Showing 96001 words to 99000 words out of 154779 words

Chapter 33 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6256

fuskarsa ya sa sun fahimci har a lokacin ransa a ɓace yake. Dada ce ta ce

"Abgona waye ya ɓata maka rai ne yanzu ya ga ɓacin raina?"

Murmushi kawai irin ta su ta manya Papa ya yi kafin ya ce.

"A bashi abu mai sanyi da abinci ya sha tukunna dai."

"Ni fa ina fama da ƙafa ya je kitchen da kansa."

"Angon ne kuwa?"

Murmushi Dada ta yi ta nufi kitchen, abincin da Zahrah ta dafa ta zuba masa, sannan ta ɗauko jug wanda Zahrah ta haɗa masu zobo wanda da dafa shi da kayan ƙamshi. Ga cucumber 🥒 da ta yayyanka a ciki ana shan soɓon ana tauna cucumber. Sugar bai yi yawa ba daidai wa daida.

Gefe kuma sai ga farfesun kazar da Zahra ta yi shi tun jiya suka saka shi a fridge, nan da nan Dada ta ɗumama ta kawo masa.

Kasancewar a yunwace yake ya fara cin abincin, ya ji dadin shinkafar da ta ji Daddawa da kifi.

Yana ji yana shan zobon wanda ya ji daɗinsa sosai da sosai.

Sai da ya ci ya ƙoshi sannan ya ci farfesun.

Kallonsa suke yi cike da so da ƙaunar jikan na su, wanda daga Zahrah sai shi ne suka fi soyuwa a cikin zuƙatansu.

Yana tunanin yadda zai yi ya koma part ɗin sa. Ga shi kuma yadda aka ɓata part ɗin Faisal ba zai iya gyara masa shi yadda zai so ba.

Gajeren tsuki ya ja wanda bai san ya fito ba. Papa ya ce.

"Lafiya kuwa?"

"Papa wallahi ɗakina ba gyara yadda ya lalace ma Faisal ba zai iya gyara Mani shi ba."

Shiru suka yi kafin Dada ta ce.

"Ina zuwa."

Tashi ta yi daidai lokacin da ya koma kan kujera mai zaman mutum uku ya kwanta. Idanunsa a lumshe


Dada na shiga ɗakin ta samu Zahrah ta shirya cikin riga da wando ba barci farare.

Ta tufke kanta da ribbon ta sanya farin hula wanda ya kama kanta.

Sanyayyaen ƙamshin turarenta ke tashi daga jikinta.

Kallon Dada ta yi tana cewa.

"Dada yau da wuri zan kwanta shi ya sa ban fito ba."

Mumrmushin ta mayar mata da mrtani ta ce.

"Don Allah ki Mani wata alfarma mana."

"Dada kin fi ƙarfin kowace alfarma a wuri na, ki fadi ko me zan yi in sha Allah."

"Ƴaƴanku ne ya nake so ki je ku gyara masa part ɗin sa saboda ba zai iya kwanciya a yadda yake ba."

Da sauri ta sake kallon ta cike da mamaki take cewa.

"Yaa Mahmud ko Yaa Sadik?"

"Ai ba su kadai ne yayyunki ne yayyunki kadai ba, kada ki banbanta su da sauran duk da kasancewar ciki ɗaya kika fito da su na sani."

Shiru ta yi cikin sanyin jiki ta ce.

"Me zan yi Dada?"

"Ki je part ɗin Babban yayanku ki gyara masa yanzu don Allah?"

Sai da gabanta ya fadi sakamakon jin maganar Dada.

"Yaa Hilal kuma?"

"Eh don Allah ki je yanzu na san ba za ki jima ba, ya sa ƴan uwanki sun bata madadin gyara, kuma baya son masu aiki su shiga masa. Kuma Faisal ba zai iya yadda ya dace ba."

Ba ta ce komai ba don ba t son ta tsaya jayayya da Dada don haka ta saka Hijabi ta fito.

