Showing 111001 words to 114000 words out of 154779 words
ce anan, ai ba wanda zai kalli wannan ya ce ba ta da lafiya ai ma ta fi ku lafiyar gaskiya."
Dariya suka yi suka fito daga cikin ɗakin, kai tsaye suka nufi wajen ajiye motoci.
dama Modibbo shi kaɗai ya zo da direbansa. Didi suka zo da motar Hajiya Bilkisu, yanzu sai Didi ta bi mijinta don Hajiya Bilkisu ta ce za ta bi su Zahrah gida. Don haka ita da Amala ne suka shiga motar sai Zahrah da Ummi suka shigo motar Hajiya Bilkisu. Ummi na gefen ƴar uwarta yayin da Amal da Zahra ke bayan motar. Dada da Papa ma tuni sun shiga Direbansu ya ja su Mahmud, Sadik, Khalil kowa ya shiga motarsa shi kadai suka bar Wajen. Khalil ma bin bayansu ya yi don zuwa gidan yar mahaifiyarsa.
Motocin guda biyar suka jeru a bakin gate suna danna horn, security ya leƙo jin horn daban-daban. Ganin su jere ya saka ya wangale masu gate ɗin suka shiga.
A parking space suka yi parking dukkansu.
Aunty Laila da sauran mutanen gidan da suke falo ne suka tashi kowa ta nufi part ɗin ta. Don sun san idan suka zauna wajen Papa ya zo ya dame su sai ya wanke su tas.
Bayan kowa ya fito daga cikin motar ne Dada da Papa suka yi gaba daga nan sauran suka take masu baya.
Part ɗin su suka nufa su dukansu yayin da su na su Hajiya Bilkisu suka bi bayan su.
A falon Ummin suka zauna su duka, dai dai Abbi da ya nufi bedroom ɗin sa.
Ummi ta shiga kitchen ta jido masu meet pie cake pizza duk ta jido a manyan farantai. Sai lemuka da ruwa mai sanyi.
Nan suka hau ci suna fira, sai dai duk ɗaya idanun da za ta daga kai sai ta kama Kamal yana kallonta . Kuma sai ya sakar mata sanyayyar murmushinsa wanda ta zame masa ɗabi'a.
Hakan ya saka ta kasa sakin jiki ta nufi bedroom ɗin ta, Amal ma ta bi bayanta bayan ta dauki meet pie da lemu a hannu ta bi bayanta.
*AMERICA/ NEW YORK CITY*
Motocin sojojin ne suka dumfaro gidan na Hilal. Motarsa ce a tsakiyarsu.
Can ya hango Sury na zaune ta haɗa tagaumi da alama tana jin tsoron ta shiga irin n ranar ya sake wulakanta ya kote t kamar yadda ya mata last time.
Murmushn gefen baki ya sake daidai lokacin da suka hada idanu. Alama ya mata da ta shigo.
Bayan motocin sun taya ne aka bude mata shi ma ya fito. Daidai lokacin da ita ma take shigowa .
Da hannu ya mata alamar da ta zo gare shi .
Da sauri take tafiya don shi din digo ne kuma komai cikin zafin Nana yake yinsa.
James na ajiye masa wasu file a falo ya fito yayin da Hilal ke jiran ƙarasowarta.
Tana ƙarasowa ta fada jikinsa tana kuka.jan ta ya yi zuwa falon.
Yana zaune a kujera da dukkan alamu a gajiye yake sosai, yayin da Sury ke sake shige masa jin take yi.
"Ina wuni?'"
Ta fada tana kallon zara-zaran yatsun hannunsa ya take masa wasa da su.
"Kina lafiya ?"
Ya faɗa idanunsa a lumshe, don kwana biyun nan a gajiye yake dawowa sakama aiki da ya masu yawa. Yanzu haka daga wani daji suke.
"Na hada maka ruwan wanka ne?"
Kai kawai gyafa mata alamar eh
Da rawar jiki ta tashi ta je ta haɗa masa ruwan wanka nai dan ɗumi.
Tashi ya yi ya nufi bathroom ɗin sa. Zama ya yi a bakin gado tana tsaye ta ce.
"Ko na taya ka rage kayan jininka ne?'
