Showing 66001 words to 69000 words out of 154779 words
ya mayar da ƙofar ya rufe. Yana sanye da ƙananan kaya, sai dai ba za'a iya shaida kakanninsa ba, sakamakon ya sanya P. Cap 🧢 a kansa sannan ya sanya face mask 😷 a fuskarsa ga bakin gilashi a idanunsa.
A hankali ya ƙara so gaban Asadullah ya janyo wata kujera ya zauna suna fuskantar juna.
"Asad ya kake?"
Kallo ɗaya Asad ya masa ya kauda kansa gefe .
Dariya mai sauti mutumin ya yi sannan ya ce.
Bari na baka wani labarin abun da ba ka sani ba, ko kuka na yi maka fashin baki akan a abinda ya shige maka duhu."
Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa na san ba za ka mance ranar 27 ga watan Oktoba ba na shekarar na shekarar dubu biya da sha huɗu. Ranar da ka kawo abokinka cikin mansion ɗin nan."
A hankali Asadullah ya fara tuno abinda ya faru a wancan ranar.
Tafiya suke yi cikin motocinsu yayin da motoci biyar ne suka suke a jere sai dai ta tsakiyar tafi kyau da tsaruwa. Don da alama ita ce wacce uban gidan na su ke ciki. Biyun da ke gabansa da biyun dake bayansa .
Sanye take cikin Suit fara ta cikinsa ma fara sai bakin necktie da ya ɗaura a wuyansa . Takaliminsa ma baki sai sheƙi suke yi agogon hannunsa ya duba tare da kan gajeren tsuki. Daidai lokacin ya kalli gefensa idanunsa ya sauks akan abokinsa Sagir wanda suka yi secondry school tare.
Alamar tsayar da motar ya yi wa Direba. Take duka motocin suka tsaya, ya yi wa ɗaya daga cikin guard ɗin alamar ya kira masa wancan mutumin.
Take kuwa suka dawo tare ya yi masa alama da ya shigo cikin motar, kasancewar a ƙasa yake tafiya. Sam bai gane Asad ba.
Guard ɗin ya ce masa
"ka shiga daga ciki."
"Na shiga ina a wannan zamanin na rashin tsaro na san ina za ku kai ni?"
Mumrmushi Asad ya yi tare da cewa.
"Sagir Ibrahim Sahabi."
Wato idanu ya yi tare da cewa
"Asadullah Ahmad Abubakar?"
Jinjina masa kai ya yi tare da sake wani murmushi.
Da sauri ya shiga ya zauna gefensa yana dariya.
Suka cigaba da tafiya.
"Sagir ya na ganka haka?"
"Ai dole ka ganni haka domin mahaifiyata da mahaifina sun rasu, ga bashin da ake bin mahaifina da aka biya jama'a bashi har da na banki haka ban tsira da komai ba, hatta gidan da nake ciki sai da aka siyar da shi yanzu haka ɗakin wani abokina nake kwana shi da ƙaninsa yanzu haka a takure nake a cikin ɗakin.
Jinjina kai Asad ya yi tare da yi masa addu'ar Allah ya ya jikin iyayen nashi. Ya amsa da Amin.
"Ya zancen aiki fa ana zuwa aiki ne?"
"Har yanzu ban samu aiki ba ka san yanayin ƙasar aiki sai mai hanya."
"Kada ka damu lokacin samun aikinka ya yi, yanzu ka koma can in da kake ka ɗebo duk wani abun da ka san kana bukata ka zo zan baka wajan zama da aikin yi."
Zaro ido Sagir ya yi tare da cewa.
"Da gaske kake yi abokina?"
Jinjina masa kai kawai ya yi alamar gamsarwa. Tasanar murna da farin ciki bai san lokacin da ya rungume Asadullah ba.
Kai tsaye suka nufi *ASADULLAH GLOBAL RESOURCES*
sai a lokacin Sagir ya lalle shi ya ce.
"Dama kai ne kake da ASADULLAH GLOBAL RESOURCES da kuma ASADULLAH INVESTMENT NIGERIA LIMITED? kai ne me wannan hamshaƙin ɗan kasuwa da ake faɗa?"
