Showing 72001 words to 75000 words out of 154779 words

Chapter 25 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6258

ba, dan idan har na ji makamancin wannan zancen a gidan nan sai na sauya maki kamanni. Kina rufe idanu tare da firgita kamar kin ga wani bakon al'amari, ke da kika san maza kika wani firgita kamar wacce ba ta san namiji ba, munafuka mai fuska biyu."

Kalmar da ta yi mata zafi kenan a kalamansa wai ta san namiji, tabbas Aunty Laila da Momy ba za ta yafe masu ba akan ƙazafin da suka mata. Ga shi an fara jifarta da kalmar da ta tsana. Alhalin ba namijin da ta ya taba rike ko da yatsarta ne. Hawaye ne suka cika mata idanu.

"Bar nan wajen tun ban illata ki ba ƴar iskar yarinya kawai "

A guje ta bar wajen tana kuka. Tana saukowa daga downstairs ta hadu da Yaa Mansur da Yaa Faisal, Mansur ya yi dariya tare da cewa.

"Na gode Yaa Hilal da kake cin uban yarinyar nan, wallahi na tsani ganinta a cikin gidan nan."

Shi dai Faisal bai ce komai ba ya nufi part ɗin sa.

Tsuki Mansur ya ja sannan shi ma ya wuce part ɗin sa.


Tsayawa ta yi a kofar part ɗin sannan ta daidaita nutsuwarta sannan ta shiga part ɗin Dada.


Hilal na komawa ya cewa Alexandra ta tashi ta kimtsa ya kai ta airport. Kai tsaye ya nufi bathroom wanda ganin haka ya saka Alexandra nufar bathroom ɗin.

Ganin haka ya saka ya fasa shiga ya ce ta shiga ta fara yin wanka ta zo ta shirya su tafi.

Tambayarsa ta yi tare da cewa.

"Me ya saka ba ka yarda mu yi wanka tare ne?"

Madadin ya ba ta amsa sai cewa ya yi .

"Lokaci na tafiua idan kika yi wasa za ki rasa jirgi don kin san ba ya jira."

Shigewa ta yi shi kuma ya juya wajen wayararsa jin tana ruri

Jamilu ne abokinsa wanda ke Kaduna da suka sauka a gidansa Lokacin da Zahrah za su yi gasar karatun Alkur'ani mai girma.

Ɗaga wayar ya yi tare da yin sallama bayan sun gaisa Jamilu ya ce.

"Ya Zahrah take?"

"Abun da ya sa ka kira ni kenan don ka tamabaye ni?"

"Kusan haka."

Ya bashi amsa yana dariya. Tsabar takaici katse wayarsa ya yi tare da ajiye wa.

Yana ji yana kiransa amma bai sake ɗagawa ba. Bayan Alexandra ta fito ne shi ma ya shiga ya yi wanka.

Cikin closet ɗin sa ya shiga ya shigar cikin riga JC red colour da wando baƙi.

Sai ƙamshin daddaɗen turarensa ke tashi daga jikinsa.ita ma ya sanya wata doguwar riga wadda ta tsaya mata iya guiwarta gashinta ta sake shi ya zubo gadon bayanta sai takalmi me tsini dake ƙafarta.

Ta ƙofar baya suka fice ta yadda ba wanda zai gansu. Kamar yadda ya shigo da ita ba wanda ya sani sai Zahrah haka yanzu ma ya fita da ita ba wanda ya sani, don gilas din motar baki ne ba wanda zai ga na cikin motar. Ko sojojinsa bai fita da su ba.


_Asadullah_

Tsawon sati ɗaya kenan ba'ayi masa allurar ko maganin da zai saka shi cikin wani hali ba.

Wannan mutumin ne ya sake shigowa dakin, waya ne kare a kunnensa yana magana.

"Eh ga ni nan na shigo ranki ya daɗe, na gane kada ki damu."

Kallo ɗaya Asad ya yi masa ya ɗauke kai daga kallonsa.

"Sir Asadullah ya kake?"

Banza ya yi da shi bai yi magana ba, don lokacin bakinsa a buɗe yake ba su rufe masa baki ba.

"Ina son na yi magana da kai idan har kana son fita daga cikin wannan ƙangin da kake ciki dole ka bi umarnin mu."

