Showing 75001 words to 78000 words out of 154779 words

Chapter 26 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6270

da ta yi magana ba ta dauki jakarta ta nufi part ɗin su. Duk yadda Ammar kar kiranta ba ta tsaya ba ta wuce ciki.

Ajiyar zuciya ya sauke sai a lokacin ya lura ashe Hilal ma ba ya wajen ya fice.

Yana shirin barin wajen sai ga Mummy, Umma da Aunty Laila sun shigo da alama daga unguwa suke.

"A'a'a yau Ammar kai ne a ƙasar ta mu?"

"Eh wallahi Mummy na zo ina tambayarku ya ce kun je biki."

Nan ya gaida su cikin girmamawa suka amsa cike da jin dad'i don sun san Ammar da hilal sosai. Don ko su idan sun tafi ƙasar London iyayen Ammar ba sa bari su sauka a hotel sai dai su sauka a gidansu. Kuma haka za su yi masu karamci har su kammala abun da za su yi su dawo . Kuma duk saboda amintar dake tsakanin Hilal da Ammar.

Aunty Laila ta ce.

"Ammar da alama ba ka ci abinci ba ko?"

"Aunty na ci abinci na yi wanka dama za mu fita ne tare da Hilal."

Mummy ce ya yi saurin cewa

"Ina Hilal ɗin yake ne?"

"Yanzu ya fira zan ce na same shi."

Yana fadar haka ya fita da sauri yayin da su kuma kowa ya nufi part ɗin sa.
"
Ammar na fita ya tarar da wani soja ya nufo shi yana sanar shi shi sakin ogansa. Akan cewa idan ya fito sojan ya dauko shi ya kai shi inda zai tafi.

Cikin takaicin halin Hilal ya sa Ammar ya koma ciki ya fasa fitar da za su yi.

Addu'a yake a zuciyarsa Allah ya saka ya sake tozali da sanyin idanunsa.

Ba kowa a Babban dakin gidan.
Zama ya yi sannan ya lalubo lambar Zahra da y samu.

Wayarsa ya lalubo ya dannawa Zahrah kira, har sau uku yana kira ba ta daga ba.

Wayarsa ta soma ruri yana dubawa ya ga sweet Mom.

Cikin farin ciki ya ce.

" Mom albishirinki."

Dariya ta yi tare da cewa.

"Ko gaisawa ba mu yi ba kana Mani albishir, kalli wannan babban albishir ne. ina jin ka"

"Mom Allah ya amshi addu'arjki yau na ga yarinyar da ta kwanta Mani."

Cikin farin ciki ta yi kabbarta tare da cewa.

"Alhamdulillah wata mai sa'ar ce haka?"

"Mom ni na yi Sa'a sai jin gan ta."

"Ƴar gidan waye?"

"Mom familyn Tafarki ce"

"Alhamdulillah ta zo gidan sauki ai."

"Dad dinsa dake gefe sai farin ciki yake yi . Ƙannensa mata biyu da Fareeda da Fareesha sai murna suke har da tsalle. Farida ta karbi wayar tare da cewa

"Yaya Please ka tura Mani pics din ta."

Nan suka dinga murna kamar wacce an ce an bashi ita .

Dad dinsa ya tabbatar masa zai zo ya samu Papa da kansa ya nema masa auren yarinyar.



*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)



*Sanarwa*

Wannan ƙirƙirerren labari ne ban yi shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali ya zo ɗaya to arashi, mai kashe auren wawa.


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page3️⃣8️⃣

Dad ɗin sa ya tabbatar masa zai zo ya samu Papa da kansa ya nema masa auren yarinyar.


*Washegari*

Kasancewar weekend ne Zahrah na gidan ba ta je school ba. Kuma dama ba ta cika zama a babban dinning table na gidan da kowa ke zama don cin abinci ba. Don dama dokar Papa ne tare ake cin abinci a gidan gabaɗaya bayan masu aiki sun kammala yin girki.

Zahrah kasancewar a ɓangaren Dada ta kwana don haka ta shiga kitchen don hada wa kanta breakfast. Don ta ce yau fankasau take son yi.

Don haka tun da asuba bayan ta gama azkar ɗin safiya ta shiga ta gaida Papa da Dada. Kitchen ta nufa ta kwaɓa fulawa ta ɗan zuba gishiri da sugar da Baking powder ta rufe.

