Showing 36001 words to 39000 words out of 154779 words

Chapter 13 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6515

ta janyo mata wuyan hijabi ta sauke mata lafiyayen mafi wanda ya saka ta saki ƙara tare da dage kumatu.

"Ke mahaukaciyar ina ce za ki taka ni ki wuce, sa'arki ce ni?"

Jinjina kai Umma tayi tare da cewa.

"Kin yi daidai, uban me take taƙama da shi, ta zo za ta shiga mota tana taƙama to ba Salisu ya siya motar ba ɗana da guminsa ya siye motar."

Kallonsu take yi ɗaya bayan ɗaya ba wanda ya yi magana ko ya tsawatar wa ko ya yi wa Kausar maganar marin da aka yi mata na cin zali.

Ji ta yi kamar kada ta shiga motarsa abun gori ba wuya har mahaifiyarsa tana mata gorin motar ɗanta ne da ya siya da kudinsa, wato ba kudin ubanta ba ne."

Zuciya ta kawo mata wuya ta ji ba za ta iya shiga motarsa ba, don haka ta juya ta koma gefe ta lalubo lambar wayar Papa akan ya haɗa ta da wani da zai kai ta. Duk da ba ta taɓa tafiya ita kadai ba.

Sai dai daga wayar Papa har ma Abbi ba wanda ya shiga.

Waige-waige ta fara yi tana neman Direban gidan amma ba ya kusa.

Tana da sanyi amma da zaran an ƙure ta fushinta baya da kyau.

Tsawa Hilal ya daka mata wanda sai da ta kowa ya tsorata.

"Za ki shigo ne ko me kike jira!?"

"Ba zan tafi da motarka ba, ina jiran Direba ya zo ya ɗauke ni ya kai ni."

Fitowa ya yi yana kallon ta da mamaki bai san cewa zuciysrta ta kai haka ba.

"Wuce ki shiga na ce."

"Ba zan shiga ba sai dai na shiga motar da ubana ya siya da guminsa ba wani..."

Saukar marin da ta ji ne ya saka ta kasa karasawa, don sai da ta daina ji da gani na wucin gadi. Jiri ne ta ji yana ƙoƙarin ɗaukarta ta yi luu za ta fadi, ya tare ta ta ai faɗa jikinsa.

Ɗaukar ta ya yi cak ya saka a bayan motar, yazo ya dauki jakkarta da ta fadi ƙasa ya bude handbag ɗin ta, ganin ta ɗauko magungunanta ya saka ya koma cikin motar ya zauna gefenta.

Umma ta ce.

"Hilal dole sai ka kai ta ne?"

"Alkawari na yi wa Papa da ya nemi na kai ta."

Ɗaya masu hannu ya yi, suma suka masa fatan sauka lafiya.

Zuwa lokacin Zahra ta sume, yaraf ta kwanta a jikinsa. Ganinta kwance a jikinsa ya saka Nadiya, Kausar, da Nabeela jin wani kishi da tsanar Zahrah a zuciyarsu.

"Kun ga karuwanci ƙiri-kiri ji yadda ta kwanta a jikinsa."

Aunty Laila ta faɗa tana kallonsu su Mummy. Umma ta ce.

"Son na tsani yarinyar nan irin tsabar da ba na son ta tsaya ko inuwa ɗaya da tsatsona. Ka bari direba ya kai ta ko kuma ka raba mota kai ka shiga wata tunda ga sojojinku nan."

"Umma kada ki damu ba na son na kwashi gayya ne."

"To ka raba jikinka da na wannan yarinyar."

Kai ya jinjina tare da cire ta ya jingine da kujerar motar. Zuge glass ɗin ya yi tare da bawa direban umarnin ya ya ja motar su tafi.



*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)





*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*


Page1️⃣8️⃣


Kai ya jinjina tare da cire ta ya jingine da kujerar motar. Zuge glass ɗin motar ya yi tare da bawa direban umarnin ya ja motar su tafi.

Sai da motar ta bar gidan sannan suka koma ciki suna ta zagin Zahrah.

Juyawa ya yi ya kalle Zahrah wacce idanunta ke lumshe, ga zara-zaran eye lashes ɗinta a kwance. sai sheƙi suke yi girarta sun kusa haɗe wa da juna.

