Showing 138001 words to 141000 words out of 154779 words
yi wasa sai yadda ta yi da Hilal kina ji kina gani, ko kin manta yadda uwarta ke iko da ubanta. Baya. Don baya son ɓacin ranta sai abinda ta ce yake yi. Ƙiri-ƙiri ta hana shi cin abinci a cikin mu sai dai na ta ita yaranta su ci, ranar Friday kawai take barinsa ya ci abinci a cikin mu shi ma don dokar Papa ne. Kika yi wasa sai sun raba ki da Hilal."
Daidai lokacin yake saukowa daga downstairs, har yana tsalleke step, cikin sauri yake tafiya. Karasawa ya yi cikinsu ya gaishe su cikin girmamawa. Kowa ya amsa ban da Mummy.
Ganin yanayin ta kuma ya san dama tun bayan da aka ɗaura auren nan take fushi, sanin idan ya tsaya zai ɓata lokaci ya saka bai yi mata wata magana ba ya fice yana sanar da su sauri yake.
Da kallo suka bi shi ya tafi ya bar su da ƙamshin turarensa.
Ƙwalla ne ya cika idanun Mummy, don tabbas tana son Hilal sosai fiye da sauran yaranta, don haka ba ta ji za ta yi saken da zai suɓuce mata. Abincin da ba ta iya ci ba kenan duk da lallaɓa ta da suka dinga yi. Ƙarshe tashj ta yi ta bar dinning area ɗin ta koma part ɗin ta.
_Dada_
Tana zaune a falonta tana shan kunun gyada da ƙosai, Zahrah ta shigo da sallama. Sakin baki Dada ta yi tana kallonta.
Direct ɗakinta ta nufa ta cire jallabiyar ta yi cilli da ita.
Wanka ta shiga yi a bathroom ɗin ta dake cikin ɗakin.
Ko da Dada ta shigo sai ta ga ba ta cikisai dai ta ji ƙarar ruwa a bathroom ɗin. Zama ta yi bakin gadon tana jiran fitowarta.
Wanka take amma kuka ne kawai mara sauti take yi, tana tuna abinda ya faru a tsakanin su a daren juyae, yadda ya kalle mata jiki cikin sauki, tana ji tana gani ta kasa hana shi. Tuan yadda ya zubawa ƙirjinta ido kamar ya ga sabon halitta ta yi. Da yadda yau ya ce sai ya yi mata mai gabaɗaya akan ta yi masa rashin kunya. Jin haushin kanta kawai take yi kenan da ba don kiran wayar da ake yi masa ba da ya yi abinda ya faɗa da ita kenan.
"Ba za ka taba samun jikina ba, ko da wasa ma ba zan yarda mu kasance mu biyu ba a waje daya ballantana ka samu galaba a kaina, na tsane ka mugu azzalumi."
Alwala ta ɗora ta fito daure da babban towel. Doguwar riga ta saka bayan ta saka underwear. Hijabi ta saka sannan ta shimfida sallaya. Har lokacin Dada na ɗakin ba ta ce mata komai ba, sai dai ta fahimci ta sha kuka, sai dai ta karkata ga cewa ko Hilal ɗin ne ya kusanci Zahrah ganin yadda ta yi kuka ga kayan hukunta ta Kudundune ta taho da su. Maganar zuci take yi tana cewa.
"Ikon Allah wanna yaron da nake yi wa kallon mishkilanci ba zai bari ya kalle ta ba shi ne har ya yi mata wani bun da ko kusa ba wanda ya yi tunanin. Ga uwa uba ba ta taɓa ganin Zahrah ta yi makarar sallah ba amma ita ce yau har gari ya waye.
Duk da ta yi mamaki ganin yanayin tafiyar Zahrah bai sauya ba, sai sai ta tabbata ko bai shige ta ba ya kama hanya. Dole ta fara ba ta abubuwan da take tsoron ba ta su.
_Asadullah_
Zaune suke a falonsa shi da Dr Isma'il, yana yi masa godiya sakamakon kudade masu yawa ya bashi kyauta, sakamakon ƙoƙarin da ya yi na tafiye-tafiye da aka yi na neman mata lafiya .