Papa ne a falon dai Hial wanda ya kwanta ya lumshe Idanu. Ƙamshin turaren ta da ya ji ya saka bude idanu sai zai bai ganta ba har ta fice.

Kai tsaye ta nufi part ɗin nasa. Toilet ta fara shiga ta wanke shi tas sai kamshi yake yi.

Kafin ta dawo bedroom, in da take tuninin za ta samu zanin gado nan ta duba, wani zanin gadon ta ciri ta zo ta shimfida ta gyara, rigunan pillows ta saka ta jera su yadda ya dace. Ta fesa turaren zanin gado a gadon. Ta ɗauko blanket ta shinfiɗa yadda ya dace.

Mopping stick ta dauko ta yi mopping ko ina tas.

Falo ta koma nan ma ta fara aikin goge kayan kallon. Sai da ta goge ko ina sannan ta yi mopping nan ma tas. Ta goge Centre table Centre Carpet dake jiƙe da ruwa ta cire ta fita da shi ta baya. A corridor ta hangi wani ta dauko ta shinfiɗa

Sai da ta tabbatar ta gyara komai ta goge ta fesa room freshener spray ta maida hijabinta da ta ajiye .

Fita ta yi bayan ta ja masa ƙofar.

Komawa ta yi part ɗin Dada da sallama suna zaune su uku.

Amsawa suka yi Dada ta kalle ta tare da Murmushi ta ce

"Sannu ƴar albarka har kin gama."

Eh kawai ta ce ta shige bedroom ɗin ta.

"Ka tashi ga Zahrah can ta gyara maka part ɗin."

"Zahrah kuma?"

Ya faɗa fuksa a tsuke.

"To idan ba ita ba ni ce zan gyara maka?"

Bai ce komai ba ya mike ya nufi kofar fita, Papa na masa sai da safe bai amsa ba ya fita .

"Wallahi wannan yaron lamarinsa sai shi."


Yana zuwa part ɗin na sa ya tura ƙofar falon. Kamshin da ya ziyarce shi ne ya saka ya saki ajiyar zuciya.
.
A hankali ya furta.

"Ma sha Allah."

Ganin komai yadda ya dace har ɗaukar Idanu ya ga falon na masa. Komai sai sanbarka.

Badroom ya nufa nan ma ya gan shi tass, ga shimfidar zanin gado an canza ya yi yi kyau. Toilet ya shiga ya ga ya fita tass.

Kayan jikinsa ya rage ya shiga bathroom don yin wanka.

Bayan ya fito ya shirye cikin kayan barci ya kwanta bayan ya yi addu'ar kwanciya barci.

Ƙamshin da gadon ke yi ya saka ya tsinci kansa cikin nishaɗi.


_Asadullah_

Sai Safa da marwa yake lokaci zuwa lokaci yake sauke idanunsa akan Jidderh.

Kallon Sulaiman ya yi kafin ya fitar da huci mai zafi ya fara magana.

"Abun mamaki ta ya ya za'a ce asibitoci uku kowanne suke cewa wai ƙwaƙwalwarta lafiya lau?"

"Sir gaskiya sakamakon iri daya ne ba wani banbanci."

"Idan nan sun kasa gano abinda ke damunta zan saka a fitar da iya waje."

"Waje kuma yallaɓai?"

"Eh ko kana da wani zaɓin ne?"

Girgiza kai ya yi sannan ya ce.

"Babu Yallaɓai "

"Okay hakan za'syi ka san sun fi mu ƙwararrun kayan aiki in sha Allah za'a dace."

"To Allah ya sa a dace."

"Amin ya Allah, wace ƙasar za'a kai ta?"

"India."

Ya faɗa a takaice har lokacin idanunsa na ga Jidderh.


_Innar Jidderh_

Tsaye take a tsakar gidan sanye da hijabi tana jiran fitowar su Isah da matarsa don zuwa Asadullah mansion.