Zama ya yi a akan kujerar dake fuskantar Asad.

"Akwai wasu takardun kanfanoni da ƙadarorinka wanda kakanka ya mallaka maka suna ina?"

Wani banzan kallo ya masa ya ɗauke kai ba tare da ya bashi amsa ba.

Sake tambayar sa ya yi a karo na biyu, nan ma shiru bai ce komai ba. Murmushi mutumin ya yi tare da cewa.

"Matukar kana son cigaba da numfashi a doron duniya dole sai ka sadakar da dukiyarka don ka ceci rayuwarka, matukar ka ce ba za ka sadaukar da dukiyar ka ga wadanda suka saka ka a cikin wanan halin ba to za su iya kashe ka."

Mumrmushin gefen baki ya yi tare da cewa


"Kai karen farauta ka fadawa iyayen gidanka ba za su taɓa samun abun da suke nema daga gare ni ba"

"Za ka mutu fa?"

"Ba na tsoron mutuwa. Ka fadawa iyayen gidanka idan har kwanakin da Allah ya ɗibar Mani a duniya suka cika dole zan koma gare shi ko sakan ɗaya ba zan kara a duniya ba. Don haka idan mai kisa ya yi hakuri wanda za'a kashe zai mutu. Idan za su taru don su cutar da ni kan wani to ba za su cutar da ni ba dai idan Allah ya rubuta shi a kaina. Ka faɗa masu haka."

Shiru ya yi yana kallon Asadullah kafin ya yi ajiyar zuciya ya ce.

"Gaskiya ka faɗa amma sun yi nisa ba sa jin kira, shi ya sa na hore ka da ka aikata abinda suke so."

"Wai da wani yare nake magana ne da ka kasa fahimta ta, na rantse da wanda raina yake a zatinsa ba zan taɓa ba su abinda suke so ba. Kuma ka faɗa masu sun yi kuskure, domin na san duk wanda ya saka ka wannan aikin na jikina ne na kusa da ni. Don bayan iyalan gidan nan ba wanda ya san cewa Kakana ne ya mallaka Mani wannan dukiyar ba ballantana a nemi sanin inda takardun suke."


"Oho wannan ba matsala ta ba ne, sai abu na karshe da zan ba ka."

Ya yi magana yana ciro wata takarda a aljihunsa. Wani takarda ya ciro ya nuna masa.

"Za ka saka hannu a wannan takarda."

Kasancewar hannunsa a daure suke ya kalli takardar, takarda ce ake so ya saka hannu a ciki wanda dole sai da saka hannunsa makudan kudade za su fita daga Kamfanin, don miliyoyin kuɗaɗe suke son cirewa sai da ya kalli takardar sannan ya yi dariya ya ce.

"Ba zan taba sanya hannu ba."

Kallomsa mutumin ya yi don ya fahimci Asad na da taurin kai, wato dama da ya kasa magana yake kallinsu saboda allurai da magunguna da suke dankara masa na dicewar gayyaci ne.

Duk yadda ya dinga magana da Asadullah akan ya saka hannu ko za su rabu da shi ta ki. Don ya rufe masa baki kamar yadda suke masa haka ya fice bayan ya rufe kofar ta waje.


_Dad_

Gabaɗaya ya shiga damuwa saboda rashin sanin halin da ɗan sa yake ciki. Ya sanar da jami'an tsaro ya saka malamai su yi ta addu'a. Yanzu ta kai gabadaya ba ya fita.

Yau ma kamar kullun, da misalin karfe biyu na dare sai Safa da marwa yake yi a cikin ɗakinsa. Kasancewar ranar girkin Mom ce ya saka ita ke tare da da shi a wannan daren.

Farkawa ta yi ta bude idanunta.

"Alhaji wai har yanzu ba ka kwanta ba, ka ragewa wa kanka damuwa haka nan, ka ajiye komai ka t
rame kamar wanda ya yi doguwar jinya.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da zama a bakin gadon.