Murmushi ya sakar masa ba tare da ya ce komai ba. Kallon Sulaiman amintaccen bodyguard ɗinsa da ke gefen direba ya yi ya sanar da shi cewa ya sa ɗaya daga cikin direbobin su ya kai Sagir gidan da zai je ya kwaso kayansa.
Haka kuwa aka yi Direban ya kai shi ya kwaso kayansa ya yi wa masu ɗakin sallama ya shiga mota suka bar layin
Asadullahi na zuwa kamfanin bai wani jima ba ya bar komai a hannun ƙaninsa Kamal, yayin da ya koma gida tare da muƙarrabansa.
Wani part ya bawa Sagir a cikin Asadullah mansion ya zauna a ciki.
Sannan ya kira Jidderh ya saka y don ta gyara part ɗin. Bayan haka ya masa alƙawarin bashi aiki a kamfanin bayan ya karbi takardunsa.
Haka kuwa aka yi washegari Asad ya ba shi gurbin aiki a kamfaninsa. Ya yi matukar farin ciki da wannan aiki. Wajen ɗaya suke da Kamal don shi ne mataimakin Kamal ɗin.
Bayan wata ɗaya da faruwar haka sai kuɗaɗen suka dinga ɓacewa a cikin kamfanin. Dan miliyoyin kuɗaɗen ne ake sacewa.
Lokacin da abun ya ishe shi bayan ya gano cewa ta hanyar Kamal da Sagir kudaden ke fita, don haka ya kira Abokin nasa Sagir da ƙanin nasa Kamal ya yi ya nuna ɓacin ransa akan abun da suke yi na almundahana da ku kudaden kamfani. Sannan ya yi masu maganar cewa idan albashi da ake biyansu ya masu kadan ne ko suna bukatar kudi su tambaye shi mana, zai iya kara masu ko ya basu. A lokacin sun bashi hakuri ne, sannan a wannan watannin kuɗaɗen suka ƙara ɓata kimanin Naira Miliyan Hamsin. A lokacin bai masu magana ba ya ƙale su bayan kwana biyu aka sake sanar da shi cewa miliyan ɗari aka rasa kuma an tabbatar ta hannunsu kai dai ne kudaden kamfani za su iya fita. Daga nan ya dakatar da su daga aiki har sai ya gama bincike.
A binciken da ya yi ne ya gano ba iya kudaden da suka ɓata ba kenan, ransa ya ɓaci ƙarshe ya ce su rubuta takardar barin aiki su kawo masa.
Kallomsu ɗaya bayan ɗaya ya yi tare da cewa.
"Ƙanina da abokina sune suka yi Mani wannan aiki. Da ace wasu ne suka yi Mani ba zan yi mamaki ba, amma a ce ku makusanta na da na yarda da ku ne kuke Mani wannan ta'asar."
Kallon Kamal ya yi da cewa.
"Ina za ka kai waɗan nan kuɗaɗen haka, me za k yi da su, idan kana bukatar abu ka tambaye ni ba zan iya yi maka ba ne? Kana jinina ne ka yi mani wannan abun me ya saka ba za ka tambaye ni ba."
Sunkuyar da kai ƙasa ya yi tare da cewa.
"Yaya dan Allah ka yi haƙuri."
Hakuri kam ya ƙare don dole za ku bar aiki a nan don ba zan sake yarda da ku ba, kun ci amanata yayin da na ɗauki yarda ba baku. Na baku damar canzawa ba ku canza ba yanzu kam bakin alkalami ya riga ya bushe."
Zufa ce ta karyo masu suka fita jiki ba ƙwari.
*Bayan awanni uku*
Yana zaune a office ɗin sa ya sanya system a gaba yana duba wasu bayanai.
Wayarsa ce ta yi ruri yana dubawa ya ga Sagir ne yake kiransa. Ya ɗaga take ya mike a firgice. Katse kiran wayar ya yi tare da fice wa a guje ko ta kan wayarsa bai yi ba ya fice.
Yana fita ya samu Sagir a tsaye, cikin tashin hankali yake cewa .
"Ina Ƙanina yake?!"
"Mu je abokina, wallahi ƙaninka yana cikin mawuyacin hali."
Ya faɗa yana bude masa murfin motarsa wanda Asad ya siya masa lokacin da ya bashi aiki."