Tare suka fito daga cikin ɗakin Sa'adatu na gaba isah na biye da ita a baya. Ta goya yaronta a baya.

A tare suka fita duk wanda ya kalli fuskarsu ya san cewa suna cikin damuwa.

Mai keke napep suka samu a bakin titin layin na su .

Sanar da su unguwar da zai kai su Isah ya yi kafin suka shiga ciki.

Hanyar da za ta sada su da hanyar unguwar suka ɗauka.


_Asadullah_

Yana zaune a falonsa shi da Barrister Haris. Cikin damuwa ya kalli Barrister Haris ya ce.

"Kafin s tafi da yarinyar nan kasar India dole ina bukatar mace da za ta kasance tare da ita. Sai dai a yanayin da nake ciki yanzu ina bukatar sirri, akwai abubuwa da yawa a gabana wanda ya kamata a ce na aiwatar da su, amma halin da yarinyar nan ke ciki ya dankwafar da duk wani motsi nawa, ba na da burin da ya wuce a ce na samawa yarinyar nan mafita kafin na yi aiwatar da abubuwa dake gaba na. A yanzu ba na da wani burin da ya wuce na ga ta dawo daidai kamar yadda take a baya. Yanzu Ina son ka samo mani wata mace wacce za ta rike mani sirri. Ta zo ta kula da yarinyar nan su tafi tare zan biya ta ko nawa yake so in dai za ta yi Mani Mani abun da nake buƙata."

"
Shiru Barrister Haris ya yi kafin ya ce.

"Akwai wata ƙanwar Matata mijinta ya rasu tana nan zaune tare da mu a gidana wajen matata. Na san za ta amince sai ta zo ta kula da aikin da kake bukatar na san ba za ta ba mu matsala ba zan mata gargadi sosai akan haka."

"Okay ba damuwa za ka iya kawo ta."

Sallama suka yi ya tashi ya mika masa hannu suka yi musabaha, kafin Asad ya ce .

"Idan ka dawo za mu yi wata magana in sha Allah akwai binciken da nake so ayi Mani."

"Okay in sha Allah."

Daga haka suka yi sallama ya fice.



_Inna_

Suna fitowa daga cikin keke napep ɗin Isah ya sallame shi.

Da ƙafa suka ƙarasa har bakin gate ɗin Asadullah mansion.

Nan security suka kore su ba su ma tsaya sauraren me ke tafe da su ba. Kuka Inna ta saka tana rokonsu su bari su shiga za ta yi magana da masu gidan ne.

Daidai lokacin wata motar ta ƙara so wajen. Gainsu ya saka motar ta tsaya a hankali Glass ɗin motar ya zuge.

A tare suka mike tsaye suka karasa jikin motar da hanzari jikin Inna har rawa yake yi.


*Naman Ihsan ce*✍️


09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect

*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*



*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*



Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.


Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.



Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩


1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more



Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.


*YAR GIDAN TAFIDA*


Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.



*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.

Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯



Page4️⃣7️⃣

A tare suka mike tsaye suka ƙarasa wajen jikin motar da hanzari jikin Inna har rawa yake yi.

Don sun tabbatar da cewa masu gidan ne suka zo, Kuma ganinsu da jin ta bakinsu zai iya tabbatar masu gaskiyar abun da suke son sani.

Dad ne a bayan motar sai Mom wacce take zaune a gefensa yayin da direbansa ke gaban motar sun je ɗauko shi daga airport.

"Bayin Allah lafiya?"

Inna ce ta ke ƙoƙarin durƙusawa Mom ta yi saurin dakatar da ita da cewa.

"Haba Mama don Allah ki tashi ba sai kin durƙusa ba, tashi mana."

Ta faɗa fudkarta ɗauke da Murmushi.

Kuɗi take ƙoƙarin ciro wa daga cikin jakarta, Inna ta yi saurin cewa.

"A'a Hajiya ba abun da ya kawo mu kenan ba."

"To me ya kawo ki?"

"Zancen ƴata dake aiki da ku ne."