Kau da kansa gefe ya yi tare da yin gajeren tsuki. Handbag ɗin ta ya duba daidai lokacin da ta ja wani ajiyar zuciya. Garin haka ya saka ya ɗauko Inhelar daga cikin jakkarta ya ya kai kai ta shaƙi iskarsa.

A hankali numfashinta ya dawo daidai. Kallonsa ta yi ta kauda kai gefe. Ga fuskarta ya kumbura don sai da shatin yatsunsa biyar suka kwana a saman kumatunta. Ga ɗayan gefen kumatunta in da Kausar ta mare ta, sai dai bai fito sosai kamar wanda Hilal ya yi mata ba.

Kau da kanta ta yi gefe tana tuna abun da aka yi mata a yau ya tsaya mata a rai sai ajiyar take saukewa akai-akai.

Wayarsa ce ta soma ruri, ya duba ya ga abokinsa ne. Ɗagawa ya yi ba tare da ya yi magana ba.

Daga can bangaren kamal ya yi sallama. Ya amsa masa kamar baya son magana.

"Ina hanyar garinku."

"Ma sha Allah, ka ce muna da babban baƙo mu shirya."

"Kada ka wahalar da Amarya kai ma ka san a hotel nake sauka, ballantana yanzu da na zo da wata."

"Wata wace ce ita?"

Sai da ya ɗan yi jim kafin ya ce ƙanwata ce, za su yi gasar karatun Alkur'ani ne."

"Ma sha Allah, gaskiya bai kamata ku sauka a hotel ba, sai dai ku zo gidana tun da akwai wadatattun ɗakuna. Ko ku nawa ne kowa zai samu ɗaki don Allah ka yi Mani wannan alfarmar."

Shiru ya yi kafin ya ce.

"Kada ka damu ni..."

Katse shi ya yi ta hanyar cewa.

"Idan ba ka sauka a gidana ba wallahi ni ma ba zana sake sauka a gidanku ba, tun da yadda na dauke ka ba haka ba ne a wajenka."

"To na ji sai mun iso."

"Hauwa ko kai fa."

Sallama suka yi ya katse kiran wayar. Zahara Idanunta a lumshe tana jin sa. Kira ne ya sake shigowa wayar. Ya duba ya ga sunan da ya bayyana akan fuskar wayar ALEXANDRA shi ne sunan da ya yi seved number ta.

Ɗauka ya yi bayan ya yi murmushi mai sauti wanda har sai da Zahra ta ji sautin murmushinsa.

Bayan ya ɗaga ne sai ya fara magana cikin yaren ƙasar Spain.

Tsawon mintina talatin suka ɗauka suna wayar kafin Zahra ta ji ya katse kiran wayar.ita dai ba ta jin me suke cewa.

Take dai ga kiran video Call ya shigo wayar . Ɗaga wa ya yi sai ga fuskar wata Baturiya ya bayyana kan fuskar wayar.

Matashiyar budurwa ce take masa magana kamar za ta yi kuka. Ba abinda take ji daga Yaren ƙasar Spain sai dai ta ji tana ambaton U.S da kuma Nigeria.

Ba ta ji me yake cewa ba amma sai ta ji sautin kukan yarinyar na fitowa daga cikin wayar.

Ɗan ɗaga kai ta yi ta saci kallon wayar sai ta ga kyakkyawar Baturiyar na masa.

Taɓe baki ta yi tare da kau da kanta gefe.

Sun mai mintuna talatin ko wajen video call sannan ya katse wayar.

Daga nan ba ta san lokacin da barci ya ɗauke ta ba, kasancewar an kashe A.C saboda yanayin ciwonta.

Ba ta san lokacin da suka isa garin Kaduna ba, don barci take yi.

A ƙofar gidan Abokinsa Jamilu ya sa direba ya yi parking.

Wayarsa ya ɗauka zai kira Jamilu kenan sai ga kiran Jamilu ya shigo wayar. Ɗaga wa ya yi ya ce.

"Muna waje."

Mai gadi ne ya wangale masu gate daidai lokacin da Jamilu ya iso harabar gidan.

Motar na shigowa direban Hilal ya nufi parking space ya yi parking.

Jamilu ne ya buɗe murfin motar ya sauke idanunsa akan fuskar Zahara dake barci.

"Tabarakallah ma sha Allah, tsarki ya tabbata ga ubangijin halittar da ya halicci wannan kyakkyawar sura."