"Na gode Yallaɓai Allah ya saka da alkhairi, ya tsare gabanka da bayanka, ya kare ka daga sharrin maƙiya."
"Amin ya rabbil izzati."
"Yallaɓai dama akwai shawara da nake son na baka."
"Go ahead."
"Dama akan Jidderh ce, tun da an yi bincike ƙasashen duniya ankai ta har yau ba'a gano matsalar ta ba mai zai hana a gwada na gargajiya ko na iskancin ko za'a dace."
Shiru Asadullah ya yi na lokaci kafin ya ce.
"To an yi bincike a asibitoci ba'a gane ba sai na gargajiya ne za'a gane?"
"Ai Yallaɓai idan lalura ya kasance na jinnu ne ko sihiri ko maita asibiti ba sa sanin ko Meye, sai dai su ce ba komai ko da mutum na jin jiki ba za su taba ganowa ba, don haka na kawo shawara a gwada na Islamic."
"To yanzu ya kake gani ina za'a kai ta."
"Ba sai an kai ta ba, domin akwai wani Mallam Mamman aikinsa ne, in sha Allah na sanar da shi har gida zai zo ya same ta, ko ma mene ne zai sanar kuma zai yi mata magunguna da ayoyin Ubangijin talikai, in sha Allah za ta koma cikin hayyacinta."
Cike da gamsuwa Asadullah ya ce.
"Ba damuwa, yanzu ina son zuwa Katsina wajen kakannina da suka haifi Mahaifiyata, Dad ya sanar da Ni suna cikin damuwa, kwana biyu zan yi a can in sha Allah idan na dawo nan da kwana uku kenan sai ka kawo shi ya ganta ."
"Allah ya dawo da kai lafiya ."
"Amin ya Allah."
Bari na tashi ina da marasa lafiya suna jira na a asibiti."
Sallama ya yi masa ya tafi .
Jidderh dake labe tana jin su ta sake ajiyar zuciya ta koma ciki. Tana tunanin yadda za ta aiwatar da shirinta bayan tafiyarsa.
Tashi tsaye ya yi yana zaga falon, na tsawon lokaci .
Kafin ya kalli ɗakin da su Jidderh suke, a hankali ya karasa yana knocking, kafin ya shiga tare da sallama, Jidderh na kwance kan sofa tana barci, gashin kanta sun zubo sun rufe gefen fuskarta.
Anisa dake waya ta ga shigowarsa cikin rashin gaskiya ta yi saurin katse kiran wayar tana kame-kame, rashin gaskiya ƙarara ya bayyana a tare de ita.
Kallon tuhuma ya yi mata na sakanni kafin ya ce.
"Lafiya ?"
Sosa kai ta yi tare da cewa.
"Amm uhm la lafiya lau."
Bai bi ta kanta ba ya nufi kujerar da ya ga Jidderh kwance ya ce.
"Ta ci abinci kuwa?"
Sunkuyawa ya yi tare da janye gashin da ya zubo ya rufe rabin fuskarta.
Zama ya yi kan kujerar ya tattara gashin ya tufke da ribbon da ya zame daga kanta.
Murmushi ya sake yana kallon fuskarta.
Fita ya yi Anisa ta bishi da kallo tana takaicin fashin kulata da baya yi, idan ya yi mata magana to na Jidderh ne, ko yana zaune ta zo don su yi fira ba ta samun kansa.
Wayarta ta duba ta kira lambar da suke magana, ta cigaba da magana abun ta.
Yana fita ya kira Sulaiman a waya ya sanar da shi ya zo ya same shi.
_Zahrah_
Zaune take a falon Dada inda Dada take ta fama da ita akan magungunan mata da take ta ɗinkira mata, ita kuma har da kuka ba ta so.
Ba ta saurare ta ba ta miƙo mata robar wata zumar mata da wata roba dake da tsumin rake.
"Za ki karba ki shanye ko sai na ɗura maki da kaina?"
Tura baki ta yi tare da cewa.
"Dada ni fa ba na son waɗan nan abubuwan in dai akan wannan mugun ne."
