Showing 141001 words to 144000 words out of 154779 words
suna Amal, Kuma jininsu ya hadu dama. Ita ma ta ji dadin ganin Zahrah.
A part ɗin Dada aka ajiye komai in da Hilal ya nunawa Dada na shi sannan ya nuna mata na sauran
Nan fa Dada ta kira sauran matan gidan don su gani, sai sai ganin kayan ya saka jininsu ya kusan hawa. Sakamakon yadda Hilal ya hada kayan har da yaran Ummi wato Mahmud da Sadik.
Babban ta tashin hankalin na su shi ne yadda suka ga kayan Zahrah da akwatunan da ya yi mata ga kaya masu tsada da aka zuba ciki, koma mai tsada ne aka zuba ga sarƙar gold da zobe da warwaro na zinari duk ya zuba. Mummy cikin bacin rai take cewa.
Akan me kayan Zahrah za su fi na sauran yawa , da me ta fi su da aka kasa sakawa ya ko Yar Gold ce ita? Nan Dada ta fara faɗa dole suka watse, Mummy tsabar bakin ciki kasa magana ta bar wajen kamar za ta yi kuka, ganin yadda ya kashe wa Zharah kudi leshi masu tsada ya zuba
Kowace daga cikin amaren dangin mahaifiyarta sun zo an kai kayan ɗaki da na kitchen don yin jere.
Haka aka yi don ko Papa ne ya bayar da makullan gidan Hilal, su Hajiya Bilkisu da wasu ƙawayen Ummi zuwa jerin.
Don Abbi ya yi kokari saitin kayan ɗaki biyu ya siya wa Zanrah. Tun daga kan kujera har gado da da sauran kayan ɗaki. Ɗakuna biyu aka yi mata jeren kayan ɗaki
Kowa sai yaba kyau da tsaruwan gidan yake yi sosai, don gida ne kamar wata fada.
Kitchen ma ta ji kayan kitchen na zamani masu kyau da tsada, don kudi Ummi ta bayar Hajiya Bilkisu suka je suka hado komai . Da kuɗin suka kare ta sake tura masu.
Duk da cewar ita da Abbi ba sa farin ciki da auren amma ba yadda suka iya, haka suka hakura suka yi wa yaran na su addu'o'i ba dare ba rana , har sallar dare sukan yi suna kai kukansu ga Allah.
Maryam ma an je gidan Mansur an yi mata jeran kayan daki da na kitchen.
Nadiya ma an jera mata kayan ta a gidan Sadik in da Umma take ta masifa tana zage-zae.
Gidan Mahmud
Duk da kasancewar mahaifin Nabeela ne ya yi komai . Aunty Laila ba ta fasa fada ba, wai an kashe kudi akan auren da ba zai je ko ina ba.
_Asadullah_
Fitowa ya yi daga part ɗin sa dake upstairs, Sulaiman na rike da trolley bag ɗin da zai yi tafiyar .
Dakin su Jidderh ya tura ya ji a datse, kasancewar safiya ce y saka ba su tashi b. Ya ji ba dad'i sosai don so yake ya ga Jidderh kafin ya tafi zuwa tafiyar da zai yi hadin Katsina.
Kamar zai yi kuka ya cewa Sulaiman.
"Ba su tashi ba, ba na so na katse masu barci sai dai hakan bai samu ba. "
Nisawa ya yi kafin ya ce
"Doctor Isma'il ya ce zai kawo wani malami da zai dinga yi mata mata addu'a da sunayen Allah, ki za ta dawo hayyacinta."
Jinjina kI Sulaiman ya yi ya kalli Asadullah ya ce.
"Shawara mai kyau Allah ya dawo da kai lafiya ya ba ta lafiya ."
Da Amin ya amsa yana yin gaba Sulaiman a binsa a baya.
Wata bakar mota tinted glass ya nufa, shiga Sulaiman ya shiga mazaunin direba, don da shi kadai zai ke Dad ya ce dole su je da Sulaiman, bai yarda a Asadullah ya je shi kadai ba, hakan ya saka za su je su biyu da Sulaiman.