"Ba dole na shiga damuwa ba Zubaida. Ki duba abun nan. Ba yadda za'ayi Asadullah ya yi tafiya wata ƙasa ba tare da ya sanar da ni ba. Ko da tafiyar gaggawa ce ta kama shi kowa sai ya sanar da ni. Amma lokaci daya a ce wai ya yi tafiya bai sanar da kowa cewa zai yi tafiya ba, sannan kuma ba'a samun wayoyinsa. Ga shi ko da bai fita da bodyguard ɗinsa ba sai ya tafi da Sulaiman. Amma wannan karon Sulaiman ma bai san in da yake ba. Duk da ta tabbatar mana da cewa wai Asad bai bar gidan ba, da ya bar gidan da ya sani."

Tashi zaune t yi yana nazarin kalaman Dad kafin ta ce.

"Alhaji bar zancen Suleiman don waɗan nan mutanen ba su san aikinsu ba, idan bai bar gidan ba ta sama ya tashi ya fire?"

"Ni ma abun da ke ɗaure Mani kai kenan."

"Alhaji ina da magana ."

Mai da hankali ya yi a kanta yana cewa

"In a Jinki?"

Gyara zama ya yi tare da cewa.

"In jinki .

"Ka san dai matar ka Zulaihat ba ƙaunar yaran gidan nan take yi ba. Musamman Asadullah ta tsane shi. Gaskiya ban yarda da ita ba."

Ɓata fuska ya yi sannan ya ce

"Kina nufin ita kike zargi ko me?"

"Eh ita nake zargi da batar Asad saboda hujjojin da zan sanar da kai."



*Kuyi hakuri da wannan*




*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)



*Sanarwa*

Wannan ƙirƙirerren labari ne ban yi shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali ya zo ɗaya to arashi, mai kashe auren wawa.


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page3️⃣7️⃣

"Eh ita nake zargi da ɓatar Asad saboda hujjojin da zan zan sanar da kai?"

"Wace hujjar ce da ke?"

"Ko ka manta cewa a gidan nan Asadullah ba ya da wani babbar makiyiyar da ta wuce Zulaihat. Tun da ta zo gidan nan ja taɓa ganin ta kula shi a matsayinta Na matar ubansa? Ko gaisuwa idan ya yi mata ciki-ciki take amsa masa ko agolar yarinyata ba ta bari ta yi mu'amala da Asad, ba ma shi kadai ba dukkan yaran gidan nan ba ta bari ta yi mu'amala da kowa. Don duk ranar da ta ganta tana shigewa yaran gidan nan sai ta duke ta . Wani irin mugun zama ne wannan?"

Shiru ya yi yana kallon Hajiya Zubaida, don tabbas abun da ta fada gaskiya ne, amma wannan ba shi ne hujjar da za'a zarge ta ba tun da ba'a kama ta da wata hujjar da zai saka a zarge ta ba.

"Kin ga wannan ba hujjar da zai saka a zarge ta ba ne, na san cewa ba ta shiga harkar kowa a gidan nan ba Asad kadai ne, duk da na yi iya yi na amma hakan bai sa ta canza ba. "

"Shikenan Alhaji Allah ya bayyanar da gaskiya."

"Amin"

Ya amsa mata cikin sanyin murya.



_Jidderh_

A hankali take tafiya har ta ƙarasa cikin ɗan ƙaramin gidansu.

Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin gidan.

"Inna, Yaa Isah, da Aunty Sa'adatu sai ɗansu dake rike a hannun Isah yana wasa. Gabaɗayansu suka amsa mata sallamar.

Zama ta yi bayan ta gaishe su da gida. Aunty Sa'adatu ce ta kalle ta tare da cewa.

"Jidderh lafiya kike kuwa?"

"Lafiyata lau Aunty Sa'adatu me kika gani?"

"Na ga duk kin rame kwana biyun nan ne."


Marairaice fuska ta yi tare da cewa.

"Yaya ya zancen da na yi maka na ji ka shiru wallahi Sir Asadullah na cikin wani hali sosai yake buƙatar taimako."

"Wai ke Jidderh ba na fada maki cewa ki fita daga harkar gidan nan ba.?"

"Haba Yaya kar ka mance da halaccin da bawan Allahn nan da ya yi mana a rayuwa. Saboda shi ne fa har yanzu matarka da ɗanka suke raye ko ka mance ne?"

"Matata da ɗana suna raye ne saboda Allah ya yi kwanansu bai ƙare ba. Ki ce dai shi ne sanadin da suke raye."