"Ki bar shi na gode.'
Ba haka ta so ba sai dai ba yadda za ta yi."
"Ki koma falo idan na fito zan zo na same ki ."
Tura baki ta yi don ita ba ya ga ranar da burin ta zai cika akan Hilal ba, amma da sannu akuya take shiga gidan kura har ta ci ta da yaƙi.
Fita ta yi daga cikin ɗakin ta bashi wuri kamar yadda ya ce.
Kayan jikinta ya rage sannan ya shiga wanka.
Ya kwashe kusan mintuna talatin yana yin wanka kafin ya fito sanye da bathrobe a jikinsa.
Sury kam tana falo tana jiran fitowarsa.
Loka-lokaci take sakin murmushi ita kaɗai. Har ya fito sanye da ƙananan kaya a jikinsa. Ƙaramar riga da kuma wando Three quarter.
Kitchen ya shiga ya fito dauke da wani biscuit da lemu. Zama ya yi kusa da ita ya fara ci. Ita ma ta saka hannu kasancewar biscuit ɗin babba ne a cikin gwangwani a tare suka ci biscuit ɗin suka sha lemun.
Da misalin karfe goma na dare ya goma na dare ya gama shirin kwanciya don yau baya jin zai iya wani aiki kafin ya kwanta .
Sury ce ta shigo ɗakin da sallama ya amsa mata, wani irin turare t shafa a jikinta wanda tun ya ji kamshin sa dai da ta haifar masa da kasala.
Lumshe udanu ya yi tare da sakin ajiyar zuciya sakamakon kamshin ya masa daɗi, dama shi mutum ne mai son jin ƙamshi shi ya sa kullum yana cikin ƙamshi.
Zama ta yi bakin gadon tana sakar masa murmushi, yana kishingide yana kallonta .
Da hannu ya mata alama, gane me yake nufi ya saka ta haurawa saman gadon ta faɗa jikinsa.
Wani remote ya danna hasken ɗalin ya ɗauke, cikin farin ciki ta ƙanƙame Hilal tana addu'a Allah ya sa kada ya yi mata abun da ya saba yi wa sauran mata da ta ji suna faɗa. Sai ya kai su ƙololuwar bukatar kasancewa da shi sai ya tashi ya bar su ba tare da ya biya masu bukata ba.
Hakan ya saka ta sa aka kawo mata wannan turaren akan cewa ina dai har ya shaki kamshin turaren dole sai ya yi sex da ita duk taurin kansa kuwa. Sai ta tsinci kanta cikin farin ciki don ta ji yadda turaren ya ji rasiri akan sa har yana sakin ajiyar zuciya.
Dama babu riga a jikinsa wando ne Three quarter ya sake sa wani. Janyo ta ya yi cikin bargon
Yamutse fuska ya tare da yi mata alama da ta cire rigar jikinta. Cikin azama ta cire rigar dama ba ta saka bra ba, pant ɗin ma ta cire shi.
Bakinsu ya haɗe waje guda suna sumbatar juna.
Kamar dai kullum yau ma haka ne, sai da ya gama sarrafa ta son ransa ya taba duk in da yake so ya shafa duk in da yake so amma bai yi gigin yin sex da ita ba kuma bai da niyya.
Ganin take-takensa kuma an fada mata in dai ya shaƙi kamshin turaren nan duk abinda take so shi zai mata ne ya saka ta kai hannu zuwa wandonsa da niyyar cire wa.
Tsawar da ya daka mata ne ya saka ta firgita tare da ƙanƙame shi.
Kamar za ta yi kuka ta fara magana.
Babu wani wajen da ba ka sani a jikina ko ka taɓa ba, to akan me kai ba za'a ga jikinka ko a taba kamar yadda kake yi wa matayen da kake mu'amala da su?"
Haka tsarina yake kuma kowace macen da ta sanni a haka ta san ɗabi'ata, babu macen da zan iya sex da ita sai dai idan na tabbatar da cewa akwai igiyar aurenta a kaina, lalacewar ta wa bai kai da zan iya shiga gonar da ba ta wa ba na yi ban ruwa, amma matukar gona ta ce zan shiga na yi ban ruwa har na samar da yabanya mai kyau. Ba ke kaɗai ba ce kuna da yawa kuma kin san wasu da nake harka da su za ki iya tambaya ko akwai wacce na taɓa yin amfani da ita. "
"To ai idan za ka sha giya ka sha ta dubu, tun fa ka iya romancing ɗin mace ka iya kissing Higgins da mace shi halal ka aikata da kake tsoron zina su Meye kake yi?"