*Bayan kwana uku*
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ƴa ta ji kunyar, yau ne ya kama ranar da amare za su tare gidan mazajen su.
A cikin kwanaki ukun nan Zahra ta canza ta yi kyau da sheƙi , fatarta ta yi kaishi kamar na auduha ga wani ƙamshi na musamman dake tashi daga jikinta, ko fisari ta yi wani ƙamshi ke fitowa. Idan ta shiga ɗaki sai ya kwana bai daina ƙamshi ba. Ko kusa da ita ka tsaya sai ƙamshin jikinta ya rabe ka.
Hajiya Bilkisu ta bada umarnin a shirya ta a kai ta gidan tafarki, don zuwa daren nan kowacce za ta kasance a gidan mijinta .
*Book 2 na kudi ne ki tura kudin ku ta wannan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank, sai a tura shsidar biya ta wannan lambar 09065327995*
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE*
Page6️⃣7️⃣
Hajiya Bilkisu ta bada umarnin a shirya ta a kai ta gidan tafarki, don zuwa daren nan kowacce za ta kasance a gidan mijinta.
Ko da aka shiga ɗakin aka tarar da ita Kudundune cikin bargo zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Kuka da take yi har idanunta sun kumbura. Amal da ƙawayenta sai A'isha ƙawar Zanrah ce a tare da ita. Don ta ce ba wanda za ta gayyato, Amal ɗin ma da ta gayyato ƙawayen ta ba da izinin Zahrah ba. Ƙawar Zanrah daya ce A'isha sai kuma amininsu wanda Zanrah ke kira da amini, shi ma niya ya zo ta fita zuwa falo suka gaisa ya yi mata Allah sanya alkhairi.
Duk yadda Amal da A'isha suka yi da ita akan ta ci abinci duk wunin ranar ƙi ta yi, ba abunda ta ci a cikinta.
Wanka ma ta shirya ta gagara tashi. Hakan ya saka Amal ta je ta sanar wa mahaifiyar ta abinda ke faruwa.
Jin jikinta da zafi ya saka Hajiya Bilkisu ta damu, ta san ba komai ya kawo mata wannan zazzaɓi ba sai yawan kuka da damuwa da ta saka wa ranta.
Taimaka mata ta yi ta tashi suka shiga bathroom dake cikin ɗakin Amal ɗin.
Ruwa mai ɗumi ta haɗa mata ta je ta daure ta yi wanka za ta iya, kuka kawai take yi.
Kafin ta fito Hajiya Bilkisu ta fito mata da wani hadaddiyar leshi fari an yi masa ado da kalar golding da pink colour, sai gyale pink colour, doguwar riga ɗinkin bubu, sai sarka da ɗan kunne na gold ta aiye mata a saman kayan, da underwear farare sannan ta fita ta nufi kitchen don kawo mata tea, don an ce mata duk yau ba ta saka komai a ciki ba, ga shi yamma ta yi. Don ita ba ta sani ba ta fita zuwa kasuwa da kuma can gidan Hilal don kai wasu kayan kitchen ɗin ita da ƙawar Ummin Zahrah.
Daƙyar take wanka don jikinta ba ƙarfi ko kaɗan, ba abinda yake saka ta bakin ciki da kuka kamar idan ta tuna cewa daga yau da shi kanan za'a kai ta gidan wannan mugun, da ya tsane ta.
Sai da ta yi brush sannan ta sake wanke jikinta ta ɗauki towel ta ɗaura.
Dakyar take tafiya ga yunwa ya ci ƙarfinta.
Daidai lokacin Hajiya Bilkisu ta shigo rike da kofin tea.
Man shafawa ta ɗan shafa sama-sama sannan ta saka underwear, Hajiya Bilkisu ta taiamaka mara ta saka rigar. Nan su Amal da A'isha suka shigo.
Suka taya ta shirya wa dama an kira mai makeup don ta tsantsar mata makeup, sai zai fir ta ƙi yarda ta ce b ta so har tana kara sakin kuka. Hakan ya saka Hajiya Bilkisu ta sallame mai makeup ɗin ta tafi.
