Showing 120001 words to 123000 words out of 154779 words
da safe kin bar gidan nan."
"To na ji ni dai ka kaini na huta na gaji."
"Ta yi magana tana mikewa tsaye, sai kuma ta yi saurin dawowa ta zauna a saman cinyarsa. Ta kwantar da kai a ƙirjinsa.
"Ke Meye haka kuma?"
Na gaji ba na jin daɗi ga jikina ya yi zafi sosai.
Da mamaki ya kai hannu wuyanta ya taɓa don tabbatar da abinda take faɗa. Zahrah da ta hangi tsutsuwar da take so ta hanyar fita garden ɗin sai ta saita Camera lokacin da take fitowa dan ta dauki tsuntsuwar, sai dai kash tsuntsuwar ta tashi ko da ta ɗauka ba tsunsuwar daidai za ta dauka ta tashi sama , a rashin sani sai ta dauki hoton Hilal wanda Sury ke zaune a saman cinyarsa, shi kuma yana taba wuyanta don tabbatar da zafin jikin da ta ce masa, wanda ɗora hannun sai ya yi kamar ya rungume ta ne, Daidai lokacin Zahrah ta ɗauke su hoto ba ta ma lura da suna wajen ba, Idanunta na kan tsuntsuwar da ta tashi sama da ba ta samu damar ɗaukar ta photon ba.
Da sauri ta fita don ko za ta hango ta sam ba ta lura da su Hilal ba, amma shi ya ganta lokacin da take fita hannunta rike da wata ƙaramar Camera wacce Abbi ya siyo mata a Saudiyya.
Ko da ta fita ba tsutsuwar Don haka ta koma don ta nuna wa su Dada .
Jin jikin Sury ba zafi ya sa hila cewa
"Ke tashi mun ko ranki ya ɓaci yanzu , Ni za ki rena wa hankali?"
Ganin ba wasa a fuskarsa ya saka ta mike tsaye.
Yana gaba tana binsa baya har suka shiga kofar part ɗin sa.
Zabarah na shiga part ɗin Dada ba kowa. Sai ta nufi bedroom ɗin ta shiga da sallama. Dada da ta gama saka kaya kenan ta kalli Zahrah ta ce.
"Ina kika shiga ne tun ɗazu ina nemanki."
"Na je garden wajen abokaina ne."
Dada ta zauna bakin gadon ta ce.
"Fatan suna lafiya ko?"
"Eh bari ki gan su."
Ta mikawa Dada Camerar yayin da Dada ta shiga rana kallon hotunan da Zahrah ta ɗauka ɗaya bayan ɗaya .
Zuciyarta ce ta tsaya cak dadai lokacin da ta ga photon Hilal ɗauke da wata mace a saman cinyarsa ya sakala hannu a wuyanta, duk wanda ya ga photon zai yi tuninin cewa rungeme ta ya yi . Kallon Zaharah ta yi kafin ta ce.
"Yayanku Hilal ya dawo ne?"
Shiru Zaheah ta yi kafin ta ce .
",Ban sani ba Dada, to ni Meye hadina da shi ne wai, wallahi gara ya yi zamansa a can US ɗin baƙin mugu idan ya dawo ta cigaba da zalintar mutane, ya zauna can har Mahadi ya bayyana."
Dada hankalin ta baya kan Zahrah mikewa ta yi ta nufi hanyar fita, ganin haka ya saka Zahrah ta ce.
"Ina za ki kai mani camera ne?"
"Zan nuna wa Kakanku abokanku ne."
Jin haka ya saka Zahrah ta yi shiru ta koma falon ta zauna.
_Hilal_
Yana na komawa part ɗin sa tare da Sury ta dame shi yunwa take ji. Dan haka ya sauko daga stairs ɗin ya nufu kitchen ɗin don ya san ba za'a rasa ma'iakata a ciki ba, sai kuma ya fasa ya nufi part ɗin Dada don shi ma yunwa yake ji kuma baya cin abincin masu aiki.
Don haka ya nufi part ɗin Dada. Zahrah na zaune a falo ta tura kofar ya yi sallama can ƙasan maƙoshinsa. Ba ta ji shi ba sai dai ƙamshin turarensa da ta ji ne ta haddasa mata faduwar gaba wanda ba ta san dalili ba.