"Ke tashi ki fita kafin na sauya maki kamanni!"
Ya faɗa a zafafe ba shiri ta mayar da kayan jikinta ta fice daga ɗakin.
Sai ƙarfe tara na dare sannan Hajiya Bilkisu da yaranta suka shirya don komawa gida. Don tare suka yi girki da Ummi Khalil kuwa tare da Sadik da Mahmud suka tafi masallaci.
Da za su tafi Khalil ya so keɓewa da Zahrah bai samu damar hakan ba, don haka ya ɗauki wayar da ya gani akan kujerar wanda ya ke da tabbacin na Zahrah ne, dubawa ya yi ba password take ya saka lambar wayarsa ya kira. Sai da ya ji kiran ya shigo wayarsa ya ajiye.
Ganin kowa ya zuba masa idanu ne ya faske tare da cewa.
"Akwai maganin da zan kawo mata ne shi ya sa na ɗauki lambar idan zan kawo sai na sanar da ita"
"Yes Doctor."
Amal ta yi maganar tana sara masa.
Dariya Sadik da Mahmud suka yi don su kadai ne a wajen Ummi da ƙanwarta suna cikin ɗaki suna magana.
A tare suka fito daga cikin ɗakin tana sauri ganin kiran mijinta na shigowa wayar.
Har parking space suka taka su sai da suka ga wucewarsu suka koma ciki.
_Sulaiman_
Yana magana da Dad wayarsa ta yi ruri. Ganin Asadullah ne ya saka bai ɗaga a gaban Dad ba. Magana suke yi akan Asad don Dad ya damu da rashin sanin halin da yake ciki, ga ramar da ya ys yi . Dad yana cikin damuwa sosai sai dai yanayin da ya ga Sulaiman a ciki ya saka shi cikin wani tunanin.
A baya idan ya ga Sulaiman yana hango tsantsan damuwa da tashin hankali, sabanin yanzu da yake ganin kamar bai damu da rashin uban gidan na sa ba. Dole akwai wani abu a ƙasa.
Bayan ya sallama Sulaiman ne ya koma ciki yayin da Sulaiman ɗin ya fito daga falon Dad ɗin.
A can bakin gate kuwa hayaniya ce ta kaure a tsakanin Isah Yayan Jidderh da security. Ya zo ne saboda ya sake jin ko an samu labarin ta, security suka hana shi shigowa shi kuma ya dage sai ya shigo.
Sulaiman na sauri don zuwa gidan Asadullah kenan ya ji hayaniya.
A can bakin gate kuwa Isah ne yake yi wa security magiya akan su bar shi ya shiga ciki karo na karshe kenan.
"Don Allah daga yau ba zan sake dawowa ban nan ba, zan so na yi magana da..."
"Kai wallahi ba zan bari ka shiga ba, wani irin bakin naci ne da kai, idan mutum ya ɓata ai police station za ka je ko gidan rediyo ba nan ba."
Dole isah ya hakura ya goge ƙwallar da ta cika masa idanu ya juya zuwa wajen babur ɗin da ya kawo shi. Wato abokinsa tun safe suna ta yawon nemanta.
Yana hawa babur ɗin daidai lokacin Sulaiman ya fito hannunsa rike da waya ya kara a kunnensa, suka haɗa idanu da Isah daidai lokacin da babur ɗin ke shirin barin wajen.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page5️⃣4️⃣
Yana hawa babur daidai lokacin Sulaiman ya fito hannunsa rike da waya ya kara a kunnensa, suka haɗa idanu da Isah daidai lokacin da babur ɗin ke shirin barin wajen.
Kallon ɗaya daga cikin security ɗin ya yi sannan ya ce.
"Hayaniyar ne nake ji?"
"Wasu mahaukata ne suke neman kawo mana shirme a nan, idan mutum ya fadi a police station amma sun damu mutane da hayaniya anan."