Sannan ta fara shirin yin miyar taushe.



_Hilal_

Yana tashi da safe ya nufi ɗakin motsa jikinsa. Kasancewar tare da Ammar suka kwana a ɗakinsa. Ammar kam yana tashi ya yi ya yi wanka bayan ya fito ne ya tsane jikinsa sannan ya shafa man shafawar Hilal ya kuma saka kayan Hilal ɗin. Turarensa ya shafa sannan ya saka takalmi ya ɗauki wayoyinsa ya sauka zuwa downstairs.

Kamar yadda Papa ya wajabta wa kowa na gidan yin breakfast a tare da juna sai dai wanda baya nan ya fita.

Duk da hakan bai saka an samu jituwa a tsakanin Abbi da mutanen gidan ba.

Gabaɗaya jama'ar gidan sun taru a dinning area. Dada da Zahrah ce ba sa Wajen. Papa, Dady, Abba, Abbi, Mummy, Umma Ummi, Aunty Laila. Haka yara mazan gidan ma Hilal ne kawai ba ya wajen amma tun daga kan Mansur, Mahmud, Faisal, Sadik duk suna wajen. Haka ƴan matan gidan ma. Nabeela, Kausar, Nadiya da Maryam duk sun hallara kowa na cin abinda ransa ke so.


Ammar ne ya karaso wajen yana tafiya cikin halittarsa ta nutsuwa da cikar kamala.

"Assalamu alaikum warahmatullah"

Ƙamshin turaren Hilal da suka ji ne sun ɗauka shi ne, amma sai suka ji saɓanin abinda suka yi zato wato sallamar da Ammar ya masu. Sabanin Hilal da idan ba wanda ya kalli fuskarsa ba ba zai san ya yi sallamar ba.

Gabaɗaya ba wanda bai san Ammar ba a cikinsu, don haka Papa da bai san cewa ya iso kasar ba yake cewa.

"A yau mutane Ingila ne a kasar ta mu?"

Murmushi Ammar ya tare da sunkuyawa cikin girmamawa ya gaida Papa, ya amsa masa cikin jin dadi tare da tambayarsa iyayensa. Ya amsa da suna lafiya. Ya sake cewa yaushe ka ƙasar ne?"

"Jiya mun shiga ɓangaren ka ba ka nan."

"Eh to haka ne gaskiya juya sai dare na dawo."

Nan ya gaida su Dady da Abba da Abbi. Suka masa masa. Sannan ya gaida su Mummy Umma da Aunty Laila. Lokacin da ya sauke idanunsa kan Ummi sai ya ga tsananin kamanninta da Zahrah kamar ta yi kaki ta ajiye. Sai ya gaishe ta cikin girmamawa ta amsa masa cikin sakin fuska da walwala duk da ba ta san shi ba. Don ita ba ta cika zama main falon gidan ba ballantana ta san masu shige da ficen da ke zuwa gidan. Ko fitowa cin abinci sai Papa na. nan take fitowa wani lokaci za ta yi girkin ta a kitchen dake part ɗin ta ne.

Nan su Kausar suka shiga gaida shi cikin kauɗi. Ya amsa masu ba yabo ba fallasa. Shi dai bai ga Zahra ba kuma ba halin ya tambaya. Don haka ya kalli Papa ya ce.

"Ina Dada take?"

"Dada tana can ba ta fito ba ita da Zahrah wai can za su yi breakfast."

Jin an ce ita da Zahra ya fara tunanin ganin Zahrah.

"Son zo ka zauna mu yi breakfast tare mana. Duk da an kai maku a part ɗin abokinka, amma idan ka biye masa ba yanzu za ka ci abinci ba sai rana ta fito."

Murmushi ya yi tare da cewa.

"Bari na je na gaida Dada."

Yana gama fadar haka ya nufi part ɗin Dada.

Da sallama a bakinsa ya shiga falon, ta amsa tare da yi masa sannu da zuwa. Tana zaune a falo ita kaɗai ta kalle shi tare da washe baki ta ce

"Ammar kai ne?"

"Eh ni ne Dada?"

Ya karasa ya gida ita cikin girmamawa. Ta amsa tare da cewa.

"Ka ga mutanen Turai."

