashe Sir Asadullah. Ko da ta kammala aikinta ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta fice daga gidan.

Tafiya take yi tana saƙe-sake hawaye ne cikin idanunta. Yau kam ba ta tsaya tare mai adaidata sahu na ta tafi da ƙafa duk da nisan wajen da unguwarsu.

Daga ganin unguwar ta masu matsakaicin ƙarfi ne, dan duk gidajen dake layin na talakawa ne.

Wani karamin gida ta shiga bakinta dauke da sallama. Wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru arba'in da biyar tana zaune a kujerar tsuguno tana tankaɗe garin tuwo ta amsa tare da cewa.

"Hauwa kuluwa har kin dawo?"

Murmushi Jidderh ta yi tare da cewa.

"Eh Ummata."

Kallo ɗaya Umman ta yi mata ta gane cewa tana cikin damuwa.

"Jidderh akwai abinda aka maki a can ne?"

Kuka ta fashe da shi tana cewa.

"Ummata kashe shi suke son yi."

"Waye za su kashe kuma me ya yi masu su waye za su kashe sh?"

"Umma mutumin da ya zama bango ga al'umma suke son ganin bayansa. Bai da wata illa a rayuwarsa yana da kirki da son taimakawa marasa ƙarfi, Allah na kawai ya san yawan adadin mutanen da suka yi arziki ta sanadiyyarsa Umma ki duba yawan mutanen da yake taimaka wa, hatta su ɗin na jikinsa da suke ƙoƙarin ganin bayansa a gidansa suke zaune cikin rufin asirinsa suke ci suka sha suke komI na rayuwa. Amma. Suke neman ganin bayansa. Wallahi zan taimaka masa ba za su taba nasara ba sai na binciko su na tona asirinsu."

"Kun ji shashasha wawiya an fada maki karo da masu kuɗi wasa ne? To maza-maza ki bar zancen nan kafin su farga dake su saka ki a dogon barci"

Wani matashin saurayi mai kimanin shekaru ashirin da biyar yake da lokacin da ya shigo gidan.

"Yaya wallahi ba ka ga yadda ya koma ba ne."

"Jidderh abinda ya kai ki shi za ki bana son shiga abinda ba ruwan ki."

"Yaya da ruwana kuma sai inda ƙarfina ya ƙare."



*CIGABAN WANNAN LITTAFIN ZAI ZO MAKU A RANAR BIYAR GA WATAN DA ZA MU SHIGA IN SHA ALLAH. 7/5/2025 BA ZAN CE NA FI KOWACE MARUBUCIYA IYA RUBUTU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login