Shigewa ya yi bodyguard ɗin sa na kokarin yin magana Sagir ya ce.
"Ku jira mu yanzu za mu dawo "
Ya faɗa sannan ya figi motar a guje ya bar kamfanin. Slaiman ne ya bawa sauran bodyguard ɗin umarnin su bi bayansu.
Take suka shiga motocinsu suka bi bayansu. Sai dai cikin rashin sa'a suka kasa gane in da motar Sagir ta bi.
Don haka sai suka bi haryar da ta sha bamban da wanda suka bi.
Gudu Sagir yake yi kamar zai tashi sama. Asadullah na tambayarsa wani asibiti Kamal yake ya ce masa bayan gari. Da mamaki yake kallonsa tare da tambayarsa.
"Kamar ya bayan gari ba asibiti ne sai bayan gari?"
"Abokina yanzu ba lokacin tambaya ba ne mu je kawai ka gan shi."
Asadullah bai sake cewa komai ba fatansa Allah ya kai su ya ga ɗan uwansa.
Sai da suka kai wajen da ba kowa sun sauka akan hanya tun daga nesa ya hangi Kamal a kwance. Suna karasawa ko parking din kirki bai bari Sagir ya yi ba ya fita ya nufa in da Kamal ke kwance. Ya
"Ƙanina lafiya me ya same ka?"
Kamal da idanunsa ke rufe ne ya buɗe idanunsa tare da watsawa Asad wani banzan kallo.
"Meke damunka tashi mu je asibi..."
Kafin ya ƙarasa magana Kamal ya fito da wuƙa daga ƙasansa ya soka wa Asadullah a ciki."
Tsabar azabar da ya ji ne ya saka ya saki wani sautin azaba, bai gama dawowa daga duniyar azabar da ya ji ba ne ya ji an sake suka mashi wukar ta bayansa.
Ya juyo don ganin wanda ya soke shi ta baya, amma bai samu ganin ko waye ba sakamakon duniyar da ya ji tana juya masa take ya zube a wajen jini na fita daga jikinsa.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page 3️⃣4️⃣
Yana juyawa dan ganin wanda ya soke shi ta baya, amma bai samu ganin ko waye ba sakamakon duniyar da ya ji tana juya masa take ya zube a wajen jini na zuba a jikinsa.
Sagir ne ya saki wata dariya yana kallon Kamal tare da yi masa jinjina da hannu, shi ma alamar jinjinnar ya yi masa. Ya mike.
"Ina fatan ya wulla lahira ko?"
Kamal ya fadi maganar ya yin da ya mike yana kakkabe rigarsa.
Sagir ne ya sunkuya ya kai hannunsa daidai saitin hancin Asadullah.
Jin baya numfashi ne ya kalli Kamal tare da cewa.
"Mun gama da shi, ka yi sauri mu bar wajen nan kada wani ya biyo ya tarar da mu."
"To ya za mu yi da gawar?"
Kamal ya tambaya cikin yanayin damuwa kamar zai yi kuka?
"Ka yi hauka ne, ta ya ya zamu dauki gawar mu ce me?"
Sagir ya bashi amsa yana hararar shi.
"To ya za ka yi na san dole guard ɗin sa sun ga fitarku dole za'a tuhume ka."
"Shi ya sa na ce maka kuɗaɗen nan za su ishe ni na bar ƙasar nan zuwa wata ƙasar na gina sabuwar rayuwa. Don haka za mu rabu a nan. Yanzu sauran aiki ya rage naka idan ka iya allonka ka wanke."
Cikin damuwa Kamal ya ce yanzu wata ƙasar za ka tafi. Sai da ya bude murfin motarsa zai shiga sannan ya ce.
"Ba zan iya fada maka in da zan tafi ba, domin hakan na iya zama hatsari a gare ni, na gode da taimakonka. Sai dai ka yi gaggawar barin wajen nan kada bincike ya biyo ta kanka. Hakan zai iya shafar siyasarka."
Dawo wa ya yi ya ya ɗauke manya-manyan wuƙaken da suka soke su da shi yana cewa wannan ma hujja ce ba zan barta ba."
Yana gama fadar haka ya shige motarsa ya bar wajen a guje.