Zama ya yi yana addu'a Allah ya sa Zahra ta fito ya ganta.
Bai gama zancen zuci ba sai ga ta ta fito daga ɗakinta ta nufi kitchen.

Tana tafiya a hankali ta nufi matattakalar stage ɗin tana sanye da wando pallazo purple colour sai shirt wanda shi ma purple ne. Wato up and down ne a jikinta.

Kanta babu ɗankwali sai gashinta da ta yi parking a tsakiyar kanta ya sauka a gadon bayanta sai lilo yake yi. powder kawai ta shafa sai lips glow pink lips ɗin ta sai shinning yake yi.

Flasks din da ta zuba fankasau ta jera a babban faranti da farfesun kayan cikin da ta yi ta jera komai ta sannan ta ɗauki don zuwa wajen Dada su yi breakfast tare.

Sanyayyaen ƙamshin turerenta ke tashi daga jikinta. Tun fitowarta yake kallonta kamar zai cinye ta. Ita ko sam ba ta lura da shi ba, tafiyarta kawai take yi cikin nutsuwa.

Ta ƙaraso ta ajiye darantin a gaban Dada, ta zauna suna fuskantar juna fuskarra ɗauke da Murmushi ta ce

"Na san yawunki ta tsinke kin Kagara ki ci girkina ko?"

Taɓe baki Dada ta yi tare da cewa.

"Ai dole yarinya kin ɗauko hannun Umminki a wajen zaƙin girki."


Mumrmushin jin dadi ta yi, jin Muryar Dada ta yi tana cewa.

"Ga Yayanki nan ba ki gaishe shi ba "

Sai da gabanta ya faɗi sakamakon ƙamshin turaren Hilal da ta ji yo, don ƙamshin girkinta ya hana ta ji ƙamshin sai yanzu.

Tura baki ta yi don ko ta gaishe shi ta san ba amsawa yake yi ba. Don haka ta share kamar ba ta ji ba. Amma sai ta juya da sauri sakamakon jin wani muryar Ammar. Idanunta ta sauke cikin nasa yana sakar mata sanyayyar murmushinsa.

Da hanzarin ta koma dakinta dake nan part ɗin. Ba jimawa ta fito sanye da hijabi iya guiwarta ya tsaya mata.

Cikin sanyin murya ta ce.

"Ina kwana?"

"Lafiya lau ya kike?"

"Alhamdulillah."

Ta furta yayin da take bude flasks ɗin funkasau. Tare ta zuba masu ita da Dada kamar yadda suka saba ci . Ta zuba masu miyar taushe da ya ji naman kan rago.

Kallonta Dada ta yi tare da cewa.

"Ki zubawa Yayanki na shi mana."

"Ba musu ta tashi ta koma kitchen ɗin ta ɗauko plate ta zo ta zuba masa. Ruwan shayin da ta dafa wanda ya ji kayan ƙamshi ta zuba na su shi ma ta zuba masa bayan ta haɗa madara da milo. Sai biredi ta jera masa a gabansa.

A hankali ya furta .

"Na gode Beauty."



"Ko ba ka ra'ayin cin wannan akwai kaloli abinci a can babban falon ka fadi abinda kake so sai a kawo maka?"

"Dada waɗan nan ma sun isa."

Daga haka ta juya wajan Dada suna cigaba da yin kalaci yayin da Ammar ke ta santin girki.

Bayan Dada ta ƙoshi ta tashi don zuwa ta yi wanka.

Ya saura daga Ammar sai Zahrah. A falon.

"Beauty."

Ɗaga kai ta yi ta kalle shi

"Me ya saka ba ki ɗauki wayata ba?"

Shiru ba ta bashi amsa ba wanda hakan ya saka shi cewa.

Ba na da lokaci gobe zan koma saboda ina da wasu zirga-zirga da zan yi. Don Allah kafin na wuce in son jin ra'ayin ki ina fatan zan samu girbi a cikin birnin zuciyarki ko tauraruwar mata."

Shiru ba ta ce komai ba, ya cigaba da cewa.

"Idan ba ki mani magana ba yanzun nan zan yi maki kuka a wajen nan."

Jin haka ya saka ta ɗaga kai ta kalle shi wai zai yi kuka kamar wani ƙaramin yaro. Ba ta san lokacin da dariya ya suɓuce mata ba har sai da dimple ta suka motsa.

