Showing 135001 words to 138000 words out of 154779 words

Chapter 46 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6274

ya kasance gaskiya. Ba zan ce ku daina zargina ba, ku cigaba da zargina Allah ne shaida ta ban taɓa aikata fasikanci ba, babu wani ɗa namiji da ya taba rike ko da hannuna ne wanda ba muharramina ba."

Tsawar da ya daka mata ne ya firgita ta sosai.

"Kar ki sake fada mani wannan banzar maganar uban waye yake zargin ki, ki ba kin manta me Doctor ya faɗa ne da na kai ki asibiti.?"

Kuka ne ya ci ƙarfinta wanda yake fitowa daga kasan zuciyarta, take numfashinta ya fara barazanar ɗauke wa. Dama ga ciwon ba wai ya sake ta ba ne, ga zazzabin dake jikinta suka taru mata.

Zubewa ta yi a wajen numfashinta ya ɗauke, kallo ɗaya ya yi mata ya dafe goshi yana cewa.

"Oh Allah Papa ka haɗa ni da aiki ka hada ni da wahala, dama na faɗa a baya duk wanda ys auri yarinyar nan na tausaya masa, ashe ni ne abun tausayi ba kowa ba, gaskiya ba zan iya ba."

Ya fada yana nufar closet ɗin sa ya shiga.

Bayan mintuna kadan ya fito sanye da riga da wando farare na barci. Sai ƙamshi tutarensa ke tashi a jikinsa. Kallon agogo ya yi ya ga karfe goma sha ɗaya na dare ne.

Ƙarasawa ya yi wajen da take kwance, ganin ta suma ne ya saka ta ɗauko robar ruwa a fridge ya ɓalle murfin ya watsa mata. Ta ke ta ja wani ajiyar zuciya ta sakin numfashi da ƙarfi.

Sai dai rawar sanyi take ta yi sakamakon sanyin dake ɗakin ya kure gudun A.C ita kuma ciwonta baya son sanyi, ga sanyin tiles da take kwance ga ruwan sanyin da ya zuba mata hakan ya saka jikinta ke kakkarwa har haƙoranta suna karo da juna saboda rawar sanyin da take yi.

Ganin yadda ta jiƙe ne ya saka ya zare mata hijabin na ta da ya jike da ruwa . Nan ma ya ga kayan jikin na ta ya jiƙe, don haka ya fara ƙoƙarin zare mata rigar jikinta ta ta jiƙe, girgiza masa kai take yi alamar a'a amma bai kalli fudkarta ba, ga zazzaɓin jikinta ya dawo sabo. Don ba ta da karfin hana shi.

Tana ji ya cire mata rigar jikinta sai bra fari da ta saka. wandon Pallazo da ta saka ma ya cire mata shi.

Hawayen baƙin ciki ne ya ke gangaro mata a fuska. Shi ko tsaya wa ya yi yana kallon surar kikinta mai matukar ɗaukar hankali, ga fatarta dake santsi da ƙyalli har ɗaukar idanu take yi. Duk yawace-yawacen da ya yi a ƙasashen duniya, da jikin matan da ya gani bai ga surar da ta ɗauki hankalinsa kamar na ta ba. Gabadaya ya rasa meke damunsa. Ita kam kikinta kara zafi ya yi wanda cikin sauri ya ɗauke ta ya ɗora kam gadonsa. Gabanta ya fadi ta yinkura da niyyar tashi sai ta kasa. Barinta ya yi ya nufi wani corridor sai ga shi ya dawo da bowl da ruwa a ciki sai ƙaramin towel a hannunsa.

Ɗago ta ya yi bayan ya haura saman gadon, bra ɗin ya ɓalle yayin da ta fashe da kukan takaici da bakin ciki. Daga ita sai pant ɗin jikinta kawai ya rage mata.

Ƙirjinta ya zubawa idanu yana kallon su yadda suke tsaye ƙyam kamar za su tsokane masa idanu. Wani abu ya ji ya tsarga masa tun daga tafin ƙafarsa har ƙwaƙwalwarsa, abu ne da bai taɓa jin irinsa ba a rayuwarsa.

