Showing 129001 words to 132000 words out of 154779 words

Chapter 44 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6284

ganin ba Hilal ya saka Papa kiransa a waya ya bashi izinin zuwa.

Ba jimawa ya shigo da sallama. Wuri y samu ya zauna a ƙasa saman Centre Carpet.

Zahrah dake kwance ba lafiya ne kawai ba ta wajen. Ita ma sai da Papa ya ce wa Dada ta taimaka mata ta fito.

Dada ta tashi ta nufi ɗakin Zahrah don taimaka mata ta fito.

Suna zaune ba wanda ya iya cewa komai.

Dada ce ta fito rike da hannun Zahrah wacce kallo ɗaya za ka mata ka san ba ta da lafiya, don tafiya ita kadai ma ta kasa da taimakon Dada suka karaso ta zaunar da ita a ƙasa ita kuma ya zauna kan kujerar dake bayan Zahrah.

Sallama Papa ya yi masu sannan ya kalli kowa dake wajen ɗaya bayan ɗaya. Kafin ya kalli Daddy ya ce.

"Abubakar."

Daddy ya amsa da

"Na'am Papa."

"Akan idanunka na zartar da hukuci akan ƴaƴanka, saboda na san cewa na isa da kai, ba za ka taɓa bijerawa umarnin da na aka ba."

Sannan ya dubi Abba ya ce.

"Adam."

Shi ma Abba ya amsa da

"Na'am Papa."

Kai ma na yanke shawarar da na yanke akan yaran Abubakar wanda na san kai ma ba za ka bani goyon baya akan abinda na saka a gaba."

Duban Abbi ya yi tare da cewa.

"Kai ma haka Salis, na san dama duk hukuncin da na yanke akan ƴaƴanka kai mai biyayya ne."

Duban Aunty Laila ya yi tare da cewa.

"Laila."

"Na'am Papa."

"Ina da iko dake amma ba na da iko akan ƴaƴanki, saboda ubansu ya fi ki iko da su, hakan ya saka na nemi amincewar sa akan shawarar da na yanke akan ƴaƴansa Nabeela da Kusar. Kuma sai ya yi Mani biyayya akan duk abinda na zartar akan ƴaƴan sa shi mai biyayya ne. Don haka na yanke shawarar da nake ganin zai kawo karshen duk wata matsaloli dake cikin wannan zuri'ar."

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonsu daya bayan daya, yayin da matan kirjinsu ke bugawa don suna fargaban jin abinda Papa zai fada.

"Na ɗaura auren Hilal da Zahrah, Mahmud tare da Nabeela, Mansur tare da Maryam, Sadik tare da Nadiya. Faisal tare da Kausar.

Tashin hankali ne ƙarara ya bayyana akan fuskokinsu, Zahrah kam gaba ɗaya ji ta yi numfashinta ya ɗauke. Duhu kawai take gani sai maganar Papa dake mata amsa kuwa a cikin kunnuwanta. Na ɗauka auren Hilal da Zahrah, take ta ji numfashinta ya ɗauke Amminta kuwa mutuwar zaune ta yi. Ga wani abu da ta ji ya tokare mata ƙirji ya mata nauyi, ji ta yi yawan jinta na neman tashi. Sauran jama'ar dake falon matan su Mummy da Umma kuwa ji suka yi kamar an soka masu mashi a zuciyarsu, Aunty Laila kasa haɗiye bacin ranta ta yi ta ɗora hannu akai tana kuka da fadin ta shiga Uku. Tsawar da Papa ya daka mata ne ya saka ta yi shiru .

"Na gama yanke hukunci ba na son jin komai.


*Na kusan kammala book 1 kamar yadda tsarin yake book 2 na kudi ne. Za ku same shi akan Naira ɗari biyar ne kacal 500*

*Da zaran ya zama complete document kuwa kudinsa Naira ɗari bakwai ne*

Za ku tura kudin ku ta wannan account ɗin 2242538358
Zainab Abdullahi U.BA bank
Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z




*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE*



Page6️⃣2️⃣


"Na gama yanke hukunci
ba na son jin komai."

Gabaɗaya suka yi shiru Mummy kam tana cikin mawuyacin hali a wannan yanayin, kamar za ta haɗiye zuciya ta mutu.