Sanye yake cikin ƙananan kaya riga ja da wando ɓaki Kyakkyawar ƙiransa na mazantaka da ƙuruciya sun bayyana . Turo ƙofar ya yi tare da yin sallama can ƙasan maƙoshi wanda shi kaɗai ya ji kayansa.

Idanunsa suka sauka akan Ammar da Zahrah da suke yi wa juna dariya. Wanda har sai da fararen haƙoranta suka bayyana, ga dimple ɗin ta ya lotsa sai dariya take masa. Shi ma kallonta yake yi ganin yadda take dariya daga cewa zai yi kuka.

Wani kallo Hilal ke bin su da shi fuskarsa ba sassauci. Zahrah dake facing ƙofar ta ga shigowar Hilal ɗin. Gabanta ne ya fadi sakamakon ganin fuskarsa da ya ba ta tsoro kamar wanda zai yi aman wuta.


*Ku yi hakuri da wannan*🙏🏻
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page3️⃣9️⃣


Wani kallo Hilal ke bin su da shi fuskarsa ba sassauci. Zahrah dake facing ƙofar ta ga shigowar Hilal ɗin . Gabanta ne ya fadi sakamakon ganin fuskarsa da ya ba ta tsoro kamar wanda zai yi aman wuta.

Kasancewar Ammar yana kallonta ne ya sa ya mai da hankali ga in da yake kallo. Bai damu da yanayin fuskar Hilal ɗin ba don ya san dama shi ba mutum mai fara'a ba ne.

Ƙarasowa ya yi ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon.

"Man ka shigo?"

Ya faɗa yana kallon Zahrah. Wacce ta sunkuyar da kanta tana juya zoben azurfan dake yatsarta.

"Eh na fito ya gajiyan hanya?"

Murmushi ya yi tare da cewa.

"Ai ba gajiya ga mutum da ya saba zirga-zirga."

Zahrah cikin sanyin muryarta ta gaida Hilal duk da ta san ba amsawa zai yi ba. Kuma bai amsar ba.


Dada ce ta dawo falon Idanunta a kan Zahrah da ta ji tana dariya.

"Ke kuma ina ta jin Muryar ki kina dariya keke baki dariya ne.'

Kallon Ammar ta yi ta ga yana kallonta yana murmushi.

"Ko ke da Ammar ne ya saka ki dariya haka, don idan ba shi ba kam ban ga abun da zai saka ki dariya."

"Kai kuma yaushe ka shigo?"

"Bai ba ta amsa ba ya ce.

"Barka da safiya."

"Yauwa barka dai ina fatan kana lafiya ya aiki?"

Ita ma bai amsa mata ba.

Zahrah ta kasa ɗaga kai saboda tasirin da kaifin idanunsa suke yi a jikinta. Tana jin tasirin Kaifin idanunsa a cikinta.

Ɗagowa ta yi ta kalle shi sai ya galla mata harara . Sauke Idanunta ta yi sannan ta ɗauki kofin shayin dake gabanta ta fara sha.

Dada ce ta kalli Ammar ta ce.

"Wai kai yaushe za ka yi aure ne, kar dai ka biyewa wa wannan abokin na ka da ya kusa zama tuzuru."

Dariya sosai Ammar ya yi tare da cewa.

"Ba zan biye masa ba Dada, ni idan har kun amince mani ma a cikin satin nan zan angwance."

Cikin rashin fahimta ta ce.

"Ni kuma Ammar?"

"Ƙwarari kuwa Kakus, idan za ki bani Wannan jikar taki."

Zahrah dake shan shayi har sai da ta ƙwarewa ta yi, cikin tashin hankali Ammar ya mika mata ruwa shi da Dada sai jera mata sannu suke yi. Shi ko gogan yana hakimce kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana latsa wayansa.

Dada ce take ɗan bubbuga bayanta tana shafawa alamar rarrashi.

Bayan tarin ya lafa ne Dada ta ce

"Ammar wannan ai ba hurumina ba ne, ka nemi soyayyar Zahrah idan ta amince ni ba ni da matsala sai ka nemi Papa. Duk da ba lallai ka samu hadin kansa ba don ban san me yake nufi da Zahrah ba. Lokacin da ta ci gasar karatun Kur'ani ta da ka gabatar na san kila ka sani ko?"