Juyawa ta yi suka yi ido biyu ya watsa mata harara, da sauri ta ɗauke idanunta daga kallonsa. Duk da ta san ba amsa mata Gaisuwa yake yi ba amma sau ta bude baki ta ce.
"Yaa Hilal Barka da dawowa."
Kamar bai ji ta ba dama ta san hakan za ta faru don haka ba ta damuwa da rashin amsa gausuwarta da bai taba yi ba.
Ɗakin Dada ta shiga ya ga bata ciki a tunaninsa unguwa ta tafi, sam bai yi tunanin Papa na gidan ba, don baya zama gidan haka kawai.
Kitchen ya shiga don neman abinci, ya san cewa da ace ya sanar wa Dada daowarsa da ta aika masa da abinci har part ɗin sa.
Dada na shiga ɗakin Papa ta same shi yana shirin fita. Ganin yanayin da take ciki ne ya saka shi cewa
"Lafiya kuwa?"
"Ka zauna ka gani."
Ba musu tsohon ya zauna yana kallon matar ta sa.
Camerar ta mika masa ya karɓa yana duba wa. Wani abu ya ji ya tsaya masa a ƙahon zuciya,
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un."
Shine kalmar da ya maimaita har sau uku a zuciyarsa.
"Yaushe aka ɗauki wannan hoton, kuma wannan kamar Camerar Zaharah ko?"
"Yau ne ta dauke su ba tare da ta sani ba ita ma."
"Yaushe ya dawo daga US ɗin ?"
"Ina wanka na ji shigowarsa amma sai na ɗauka kunnena ne ya jiyo mani ba daidai ba. ashe shi ɗin ne."
Jikin Papa ne ya yi sanyi yanzu har an kai matakin da daya daga cikin jikokinsa zai kawo masa mace har cikin gidan nan, kuma duk wanda ya kalli hoton nan zai tabbatar da cewar sun saba mu'amalar banza ba wannan ne na farko ba, daga ganin yarinyar ƴar duniya ce .
Ransa ya kai ƙololuwar ɓaci ya ce
"Zan yi abinda nake ganin ya dace."
Ya mika mata Camerar ya ce .
Ya taso suka nufi falon a tare, Daidai lokacin da Hilal ya fito kitchen ɗin dauke da ture da food flask a kai sai plate 🍽️ spoon.
Mamaki ne ya kama Zahrah ganin yadda ya dauko flask ɗin gabadaya. Ita da ta girka abincin ko ci ba ta yi ba ga shi yunwa take ji. Ga shi lokacin zuwa haddarta da take koyar wa ya yi ba lokacin da za ta sake wani grikb, dama Papa da Dada suka sun ci na su .
"Yaa Hilal abincin duka zai maka yawa, kuma Ni ban ci ba don Allah bari na ɗebi kadan zan tafi islamiya yau Alhamis muna zuwa hadda."
"Ke! Har kin yi tasirin idon da za ki tari gabana ki fada mani magana haka don rashin kunya, ba na ɗaukar iskanci."
"Har yanzu ban ga iskancin da ake kira wa yarinyar nan ba, hasalima ana zaton wuta a makera ne abun mamaki sai aka same ta a masaƙa."
Da mamaki ya juya yana kallon Dada dake maganar.Papa ne a bayanta fuskarsa a murtuƙe, kallo ɗaya za ka masa ka fahimci zallar ɓacin ran dake fuskarsa.
Mamaki ne ya kama Hilal jin kalaman Dada don tun da yake yi wa yaran gidan nan magana ba ta taɓa cewa komai ba, amma yau ita ce da masa magana mai harshen damo.
Tambyar zuciyarsa ya yi
'Ko dai yarinyar nan ta fada masu ta ganshi garden tare da Sury ne? Kai ba za ta fada ba ai da za ta fada da ta sanar da su lokacin da suka je Kaduna ta kama shi a ɗaki shi da Alexandra babu kaya a jikin Alexandra yana romancing ɗin ta da sauri Zahrah ta fito ta bar masu ɗakin. Kuma ta kama shi a nan gidan shi da Alexandra lokacin da Dada ta aike ta wajensa ta kai masa kwaɗon zogale, duk ba ta faɗa ba ta yi shiru ta tabbata ganinsa a garden da Sury ma ba za ta fada ba sai sai ta yi shiru. Don haka ya juya ransa a ɓace da kalaman Dada.
