Showing 153001 words to 154779 words out of 154779 words

Chapter 52 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6276

je yi mata komai. Wankan ne kawai yake bari Anisa ke yi mata shi ma sai ya tabbatar an yi mata da sabulun da Mallam ya bayar.

Mallam ya tashi tafiya Asad ya mike zai raka shi zuwa wajen mashin ɗin sa dake waje. Da

Bayan ya raka shi ne Isa wajan mashin ɗin sa ya hau mashin ɗin ya tafi. Har lokacin Facemask ne a fuskar Asad wanda idan ba ka yi masa farin sani ba to ba za ka gane shi ne ba

Tashin mashin ɗin kenan yana barin wajen Asad ya juya da niyyar komawa cikin gidan. Da sauri ya durƙusa don kare kansa.

Ta jikin gate ɗin gidan ya kalli wanda ke bayan da rike da wani karfe zai buga masa a kai.

Sake yunkurin buga masa ya yi a karo na biyu, nan ma ya kauce daga nan suka fara kokawa da shi, sosai suke kokawa da juna.

Cikin ikon Allah Asad ya kayar da mutumin ƙasa yana ƙoƙarin cire cire masa abinda ya rufe fuska da shi indanusa kawai ake gani.

Suna tsaka da kokowa sai motar Sulaiman ta karaso wajen, a lokacin mutumin ya samu wani karfi har ya iya ƙwayar kansa daga hannun Asad ya ruga a guje kafin Sulaiman ya karaso wajen.

Bin bayansa ya yi suna gudu kafin ya cin masa ya ga ya hau bayan wani mai mashin da alama jirsnsa yake yi.

A guje suka bar wajen Sulaiman ya dumƙule hannu ya naushi iska.

Dawowa ya yi ya samu uban gidansa tsaye kamar wanda aka dasa a wajen.

"Sir."

Sai a lokacin ya ɗago ya kalli Sulaiman ba tare da ya ce komai ba.

"Are you okay?"

Kai kawai ya jinjina sannan ya yi magana cikin kamilalliyar muryarsa mai cike da nutsuwa ya ce.

"Am okay"

Cikin gidan suka shiga in da suka yada zango a falo. Jidderh ce kawai ke barci a falon kan kujerar mai zaman mutum uku.

Asad ya zauna har lokacin ya sa magana a abubuwa sun yi masa. Indanusa sun yi ja ya dafe kansa da hannayensa biyu.

"Me ya faru ne har hakan ta faru?"

"Mallam dake wa Jidderh magani ne ya zo sai na raka shi iya ka ta bakin gate ɗin.

Yana hawa mashin na juyo zan dawo sai na hangi mutum ta jikin glass ɗin, da ba don Allah ne ya kare ni ba dan Allah ya kare ni wannan karfe bai daki kai na ba da yanzu sai dai wani labarin ake yi."

"Sir, shi ya na ce ka yi tunani cikin mutane ukun da suka san inda kake tabbas ko ma waye yana daya daga cikin masu son ganin bayanka. Amma kai ka yarda da kowa, kuka a wannan yanayin da ake ciki bai kamata a ce kana saurin yarda da kowa ba, domin wani lokacin wanda ka yarda shi ko ba ka yi zato ba sai a wayi gari ya cuce ka

Tashi ya yi ya nufi upstairs Yana cewa.

"Ka tafi ina son kadaici z ka iya dawowa gobe."

Yana fadar haka ya haura sama.


_Hilal_

Fitowar sa daga wanka kenan yana goge jikinsa wayarsa ta yi ruri, yana dubawa ya ga Jamilu ne mijin Sumayyaa da suka sauka a gidansa shi da Zahrah.

Ɗagawa ya yi suka gaisa da shi.

"Ina Amarya ne wallahi ga Sumayya sai farin ciki take yi tun da na sanar da ita aurenka da Zahrah."

Bai ce komai ba in da Jamilu ya cigaba da cewa.

"Gaskiya na taya ka murna ka yi sa'ar mace tagari, ai ina ga yadda ta dame ni zuwa next week za mu shigo mu ga Amarya. Kafin nan tana son ta yi magana da ita."

"Ban sani ba ko ta tashi yanzu."

"Kamar ya kai kana ina?"

"Ina ɗakina."