Shagala ya yi da kallon ƙirjinta da suka saka shi wani yanayi, don duk ƴan matan da suke kawo masa kansu ba wacce ya ga surarta ya ɗimauta shi lokaci guda kamar na Zahrah.

Sautin kukan ta ya ƙaru ganin yadda ya cire mata kaya yana kallonta. Sai a lokacin ya dawo cikin tunanin da ya shiga. Towel ɗin yake jiƙawa da ruwa idan ya ɗan matse yana shafa mata a jiki, saboda zafin jikin ya ragu.

Babban abinda ya bashi mamaki da ɗore kai yadda jikinta suke a kame, saɓanin macen da ta san namiji. Don idan har mace ana taɓa jikinta dole zai fara sakewa amma ita ga jikinta a kame ƙirjinta ƙyam nipple ɗin ta ma kamar sun ɗan shige babu wata alama da ya nuna cewa namiji ya taba jikinta, da ace ta san namiji ba haka jikinta zai kasance ba ballantana ita da aka ce ta saba zubar da ciki. Tsayayyun ƙirjinta da ya gangaro wajen da towel daidai kan na shanunta ta tsayar da hannunsa yana gogawa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara. Kan nonon na ta da ya ga kamar ya shige ne ya sa yatsunsa biyu ya ɗan janyo su, ƙara ta saki sakamakon zafin da ta ji.

"Me nake gani ne, kuma me ke faruwa ne?"

Ya faɗa a fili cike da mamaki a ƙirjin na ta ya kai kai hannu ya taɓa, nan ma ya sake tabbatar wa kansa sabo ne fil ba alamar an taɓa wasa da su ba su saki ba.

Gabaɗaya kansa ya ɗaure, saboda ya san komai ba sai an faɗa masa ba, sai da ya gama shafa mata ruwan a jiki ya tabbatar zafin jikin ya ragu kafin ya tashi ya bar ta. Ba jimawa ya dawo da farar jallabiyarsa ya zira mata, sai dai har lokacin bai cire mata pant ɗin jikinta ba.

Magani da bottle watar ya ɗauko ya bata. Kallonsa kawai take yi tana hawaye, ganin haka ya saka shi ya ce.

"Za ki sha ko sai na ɗura maki."

Jin haka ta sha maganin sai dai kanta kamar zai fashe a hankali take magana.

"Wayyo Ammina kaina zai fashe."

Ciwon kai mai tsanani take ji kallon pink lips ɗin ta yake yi da take motsawa tana kiran sunan Ammi da Dada tana cewa kanta.

Kallonta yake yi yana mamakin yadda ya ga jikinta, wanda duk macen da take harka da maza harka da maza karya ne a ga jikinta haka, gefe ɗaya yana tuna raunin da ya yi mata na tabon da ya gani da bai gama warkewa ba, ya san dukan da ya yi mata ne.

'To ko dai haka yanayin jikinta yake ne?'


Take sai barci ya ɗauke ta yana kiran sunan Yaa Sadik yana cewa ya zo ya ɗauke ta.


_Dada_

Ganin har awa biyu Zahrah ba ta dawo ba ne ya saka ta kalli Papa ta ce.

"Yarinyar nan fa ba ta dawo ba."

"Wace yarinyar?"

"Zahrah mana, daga ta je ta samu Hilal ko za su yi wani abu kafin tare wa fa shiru."

Ganin bai ce komai ba ya saka ta maimaita maganar na ta.

"Ka yi shiru a kira ta sai ta dawo."

"Ki bar ta mana, ai tana tare da mijinta ne, ko kwana ta yi a wajensa ba laifi ba ne."

"To ai ba ta tare ba."

"Kada ki damu mijinta ne ko kwana ta yi kada ki ce komai."

Ka san fa ba jituwa suke yi ba, ya tsane ta kada ya yi mata wani abun, ni wannan hadin auren da ka yi ina tausayin Zahrah ne yaron nan fa wallahi ni kaina tsoronsa nake yi akan lamarin sa baya son ta fa.

Murmushi Papa ya yi tare da cewa.