Papa ya zauna yana kallon Zahrah ya ce.
"Ki yi hakuri ki nemi wani abun da za ki ci, kafin ki makara. Ko Amminki yau girkin gidan suka ci."
"Eh Papa dama idan Abbi na gida ne take shiga ta girka masa ba tare da ta bari ya ci abincin masu aiki ba."
"To ga lokacin tafiyarki islamiyya ya yi."
"Ba damuwa akwai sauran cake da na yi juya bari na ci kawai na tafi."
Murmushi Papa ya yi ya ce.
"Amminki da Dada sun koya maki rashin cin abincin gidan ko? Ai yanzu ƴan uwanki suke yi kuka na tabbatar za ki samu abinci sama da kala uku ."
"A'a Papa ba zan ci ba."
Ta yi maganar tana nufar kitchen.
Hilal na komawa ya kai wa Sury abinci, ya ce ta dauki abun sha a fridge.
Ta buɗe ta ga tuwon shinkafa ne leda uku da miyar egusi da ganyen Ogun ya ji naman rago. Sai kuma farfesun ɗanyen kifi.
Tura baki ta yi tana cewa .
"Sojana ba na son tuwo."
"Sai ki ci farfesun kifin."
"Ba na cin kifi, ko za mu fita zuwa restaurant."
Wani kallo ya mata, wanda ya sa ba ta sake masa magana ba.
Bedroom ya shiga ya rage kayan jikinsa, ya shiga bathroom don yin wanka.
Papa kuwa sai safa da marwa yake yi a Falo, abinda ya ga Hilal na aikatawa ya tsaya masa a rai. Kallon Dada ya yi tare da cewa.
"Ki kira mani Laila a waya."
Ba musu ta kira ta bayan ta daga ta sanar da ita kiran da mahaifinta ke mata.
Dadai lokacin da Aunty Laila ke shigowa Zahrah ta shirya za ta je islamiyya.
"Aunty Laila ina wuni?"
Sai da ta watsa mata harara a fakaice kafin ta amsa da
"Lafiya ."
Zahrah ta yi wa su Dada sallama ta fita sanye da dogon hijabi da niƙab.
Aunty Laila kanta ta tsorata da ganin yanayin fuskar mahainta.
Ki kira Mani mutanen gidan nan manya amma ban da yaran. Iyayen nake buƙata maza da mata. Wadanda ba sa gidan ma a kira su a waya su dawo gidan."
Ya yi magana cikin bayar da umarni ba wasa. A fuskarsa ballantana ta yi masa wata tambayar. Jiki ba ƙwari ya ta bar part ɗin ta tafi don aiwatar da umarnin Papa.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE*
Page5️⃣8️⃣
Ya yi maganar cikin bayar da umarni ba wasa a fuskarsa ballantana ta yi masa wata tambayar. Jiki ba ƙari ta bar part ɗin ta tafi dan aiwatar umarnin Papa .
_Dad_
Ko da ya koma gida a daren kasa rintsawa ya yi, saboda halin da ɗansa Asadullah ya tsinci kansa a ciki, shin a cikin mansion ɗin nan waye zai iya farmakan Asadullah? Da ba don Allah ya yi yana sa sauran kwana a duniya ba da ta wannan hanyar ma kaɗai zai iya rasa rayuwarsa. Waye ko suke ƙoƙarin ganin bayan sa, ta wace hanya zai iya taimaka masa don ganin ya tseratar da rayuwarsa. Ga shi ba wata hanyar da za su gane su waye su a cikin sauki. Shi family Doctor na su da ya za su iya gane ko su waye an kashe shi don ɓatar da hujja. Nan ya dinga tufka da warwara amma ba wata hanya da ya hango wanda zai kai su magance matsalolin da suke ciki .
Kasancewar ranar Aunty ce da girki ya saka ita ce tare da shi a ɗakinsa. Dare ya tsaka sosai gari ya yi tsit.
