Showing 6001 words to 9000 words out of 154779 words

Chapter 3 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6257

har ƴaƴanta.

Sai na tsuki da suka ja. Dama ba ta saka ran cewa za su amsa ba. Don idan da sabo sun saba.

Kai tsaye ta nufi part ɗin Kakanninta. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga falon.

Dada ce ta amsa yayin da take ajiye wani bowl a saman Centre table.

Amsa mata sallamar ta yi tare da cewa.

"Duk wayewar garin yau sai yanzu kika shigo."

"Ba haka ba ne Dada kin san next month zan yi walima ina karatu ne."

"Haka fa ƴar albarka duk kin fi sauran yaran ke da yayunki, amma sauran ba abunda iyayensu suka koya masu sai gaba da baƙar zuciya."

Mumrmushin kawai Zahrah ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sai ta kawar da zancen ta hanyar cewa.

"Dada me kika dafa ne?"

"Yayanki da ya dawo ne yake son kwaɗon zogale shi ne na masa."

Kallon rashin fahimta ta yi mata tare da cewa.

"Wani Yayana kuma?"

"Wanann mara imanin mana, ai na gayawa kowa na gidan ya shiga hankalinsa kafin ya illata su, ke na san baki da tsokana ballantana ki shiga gonarsa ya illata ki a banza, ga shi ke ba isashshiyar lafiya ba. Ya zo ya dukanki ya illata ki a banza wai shi soja ."

Zama Fatima Zahrah ke ƙoƙarin yi Dada ta ce.

"Na ji har yanzu bai zo ba, ki je ki kira mani shi ko ki tambaye shi a kawo masa nan ne a ɗakinsa?

Da sauri ta kalli Dada tana cewa.

"Ni kuma?"

"Ko kema baƙin halin kika fara koya ne da kuma gaba? Kafa ku biye masu kin ji shi wanda na ce ki kira a matsayin Yayanki ne kamar yadda na haifi ubansa haka na haifi ubanki, kuma Hilal bai ɗauko baƙar zuciyar uwarsa ba, yana da kirki gara yanzu da ya zama soja ya fara canza halaye, na rashin imani da tausayi irin ta su ta sojoji Ko kema an koya maki gabar ne?"

Da sauri ta girgiza kai tare da cewa.

'A'a"

"To kira shi."

Cikin sanyi. Jiki ta tashi ta nufi ɗakinsa duk da cewar lokacin ƙarfe tara na dare ne.

Ba kowa a main falo dama idan dare ya yi ba su cika zama ba kowa na part ɗin sa.

Upstair ta haura don a can part ɗin sa yake, duk da cewar tunda ya gama karatu ya dawo ƙasar ba ta taɓa zuwa ɗakinsa ba.


_Hilal_

Fitowarsa daga wanka kenan ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa. Sai wani da yake goge ruwan dake kansa.

Gashin ƙirjinsa ya kwanta luf a fafdaɗen ƙirjinsa. Kallo ɗaya za ka masa ka san cewa ƙakkarfa ne don surar jikinsa a murɗe take ga ƙwanjin dake hannunsa wanda kallo ɗaya za ka masa kasan cewa yana yawan motsa jiki da exercise. Ba fari ba ne kuma ba za ka kira shi da baƙi ba za ka iya kiransa da wankan tawaɗa. Dogo ne sosai yana da ƙira da cikar halitta irin na lafiyayen ɗa namiji ga kyau ga cikar zati Allah ya bashi. Sannan yana da ƙira irin na ƙakkarfan namiji jarumi na azo a gani

Bayan ya gama tsanar ruwan jinkinsa ne ya ajiye ƙaramin towel ɗin.

Sallama Fatima Zahrah ta yi a falon ta ji shiru don sai ta yi tunanin baya nan, har za ta juya sai ta yanke shawarar duba shi a bedroom ɗin sa.

Sallama ta yi kai tsaye ta tura ƙofar falon. Ƙamshi ne ya ziyarce ta ta tsaya tana ƙarewwa falon kallo. Ya burge ta komai fari ne a cikin dakin kama daga fentin da labulaye da kujeru komai fari ne, hatta Centre carpet da Centre table komai fari ne sai ɗaukar ido suke yi kamar ba'a taɓa amfani da su ba. Hatta tiyel ɗin ma fari ne.

Ƙofar bedroom ɗin da ya kasance shi ma fari ne ta yi knocking.

Yana tsaye gaban dressing mirror 🪞 ya juya ya kalli ƙofar ba tare da ya yi magana ba. Sai da aka sake knocking sau uku kafin ya ce.

"Come in."

Da sallama a bakinta ta shiga ɗakin, kallo ɗaya ya yi mata ta cikin dressing mirror ya ɗauke kansa.