"Wannan hadin shi ne daidai za ki gane abinda ya sa na ce haka zuwa gaba, amma na tabbatar daga ranar da aka aura masa ita ba zai iya yi mata abubuwan da yake yi a a baya ba."

"Allah ya sa haka."

Da Amin Papa ya amsa yana murmushi.


Zahrah kuwa barci ne mai mai nauyin ta ɗauke ta ba tare de ta shirya yin barcin ba.

Shi kam kallonta kawai yake yi abubuwa da yawa ne sake a cikin ransa. Ga shi gabaɗaya surar jikinta ne ke masa yawo a cikin idanunsa da ƙwaƙwalwarsa ya kasa sukuni gabaɗaya, wani yanayi ne yake ji a jikinsa wa da bai taɓa jin irinsa ba a rayuwarsa.

Kayanta ya tattare ya kai toilet ya zuba cikin washing machine.

Kayan jikinsa ya cire ya yi wanka sannan ya fito sanye da bathrobe.

Wasu kayan barcin ya saka sannan ya koma can ƙarshen gadon nesa da ita ya kwanta kasancewar tana farkon gadon ne.

Bargo ya ja masu sannan ya rage hasken ɗakin.

Madadin ya yi barci sai ya saka rintsawa, ba abinda yake masa yawo a idanunsa da ƙwaƙwalwarsa sai kyakkyawar surar jikinta.

Awa ɗaya biyu shiru ba barci sai juyi yake yi a cikin bargo.

Yanayin da yake ciki ba zai iya barinsa barci ba.

A zuciyarsa yake cewa.

'Wai keke damuna haka ne, yarinya kamar mayya gabadaya tunda na kalle ta ta sukurkuta ni ta hana ni nutsuwa.'

Tsuki yake ja lokaci zuwa lokaci zuwa lokaci har karshe biyun dare bai runtsa ba, daga karshe ya tashi ya sakarwa kansa ruwa sannan ya doro alwala ya zo ya gabatar da sallah.

Sai ƙarfe huɗun asuba sannan barci ya yi nasarar ɗaukarsa.

Haka ya saka bai farka da ba har ya makara sallar asuba. Ita dama tun da take rashin lafiya magunguna da take sha yake saka ta barci. Don kullum sai Dada ta tayar da ita sallar asuba, amma kafin nan da lokacin sallar ya yi take farkawa. Amma yau ita ma ta makara.

Sai ƙarfe bakwai na safiya suka tashi. Don ita ta farka a hankali ta buɗe idanunta. Ganin ɗakin da take kwance ya saka komai ya dawo mata sabo. Kuka ne sosai ta dake da takaicin abinda ya yi mata, tana ji tana gani ya raba ta da kayan jikinta ya dinga wasa da jikinta da sunan wai yana taimaka wa zafin jikinta. In da Allah ya taimake ta bai cire mata pant ba da ya gama da ita.

Kukan da take yi na ya saka shi ya farka, tashi zaune ya yi yana addu'a.

"What's happen?"

Banza ta yi masa ta mike tana harararsa, abinda ba ta taɓa yi masa ba kenan a rayuwarta. Kallon ta ya sake yi ya tabbatar harararsa take yi, ya cije lips ɗin sa na ƙasa ya yi tare da tashi ya shiga bathroom ganin lokacin sallah ya tafi .

Sauri-sauri ya yi wanka ya fito, closed ɗin sa ya shiga ya shirya cikin ƙanana kaya dai ƙamshin tutarensa yake yi.

Sallah ya tayar yayin da ita kuma ta yinƙura da ƙyar ta tashi, sai a lokacin ta lura da kayan jikinta. Sanin ba za ta iya fita haka ba ne ya saka ta tsaya tana jirsnsa sai cika take tana batsewa.

Bayan ya isar ta kalle shi ta ce.

"Kayana fa?"

Kau da kansa ya yi kafin ya ce.

"Ki ɗauro alwala ki zo ki yi sallah."

Banza ta yi masa, ya ɗauka ba ta ji ba ne, sai ya daga kai ya kalle ta, ga mamakinsa ya ga tana tura baki.

Tsuke fuska ya yi tare da cewa.