Cikin tashin hankali da Fargaba shi ma ya shiga motarsa ya bar wajen.
Bayan mintuna biyar da barinsa wajen dai ga guard ɗin Asadullah sun ƙaraso wajen sakamakon hanyar da suka bi ba su ga alamar su hanyar ba.
Burki suka ja da karfi suka fito a guje zuwa in da yake kwance.
Baya motsi ga shi kwance cikin jini. Cikin tashin hankali suka ɗauke shi zuwa asibiti baya numfashi.
Tsawon sati ɗaya bai farfaɗo ba, sai dai likitoci sun dukafa akansa. Sai dai sun tabbatar yana raye zai iya farfaɗo wa a kowane lokaci. Ga shi abokinsa da aka ce sun fita tare da Asad kafin aka tsince shi ba wanda ya san in da abokin yake ba.
Ganin halin da yake ciki ne ya saka Dad da Uncle Adam suka matsa akan a fitar da shi ƙasar waje.
Ba tare da ɓata lokaci ba aka shirya komai aka ɗauke shi zuwa ƙasar India. Dad, Mom, da uncle Adam suka tafi tare da shi.
Cikin ikon Allah washegarin ranar da aka kai shi ya dawo cikin hayyacinsa.
A ranar da ya dawo cikin hayyacinsa. A ranar Uncle Adam ya koma Nigeria. Mom da Dad suke tare da shi. Duk da ba zama wajensa suke yi ba kasancewar ma'aikatan asibitin ne ke kula da shi. Mom da Dad a hotel suke kwana washegari su dawo nan asibiti.
Bayan sati biyu aka sallame su ya warware garau. Har lokacin ba wanda ya tambaye shi wanda ya yi masa wannan aika-aikar. Ganin yanayin da yake ciki kamar wanda ke cikin ruɗani.
A ranar ne suka dawo ƙasar 9ja cikin farin ciki da annuri.
Dad ya dinga kiran wayar Kamal don ya kira shi ya zo ya ɗauke su amma wayar a kashe take.
Don haka ya kira Uncle Adam ya sanar da shi, Uncle Adam ba ya gari don haka ya kira ɗan sa Nasir ya sanar da shi. Take ya ɗauki key ɗin mota yana sanar da Mami in da zai je. Ganin haka ya saka Abida ta mike zurun za ta bishi. Maryam ma haka ta je za ta je ta tarbo masoyinta. Dakatar da su ya yi tare da cewa da mutum ɗaya zai tafi, sai ya yanke shawarar zuwa da Abida kasancewar ita ta fara yin magana. Maryam ya ce ta yi hakuri ta tarebe shi a gida.
Ba da son ranta ba ta hakura Abida ta bishi cikin rawar jiki. Cike da farin ciki suka fita daga cikin ASADULLAH MANSION ɗin.
Bayan sun ɗauko su akan hanyarsu ta dawowa ne Dad ke tambayar Nasir in da Kamal yake don wayarsa ba ta shiga.
Ya ce juya dai sun ga juna da safe amma yau bai saka Kamal a idanunsa ba kenan.
Mummy ta ce.
"Ko yana kamfani ne tun da shi ke kula da kamfanonin ɗan uwansa."
Ba mai Wannan amsar don haka suka yi shiru aka koma gida. Kowa ya ga Canji a wajen Asadullah don ko magana ba ya son yi. Wannan murmushi da ya saba yi a cikin ƴan uwansa duk babu ga kowa ya taru har da uncle Adam da iyalansa bangaren Dad ma kowa na nan hatta Hajiya Zulaihat wacce suke kira da Aunty ta zo duk da kasancewar ba ta shiga lamarin mutanen gidan musamman Asadullah.
Har da ƴarta Suhailat sun zo.
Wanka kawai Asadullah ya yi ya sanya riga JC da wando ya fito zuwa falon.