"Na san dukkan ku ba ku kammala gidan da kuke gina wa ba, saboda ba ku shirya aure ba ko? Alhamdulillah zan ba kowanne gidan da zai zauna da matarsa ."

Kallon Hilal ya yi wanda tsabar ɓacin rai kamar ya yi Amon wuta ya ce.

"Kai na san ja kammala komai na gidanka, kuma duka gidajen da zan rabar ba su kai na ka gidan ba, amma duk da haka kau ma zan baka kamar yadda ba ba kowa ."

"Ba na bukata."

Ya fada a takaice ba tare de ya kalli Papa ba. Murmushi Papa ya yi dama ya san ba zai taba karba ba, don ya san Hilal ɗin ma ya tara dukiya sosai .

Dada ce ta kalli Hilal ta ce.

"To maganar lefe fa kai da ƴan uwanka, kowa dole ya yi wa matarsa kayan lefe don ba Sadaka aka ba ku ba, ku bar ganin kun same su daga sama. Kakanku ya biya sadaki ya ba ku gida, lefe dole ne ku siyawa matanku da kanku, wannan karon aljihunku ne zai yi bayani, don haka kowanne ya bayar da kuɗin da za'a haɗa lefe, ko kuma na kira Hajiya Amina ƴar Aminin Papa ta zo mu tafi da ku ko ta sanar da ku yawan kufun da za'a kashe sau mu je da ita a hada kayan."

Kallon Hilal ta yi ta ce

"Ya ka ce?"

Ba tare da ya kalle ta b ya ce

"Akwai matar abokina tana kasuwanci zuwa Dubai, za ta hado komai."

"Ma sha Allah, na ka za ta hado daga can kenan."

"Ba nawa kadai ba, ba dukkansu za'a a hado wa na ɗauke masu nauyin."

Ya yi maganar yana kallon ƙannen na sa wanda kalli ɗaya za ka gane suna cikin tashin hankali, idanunsu duk ya ya yi ja.

Dada da Papa ba karamin farin ciki suka yi ba.

Tashi Hilal ya yi ba tare da ya kalli kowa ba, ya fice ransa na masa suya, da kallo suka bi shi kamar baya cikin wata damuwa idan ka kalle shi a zahiri, saboda jarumta da juriya da wuya ka ga rauninsa. Amma a baɗini ba ƙaramin zafi da zugi zuciyarsa ke yi ba.

Papa ne ya lura da Zahrah da ta sandare tana jijjiga. Cikin tashin hankali ya ce.

"Subhanallah Zahrah."

Umminta da Abbi suka karasa kanta. Ummin tana cikin wani hali, don zama ta yi tana dafe kanta dake sara mata kamar zai fashe.

Mummy ta mike tana hada hanya tana ganin duhu ta fita, tana fita zuwa falon gidan ta saki jiki za ta zube a wajen, Hilal dake tsaye ya kasa motsawa ya hango ta, cikin zafin nama ya tare ta hakan ya saka ta faɗa a jikinsa.

Da sauri ya nufi bangarenta da ita cikin tashin hankali.

"Kowa ya tafi kafin anijma zan neme ku."

Papa ya yi magana ganin kowa na cikin tashin hankali. Tashi suka yi kowa ya bar fakon cikin mawuyacin hali. Aka bar Abbi dake fama da Ummi, don Dada da Papa suna kan Zahra, ga Ummi na yi kamar za ta shiɗe ita ma. Abbi ya kira Doctor domin ya zo ya duba su.

Aunty Laila da Umms ikon Allah ne masu ya kai su part ɗin su.

Angwaye tashi da suka yi cikin sanyin Jiki suka bar part ɗin bisa umarnin Papa, duk da Sadik da Mahmud sun so tsayawa saboda halin da Ummi da Zahrah ke ciki, Papa ya ce su tafi.

Nan da nan Doctor ya zo saboda kiran gaggawar da Papa ya yi masa, Abbi ya ɗauki Zahrah ya nufi ɗakinta da ita, ya kwantar akan gado. Taimakon gaggawa Doctor ya shiga ba wa Zahrah, ga zazzabi mai zafi da ya rufe ta lokaci guda.