"Waye mugun?"
Ba ta ce komai ba ta kau da kai tana ayyana cewa ba abinda zai shiga tsakaninta da shi ballantana har ta yi abinda zai ji dad'i da ita."
"Dalla shanye ki ajiye robar, da na san mijin na ki ba ƙyale ki zai yi ba ai da tuni na fara tsuma ki, amma yadda jiya ya rike ki kika kwana na tabbatar idan na kai ki ba ƙyale ki zai yi ba."
Hajiya Bilkisu ƙanwar Ummin Zahrah ta yi sallama ta shigo, daga wajan Ummi take ta sanar da ita Zahrah na wajen Dada shi ne ta biyo nan.
Cikin jin dadi Zahrah ta tashi ta rungume ta tana tambayar ina Amal, ta sanar da ita tana school zuwa anijma ko gobe Khalili zai kawo ta.
Nan Dada ta kalle ta tare da cewa.
"Yauwa tun da ke uwa ce za ta ji tsoron ki."
Mika mata magungunan Dada ta yi tare da cewa.
"Ga su ki tabbatar ta sunaye su duka."
Tashi ta yi ta basu waje ta koma bedroom ɗin ta.
Fuska babu wasa Hajiya Bilkisu ta tsuke fuska ta mikawa Zahrah robar, tana hawaye ta karba ta sanye tas, sannan ta mika mata ɗayar, shi ma ta shanye sannan ta mika mata wani cup da aka yi wani hadin nan ma ta bata, ta shanye tana kuka.
Janyo ta ya yi ta rungume tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, har sai da ta ji ta sassauta kukan da take yi sannan ta ɗago ta tana cewa.
"Daughter ki yi hakuri kin ji, Yaya ta fada Mani komai na halin da kike ciki, da yadda auren ya kasance, da abubuwan da suka faru tsakanin Hilal ɗin da ke a baya duk na san komai."
Nisawa ta yi tare da cewa.
"Ki yi hakuri kin ji, ki rungumi ƙaddararki a duk yadda ya zo maki, kada ki watsawa tsofaffin nan ƙasa a ido, na san irin kaunar da suke yi maki ba za su yi abun da zai cutar da ke ba.
"Aunty wallahi ba so na yake yi ba, wahala kawai zan sha a hannunsa, ina nan gidan ya azabtar da ni ina ga na tare a gidansa?"
Rarrashinta Hajiya Bilkisu ta dinga yi tare da ba ta shawarwari. Ita dai ba abinda ta tsana ji take jin tsanarsa kamar idan ta tuna yanayin da da gan shi da wasu matan, duk da ba ta gan shi yana yin sex da su ba amma ba ta yi tuninin iya abinda da yake yi kenan ba.
"Me ya saka bakya son sa, na ga duk in da ɗa namiji ya kai ya kai. Ba wai ina fada maki haka ba ne saboda na kwantar maki da hankali ba. Hilal namiji ne da kowace mace mai hangen nesa za ta yi fatan mallakarsa a matsayin mijin aure, yana da kyau da kwarjini sannan da kin ga idanunsa kin ga zarra, ga shi da ƙirar jaruman maza kuma zarata, kin yi mijin wimuce sa'a fa Daughter."
Ta karasa maganar tana shafar gefen fuskarta. Ita kam ba ta ga nagartarsa da ƙanwar mahaifiyarta ke faɗa ba, sai dai ba ta taɓa fada wa kowa ta gan shi da wata a cikin wani yanayi ba, ta bar abun a zuciyarta.
"Na san kina fargaba na cewa baya son ki ko? To ina mai tabbatar maki da cewa matukar za ku rike sirrinkan da zan baki duk taurin kai na ɗa namiji ko ƙaho ne a saman kansa sai ya dawo kasa yana bin ki."
Daidai lokacin Dada ta dawo Hajiya Bilkisu ta kalli Dada tana cewa.
"Na ga lokaci ya kure ba'a fara yi mata gyara da wuri ba, idan ba damuwa ko za ku iya bani ita mu tafi gidana nan da kwanaki uku sai na dawo da ita ta tare a gidan mijinta. Akwai wata maƙociyata kuma ƙawata tana gyaran amare sosai, za ta taimaka Mani wajen cigaba da gyaran a cikin kwanaki ukun ko hudu da suka rage mana."