Haka bedroom ɗin ma ya tafi da ita don shi ma komai nasa farin ne. Idanunta ne ya sauka akan wani butterfly 🦋 da aka yi ƙaton elergment aka zana butterfly din shima fari dai ɗaukar idanu yake yi, don har shinning yake yi. Ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba har sai dai dimpul ɗinta suka lots. Jin shiru ta shigo ɗakin ba ta ce komai ba ne ya saka ya kalle ta ta cikin mirror ya ga murmushi ma take yi. Gyaran murya ya yi wanda ya sa ta dawo nutsuwarta. Kallo ɗaya ta yi masa ta ganshi ɗaure da towel iya ƙugu. Kau da kanta daga kallonsa ta yi tare da cewa.

"Ina wuni?"

Banzan ya yi da ita kamar bai ji me yake cewa ba. Sanin cewa ya ji ta kuma ba ta saka ran zai amsa mata ba, don bai taba amsa mata gaisuwa ba ko ta gaishe shi. Idan ya amsa sallamarta shi ne nan.

"Dama Dada ce ta aiko ni wai a kawo maka zogalen anan ne ko za ka zo can ka ci?"

Nan ma banza ya yi mata kamar ba da shi take yi ba. Don har sake maimaitawa ta yi nan ma ya share ta kamar bai ji ta ba. Closet din kayansa ya shiga ya bar ta nan tsaye.

Tana ganin haka ta juya ta fita tana magana ƙasa-ƙasa.

"Mutum sai jin kai da nuna isa. Idan ba don Dada ba mai zai shigo da ni ɗakinka ballantana ka nuna ni banza ce a wajenka, idan ba don naka-naka ne ba da ko kallonka zan yi."

Haka ta dinga gunguni ita kaɗai har ya karasa ɓangaren Dada.

Dada na kallonta ta ce.

"Me ya ce a kai masa ne, ko zai zo nan ya ci?"

Tura baki ta yi tare cewa

"Bai ce mani komai ba kuma ya ji ni."

Shiru Dada ta yi kafin ta ce.

"Kada wannan ya dame ki, kin san yana da mishkilanci haka yake ba kowane lokaci yake magana ba yin ta yake ba sai ya zama dole."

"Ina nawa zogalen na ci?

"Ga naki a kitchen ki je ki ɗauk."

Ta dauko nata zogalen da ya ji yajin ƙuli da yanke-yanke ta yi bisimillah ta fara ci.


Har ta gama Hilal bai zo ba, hakan ya saka Dada ta ce ta ɗauka ta kaiasa kafin ta wuce part ɗin su.

"Da ko na je wulakanta ni zai yi, zan ke na kwanta gobe ina da jarabawa."

"To idan ba ke ba waye a nan da zan aika, dare ya yi ni ba lafiyar ƙafa ba ballantana na haye upstair."

Haka ba don ranta ya so ba ta ɗauki bowl ɗin ta nufi kofar fita, ta ji Dada na cewa .

"Nan za ki dawo mu kwana ko ɓangarenku za ki koma ? "

Ba ta ce komai ba ta fita don ranta ya ɓaci da komawa part ɗin sa.


_Jidderh_

Tafe take sanye Da Kayan makarantan secondry school, makarantar Gwamnati ce take zuwa mai suna Government Day secondry school. Tafiya take yi ga rana ana ƙwalawa tun karfe biyu aka tashi amma kasancewar unguwarsu da nisa da makarantar yake daukarta karfe uku da rabi kafin ta isa gida.

Sanye take ta riga fari wanda ya sauko har guiwarta sai farin hijabi da dogon wando wanda ya kasance blue.

Sanye take da farin socks socks da takalmin sandal baƙi na roba, duk ya yi ƙura sakamakon tafiyar ƙasa da ta sha.

Madaidaicin gidansu ta shiga gida ne mai ɗauke da ɗakuna huɗu Isah yayanta yana zaune a ɗaki biyu ciki da falo, sai ɗakuna biyu wanda Innarsu Jidderh ke amfani da shi Jidderh kuma tana amfani da ɗaki ɗaya.

Sai ƙaramin kitchen a tsakar gida da kuma banɗaki shi ma a tsakar gidan.

Da sallama Jidderh ta dawo sai dai ba ta ji an amsa ba, amma hakan bai bata mamaki ba saboda ta san Innarsu ba ta nan, sai matar Yayanta Isah wacce kwana biyu take naƙuda a tsaitsaye.

Tana shiga tsakar gidan ta nufi randar ƙasa da suke zuba ruwa. Ta bude ta ɗebi ruwa ta sha saboda ƙishirwa ga rana da ta kwaso.

Bayan ta sha ruwan ne ta je za ta shiga ɗakinta don ɗakin Inna a rufe Sa'adatu matar Isah kullum cikin barcin rana take, hakan ya sa kai tsaye za ta shiga ɗalibta sai ta ga jini a ƙofar ɗakin Sa'adatu. Ta bi jinin da kallo har jikin labulen, cikin tashin hankali ta nufi ɗakin ta fad'a ciki.


_Fatima Zahrah_

Knocking ta yi a bakin kofar falon Hilal, jin shiru sai ta tuna cewa ta barshi a bedroom ne da ta shigo isar masa da saƙon Dada.