Tsawon kokaci Dad ya ɗauka yan ta aikin tunini har Aunty ta ta juya akan gado cikin barci ta ji alamar Dad baya nan, sake lalubawa ta yi na.n ma ba ta ji alamar sa ba.
Sai ta bude idanunta tana kallonsa a tsaye ya Lula can wata duniyar na tunini
"Alhaji lafiya kuwa?"
"Lafiya lau."
Ya bata amsa a takaice.
"To me zai saka ka kasa barci kana tunini a cikin wannan tsohon dare?"
"Ba komai."
Ƙarshe ya yanke shawar yin sallar dare ya kai kukansa ga Allah.
Don haka ya nufi bathroom ya ɗauro alwala, sallaya ya shimfida ya tayar da sallar nafilfili .
Ganin haka ya sa Aunty ta koma barci tun da ba fada mata zai yi ba
_Asadullah,_
Shi ma ɓangarensa haka abun yake, tun da ya dawo gidan nan bai yi barci mai tsawo ba, taɓa dare yake yi yana kai kukansa ga Allah. Musamman yanzu da nakiya suka taso shi a gaba.
Tsaye yake akan sallaya, farar jallabiya ce a jikinsa yana tsayuwar dare. Tun karfe biyun dare da ya farka sai karfe huɗun asuba ya idar da sallar . Addu'o'i ya yi sosai akan makiyansa da addu'a Allah ya ba da Jidderh lafiya. Don Doctor Isma'il ya sanar da shi dawawarsu nan da kwanaki biyu, zuwa jibi kenan in sha Allah.
_Aunty Laila_
Part ɗin Daddy ta fara nufa, ta tarar da Mummy a falo ita kaɗai, ganin Aunty Laila ya saka ta ce .
"Kin shigo?"
"Eh.'
"Yanzu nake shirin zuwa na ga ɗan na ki da ya dawo."
Aunty Laila ta ce
"Duk ba wannan ba, da alama gidan ba lafiya . Don Papa ya ce na tara masa kowa na gidan nan. Ban da yara amma yana son ganin iyaye maza da mata."
Gaban Mummy haka kawai ta ji yana faduwa .
"Daddyn yara da baya nan fa?"
"Ya ce wadanda ba sa nan a kira su a waya
Cikin sanyin jiki ta dauki wayart ta lalubo lambar Daddy, bayan ya daga ta sanar da shi sakon mahaifinsa. Hankalinsa ba ya tashi don ya san ba dai laflya Papa zai kira su dawo gida b.
Cewa ya yi ga shi nan dawowa.
Daga nan Sunyi Laila ta nufi ɓangaren Umma nan ma ta sanar da ita yadda ta sanarwar Mummy. Ita ma waya x ɗauka t kira Abba ta sanar shi kiran da Mahaifinsa ke masu.
Sunyi Laila ta fito kamar za ta nufi part ɗin Abbi sau ta yi tsuki ta koma part ɗin Papa ta sanar da shi yadda suka yi .
"Yayanki Salis da?"
"Ban ke part ɗin ba.'
Cikin bayar da umarni ya ce.
"Ki je ku sanar da su kafin na hucr haushi na akanki."
Ba ta da wani zaɓi dole ta wuce Part ɗin Abbi.
Tura kofar ta yi rai a ɓaci babu ko sallama ta shiga falon. Ƙamshi ne ya ziyarce ta mai daɗi, tabe baki ta yi tana karawa Falon kallo. Wanda ko ba'a fada ba an san yana shan gyara, don alma ya nuna mamallakin falon akwai tsananin tsafta da son ƙamshi. Nan Zahara ta yi gado.
Ƙarar buga kofar ne ya saka Ummi fitowa ta ga Aunty Laila.
Mamaki ya kama ta don ganin Aunt Laila a part ɗin. Shanye ta ce
"Barka da shigowa bisimillah ki zauna."
Tsuki ta yi kafin ta ce
"Ki kira mijinki duk abinda yake yi ya ajiye ku zo tare a bangaren Papa."
Tana gama fadar haka ta juya su ta ta fice
Cikin sanyi. jiki Ummi ta dauka oh wayarta ta kira Abbi ta sanar da ji komai .