"Ita kuma tana ina?"

"Tana ɗakinta."

"Man idan za ka ajiye girman kai da izzar da kake da shi ka ajiye, mata duniya ne."

"Ba sai kun yi wahalar zuwa ba."

"Saboda me?"

"Saboda ta ce na sake ta ba ta sona, idan ba haka ba za'a wayi gari a ga gawar ta."

"Subhanallah, kai yanzu za ka iya sakinta?"

"Why not?"

"Kada ka biye mata na san idan ka cigaba da lallaɓa ta da kyautata mata za ta so ka, domin ita zuciya an halicce ta na bisa ga son wanda ya kyautata mata da kuma kin wanda ya munana mata."

"Akwai wani abokina Ammar na san ka san shi, to ya fara nemanta suna soyayya ta ce Mani shi take so, ta nemi na sake ta."

"To yanzu sakinta za ka yi?"

Murmushin gefen baki ya saki kafin ya ce.

"To ya zan yi?"

Ganin ɗayar wayarsa na ruri ya saka ya yi wa Jamil Sallama ya katse kiran wayar.



_Aunty Laila_

Bayan sun gama magana da Umma akan za ta je gidan Sadik ta binciko gaskiyar magana ko Sadik ya yi mu'amalar aure da ita kamar yadda Nabeela ta faɗa. Mummy da Ummar sun goyi bayanta idan har da gaske ne to Aunty Laila ta yi mata dukan tsiya, sannan ta tabbatar tare da ita ta bar gidan Sadik, ba za su kawo ta nan ba, sai dai za su kai ta gidan ƙanwar Umma."


Direba ta saka ya kai ta gidan Sadik ɗin, kai tsaye ya dauki hanyar zuwa gidan, horn ya yi maigadi ya bude yana masu sannu da zuwa.

Tambayar sa ta yi ko Sadik na gidan, ya ce mata baya nan ya fita.


Ta ce wa Direban ya ajiye motar a waje yanzu za ta dawo.

Tana shiga falon ko sallama babu.

"Nadeeya dake waya da Sadik tana ta zuba masa shagwaɓa wai har yanzu ba ta warke bai tsaya jinyar ta ba ya wuce ya bar ta. Tana wayar cike da shagwaɓa, tana jin dadin yadda yake kula da ita yana biye wa shagwaɓa da take masa abun da ba ta yi tuninin samun kansa cikin sauki ba, amma saboda samunta ya dace ta kawo masa mutumcin ta gidan sa ya saka yake ganin wani ƙimarta a idanusa.

Ba ƙaramin firgici Nadeeya ta yi ba na ganin Aunty Laila, ta san ba alkhairi ya kawo ta ba.

"Aunty kece da safen nan?"

Sadik da ya ji Muryar ta cikin firgici ya saka ya katse kiran wayar, ƙara taka motar ya yi sakamakon ya san Sunyi Laila ce ta je gidan. Kuma da gangan ya yi maganar a gaban Nabeela saboda ta isar da sakon ga iyayenta. Don ya san komai

Hakuri yake bata akan cewa tana ransa ga shi nan dawowa.

Don a lokacin Driving yake yi suke waya.

Ganin Aunty Laila ta shigo cikin mamaki ta ce "Aunty kece?"

"Wato ke dake yar banzar yarinya ce duk maganar da muka yi maki ya shiga ya fita daga kunnenki ne ko?"

"Aunty me na yi?"

"Ba komai je ki kawo Mani ruwa na sha."

"Lah ga ruwa a nan ai yanzu na dauko ban sha ba."

Ta yi maganar tana ɗaukar bottle watar mai sanyi za ta zuba wa Aunty Laila.

"Ba lemu a gidan ne?"

Sanin halin Sunyi Laila da bin ƙwakkwafi idan ta tashi zarta gane wani abunne ya faru tsakanin ta da Sadik, tunda yanayin tafiyarta ya canza.

"Aunty ba lemu ruwa ne kawai a gidan, tun da jiya muka tare sai yau zai kawo."

Jinjina kai Aunty Laila ta yi tare da cewa.

"Okay wannan ruwan ya mani sanyi ina mura, je ki kawo mara sanyi."

Jikinta ne ya yi sanyi, amma ba wata hanyar dole sai ta tashi.