"Wani ne ya ɓata?"
Cewar Sulaiman yana tsare securityn da idanu.
"Wai wata ce da take aiki a gidan nan suka nema suka rasa?"
A kiɗime Sulaiman ya tambaya security ɗin.
"Wai tun ranar da aka yi gobarar nan aka..."
Kafin security ya karasa fada masa tuni Sulaiman ya bi hanyar da ya ga sun bi da babur ɗin a guje.
Security da suke waje suka saki baki suna kallonsa cike da mamaki.
Ganin ba alamar su ya saka ya dawo da sauri yana cewa security su bude masa kofar gate ɗin da sauri.
Da gudu ya nufi parking space ya shiga daya daga cikin motocin da ke wajan ya saka makullin ya yi mata key ya fige ta.
Zuwa lokacin har an wangale masu gate a guje ya bar wajen suka mamakin rikicewar da ya yi lokaci ɗaya .
_Washegari_
Jirginsu na sauka a filin jirgin sama, tun daga nesa suka hango kakan na su da direban na sa, fuskarsa dauke da murmushi yayin da shi ma murmushin take sakar masa. Ita ma murmushin take yi.
Kowa na rike da madaidaicin jakarsu.
Direban Kakan na su ne ya karbi jakarsu ya saka a bayan motar .
Rungume tattijon Ammar ta yi ita ma Humaira ta rungume shi ta baya.
Farin ciki ne ya daka idanun Dattijon ciki da ƙealla, cike da son jikokin na sa ya ke saka masu albarka. Don Allah ya sani yana son kusanci da iyalinsa, sai dai ɗan na sa wato mahaifin su Ammar ya nisanta kansa da gida. Sai shekara yake zuwa da iyalansa. Sai dai wani lokaci ya kan ga Ammar ya zo shi ma dalilin abotarsu da Hilal ne idan ya kawo masa ziyara. Saboda Hilal yakan shigo ko na lokacin ziyara da suka saba zuwa .
ba.
Yanzu kuma dalilin zuwan na su saboda Zahrah ce, tun da aka fada masa ba ta da lafiya ta kwanta asibiti shi kenan hanakilinsa ya tashi ya ce dai ya zo ya ga halin da take ciki.
Lokacin da ya kira wayar da niyyar ya haɗa Zahrah da ƙanwarsa Humaira don su gaisa ne dai Dada ta ɗauka take sanar da shi rashin da Zahrah ke fama da shi .
"Ba shi kaɗai ya shiga tashin hankalin ba Humaira da yake tare da ita a lokacin ta shiga damuwa sosai ba kaɗan ba. Don haka da ya ce zai zo da ta ce za ta biyo shi, iyayen sun ɗauka cewa za su zo saboda kakanninsu ne amma su kam sun san dalilin zuwansu ba don ziyara ga kakanninsu suka zo ba.
Shi ma Baba Alhaji wato Kakansu ya ɗauka sun zo don su sada zumunta ne, shi ya sa har ƙwallar farin ciki ya yi .
Mota suka shiga Direban ya ja don kai su gida.
Ko da suka isa gidan Kakansu mace wato Hajiya Mama ta yi farin cikin ganin jikokin na ta.
Farin ciki sosai ya cika gidan. Sail da suka yi wanka suka ci abinci ne sai suka ce za su fita
Mutanen gidan sun yi mamakin jin cewa za su fita, sai ya sanar da su gidan Aninin na sa zai je. Ba su da wani zaɓi suka bar su.
Ɗaya daga cikin motocin ya ɗauki key ɗin, sannan ya basu tsarabar su bayan ya ce wa Humaira ta kai na Zahrah mota.
Bayan ya ji wa motar key ne ya danna horn maigadi ya wangale masu gate ɗin suka bar gidan.
Suna ta fira duk yana bata labari akan Zaheah har suka karasa gidan.
A parking space ya yi parking ba tare da ya fito ba. Kallonsa Humaira ta yi tare da cewa.
"Lafiya kuwa Yaya?"