Wani kallon Hilal ya masa sannan ya ɗauke kai ya mayar kan fatima Zahra, har lokacin barci take yi, tsawa ya daka mata wanda ya saka ta farka a firgice.

Dara-daran idanunta ta hau raba wa sai ta tuna in da suke, don haka ta tsuke fuska tare da kau da kai daga kallonsa.

"Haba meye haka ka yi haka ake tashin mutum daga barci?"

Bai kalle shi ba ya fita bayan direbansa ya bude masa murfin motar.

Jamilu ne ya kalli Zahra tare da sakar mata murmushi ya ce.

"Ƙanwata zo mu shiga ciki ko?"

Ba musu ta ɗauki jakkar kayanta ta ta fito.

Jamilu ya masu jagora zuwa ciki, yana gaba shi da Hilal Zahrah na binsu a baya.

A falon gidan suka tsinci kansu. Da sallama suka shiga a bakinsu.


"Ku zauna bari na kira matar gidan."

Yana gama fadar haka ya nufi wani corridor.

Bayan mintuna biyu sai ga shi ya dawo tare da matarsa hannunsu sarƙe cikin na juna.

Murmushi take sakarwa Zahra lokacin da suka ƙaraso falon. Ita ma Zahra murmushin ta sakar masa.

"Sannunku da zuwa."

Ta faɗa yayin da suke da zama akan kujera mai zaman mutum biyu.

Kallon Hilal ta yi tare da cewa.

"Barka da zuwa mazan fama ya aikin?"

"Barkanki dai Alhamdulillah."

Ya amsa ba tare da ya daga kai ya kalle ta ba.

Kallon Zahra ta yi tare da cewa sannu da zuwa ƴar uwa."

Murmushi Zahra ta saki tare da cewa.

"Yauwa ina wuni?"

"Lafiya lau kin zo lafiya ?"

"Alhamdulillah."

Jamilu ya kalli Hial ya ce.

"Mr Man ya za ku yi wanka ne ko dai kun ci abinci?"

Kamar bai ji me ya ce ba, ya cigaba da danne-danne a wayarsa.

"Ka ce Mani tare da ƙanwarka kake to na ga dai wannan ba ta yi kama da Maryam ba, ina ka samo ta, ko ita ce mai shirin zama Amaryarmu?"

Sai a lokacin ya ɗago ya yi masa wani bazan kallo mai nuna cewa na fi ƙarfin ajin yarinyar.

"Me kake nufi ai wallahi wannan matar wuce sa'a ce, don Allah ina ka samo ta?"

Sai da ya yi kamar ba zai amsa ba sannan ya ce.

"Ƴar ƙanin mahaifina ne."

"Wow gaskiya ban san ta ba "

"Ai ba za ka sani ba."

Ƴar uwa mu je na kai ki ɗaki ki yi wanka ki ci abinci ko?"

Sumayya matar Jamilu ce ta faɗi haka tana jan hannun Zahrah, har masaukinta ta kai ta sannan ta janyo mata ƙofar.

Zama ta yi tana kallon ɗakin sai ta miƙe da niyyar shiga wanka sai ta ji tana son jin muryar iyayenta.

Don haka sai ta nufi Falo da niyyar ɗaukar wayarta ta manta ta barta a in da take zaune.


A can falon kuwa Jamilu ya kalli Hilal ya ce.

"Amma gaskiya da zan baka shawara ka ji da ka auri yarinyar nan Zahrah"

Zahra dake shirin zuwa ɗaukar waya cak ta tsaya gabanta na faɗuwa. Don haka ta tsaya dafe da ƙirjinta.

Wani kallo ba ka da hankali Hilal ya yi masa tare da cewa.

"Allah ya kiyaye sa ai nafi ƙarfin ajin yarinyar nan, ko mata sun ƙare ba abinda zan yi da ita."

"Ina ga dai ka makance ne yarinyar nan wallahi ko maƙiyina idan ya lalle ta ya san Allah ya yi halitta a wajen. Don wallahi ba za ka taɓa cewa ita ƴar Afrika ba ce. Ga ta nan kamar wacce ta fito daga jinsin Larabawa ko indiyawa."

"Kai ka daina ƙoɗa yarinyar nan don ba ta gabana ko mata sun ƙare ba zan iya aurenta ba, don ba ta da banbanci da namiji a wajena."