"Na dai ji labarin ƴar gidan nan ce ban ma san ita ba ce."

Murmushi ya yi tare da cewa.

"Allah akbar ashe hafizan alƙur'arni ce, tabbas na san na zaɓawa ƴaƴana uwa ta gari."

Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa.

"Dada kina nufin Papa ba zai yarda ba ne?"

"Ban san ya zai karbi zancen ka ba, amma a lokacin mutane manyan ƙasar nan sun zo nemam auren Zahrah wasu ƴaƴansu suka zo nema wa auren wasu kuma kansu suka zo nema wa. Kuma manyan mutane masu daraja da ba sa da aibu. Kai har ƴaƴan Gwamnoni da minister har kan manyan Mallamai amma Kakanta ya basu haƙuri don bai ma bari sun ga Zahrah ba. Sai ya ce tana da wanda za ta aura. Sai dai gaskiya ban sani ba ko a cikin samarin ta dake sonta ne. Don da wuya ta fita ba ta yi samu wanda ya nuna yana son ta ba. Hakan ya saka take fita da niƙab ko facemask."

Jinjina kai Ammar ya yi tare da cewa.

"Hakan ya mani."


Dada ta ce.

"Gaskiya sai dai ka nemi soyayyar Zahrah idan ta amince na tabbatar Papa ba zai yi mata dole ba zai bari ta zabi son ranta ne."

Jinjina kai ya yi tare da cewa.

"In sha Allah Dadarmu zan yi yadda kika ce."

Kallon Zahrah ya yi tare da cewa.

",Yau nake son komawa dama kwana ɗaya na zo da niyyar yi. Ban san ina ne part ɗin na ku ba, ki zo ki yi Mani jagora ina son na gaida su..."

Yadda ta zaro idanu ta rike baki ne ya saka bai karasa ba ya yi dariya.

"Ina son gabatar masu da kaina ne kafin na wuce. Na san yanzu kowa ya bar dinning area .

Kallonsa ta yi wato tun bai ji ra'ayinta ba har yana shirin gabatar da kansa ga su Abbi

Shiru ta yi masa ba ta motsa ba, ya cigaba da cewa.

"Please beauty ganin mu tare zai saka su san cewa saboda ke na je gaishe su "

"Tura baki ta yi a hankali ta ce ka je saboda Allah mana."

Hilal ne kawai ya ji me ta ce saboda yana da ƙarfin ji, duk yadda aka yi magana a hankali yana ji ko gulmarsa ba'ayi yana wajen. Duk da idanunsa na kan waya amma duk maganar da suke yi yana jin su. Ammar ya kalli Hilal ya ce.

"Man kai ya kamata ma na kama ƙafa da kai babban Yaya, ka raka ni sai ka gabatar masu da kaina."

Bai tanka ba ganin haka Ammar ya ce.

"Wannan bahagon mutum ba in da zai je na ga alama tun da bai san ciwon so ba, sai dai ka ji na yi aure na barka a tuzuru don ko zancen ba ka yi."

Ganin bai tanka shi ba ya kalli Zahra ya ce.

"Beauty."

Ita kunya ce ma ya bata tana don tashi ta bar wajen ta kasa.

",Bana da isasshen lokaci Please ko ba za ku shiga ba ki tsaya daga main falo ki nuna mani zan shiga ni kaɗai."

Ganin ko motsi ba ta yi ba Dada ta ce.

"Ba na son gulma ba tun ina ciki nake jiyo Muryarki kina ta masa dariya ba kuma
Fira. Yanzu ki nuna masa waje ne kike wani ñoƙe-noƙe?"

Tashi ya yi ya yi gaba ita ma ta mike za ta bi bayansa. Tana kawowa saitin kujerar da Hilal ke zaune ya sanya ƙafarsa ya harɗe mata ƙafa ta faɗi ƙasa. Ƙara ta saki ya sa yatsarsa ya ɗalle mata baki ta saka kuka."

Dada ta ɗauka faɗuwa ce ta yi sai salati take yi tare da tambayarta garin ya ta fadi haka. Ammar ne ya yi wa Hilal wani kallon mamaki don ya ga sanda ya harɗe ta sannan ya bugar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login