Shi ma ɓangarensa jikinsa ya bashi ba lafiya ba, tattara takardun da zai dawo gidan da su.
_Hilal_
Yana zaune a dinning table Yana cin abinci tuwon shinkafar ne, Sury da ta ga alamar ba zai kia ta restaurant ba sai ta dole ta zauna suna cin tuwon a tare.
Sai dai shi baya cikin walwala musamman idan ya tuna kallon da Papa ke maza wanda bai taba yi masa irin sa ba .
Falon ya yi shiru kamar ba mutane a ciki, Papa, Dada, suna zaune a ka kujerar yayin Mummy, Daddy, Abba, Umma Abbi, Ummi suke zaune kasa kowa yana jiran jin dalilin kiran.
Camera da Zahrah ta ɗauke Hilal da Sury ba tare da ta san ta yi ba ya mikawa Daddy da Mummy da suke zaune a tare.
Karba Daddy ya yi ya duba Mummy ta matso dab da shi tana dubawa.
Gabansu ne ya fadi a tare lokacin da suka ga babban ɗan su dauke da wata mace a cinyarsa ya rungume ta. Salati suka hau ya yayin da Abba ya karba suka duba a tare da Umma, nan su ka suka yi mugun gani tare da yin salati.
"Salis karba ka gani."
Papa ya yi maganar yana kallon Abbi.
Cikin sanyi. Jiki Abbi ya karba ya matsa kusa da Ummi inda suka yi karo da photon,.
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un."
Shi ne kalmar da Abbi da Ummi suka furta a tatet.
Hannun Sunyi Laila na rawa ta amsa tana dubawa.
"Na shiga uku na lalace, yaushe Hial ya fara mu'amala da matan banza?"
"Ba wanda zai baki amsar wannan tambyar sai shi. Wannan daowar da ya yi tare da mace ya dawo wato ita wannan yarinyar."
Mummy ce ta yi saurin cewa.
"A'a Papa wannan ba halinsa ba ne, ba zai kawo mace har cikin gidan nan ba ."
Murmushin takiaci Papa ya yi kafin ya ce.
"Wannan hoton yau Zahrah ta ɗauke shi a garden, ita kanta ba ta san cewa ta ɗauke su ba, ta je tana ɗaukar hoto a can kamar yadda take yi shi ne bayan ta gama Allah ya yi asirinsa zai tonu yau din nan. Idan kun fahimta a hoton a karkace ta ɗauke shi ba tare da ta sani ba ne . Amma tun x kin ce ɗanki ba zai kawo mace ba zan tabbatar."
Kallon Aunty Laila ya yi kafin ya ce.
"Laila tashi ki je ki duba Mani ɓangaren sa idan shi da mace ce ki tabbatar ta bar gidan nan, sannan shi kuma ina bukatar ganinsa yanzu ."
Sunyi Laila ta mike da sauri tana cewa.
"Lallai za ta ci ubanta yau kuwa yar iska karuwa."
"Kada ki sake ki taba lafiyar jikinta, ki kore ta na ce ta bar gidan ban da duka na san halin ki."
"To Papa"
Ta fada tana ficewa da sauri .
Haka ta haura stairs ɗin da sauri -sauri, knocking ta yi jin kofar a rufe. Daidai lokacin da suka gama cin abincin.
"Tashi ki shiga bedroom."
Da sauri Suryta mike ta shiga ɗakunan yayin da ya bude ƙofar. Don ya san ko waye ba zai shiga masa bedroom shi yana fakon ba Ganin Aunty Laila ya ce.
"Aunty lafiya ko?"
Bata saurare shi ba ta kutsa kai ciki tana huci, kafin ya yi wani yunkurin har ta shiga bedroom. Nan ta yi ido biyu da Sury dake kwance kan gadon. Afusace ta nufe ta wanda tuni Sury ta tsorata ta yi toilet za ta rufe.
Zo ki tattara kayanki ki bar gidan nan, idan kika shiga kika rufe sai na saka an yi maki dukan mutuwa.
Jiki na rawa ta zo ta dauki trolling bag ɗin ta da handbag har tana hada hanya ta fice. Ita a tununta mahaifiyar Hilal ce.
Ta kofar baya ta fice kafin