Dai kuka take tana suratai bayan ta farfaɗo, sai dai dole ta saka Doctor ya yi mata alluran barci, wanda hakan ya saka barci ya yi awon gaba da ita nan take.

Mummy dai shock da ta shiga lokaci guda ne, Hilal ya ajiye ta akan gadonta ya kwantar, ganin halin da take ciki ne ya saka ya ɗauko mata magungunan hawan jininta ya ba ta.

Bayan ya dauko mata robar ruwa daga cikin fridge ya tsiyaya mata ruwan a kofi ta gama shan maganin ta koma ta kwanta. Hawaye ne kawai ke zuba daga cikin Idanunta, kawai ta juya masa baya wanda hakan ya saka ya bar ta ya fice, don ya ga ta ɗan samu Sa'ida.

Shi kansa karfin hali ne kawai yake yi, don zuciyar sa sam ba dad'i, jarumta ce kawai yake da ita wanda ba za ka kalle shi ka gane yana cikin damuwa ba.

Bedroom ɗin sa ya nufa, ba tare da ya cire kayan jikinsa ba ya sakarwa kansa shower 🚿 tsawon mintuna talatin ruwa na zuba a kansa kafin ya cire kayan jikinsa ya yi wanka.

Ya fito ɗaure da farin towel a ƙugunsa. Wayarsa dake saman bedside Drawar ce ta soma ruri.

Bai kalli wayar ba ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskarsa dake ɗaure tamau, ga idanunsa har yanzu sun yi jajir da su.

Wayar ce sake turi ya karasa yana kallon wayar. KB shi ne sunan da ya bayyana akan fuskar wayar.

Ɗaga wayar ya yi tare da karawa a kunnensa ba tare da ya yi magana ba.

"Ango! Ango!! Ango!"

Muryar KB ce ta karade kunnensa yana masa kirari.

"Waye angon?"

"Kai Mallam na san komai fa, Granny ɗi na yake sanar da ni akan idonsa aka daura maku aure, wato ko gayyata babu ko? Haba ai sai ka sanar da ni, ko auren sirri ne ai bai kamata ka boye Mani ba."

"Kai ban san komai ba, ni ma ɗaurin auren kawai na ji tsoron nan ya yi ba tare da izininmu ko amincermu ba."

Dariya KB ya yi tare da cewa.

"Gaskiya wannan tsohon ya kyauta sosai ba kaɗan ba, ya taimaka wa wannan Gwauron Allah ya kara masa lafiya da nisan Kwana."

Hilal dai bai ce komai ba, yana shirin Sallamar sa ya ji Kb yana cewa

"Na ji an ce dukkan ku aka aurar maza da mata, wato ba zai bari bare ya zo ya aure masa zuri'a ba ko, a cikin ku waye mai sa'ar da aka aurawa Fatima Zahrah?"

"Mai sa'a ko kuma mara Sa'a ba, to ni ne wannan mara sa'ar nan da aka aurawa ita. "

"Haba Man me kake cewa haka ne, ai ka godewa Allah da ya saka ba daya daga cikn yaran gidan nan aka aura maka ba, don kaf ba mai tarbiyya da hankali irin na Zahrah. Duk da cewar ba wai wani saninta na yi ba, amma na ji labarin ta a wajen Granny da kuma lokacin da hotunan ta suka dinga yawo a social media da gidajen Tv da..."

"Dalla kar ka dame ni da yawan magana, ka bar ni na ji da halin da nake ciki."

Yana fadar haka zai katse kiran wayar ya ji Kb ya ce.

"Please minti ɗaya."

Hilal cije leɓensa na ƙasa ya yi yana cewa .

"Meye?"

"Tambayar ka zan yi don Allah ka bani amsa ta gaskiya."

"Waye kai da zan yi maka ƙarya, kai ma ka san ba na faɗin karya ko na taba yi maka ne?"

"A'a, dan Allah ya ake ciki ne, ka san mune abokan na ka ya kamata mu san halin da ake ciki, akwai wani shirye-shirye da za'ayi ne?"

"Babu."

"Ba wani reception ko dinner da za'ayi ne?"

"KB ka bar ni ko za'ayi ni ba abinda zan yi, sannan kuma kar ka sake..."