"Okay ku shiga ciki sai mu yi magana ko?"

Security ɗin ta sanar da su cewa a bari su shiga ciki.

Nan suka bi bayan motar su zuwa cikin mansion ɗin.



_Maryam_

Tun daga ranar da Hilal ya saka masu dokar yin aiki da kansu ya kafu. Domin ba ƴar aikin da ta shiga ɓangaren su da sunan yi masu aiki. Haka zalika duk sanda za'ayi girki a gidan suna nan su za su yi amma da taimakon masu aiki.

Dan Maryam da Nabeela ke zuwa school su ma suna shekarar su ƙarshe ne, Nadeeya da Kausar kam sun gama. Zaharah dake ita ce ƙaramar gidan yanzu tana level 2.



_Hilal_

Fitowa ya yi daga part ɗin sa shi da ɗaya daga cikin sojojinsa. Wanda ake kira da James. Yana gaba James na binsa a baya. James ya nufi ƙofar fita hannunsa rike da wata ƴar jakka.

Hilal kai tsaye part ɗin mahaifiyarsa ya nufa.

Daddy da Faisal ne a falon. Gaida Daddy ya yi sannan Faisal ya gaishe shi.

Ya amsa sannan ya sanar wa Daddy zai koma America yanzu in sha Allah. Kallonsa Daddy ya yi sannan ya ce.

"Dama yau za ka tafi sau da ka shirya muke sani?"

"Kiran gaggawa na samu shi ya sa zan koma yau, da na so sai next week zan koma sai na sanar da ku yau."

Jinjina kai Daddy ya yi cike da gamsuwa sannan ya masa fatan alkahiri. Faisal ma ya masa fatan alkahiri, kallonsa ya yi ya ce.

"Ina Maryam?"
Ya yanzu ta tafi school."

Jinjina kai ya yi tare da cewa.

"Okay"

Bedroom ɗin Mummy ya nufa, knocking ya yi sai da ta bayar da izinin shiga sannan ya shiga.

"Assalamu alaikum"

"Ba ta amsa masa ba don a ƙule take da shi dama. Bai damu da rashin amsawar ba sai ya shiga ɗakin tana zaune a bakin gado fuskarta ba walwala.


"Barka da safiya Mummy."

Ba ta amsa masa ba sai ya yi shiru na sakanni kafin ya ce

"Dama tafiyar gaggawa ce ga taso mani, zan koma US yau in sha Allah."

Sai da ta yi kamar ba za ta yi magana ba sanan ta ce.

"Hilal wai me ka ɗauke ni ne?" Ina matsayin mahaifiyarka amma idan ka shigo ka gaishe ni shikenan, ba za ka bani lokaci mu yi magana ko wata fira tsakanin uwa da ɗa ba sai dai waɗan can tsofaffin Kakanninka su ka mayar uwa da uba ko? Ka fifita matsayinsu da kowa a wajenka. Ba ka da wajen cin abinci sai wajensu. Ba ka da wajen fira sai ɓangarensu. Hatta gidanka da ka kammala kafin ka kai ni ko Daddynka sai da ka kai su abin takaici har da wannan yarinyar mai ƙirar aljanun har da ita ka kai. Wai ma Meye hadinka da ita dama jira nake ka amsa mani ya aka yi turaren rigarka ya shafi rigarka, sanan ga shatin laɓɓanta a gaban rigarka alamar ka rungume ta kenan. To ka sani matukar kana son zamanka lafiya cikin salama ko magana ba na ƙaunar ta sake shiga tsakaninka da Zaharah ba da iyayenta kamar yadda kowa gidan nan ya killace kansa daga gare su amma kai na lura kai kaɗai ne a cikin yaran gidan nan ke da ra'ayin riƙau wanda sai abinda ka ga dama kake yi. To ka sani kan wannan yarinyar zan iya aikata maka komai akanta."

Ta karasa maganar tana huci.