Shiru Dada ta yi kafin ta ce.
"Ba matsala, idan Papa ya dawo zan sanar da shi, zuwa yamma sai ki aiko a dauke ta."
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"Zan aiko Khalili ya ɗauke ta in sha Allah."
Godiya ta yi mata sannan ta ɗauki handbag ɗin ta ta fice tana masu sallama Zanrah dai kuka kawai take yi, har ga Allah ba ta kaunar abubuwan da suke mata.
Bayan fitar Hajiya Bilkisu da kamar mintuna talatin ta ji kamshin turaren sa, wanda ya haddasa mata faduwar gaba, ta juya ta kalli ƙofar, tsaye yake bakin ƙofar suka hada Idanu, fuskarsa kamar kullum a murtuƙe. Kallon daya ta yi masa ta ɗauke kai.
Ƙsrasowa ya yi dadai lokacin da Dada ta fito tana kallonsa.
"Ka ci abinci kuwa ban ga ka shigo yau ba."
Yamutse fuska ya yi sannan ya ce.
"An kira ni abokina matarsa ta haɗo kayan da akwatuna nan za'a kawo maki ne ko ya ya?"
"Ma sha Allah, a kawo nan ɗin ai."
Wayar Zanrah ce ta yi ruri dukkansu uku suka kalli wayar, ba suna da emoji aka yi seved sun lambar wayar.
Ɗaga wa ta yi tare da karawa a ƙunnenta, Ammar ne don dama da emoji ta yi seved number sa.
Magana take yi da shi a hankali, ko Dada da Hilal da suke falon ba mai jin abinda take faɗa. Da
Ƙamshinsa ne ta ji ya ƙaru sosai don haka ta daga kai ba tare da ta cire wayar a kunnenta ba, ganinsa ta yi gabanta dab da ita fuskar nan a murtuƙe fiye da kullum. Idanun nan kamar wuta za su fito.
*Book 1 ya kawo gangara book 2 na kudi ne za ku same shi akan Naira ɗari biyar #500. Ta wannan account ɗin 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wanan lambar 09065327995*
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page6️⃣6️⃣
Ƙamshinsa ne ta ji ya ya karu sosai, don haka ta ɗaga kai ba tare da ta cire wayar a kunnenta ba. Ganinsa ta yi gabanta dab da ita fuskar nan a murtuƙe fiye da kullum, idanun nan kamar wuta za su fito.
Hannu ya mika mata alamar ta bashi wayar, ganin yanyainsa ya tsorata ta sai ta mika masa wayar, yana karɓa ya ji muryar Ammar na cewa.
"Na ga kin canza mani masoyiya kwanan nan ba ki ɗaga wayata idan na messages ba reply, any problem?"
"Ammar daga yau kada ka sake kiran wayar nan."
Ya fada a kausashe, jin Muryar Hilal ya saka Ammar cewa.
"Man wai barazana kake yi mani ne?"
"Ba barazana ba ne gargaɗi ne."
"Wai kai Meye matsalarka da yarinyar nan ne, akan idanuna na fa ranar da ba ce ta raka ni na gaida Ummi ka harɗe mata ƙafa, bayan haka ka daki bakinta, tun ranar na rike wanan abun da ka yi mata akan ido na ..."
Katse shi Hilal ya yi da cewa
"Ai da ka ɗauki mataki da ka san hakan ya zafe ka. Wallahi Ammar ka sake kiran wayar nan zan shayar da kai madarar mamaki."
A fusace Ammar ya ce .
"Wai me kake taƙama da shi ne, ba ka da iko da Zahrah ballantana ka yi Mani shamaki da ita , kuma aurenta zan yi ko da hakan zai kawo karshen abotarmu ne."
"Okay don't be a loser."