"Ina tunanin yadda zan shiga gidan ne da sunan wajen Zahrah na zo, ai ba baki labarin irin zaman da suke yi a cikin gidan nan. Ta ya ya xan kalli iyayen abokina bayan na san ba jituwa a tsakanin su da su Zahrah. Wancan zuwan na ga kallon da suke yi wa Zahrah."
Taɓe baki ta yi sannan ta ce.
"Kada ka damu Yaya ka share su ka yi abinda da ya kawo ka."
Wayarsa ya ɗauka sannan ta lalubo lambar Zahrah, tana ganin kiransa da ɗauka da sauri ganin lambarsa ta Nigeria ce
"Assalamu alaikum Ya Ammar ka zo ne?"
Mumrmushi ya yi sannan ya ce.
"Ina mota har da ƙanwata ki fito ki same mu a parking space."
"Okay"
Ta fada ta kashe wayar sannan ta kalli Dada dake kallonta. Don su biyu ne a falon Dada .
"Wai Yaa Ammar ne ya zo da ƙanwarsa suna parking space wai na je."
"To jeki amma ki tabbatar iyakar ki wajen kada ki fita daga cikin gidan nan."
"In sha Allahu."
Ta saka hijabinta har ƙasa sannan ta saka flat shoe ɗinta ta fita .
Mutanen gidan kuwa suna fakon gidan suna fira, don gabaɗaya sun hallara idan aka cire ƴan part ɗin su Zahrah. Maza da mata iyaye da yara, har da iyayen maza suna cikinsu sau fira suke yi cike da nishaɗi.
Zahrah ta zo ta wuce su ta nufi hanyar fita.
Tun daga nesa suke hango ta tana karasawa in da suke cikin takunta na nutsuwa.
"Wow"
Humaira ta furta tana murmushi.
"Gaskiya Yaya Zahrah hadaddiya ce, wannan tsantsar kyau haka?"
Mumrmushi kawai yake yi idanunsa na ga Zahrah.
"Ba iya kyau kawai take da shi ba, tana da kyawun zuciya da halayya masu kyau, Zahrah nagartacciyar mace ce wacce ko wane namijin da ya san kansa zai yi kokari mallakar ta a matsayin mahadin rayuwarsa uwar ƴaƴansa."
Gakskiya ka yi sauri ka aure ta kada ka tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi maka kafa. Ba namijin da zai ganta ya kaida kai."
Haka ne, shi ya sa kullum take sanya niƙab ko Facemask idan za ta fita waje."
Daidai lokacin ta karaso bakinta ɗauke da sallama cikin zazzaƙar muryarta.
Amsa mata suka yi s tare suka fito daga motar.
"Yaa Ammar sannu da zuwa ."
"Yauwa Sanni sarauniyar mata, kin warke ma ko?"
Ya faɗa yana mata murmushi.
"Tare da ita kuka zo tun daga London ne?"
"Eh wai za ta zo ta duba jininki."
"Sannu da zuwa ƴar uwa, ya hanya?"
Ta faɗa tana murmushi, rike hannun juna suka yi suka shiga daga cikin gidan.
A falon gidan suka yi sallama dukkansu, gabaɗaya suka juyo suna kallonsu. Humaira ta sunkuya cikin girmamawa ta gaida mutanen gidan. Ganin ta da Zahrah ya saka ba wanda ya amsa, sai dai Mommy da Aunty Laila suna mata kallon sani, sai dai sun rasa ina suka san ta.
Jan hannunta Zahrah ta yi suka nufi part ɗin Dada, da sallama Dada ta amsa masu cike da fara'a.
Nan Humaira ta gaishe ta ta amsa mata cikin sakin fuska da walwala.
Sallamarsa ne ya saka suka amsa suna kallonsa.
"Yaa Ammar."
Da mamaki kowa ke kallonsa, ganin cewa bai taba zuwa idan Hilal baya nan ba, duk zuwansa sai Hilal na ƙasar yake zuwa.
"Ammar saukar yaushe a ƙasar?"
"Yau na zo."
Da fara'a kowa ya tarbe shi ya zauna suka gaisa da kowa.
"Ga shi abokin na ka baya ƙasar."
Cewar Mummy.
"Eh wajen Zahrah na zo."
"Wajen Zahrah?"
Suka haɗa baki kusan dukkansu wajen furta