Shayi ma ƙin sha ta yi dole Hajiya Bilkisu ta matsa mata sakiyar ta sha kadan .
Amal ce ta yi mata simple makeup shi ma sai da ta ga ɓacin ran Hajiya Bilkisu sannan ta amince.
Bayan ta gama mata sai ta yi kyau kuwa ƙaramin bakinta da ya kasance pink sai shinning yake yi.
Takalmi da jaka golding ta saka.
"Mu ke sai kiran waya ake yi wai ni ake jira na kawo ki."
Wayarta ta ɗauka ta kira Dr Khalil akan ya zo ya kai su tun da yana gidan.
Hannunta na rike cikin na Hajiya Bilkisu suka fita zuwa harabar gidan. Wajen motar Dr Khalil suka nufa, ita da Hajiya Bilkisu suka zauna baya, yayin da Amal ta zauna gefen Yayanta.
Suna isa gidan kukanta ya ƙaru.daƙyar ta iya takawa Hajiya Bilkisu na rike da hannunta.
Gabadaya ilahirin jama'ar gidan suna babban falon gidan. Nan ta samu waje ta rakuɓe kusa da Yaa Mahmud.
Papa, Dada, Daddy, Mummy, Abba, Umma, Abbi, Ummi da Aunty Laila, kowa na falon. Sai sai kallo ɗaya za ka yi masu ka gane ɓaci rai da suke ciki idan aka cire Papa da Dada.
Gefe suma ga Mahaifin Mummy da mahaifinta, sai mahaifin Umma da Mahaifiyarta, sai kuma Modibbo mahaifin Ummi da matarsa da mahaifiyarta. Sai tsohon mijin Aunty Laila wato mahaifin Nabeela da Kausar.
Sai su amaren da angwayen kowa na nan an hadu.
Papa ne ya fara buɗe taro da addu'a sannan ya yi masu nasiha daga amaren har an angwayen.
Sannan ya mahaifin Mummy, Kakansu Hilal kenan ya yi masu masu nasiha sosai akan zaman aure da haƙuri. Sannan ya gargadi Mummy akan tayar da fitina ko saka idanu a cikin lamarin yaran matukar ba gyara ne za ta yi ba, ya kuma sanar da ita matukar ya ji wani matsala ya fito daga gare ta ranta ne zai ɓaci.
Shiru ta yi tana sauraren sa tana kuma ayyana ba abinda zai sa ta bar Hilal ya zauna da Zahrah matukar tana raye.
Sai mahaifin Umma ma ya yi masu na su nasihar ya kuma gargadi iyayen akan su cire idanunsu akan lamuran yaran.
Don dama Papa ya sanar da su abinda ke faruwa a gidan da kuma dalilin hada auren, yana ganin ta haka ne zai gyara kuskuren da ya yi a baya, don fifiko da banbanci da ya nuna wa Sauran ƴaƴansa sune umul'aba'isin faruwar komai. Da ya nuna adalci a tsakanin yaransa da ba su tsinci kansu cikin kaso saba'in na wannan matsalar da suke fuskanta ba.
Modibbo mahaifin Ummi ya yi nasa nasihar sannan aka ba wa iyayen damar fadar abinda suke da shi da za su faɗa.
Kasancewar dukkansu ba wanda ke farin ciki da auren ya saka suka yi shiru. Ummi dai sai hawaye take yi. Abbi ne ya yi karfin halin cewa.
"Hilal."
Ɗago kai ya yi ya kalli Abbi ba tare da ya ce komai ba. Abbi ya cigaba da cewa.
"Zahrah ba isashshiyar lafiya ce da ita ba, kusan kowa a nan ya san tana dauke da ciwon athma mai tsanani, wanda yakan uwan tashi mata lokuta da dama. Musamman lokutan sanyi don ciwon baya son sanyi. Ko hayaƙi ko kura na san dai ka sani kai ma ba sai na yi ta lissafa maka ba, wani lokacin ko kula take yi ko ranta ya ɓaci ba wuya ciwon ya tashi. Hakan ya saka na sa a raina ba zan aurar da ita ga kowane irin mutum ba, har sai wanda na ga ya cancanci zama da ita, kuma na sanar da shi yanayin ta idan zai iya ɗaukar ɗawainiyar ta kuma ya yarda zai kiyaye lafiyar ta sannan zan bashi aurenta. Sai ga hukuncin da Papa ya ɗauka na aurar da ita ba tare da sanin ya shirya hakan ba, kuma ba na bakin ciki da hakan, don na tabbatar akwai babban dalilin da ya saka ya aikata hakan. Kuma ba zai yi abu don cutar da daya daga cikin ahalin gidan ba."