"Ba magana nake maki ba ne, kika ce za ki yi mani taurin kai za ki sha wahala ne."

Bathroom ta nufa ta ɗauro alwala ta fito, sai dai ba hijabin da za ta saka. Tsaya wa ta yi tana kallonsa, gane me take nufi ya saka shi cewa.

"Kayan ki sun jiƙe har da hijabin ba na da hijabi anan."

Ciki-ciki ta yi magana tana cewa.

"Dama ai ba za'a samu hijabi ba, tun da karuwanka da kake kawo su ba sa sallah suke yi ba sai iskanci, ni dai wallahi Allah ya isa na abinda ka yi Mani a daren jiya."

Mikewa ya yi tsaye yana mata wani kallo, sai a lokacin ta san cewa ashe Maganar ta ya fito ya ji ta.

"Wa kike yi wa Allah ya isa?"

Shiru ta yi gabanta na tsananta faduwa, don ta san tabbas idan ya rike ta ko bai sumar da ita ba sai ya bar ta kwance.

"Daga na taimaka maki, kin warke har kina da bakin rashin kunya ko, wai ma uban me ya shigo dake ɗakina? Allah ya isa na banza da kofi, ai duk abinda na yi dake daidai ne, domin akwai igiyoyin aurena uku a kanki. Na auren ƙaddarar da aka ɗaura mani, da ba don haka ba kin isa na kalle ki a mace?"

Cikin takaici ta ce mata suna suka tara, ban kai ka kalle ni mace ba, saboda ni ba ballagaza ba ce dake barin kowane jaki da doki su kalli jikina . Ba zan taɓa hada jiki ba, duk da kana mani kallon ƴar iska mai bin maza amma Alhamdulillah sai dai zargi ba wanda ya taɓa ganina tare de wani namiji ya rike ko da ƙumbata ballantana jikina, amma kai na ganka tare da mace a Kaduna kuna romancing ɗin juna babu kaya a jikinta kuna kissing lips ɗin juna, sannan na ganka da wata mace a garden tana zaune a saman cinyarka ban kira ka ɗan iska ba, to kai wata hujjar kake da shi a kaina? Ba zan taɓa hada jiki da kai ba, don ƙyamar hakan nake ji daga gare ka, kuma taba ni da janyo jiya ba zan yafe ba na ji na tsane ka."

Idanunsa ya zuba mata cike da mamakin yarinyar.

"Wato ni kike faɗa wa haka ba, to zan yi maki abinda ya fi na daren jiya mai kankat zan yi maki sai ki yi Allah ya isa da tushe, zan yi maki abinda ban taɓa yi wa wata mace ba, amma ke ina da lasisin hakan daga gare ki, dama abinda ya kawo ki kenan daren jiya saboda ba bakon abu ba ne a wajenki."

Nufo ta yi gadan-gadan wanda hakan ya saka ta nufi kofar fita za ta fice, sai dai ta ga kofar a rufe da key.

Jikinta ya soma rawa tana ja da baya ganin ya nufo ta, tana jikin bango Ya rankwafo saitin fuskarta ta rintse Idanunta.

Abubuwa ne ke daure masa kai da lamarinta, yadda ya ake faɗa da yadda ya ga jikinta daren jiya, tabbas yana cikin duhun kai sai dai baya ƙaunar bin hanyar da zai gano gaskikiyar yadda take

😳 Zaharah Allah ya fitar da ke, idan ya gane cewa ke cikakkiyar buduwarwa ya samu budurcin ki da wane ido zai kalle ki.


*Book 2 na Gabar cikin gida na kudi ne, za ki same shi akan Naira ɗari biyar kacal. Za ku tura kudin ku ta wannan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank, sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 09065327995*
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page6️⃣5️⃣


Abubuwa ne ke ɗaure masa mai da lamarinta. Yadda ake faɗa da yadda ya ga jikinta a daren jiya, tabbas yana cikin duhun kai sai dai baya ƙaunar bin hanyar da zai gano gaskiyar yadda take .

Ƙamshin turarensa ya cika mata hanci, saboda rigarsa da ya saka yanzu ya fesa tutarensa. Ba ta aknkare ba ta ji ya gada jikinsa da na ta ya ce .