Rintse idanu Zahra ta yi don kalamansa sun taɓa mata zuciya .

"Lallai ba ka da hankali Hilal ko ƴan matanka na can ba abinda suka fi Zahra da shi, sai dai wata ƙila su fita hasken fata, amma bayan haka ba kyau ko diri suka fita ba , idan dogon gashi ne na ga alamar ita za ta yi gashin. Ba za ka gane baiwar da Allah ya yi mata ba sai ka aure ta.

"Na auri wa? Ai da na auri yarinyar nan gara na yi kiwon kare."

"Subhanallah, wace irin ƙiyasta kake yi wa yarinyar nan har kake danganta ta da dabba? Dabbar ma karya?"

Zahra dake tsaye ba ta san sanda kuka ya suɓuce mata ba, har dai da suka ji kukan nata suka juya suka kalle ta. Dafe goshi Jamilu ya yi cike ta jin haushin hakan, don bai so yarinyar ta ji wannan kalmar ba.

Hilal kam ko a jikinsa. Wayar da ba ta iya ƙsrasowa ta ɗauka ba kenan . Ta juya ta koma ɗakin da ka sauke ta. Don ta muzanta yau, bs'a taba muzanta ta ko an ci zarafinta irin yau ba. Lallai family ɗin sun sun yi mata tsana mafi muni. Da ace tana da damar zaɓin yadda rayuwarta za ta kasance to da ba za ta taɓa zamowa a cikin wannan zuri'a ta su ba. Ba ta taɓa tsanar Hilal irin na yau ba .


"Ka gani ko yarinyar nan fa ta ji ka, dole ranta ya ɓaci ."

"Wannan ba matsala ta ba ce."

Ya tashi yana cewa

"ina bukatar yin wanka."

Miƙewa ya yi ya masa jagora zuwa wani ɗaki dake jikin na ɗakin da aka sauke Zahrah.



*Prison / Gidan yari*

Wayarsa ya ɗauka tare da lalubo wata lamba wacce ya yi savin da LAUYANA. Ya yi ta kira har sau uku ba'a ɗaga ba, sai a na huɗu sannan ya ɗaga.

"Barista lafiya ina ta kiran wayarka ba'a ɗagawa?"

Daga ɗayan gefen ya ce.

"Ina fa lafiya ni ma kai na a matsayina na lauyan dake kare ka dakyar na sha."

Cikin nuna halin ko ina kula da lamarinsa ya ce.

"Kuɗaɗen da suke hannuna ya ƙare, kuma ka san ba zan iya rayuwar da sauran prisoners suke yi ba, don ka san ba na iya cin abinci da abinda suke sha, duk siya nake yi kuma ga kuɗin hannuna sukan kare. Ko siyen abinci da abin sha ma kudi nake kashewa."

Sai jin muryar lauyan ya yi yana cewa.

"Ai ko ka fara koyon cin abincin da suke ci."

"Ba gane ba me kake nufi, akwai abinda ya faru ne?"

"Komai ma ya faru, domin sakamakon shari'ar da aka yi maku kai da Asadullah ka san cewa kotu ta binciko duk wasu ƙadarorin da ka tara na Asadullah ne, bayan gano komai kotu ta kwace duk wasu ƙadarorinka tun daga kan gidaje, filaye da gonaki da motocin da ka tara duk koto ta ƙwace yanzu haka an rufe asusun bakinka (Bank account) duk an rufe ba kudin da zai iya fita daga ciki.

Wayarce ta suɓuce a hannunsa ta faɗi a wajen sumamme.


*To na dan fans zuciyarku tana cike ta tarin tambayoyi, ku dai ku cigaba da bin alƙalanina da sannu zan warware maku wannan albarin mai cike da sarkakiya*


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z




*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page1️⃣9️⃣


Wayarsa ce ta suɓuce a hannunsa ta daɗi ƙasa , a wajen ya fadi sumamme.


Bayan kamar mintuna talatin sai ga wani ma'ikatcin gidan yarin ya yi sallama ya shigo, hannunsa rike da jarida da ya kawo masa.

Saboda kullun cikin neman jaridu yake ko zai yi tozali da ta mutuwar Asadullah. Sai dai ba haka ba bai taba katari da abin da yake son ji ba .

Fridge ma'iakacin ya nufa tare da ɗauko ruwan sanyi ya yayyafa masa.