A hankali ta mike ta fara tafiya cikin kokarin daidaita tafiyar yadda Aunty Laila ba za ta fahimci komai ba.

Shigar ta kitchen ba jimawa sai ga ta ɗauke da faranti da ruwa har da lemu.

Tana zuwa ta zauna bayan ya ajiye mata a gaban ta saman Centre table.

"Ina fatan dai kin dauki zantukan da muka yi maki, kina gasa masa aya a hannu."

"Sosai kuwa."

Finciko ta ta yi tare da cewa .

"Munafuka zo na dubu ki ban yarda da ke ba sai ba duba ki, kwanta na gani Allah sai na dub ko na tabbatar bai taba ki ba."

Ta yiagamar yana nuna wa Nadeeya doguwar kujerar wai ta kwanta.

Kuka Nadeeya ta saka tana cewa ba abinda ya faru tsakanin ta da Sadik.

"Za ki tsaya na duba ki ko sai na ci mutuncin ki a wajan nan?"

A hankali ta durkusa tana kuka.

"Kum yanzu za ki bar gidan nan, ba za ki kwanta na duba ki ba sai na Maki dukan tsiya.

"Tana kuka za ta kwanta kenan sai ga Sadik ya turo kofar y shigo."

"Akan me za ki duba ta saboda ta aikata zunubi?"

"Kai mara kunya ka iya bakinka ko uwar ka A'isha ba ta isa..."

Kafin ta yi wata magana sai ya finciki hannunta y yi waje da ita, a harabar gidan sannan ya sake hannunta.

Alama ya yi wa Maigadi, wanda a guje ya tashi ya nufi ɗakin karnuka.

A bude karnukan suka yi kan Aunty Laila, a guje suna haushi.

Ihu ta ƙwala ta nufi hanyar gate ɗin. Takaliminta ma faduwa suka yi, sai da ta fadi ta fasa baki kafin ta tashi da ƙyar ta cigaba da gudun. Mayafinta ma faduwa ya yi, tana fita ta fada mota ba tare da ta jira direban ya bude ba.

Sai haki take yi tana tsinewa Sadik albarka.

"Hajiya lafiya ?"

"Dalla mu je ina ruwanka."

Bakinta da ya fashe jini ke fita ta goge tana cewa.

"Allah ya tsinewa Sadik albarka A'isha ta haifo mana masifa da bala'i a cikin zuriya."

Tsinewa Sadik take yi har suka isa gidan.



_Hilal_

Fita y yi daga cikin gidan bayan ya yi order abinci ya ajiye wa Zahrah.

Driving yake yi ransa a ɓace , sai magan yake yi shi kadai a cikin motar.

"Mummi, Aunty Laila, Doctor why? MD ya saka kuka aikata haka? Tabbas zan aikata abinda ba yi maku dadi ba, Doctor yau zan hadu da ko kuma za ka girbi abunda ka shuka. Ba abinda zan wanke Zahrah da shi kamar na sex da ita a cikin gidan tafarki, na kira Sunyi Laila da Mummy zan ce su taimaka mata, a lokacin za ku amsa Mani tambayoyin da zan yi maku tambayoyi dole ku amsa Mani tambayoyin da zan yi maku."



_Asadullah_

Yana zaune bakin swimming pool ya yi nisa cikin tunani,

Wata mace sanye da bakin kaya har da niƙab a fuskarta. Hannunta rike da wauka, tana zuwa bayansa ta soka masa wuƙar ta bayansa .

Daidai lokazin Jidderh ta farka ta daki wani ihu mai ƙarfi, tana cewa.

"Yallaɓai.!?"

Ihu ta yi fa kati sakamakon mafarkin an soka wa Asadullah wuka ta rikice.

" Guje ta fito daga dakin ta hadu da kuku, kallonta yake yi yana mamakin jin tana magana. Son shi bai taɓa jin ta yi magana.

"Ina yallaɓai yake yake?"
Mamaki yake yana farin ciki da alama ta samu lafiya.

Fita ta yi zuwa harabar gidanz, zare idanu ta yi tana kallon wajen, kafin ta ruga zuwa wajen guje.


*Alhamdulillah na kammala book 1 ga mai son karanta book 2 sai tura ₦500 ta wannan account number. 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wannan lambar waya.09065327995*


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login