Nan ya same su Dad ya tamabaye shi abinda ya faru da shi su waye suka so kashe shi. Nan ya basu labarin komai tun kiran da Sagir ya masa akan cewa Kamal na cikin mawuyacin hali har soka masa wukan da suka yi. Sai dai ya ce bayan Kamal ya soke shi ta gaba ya ji wani sukan ta baya ko da ya juyo bai iya gane ko waye ba, sai dai yana zargin Sagir ne, dan duk da yana kwance cikin jini yana jiyo maganganun da suke yi har sanda Sagir ya kai hannu sautin hancinsa don ya ji ko yana numfashi. Hakan ya saka ya ɗauke mumfanin na wasu daƙiƙu yadda za su yi zargin cewa Mutuwa ya yi. Har zuwa ɗaukar sa da guard ɗin sa suka yi ya sani akan hanyar zuwa asibiti ne bai sake sanin in da kansa yake ba sai da ya tsinci kansa a kasar India.
Gabaɗaya firgici da tashin hankali ne ya ziyarci jama'ar wajen. Salati kawai suke yi yayin da ƴan matan ke kuka.
Mum ce ta ɗauki wayarata ta kira jami'an tsaro akan su nemo Kamal duk in da yake a fadin garin nan. Kasancewar Kamla sanannen mutum ne kasancewarsa yana siyasa.
Kuka Mom ke yi tana alwadai da halin ɗan nata. Tare da cewa sai ya girbi abun da ya shuka daga shi har abokin na sa.
Uncle Adam ne ya tambaye Asad cewa wani abu ya taba shiga tsakaninsa da ɗan uwan nasa ne ko abokinsa. Nan ya sanar da su miliyoyin kuɗaɗen da suke diba daga kamfanin, wanda sanadiyar haka ya masu gargaɗi ba su daina ba ya dakatar da su.
Nan aka dinga alwadai da halin na su musamman Kamal da suke uba ɗaya Asadullah a ce ya masa haka.
A ranar aka kama Kama yana ƙoƙarin barin ƙasar a filin jirgin sama aka kama shi.
Bayan jami'an tsaro sun tura su kotu an taru ana tuhumar Kamal akam laifin da ya aikata amma ya ce sam bai aikata abin da ake zargin sa da shi ba.
An tambaye shi in da Sagir yake ya ce bai sani ba. alkali ya bayar da hutun Sa'a ɗaya kafin a cigaba da shari'ar.
Nan ya nemi ganin Dad da iyalansa suka hadu a keɓance kasancewar Alkalin ma abokin Dad ne. Bayan sun haɗu Mom, Dad, uncle Adam, Aunty, Asadullah da Kamal.
Kallonsu alkalin ya yi tare da yin gyara murya.
"Hakika ban ji dadin yadda wannan lamarin ya kasance ba, Kamal ka amsa laifinka ba tare da ka wahalar da shari'a ba, yanayin da kake ciki ya isa ya tabbatar ba ka da gaskiya, an yi magana ka ce a kawo hujja saboda ka san kun binne duk wata hujja da za'a gane ku ko? To fa ka sani ina da hanyoyi da yawa da zan gane abun da kuke binnewa. Me ɗan uwanka ya yi maka haka?"
Ya yi maganar yana kallon Asadullah wanda idanunsa suka yi jajir saboda tashin hankali.
Kafin ya cigaba da cewa.
"Ka masa laifinka zan maka sassauci a wurin Shari'a. Kasancewar wanda kuka yi yunkurin kashewa bai mutu ba yana nan da ransa. Ka ga ba hukuncin kisa zan yake maka ba ko?"
Sai a lokacin Asadullah ya yi magana ya ce.
"Ba zai taɓa fada ba yallaɓai, zaman gidan gyaran hali ne ya dace da shi kafin ya girbi abinda ya shuka. Butulu maci amana."
Duk yadda aka kaɗa aka raya bai amsa laifinsa ba, kuma ya ki fadar in da Sagir yake. Tsabar ɓacin rai ya saka Mom ta shi ta wanke shi da mari tare da kai masa duka ta ko ina, sai da Uncle Adam ya ƙwace shi.
Bayan awa ɗaya aka koma zaman Shari'a nan ma babu wani cigaba da aka samu. Daga nan Alkali ya bada umarnin akai Kamal gidan yari ajiyarsa za'ayi kafin a kamo Sagir a yanke masu hukunci daidai da abinda suka aikata.
Daga nan ne Ka dauki Kamal aka kai shi gidan yari aka ajiye shi.
Kallon Asadullah mutumin ya yi ba tare da ya cire facemask din ba ya kalli