Nisawa ya yi kafin ya cigaba da cewa.
"Na san ba ka son Zahrah kuma ba lallai k jure ɗawainiyar ta ba, sai dai ina rokon ka da ka rike ta amana fisabilillah ba tare da cuta ko cutarwa ba ko da ba za ka so ta ba, ko ba za ka yi mata kallon macen da kake so ba, ka bata kulawa a matsayin ta na ƙanwa a gare ka, na sani jini ba ƙarya ba ta samu wannan kulawar daga gare ka a gidan nan ba, to a yanzu ina son ka zame mata uwa uba Yaya jigo kuka Garkuwa a gare ta. Zahrah tana da rauni, ka yi hakuri da ita, idan ta saɓa maka ko bijire maka ka sanar da ni zan ɗauki mataki akan ta Allah ya yi maku albarka."
Ya karasa maganar ƙwalla na cika Idanunsa.
Jikin Hilal ya yi sanyi da kalaman Abbi sunkuyar da kai kawai ya yi ba tare de ya yi wata magana ba.
Zahrah kukan ta ne ya ƙaru har ta ji numfashinta na neman ɗauke wa tashi ta yi ta nufi part ɗin Umminta, ganin haka ya saka suka ga alamar ba ta jin dadi za ta dauki maganin ta ne.
Tana shiga madadin ta samu Maganin ta ko Inhelar ta shaƙa sai ta kwanta kawai ba ta nemi komai ba.
A can kuwa ganin dare na yi ya saka aka ce kowane daga cikin angwayen ya ɗauki Amaryarsa su tafi Allah sanya alkhairi.
Mansur ya mike tsaye Papa ya kalli Maryam ya ce .
"Maryam tashi ki bi Mansur, ku yi hakuri da juna Allah ya maku albarka."
Tana kuka ta tashi tsaye, Papa ya kalle shi ya ce.
"Rike hannunta."
Ba musu ya rike hannunta.
"Kada ka taɓa sake hannunta ka rike ta duk rintsi da wuya kada ku rabu ka rike ta kenan har ƙarshen rayuwarku."
Fita suka yi tana kuka suka fice daga falon.
"Sadik ka kama hannun Nadeeya ku tafi, Ku yi hakuri da juna ku zauna lafiya, kowace mace ta yi hakuri da mijinta, idan da wata matsala za ku iya sanar da iyayen ku ko kuma ni da Dada, kada wacce ta yi yaji ta zo nan gidan."
Kallon Nadiya ya yi tare da cewa.
"Tashi ki bi mijinki Allah ya yi maki albarka."
Tashi ta yi tana hawaye ta bi bayan Sadik, ya masu sallama, shi ma hannunta Papa ya ce ya rike tare da bashi amanarta kamar yadda ya yi wa Mansur.
Yana rike hannunta sai ita ma ta ƙanƙame hannunsa da ƙarfi wanda sai da ya kalle ta, sai dai ba shi yake kallo ba kanta na ƙasa. Kallon Umminsa ya yi ya tana kuka, girgiza mata kai ya yi Alamar ta kwantar da hankali, gyada masa kai ta yi ya nufi hanyar fita suka fice, jama'a dake falon suna masu fatan alkhairi.
A parking space Mansur dauke shirin ya wa motarsa key ya hango Sadik da ƙanwarsa suna nufo wajan motar Sadik ɗin, da alama su ma tafiya za su yi .
Wani baƙin ciki ya cika masa zuciya cike da tsanar Sadik ya fito daga cikin motar ya nufi in da suke, har Nadeeya ta shiga gaban motar ta ji Muryar Yayan na ta na cewa.