Dakatar da shi KB ya yi ta hanyar cewa.

"Wait tunda ba na shiri ba ne amma na san lefe dole za ku yi masu ai."

Cikin ƙosawa Hilal ya ce.

"Ka fadawa matarka ta haɗa masu kayan lefe kowacce ta miliyan biyar."

"Dukakkan su matan biyar za'a haɗawa lefen, kowanne ango ka ɗauke masa kenan?"

"Eh ita abinda zan iya yi masu kenan, idan an gama wanda ya ga zU karawa matarsa sai ya kara mata."

"Ka kyauta babban Yaya, amma gaskiya Zahrah kam ta fi ƙarfin ka haɗa mata lefen miliyan biyar, su sauran dai za'a haɗa masu na miliyan biyar din da ka ce su hudu amma Zahrah sai dai na miliyan goma za'a haɗa mata."

KB ya faɗa masa cin n tabbatar wa.

"Saboda ita ƴar Gold ce ko, ai ba ta fi su ba, don haka zan ba ka 25 million kowace 5 million."

Yana fadar haka ya katse kiran wayarsa tare da ajiye wayar.


_Sadik_

Ko da ya karasa zuwa part ɗin sa shi da Yaa Mahmud ba wanda ya iya yin magana, don sun bar Abbi da Ummi a part ɗin Dada.

Sadik ya kalli Yaa Mahmud ya ce.

"Ya wallahi a cikin wannan al'amari ba wanda nake tausaya wa sai Zahrah."

Mahmud ya kalle shi tare da cewa.

"Kai ma kanka abin tausayi ne, don na tabbata da sai mun ji jiki a wajen yaran nan, don tarbiyya ba ta ishe su ba."

Dariya Sadik ya yi tare da cewa.

"Wallahi a duniyar nan ba macen da zan ji jiki a hannun ta, sai dai ta ji jiki a hannuna, don wallahi ita ce abin tausayi ba ni ba ."

Mahmud kallon Sadik ya yi don ya san waye Sadik, karye ne wani ya taka sa ballantana macen da aka aura masa, sai dai dukkannin su za su ji jiki idan ba ta kwantar da kai ba.

Bedroom ɗin sa ya nufa ba tare da ya sake yin magana ba.


_Mansur_

Ko da ya shiga part ɗin su ya tarar da Abba da Umma suna a falo kowa ya yi jigum cikin damuwa .

A fusace Sadik ya ce.

"Wallahi ban yarda da wanan auren ba ta ya ya za'a aura mani wata da ban ce ina son ta ba, sanann wani karin abun takaicin ma wai Nadiya ƙanwata ce za'a aurawa Sadik , yaron da sam baya da mutunci. Na tsane shi daga shi har ƙanwar ta sa Zabarah na tsane su, don da a ce ni aka bawa auren Zahrah sai dai wata rana aji labarin mutuwarta. Sai sai ko Yaa Hilal ɗin ma ba baya ba, na san sai ta ɗanɗani kuɗarta kafin mutuwarta. Ita kuma Nadiya na san haryar da zan ɗora ta, ina take ne?"

"Da kyau."

Cewar Umma cikin damuwa.


_Faisal_

Bayan fitar Hilal daga wajan mahaifiyarsu shi ne ya shiga ɗakin na ta bakinsa da sallama.

"Ni wallahi duk cikin dalilin nan ba wanda aka cuta sama da ni, a rasa wanda za'a aura Mani sai Kausar ɗin Aunty Laila, yarinyar da ta fi kowace yarinya rashin tarbiyya, Aunty Laila fa aka ce ƙarshen masifa da bala'i wallahi Papa ka cuce ni."

Dad da shigowar sa kenan ya ce.

"Faisal dama ba ka da kunya kai ma, ƙanwar ta wa ce masifa da bala'i?"

Faisal bai sake magana ba ya fice, yayin da Daddy ya nufi Mummy dake kwance tana jin su ta kasa magana.


_Hilal_

Hilal bayan ta kammala saka kaya ya shirya cikin ƙananan kaya sai ya ji knocking.

Bai bada izinin shigowa ba ya fa KB ya shigo yana murmushi.