"To na ji, yanzu ta wata hanyar kake ganin za ki kuɓutar da shi daga cikin wannan halin da yake ciki, kin ga dai gidan nan masu kuɗi ne sosai kuma in fada maki gaskiya ina tsoron shiga sabgar masu kudin nan nake yi. Don za su iya sakawa a ɓatar da mu matukar asirin mu ya tonu. Sannan kin ce yana cikin gidan kin bani labarin matakan tsaron dake cikin gidan ta ya ya zamu fitar da shi ba tare da kowa ya sani ba?"

Shiru ta yi tana nazari kafin ta ce.

"Zan yi tunani akan hakan sai na sanar da Kai, fatan za ka bani hadin kai.Matukar na ga hanyar za ta iya ɓullewa ina goyon bayan ki ɗari bisa ɗari ma kuwa."

Inna dai tana jin su ba ta ce komai baz duk da can ƙasar zuviyarta tana fargabr halin da Autarta take kokarin jefa kanta a ciki.


*Bayan sati ɗaya*

A hankali take tafiya cikin nutsuwa tana fitowa daga department din take. Sanye take da hijabi Union color, hijabin ya sauka mata har ƙasa takaliminta mai tsini kawai ake hangowa wanda shi ma ya kasance Union color ne. Fuskarta sanye da farin glass sai facemask da ta sanya. Hannunta rike da wasu takardu ta nufi wajen motarta.

Ta kai hannu za ta buɗe murfin motar kenan sai ta ga an bude mata, juyawa ta yi ta sauke idanunta akan fuskarsa yana sakar mata murmushi.

"Aminiyata yau shi ne za ki wuce ko ganin juna ba mu yi ba.?"

Mumrmushi ta yi tare da cewa.

"Wallahi na gaji ne Aminin ya kake?"

"Alhamdulillah ina lafiya ?"

Kafin ta yi magana sai ga A'isha ƙawarta ta karaso wajen tana cewa.

"Zahrah har za ki tafi gida ne,?"

"Eh zan tafi tun da mun gama me zan tsaya jira?"

Wani saurayi sanye da ƙananan kaya ya zuba hannayensa a Aljihu ya yi sallama yana ƙarasowa wajen.

Gabaɗaya suka amsa masa yayin da Zahrah ta shige motarta.

"Zahrah magana nake son mu yi da ke."

Ta san zancen akan soyayya ne dai wanda ya dade yana bin ta tana masa yawo da hankali. Yau ne ya tura mata sakon idan sun tashi yana son ganinta. Ba ta masa reply ba.

"Am dan Allah Mustapha ka yi hakuri Wallahi na gaji ne za mu iya yin magana gobe?"

Sanyayyaen murmushinsa ya sakar mata wanda ya zame masa ɗabi'a ya ce.

"Ba damuwa Allah ya kai mu goben."

"Amin na gode."

Ya bar wajen suka bishi da kallo. Amininta ya ce.

"Aminiya wannan gayen akwai hankali da nutsuwa ki bashi dama kawai na san zai kula mana dake sosai."

Ba ta ce komai ba ta yi wa motar key suka yi mata sallama akan sai sun yi waya.

A hankali take driving cikin nutsuwa tana rera karatun Alqur'ani mai girma cikin zazzaƙar muryarta.

Har ta karasa gidan ta yi horn maigadi ya bude mata ta shiga cikin gidan. A parking space ta yi parking ta kashe motar ta fito.

Wata baƙuwar mota ta gani a cikin jerin motocin dake wajen parking ɗin.

Da sallama a bakinta ta shiga yayin da take cire facemask da ke fuskarta, Ba kowa a babban falon gidan, glass din ma ta cire tare da zare shi.

Hijabin ma ta cire shi tare da ajiye kayan daje hannunta akan kujerar da ya zauna mai zaman mutum biyu.

Riga da siket ne a jinkinta ɗinkin ya ɗan kama ta duk da ba ta da ƙiba shape ɗinta ya fito sosai kasancewar tana da cikar ƙirji ga hips ma tana da shi masu ɗaukar hankalin. Tashi ta yi don ɗauko remote control dake samann Centre table. Daidai lokacin da Hilal da wani abokinsa mai suna Ammar suna saukowa daga upstairs.