"Ke Nadeeya fito zan yi magana da ke?"
Kallon Sadik ta yi sanin ba sa jituwa da Mansur, ba ta mance dambe da shi yi a parking space dun ba kwanakin baya. Ta ga Sadik ko kallonta bai yi ba. Ta buɗe murfin motar ta fito.
"Yaya ga ni."
Ba yadda na iya ne zan bar ki ki tafi da wannan, amma idan har ya yi maki wani abun da ba daidai ba ki kira ni, sai na koya masa hankali. Kada ki yi shiru ya zalunce ki, kuma kada ki sa a ranki zaman aure za ki yi da shi, ki ɗauka zaman wucin gadi ne, don ba zan taba bari ki zauna da shi ba ."
Sadik yana jin sa bai tanka ba, sai ya ji Muryar Mansur na cewa.
"Kai kuma idan ka sake wani abu ya samu ƙanwata sai na koya maka tarbiyya, kada ka ce za ka yi zaman aure da ƙanwata domin ba ka kai ba, kuma ba za ka kai ba."
Sadik ya bude murfin motarsa y fito ya kalli Mansur cikin ido ya ce
"Idan ban kai ba ga ƙanwarka nan sai ka je ka ɗauke ta ka ba wanda ya kai, ko an fada maka son ta nake yi ne da z ka ka cika ni da suratai na banza da wofi, ba don biyayya ga na gaba da ni ba har ka isa ka faɗa mani zancen banza ne?"
"Nadeeya kina jin me yake fadawa yayanki ko? Kar ki manta har mahaifinki ya yi rashin kunya, idan ke ƴar halak ce ki nuna masa mahimmanci mahaifinki."
Kuka kawia take yi ta tuna ranar da Sadik ya yi Abbi rashin kunya, amma ai Abbin ne bai kama girman sa ba, kuma ba dan da zai ga ana cin mutumcin iyayensa ya yi shiru.
Nan suka cigaba da sa'insa har Mansur ya ɗaga hannu ya mari Sadik, shi ma kafin ya sauke hannu ya sauke masa marin dambe ne ya kaure, ga Kukan Nadeeya. Ma'ikatan gidan suka shiga tsakani.
Jin an ce za'a sanar da Papa ya saka Sadik da Mansur kowa ya shiga motar sa Nadeeya m ta shiga ya yi wa motar key suka bar wajen.
Maryam dai tana zaune har Mansur ya shigo yana huci.
Papa ma ya sallami Mahmud Mahmud da Nabeela kamar yadda ya yi wa Sadik shi ma fatan alkhairi ya yi masu da sauran kakannin da suke gidan.
Sai kuma aka zo kan Faisal shi ma aka bashi Kausar suka fita ana sanya masu albarka bayan mahaifinsu Alh. Nasir ya masu nasiha.
Duk an sallame su ba kowa a wajen, Ummi ta mike ta nufi part ɗin ta. Papa ya kalli Hilal ya ce .
"Me kake jira ka dauki matarka ku tafi mana ."
Kallon Abbi ya yi tare da cewa.
"Salis ka bashi matarsa su tafi ."
Da to ya amsa ya mike ya fice, yayin da Papa ya ce ya bishi can su tafi Allah sanya alkhairi ya rike amanar da mahaifinta ya bash.
Abbi na gaba cikin sanyin jiki yake tafiya, Hilal na biye da shi a baya.
A falo ya yi sallama in da Abbi ya amsa, ya shiga in da ya tarar da Ummi na kuka sosai kamar an yi mata mutuwa. Ƙasa ɗayaejafa ya yi sai ya tsaya kallon Abbi.
Ganin Hilal ya saka Ummi ta shiga dakin Zahrah, nan ta tarar da Zahrah kwance tana rawar sanyi Aunty Sai Amal da ta shigo ta sane t tana jera mata sannu. Don Sunyi Bilkisu na can.
Zafi jikinta ya yi sida zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Ga numshinta sama-sama.
Papa ne u shigo yana fadar dare na yi su tashi ku su tafi.
Ganin