Daga nan ya karfe kiran wayar, ya duba in da take zaune rai a ɓace, sai dai bai ganta ba. Tana can bayan Dada ta tsaya don ta san halinsa idan ransa ya ɓaci komai na iya faruwa. Don haka ta tsaya kusa da Dada. Kallonta ya yi da idanunsa da suka rikide zuwa ja ya ce.
"Zo nan."
Ba ta motsa daga in da take ba, ta san dai dole sai ya wuce Dada zai isa gare ta, kuma Dada ba za ta bari ya taba ta ba.
"Za ki zo ne ko ni na zo na same ki nan?"
"Me ta yi maka, kake zare mata idanu haka, yanzu fa ba kamar baya ba ne , matsayin mata take a wajen ka, ya kamata ku zama masu fahimtar juna. "
Cikin ɓaci rai har yana huci ya ce.
"Dada wani fahimta kuma, ki duba da waya take yi da wani namiji a matsayin wai macen aure da?"
"A'uzubillahi minash shaiɗani rajim, Zahrah ta yanzu ba ki san hakkin aure ba duk ilimin ki?"
"Dada wallahi ba yadda kika dauka ba ne, tun ranar da aka ɗaura Mani aure, ko wayarsa ba na ɗagawa ko text message ba na masa reply. Yau ma na ɗauki kiran na sa me da niyyar na sanar da shi auren dake kaina ne."
"To ka yi hakuri na san Zahrah ba za ta taɓa aikata abinda ba daidai ba."
Bai tsaya sauraren wani zancen ba ya fice rai a ɓace. A Aljihun wandonsa ya saka wayar ya nufi parking space. Motarsa ya shiga ya fice daga cikin gidan.
Kai tsaye gidan KB ya nufa kamar yadda ya sanar da shi matarsa ta haɗo kayan lefen.
Gidan ya tsaya ya yi horn, maigadi ya bude masa gate ya shiga da motarsa , parking ya yi sannan ya kira KB a waya, ba bata lokaci ya fito ya shiga da shi cikin gidan.
Nan ya ga babban falon ya cika da akwatuna, zama ya yi ɗaya daga cikin kujerun dake falon.
"Na ga wat saura Zahrah."
Bai tanka masa ba ya yi kamar bai ji shi ba.
"Angon Zanrah ka sha ƙamshi, ya Amaryar ta mu ce.?"
Nan ma shiru y yi masa kafin ya ce.
"Mallam ba na da lokacin ɓata wa Meye dalilin kiran da ka yi Mani na zo."
Daidai wannan lokacin Hafsat matar Kb ta fito zuwa falo. Ganin Hilal ta saki fara'a tana cewa.
"Barka da zuwa ango."
Ba yabo ba fallasa ya amsa mata.
Ruwa da lemu ta kawo masa sannan ta gabatar masa da kayan da hado. Ta ware masa na sa akwatuna goma sha biyu, sannan ta ware masa na sauran yan uwan na sa kowace akwatuna guda takwas za ta samu , sarauniyar ka kuma akwatuna goma sha biyu ne na ta, kuma komai na ta ya fi na su tsada, don abokin ka ya ce su miliyan biyar ne za'a kashe wa kowacce, amma gimbiyarka miliyan goma ya ce idan na dawo za ka bani miliyan biyar, don 25 million ka bayar saura 5 million za ka bayar cikon na gimbiyarka "
Kallon KB ya yi wato da ya ce kowace miliyan biyar shi ne ya ya sa aka kashe wa Zahrah miliyan goma.
"Bani account number da zan saka maki, don bai isa ya ce ba zai bayar ba "
Take ya tura mata miliyan biyar. Sai dai kasancewar motaras ba za su kwashi kayan duka ba, don haka sai KB ya fito da motarsa da taiamakon masu aikin gidan aka jera kayan a motocin.
A yammacin ranar ne kuka Dr Khalil dan Hajiya Bilkisu ya zo ya dauki Zahrah, bisa umarnin Mahaifiyarsa. Dama Papa bai hana ba Abbi ma ya amince.
A ranar da aka kai ta gidan Hajiya Bilkisu aka fara yi mata gyara ciki da waje ba ƙarya.
Kuma Zahrah ta saki jiki sosai saboda ta hadu da yar Hajiya Bilkisu mai