"Dama ina kusa da ku shi ne na karaso don gobe matata za ta je Dubai na ji ka yi maganar lefen shi ne na tuna na zo ka bayar da kuɗin."

Ya yi maganar yana zama kan sofa.

Sanin halinsa na tsokana ya sa Hilal ba i ɓata lokaci ba ya shiga cikin bedroom ɗin sa, don ya sallame shi

Bayan mintuna sai ga shi ya fito rike da wayarsa.

"Nawa account ɗin ka ke ɗauka?"

"Mallam idan za ka tura Mani kudi ka tura Mani, ka ɗauka karamin account ne da ni?"

Danne-danne ya yi a wayarsa ya sannan ya ajiye, take alert ya shigo account ɗin KB.

Kallonsa ya yi tare da cewa.

"Na ga ka tura Mani miliyan asirin da biyar, talatin za ka tura, don na Zahrah kayan miliyan goma za'a haɗa mata, sauran miliyan biyar-biyar."

"Mallam abinda zan iya kenan, ko ƙwandala ba zan kara ba, ai ba fin su ta yi ba."

"Wallahi tafi su, ko a ilimi da tarbiyya ga kyawun..."

Kallon da Hilal ya masa ya saka ya kasa karasa wa, amma ya share tare da cewa.

"Mallam dole sai ka cika 5 million ɗin nan."

Bai ce masa komai ba, ya nufi kofar da za ta sada shi da garden ɗin gidan. KB na masa magana ya share shi.



_Asadullah_

Fitowa ya yi daga cikin gidan, sanye da riga mai hula, ya janyo hular ta rufe masa rabin fuskarsa. Ya sanya bakin glass a idanunsa. yya nufi parking space, ɗaya daga cikin motocin dake wajen ya bude wata bakar motar ya buɗe ya shiga, wanda ba wanda zai iya ganinsa sai dai shi ya kalli mutum.

Horn ya yi maigadi ya bude masa gate ya fice da motar.

Kai tsaye shopping mail ya nufa. Abakin wajen ya yi parking motarsa ba tare da ya fito ba, wayarsa ya ɗauka yana danne-danne, da wayarsa ya yi siyayyan da zai yi ya tura masu kudin ta wayarsa, sai ga ma'ikatan wajen sun fito rike da ledoji suka saka masa a bayan motar.

Bayan sun gama saka wa ya ja motarsa ya bar wajen.

Ja tsaye airport ya nufa da kansa.

Daga nesa ya hango su suna fitowa daga airport ɗin.

Kallonta yake yi ta cikin bakin glass dake kan fuskarsa.

Sanye take cikin jallabiya baƙa ta yi kyau kuma ta kara haske.

Har wajen motar suka karaso kasancewar Doctor Isma'il ya sanar wa Anisa da Asad yana jiran su.

Anisa da Doctor Isma'il na rike da kaya yayin da Jidderh kuma tana rike da hannun Anisa ɗaya

Doctor Isma'il ya saka kayan a bayan motar, sannan ya zagaya zai shiga gefen mai zaman banza, Asadullah ya masa nuni da Jidderh, don Doctor Isma'il murmushi ya yi tare da cewa Jidderh ta shiga.

Ba musu ta shiga ta zauna, shi da Anisa suka shiga baya.

Kallon Jidderh ya yi tare da janye hularas baya, ya cire bakin glass ɗin ya saka . Kamilalliyar fuskarsa kai cike da haiba ta bayyana. Sanyayyar murmushinsa ya sakar mata.



*Masu sha'awar karanta book 2 za su tura kuɗinsu Naira ɗari biyar ₦500 ta wannan account ɗin. 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wannan lambar waya 09065327995*
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z






*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE*

Page6️⃣3️⃣


Kallon Jidderh ya yi tare da janye hularas ya ya cire bakin glass ɗin da ya saka. Kamilalliyar fuskarsa mai cike da haiba ta bayyana. Sanyayyar murmushinsa ya sakar mata.


Tayar da motar ya yi suka bar wajen. Suna cikin tafiya ya ji muryar Anisa tana gaishe shi.

"Ina wuni Yallaɓai?"

"Lafiya lau fatan kun iso lafiya?"

"Lafiya lau, na ga ba ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login