A ciyar zuciya ya yi yana duba agogo dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa.

"Mommy na ga don na yi kusanci da Dada da Papa ba wani abu ba ne, su suka haifi Mahaifina da sune sanadin zuwansu duniya . Kuma gaskiya na fi jin dadi da samun nutsuwa a tare da su in dai ina kasar nan. Zancen Zahrah ko kusa ba na da wata ɓoyayyen alaƙa da ita ko iyayenta da yayunta."

"Na dai faɗa maka ko Gaisuwa ban yarda ta haɗa ka da su ba don wallahi idan ka ce za ka bijire wa magana ta akan waɗan nan mutanen zan iya yafe masu kai ko ma na cire ka daga cikin ƴaƴana. Duk yadda ya kasance ƙanin mahaifinka kuwa."

Bai ce komai ba don dai in da sabo ya saba jin tana masa fadar ya rage shigewa Kakannin na sa wai ba sa ƙaunarsu kowa sai Abbi da iyalansa.

Sallama ya yi mata ya fice tana sake jaddada masa abun da take faɗa.


Ɓangaren Abba ya nufa in da ya sake su gabadaya a falo. Gaishe da Abba da Umma ya yi sai Mansur da Nadiya suka gaishe shi.

Sallama ya yi wa masu suka masa fatan sauka lafiya ya fice daga part ɗin .

Daga nan ya nufi part ɗin Aunty Laila.

Sallama ya yi Aunty Laila dake zaune a falo taasa masa.

Bayan ta gaishe ta ne ya sanar da ita tafiyar da zai yi . Murmushi ta sakar masa tana cewa.

"Yanzu da ka aminci an yi aurenka da Kausar ko Nabeela ai da ka ga sai ka tafi da matarka can American."

Gajeren murmushi kawai ya yi wanda ya laɓɓansa kawai ya tsaya. Da

"Na san a cikin su biyu ba za ka rasa wacce ta kwanta maka a rai ba. Mun yi magana da Mummyn ta ka ta ce za ta maka magana akai."

"Aunty bari na wuce zan iya rasa jirgi."

Ba haka ta so ba sai dai ta yi masa fatan sauka lafiya . Don ta tsara cewar idan Hilal ya auri ɗaya daga cikin yaran na ta sai ta san yadda ta yi Ammar ya auri ɗaya daga cikinsu.


Daga nan ne ya nufi part ɗin Kakannin na su. Da sallama ya shiga ciki falon, Zaharah dake fitowa daga kitchen hannunta dauke da food flask da alama girki ta gama. Amsa masa sallamar ta yi daidai lokacin da suka haɗa Idanu. Harara ya galla mata fuska a murtuƙe.

Ɗauke Idanunta ta yi daga kallonsa cikin sanyin muryarta ta ce.

"Yaa Hilal da safiya."

Bai tanka mata ba dama ta sani kuma hakan bai dame ta ba in da sabo ta saba.

Wucewa ya yi ɗakin Papa duk da ya san cewa wanna lokacin yana barci.

Kwance ya same shi yana barci kamar yadda ya yi tunani,

'Tsoho ni zan tafi sai mun yi waya in sha Allah.'

Maganar da ya yi a zuciyarsa kenan sannan ya fice bayan ya shafi kan Papa wanda ke cike da furfura.

Fita ya yi in da ya tarar da Dada a falo tana yi wa Zahrah sannu da aiki. Ganinsa ya sa ta saki fara'a tana cewa

"Yaushe ka shigo?"

"Yanzu, kuma zan koma U.S ne?

"To kafin ka tafi ka zauna ka ci abinci ko?"

"Ina sauri ne kin san jirgi baya jiran mutum."

Addu'ar sauka lafiya ta yi masa ya amsa ya fice cikin zafin nama yake tafiya.

Zaharah ta cigaba da jera abincinta sannan ta kalli Dada dake daman kwararo masa addu'o'i.



_Mom_

Bayan direba ya yi parking motar ne ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login