Sai da ya yayyafa masa a karo na biyu sannan ya farfaɗo a firgice.


_Fatima Zahrah_

Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, ta rasa wani irin tsana ne familyn su suke yi mata. Yanzu ƙiyayyar har ta kai a danganta ta da ƙasaitacciyar dabba kamar Karya. Kuka take mai cike ta ƙunar zuciya dake nuna tsantsar bakin cikin dake zuciyarta. Don Hilal ya ci zarafinta a gaban abokinsa.


A can kuwa bayan Jamilu ya raka Hilal ɗaki ne ya wuce ɗakin Sumayya matarsa.

Ganin yanayin kamar yana cikin damuwa ne ya saka ta ajiye wayar dake hannunta, tare da mai da hankali akan mijinta.

Zama ya yi gefenta ta riko hannunsa cikin na ta.

"Please ki ke ki rarrashi yarinyar nan."

"Wace yarinyar kuma ?"

"Baƙuwarmu."

"Me ya same ta?"

Nan ya sanar da ita yadda suka yi da Hilal, ita ma ranta ya ɓaci sosai. Cikin takaici take cewa.

"Me ta yi masa ne haka?"

"Ba abun da ta yi masa, kawai dai sun tsani yarinyar da ƴan uwanta da iyayenta ne."

"Me ya saka haka suka zama kamar maƙiyan juna, alhalin jini ɗaya suke?"

Na ya bata labarin komai da musabbabin tushen GABAR CIKIN GIDA da suke yi. Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa.

"Wannan matsala tun farko kakanninsu ne suka haddasa ta, domin kuwa idan Allah ya baka ƴaƴa an sani dole akwai wanda kafi so a cikin ƴaƴanka amma kafa ja taɓa nuna wa ballantana sauran su fahimci kafi son ɗaya daga cikin yaran. Hakan na kawo matsala a tsakaninsu. Ballantana yadda ka sanar da ni sun fifita mahaifan Zahra da yawa. Kamar shi mahaifinta kaɗai suka haifa, ta yaya za ka banbance yaranka ta kowace fuska ka min yafi sauran ba kyau."

'Tashi ki je ki rarrashe ta Please."

Tashi ta yi ta je ta yi knocking a ɗakin. Sai da Zahra ta yi sauri ta goge hawayenta hawayenta tare da daidaita nutsuwata sannan ta ba da izinin shigowa .

Sumayya ce ta tashi tare shigo tsare da yin sallama. Zahra ta amsa mata tana ƙakalo mumrmushin wanda iya fatar bakinta kawai ta tsaya.

"Yi hakuri har kin shigo ban shirya ba na fito ba ko?"

'lafiya kamar kin yi kuka meke faruwa?"

A ganinta ba za ta iya fada mata ba, don haka sai ta ji murmushi tare da cewa.

"Ba damuwa bari na yi wankan yanzu na fito Aunty."

Kar ki kira ni da Aunty ina son mu zama ƙawaye ko bakya son mu kasance ƙawaye?"

Mumrmushin ta yi tare da cewa.

"To na daina in sha Allah."

Tana fadar haka ta nufi hanayar toilet tana cewa.

"Ina zuwa."

Murmushi kawai Sumayya ta yi don yarinyar ta burge ta, da wata ce da tana tambayar ta za ta saki baki ta dinga bada labarin familyn da abinda ake mata, ko zancen abun da Hilal ya mata ba t dauka za ta iya fada mata ba."

Wank ta yi tare da ɗauro alwala sannan ta fito, don lokacin sallar ta gabato

Mumrmushi suka sakarwa juna yayin da Sumayya ta ce

"Bari na zo Zahrah.'

Kai ta jinjina tare da cewa to.

Tana fita ta sanar wa mijinta yadda suka yi shima yarinyar ta burge shi.

Zahara kuwa jakarta ta bude ta ciri man shafawarta da powder.

Kaya ta ɗauko ta saka riga doguwar riga fitted grown na atamfar super england mai ruwan ƙasa da fari. Ɗan ƙaramin shafe ɗin ta ya fito ɗinkin ya karbe ta kuma ya zauna mata a jiki.

Gashin kanta ta tufke ta nannaɗe sannan ta ɗaura ɗankwali ta saka hijabi, in da ta ga sallaya ta nufa ta gabatar da sallar azahar.


Hilal wanka ya yi shi ma ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login