"Wow"

Ammar ya faɗa yana zare idanunsa akan Zahrah.Hilal da yake danne-danne a waya bai kalle shi ba ballantana ya san me yake nufi.

"Man waccen lu'ulu'un fa?'

Sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalli Zahra dake shirin zama tare da remote control a hannunta.

Tsuke fuska ya yi kamar bai ji me yake cewa ba.

"Sister ɗin ka ce ita?"

Banza ya masa kamar bai ji shi ba.

Zahra ta kamo tashar Sunnah TV. In da suka saka wa'azin Sheikh Imam Abubakar Ghana in da yake wa'azi akan matan da suke ba sa kula daazajenu da yada wata macen take magana da mijinta. Har Zahrah ta yi dariya wanda sai da dimple ɗin ta ya lotsa. Ba ta san sun ƙara so wajen ba sai gani ta yi mutum ya zo ya tsaya gabanta fuskarsa ɗauke da Murmushi. Ɗaga kai ta yi ta kalle shi. Da sauri ta ta janyo hijabinta ta saka. Sai a lokacin ta lura da Hilal dake tsaye a bayansa fuska babu walwala kamar ko da yaushe.

"Beauty ya kike?"

Ba ta tanka masa ba ta yi kamar ba ta gan shi ba. Murmushi ya yi tare da cewa.

"Assalamu alaikum warahmatullah"

Sai a lokacin ta buɗe baki ta ce.

"Wa'alaiki Salam warahmatullah"

"Zan iya zama?"

Ba ta ce masa komai ba don da alama wajen Hilal ya zo.

"Da alama rowar Muryar ake yi mani ko?"

A ƙufule Hilal ya ce.

"Look Ammar kar ka ɓata mani lokcin idan ba za ka tafi ba zan tafi na bar ka."

Ammar ya zauna gefen Zahrah ko kula Hilal bai yi ba ya cigaba da cewa.

"Beauty ya sunanki?"

"Fatima Zahrah."

Ta faɗa a hankali.

"Wow nice name."

Wayarta dake ajiye a gefenta ya ɗauka, cikin Sa'a kuwa ba password don haka ba tare da ɓata lokaci ba ya saka lambar wayarsa ya danna kira.

Take kuwa kira ya shigo wayarsa, murmushi ya yi tare da cewa.

"Sunana Ammar Umar Galadima. Ni haifaffen garin nan ne, sai dai ban tashi a garin nan ba sakamakon iyayena sun koma ƙasar London da zama, a can muka hadu da Yayanki da yake a can ya yi karatu. Allah ya haɗa jinina da shi sosai mun zama aminan juna. Yanzu haka ni direba ne."

Sai a lokacin ta ɗaga kai ta kalle shi jin ya ce wai direba ne shi.

Dariya ya yi tare da cewa.

"Kina mamaki ne? Ina nufi pilot me wato Direban jirgin sama."

Nan ma kallonsa ta yi.

"Okay ko aikin ba ya burge ki ne, haka ma ko iyayena ba sa son aikin sun fi son na zama injiniya. Sai dai wannan aikin shi ne burina tun ina yaro nake sha'awa na zama Pilot idan na girma, idan bakya ra'ayi sai na bari cox dama ba na samun zama cikin ahalina kamar yadda ya dace."

"Ni kuma meye damuwata da aikinka?"

"Bayan mun yi aure yadda zan zauna dake na baki cikakkiyar kulawar da ya dace na tarairaye ki."

"Aure kuma? Da ni?"

"Ai tun da na ganki na ga matar aure."

Kallonsa ta yi tabbas Ammar ƙyakyatawar mutum ne, yana da hasken fata sai dai ba sosai ba. Matsakaicin tsayi ne da shi fuskarsa mai ɗauke da saje da gemu wanda ya ƙawata kyakkyawar fuskarsa.

"Ban taɓa ganinki a nan ba duk ba nan cika zuwa ƙasar ba ni ma, ke ƴar waye a cikin gidan nan, don na san Hilal sister ɗin sa da suke ciki ɗaya Maryam ce."

Kasancewar ba ta son abun da zai hada ta da kowa na gidan kamar yadda Ummi ke ja mata kunne akan shiga lamurran al'ummar gidan, gashi abokin Hilal hakan na iya ba ta matsala."

Tashi ta yi ba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login