"Maimaita abin da kika faɗa."

Tsabar tsoro fitsari ne kawai ba ta yi ba.

Wayarsa ce ta soma ruri wanda jin hakan ya saka ya nufa wajen wayoyinsa, sanin wayar kiran gaggawa ne ya saka ya duba tsadadden agogon hannunsa ya saka.

A hankali ta buɗe idanunta ta ga yana saka takalmi, ajiyar zuciya ta sauke da karfi ganin yana sauri zai fita .

"Don Allah kayana."

"Suna cikin washing machine."

Da sauri ta nufi bathroom ɗin, na ta duba ta ga kayanta da kayan da ya cire ya zuba don dama kowane safe mai mashi wanki yake zuwa yi.

Ciro riga da wandonta ta yi sai hijabi da bra. Duk sun jike, haka ta ɗauko su ta fito.

Idanunta suka sauka akan bindigar da ya soke a ƙugunsa. Ɗauke kai t yi da sauri ta nufi ƙofa, jin ta a rufe ta tuna ta juyo za ga yi magana kenan sai suka kusan cin karo da shi har sai dai gabanta ya fadi ganin yanayin fuskarsa a sauye daga gani bai ras nasaba da kiran waya da aka yi masa.

Buɗe ƙofar ya yi ta fice da sauri tana rungume da kayan da ta cire sannan tana sanye da jallabiyarsa a jikinta.

Addu'a ɗaya ta yi Allah ya sa kada ta hadu da kowa a babban falon gidan.


Takun tafiya da suka ji ne ya saka suka juya suna kallon hanyar matattakalar. Mummy, Daddy, Abba, Umma, Aunty Laila, Mansur, Faisal, Nadiya, Maryam, Kausar, Nabeela. Duk suna falon suna yin breakfast. Sai dai ba Abbi da iyalansa, don dama ba su cika zuwa ba saboda matsalar da ke faruwa, sai an yi masu ba daidai ba, ga Sadik baya iya hakuri duk wanda ya yi wa iyayensa maganar banza sai ya mayar maka da martani duk girmanka kuwa.

Gabaɗaya suka sake baki suna kallon Zahrah dake saukowa daga part ɗin Hilal, ga jallabiyarsa a jinkinta, ga Kayanta a hannu, kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci daga can ta kwana.

Wani malolon bakin ciki ne ya tokare zuciyar Mummy. Aunty Laila ma mamaki ta takiaci ya lulluɓe ta, wanda har ta kasa yin shiru ta saka salatai tana kallon Zahrah. Hakan ya saka hankalin kowa dake wajen ya koma kanta suna kallonta.

Ita kuma sai ta tsargu da kallon da suke mata, don duk wanda ya ganta da Kayanta a hannu ga rigarsa a jikinta zai yi tuninin wani abu.

Wani kallon tsana Aunty Laila da Mummy suke yi mata, yayin da Aunty Laila ta ce.

"Tsabar jaraba da sabawa da maza ya saka daga jin an ɗaura maki aure da mutum kin kwashi jiki kina binsa ɗakinsa don ya yi maki abinda kika saba ko? To burinki ba zai taba cika ba duk harkar kasuwanci kin iya su."

Umma ce ta ce.

"Burinta ba zai taɓa cika ba na nawa kuma? Ai daga ganin ta da kayanta a hannu ga ta sanye da rigarsa ai mai afkuwa ta afku."

Kallon Mummy ta yi kafin kafin ta cigaba da cewa.

"Ke da kike cewa za ki hana shi ya kasance ta kin makara domin mai afkuwa ta afku."

Zahrah da sauri ta nufi part ɗin ta, gaisuwar da ta yi niyyar karasawa ta yi masu ji ta yi ba za ta iya jure jin mugayen kalaman su akanta ba.

"Ai ba laifin kowa b ne laifin Hilal ne, tun da shi ma bai san ciwon kansa ba."

Cewar Mummy cike da takaici.

Aunty Laila ta ce.

"Ai kar ki yi mamakin ba banza ya kula ta ba, uwarta ta koya mata kisisina, idan kika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login