Don haka ta nufi bedroom ɗin nasa sanin cewa ko ta yi magana ba zai amsa ba ya sa ta yanke shawarar shiga ta ajiye masa.

Tura ƙofaf ta yi tare da sallama. Ba ta ga kowa a ɗakin ba, da alama ya fita. Don haka ne ma ya ajiye masa bowl ɗin zogalen a table da ta gani a gaban kujera.

Har za ta fita sai ta tuna fa butterfly da ta gani a ɗakin da sauri ta juya ta nufi wajen, sai dai tsayinta bai kai ta taɓa shi ba, kuka tana son ta shafa photon. Don haka ta juya in da ta ga wani kujera da yake zama.

Janyo kujerar ta yi ta ajiye a wajen, sai ta hau kujerar ta taka ta. Hakan ya saka ta miƙa hannu ta ciro glass din photon

Tana shafar photon tana murmushi cike da shauki. Tsawon mintuna goma ta dauka a haka, kafin ta kai hannu da niyyar mayar da photon bisa tsautsayi dai ya faɗo ya tarwatse.

Hilal dake cikin closet yana shiryawa ya ji wannan karar, da sauri ya fito in da ya yi tozali da ɓarnar da ta yi masa.

Ganin ɓacin ran dake kan fuskarsa ya wanda babu sassauci a tattare da shi ne ya saka jikinta ya fara rawa.

Nufo ta ya yi wanda ganin haka ya sa ta fara neman hanyar tsira don ta san mai ƙwatarta a wajensa sai dai Allah.

Tsalle ta yi ta diro daga kan kujerar a guje ta nufi hanyar fita za ta fice. Cikin zafin nama ya zare takalmin dake ƙafarsa ya jefi ƙafarta ta dama daidai saitin guiwarta, kasancewar ta baya ya jefe ta hakan ya sa ƙafarta ta lanƙwashe ta faɗi a wajen. Ƙara ta saki saboda ta ji zafi kuma ga buhuwar da ta yi.

Tsawon mintuna biyar tana kwance a ƙasan kafin ta yunƙura idanunta na zubar da ba hawaye ta juyo ta kalle shi ta ga ya wurga mata harara tare da yi mata alama da hannu na ta zo.

Tana ɗingisa ƙafa ta karasa gabansa, tsawon mintuna uku bai yi magana ba kafin ya fara magana cikin fusata.

"Kin yi mun ɓarna za ki gudu uban waye zai kwashe tarkacen da kika tarwatsa!?"

Waige-waige ta fara yi can hanyar bathroom a cikin wani corridor ta hangi kwandon zuba shara da da abin kwashewa. Ɗauka ta yi ta zo ta tattara Wajen ta share tas. Sai da ta gama ta mayar ta ajiye, kallonsa ta yi ta ga ya zuba mata rikitattun idanunsa ba tare da ya yi magana ba.

"Na rasa wani rin hukunci zan maki ma, ke ba abar a daka ba, idan na ce zan dake ki sai kin kusa mutuwa a hannunsa."

Ƙofar fita ya nufa kafin ya fice ya juyo ya kalle ta ya ce.

"Ki fada tsallen kwaɗo ba tare da kin tsaya ba, idan kuma kika tsaya na lahira sai ya fi ki jin daɗi. Kuma ki sani duk abinda za ki yi a cikin ɗakin nan akan idanuna kike yinsa, don ina kallonki."


Yana gama fadar haka ya fice yayin da ta fara tsallen kwaɗo tana kuka.




*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z




*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page0️⃣4️⃣

Yana gama fadar haka ya fice yayin da ta fara tsallen kwaɗo tana kuka.


Ummin Zahrah kuwa tana ganin karfe goma ta yi Zahrah ba t dawo ba ta yi tunanin kila a ɗakin Dada za ta kwana. Don dama wani lokacin tana kwana a wajen kakarta. Sai da asuba take dawowa part ɗin su. Don haka Ummi na leka ɗakin Zahrah ta ga ba ta nan ta san tana wajen Dada don ba ta fita.

Yayin da ita kuma Dada ganin Zahrah ta jima ba ta dawo ba ne ya sa ya yi tunanin bayan ta sanar wa Hilal ɗin saƙonta ta koma wajen Umminta ne. Don dama daga kaka har Papa cikin jikokin su sun fi son Hilal da Zahrah. Duk da cewar iyayensu ba sa ko ko ga maciji da juna.


_Hilal_

Yana fitowa daga part ɗin sa downstairs ya nufi ɓangaren Kakanninsa. A can ƙasar maƙoshi ya yi sallama, don ko Dada ba ta ji shi ba, ganinsa kawai ta yi ya shigo. Kallonsa ta yi daga sama har ƙasa don ta ga alamar shirin fita yake yi. Don haka ta ce.

"Kai kuka ina zuwa cikin daren nan, sannan k shigo Mani ko sallama babu kamar gidan kafirai ko, to ai ko kafirai ne ka ƙwankwasa ƙofa, saboda an kai ka cikin nasara asarar duniya ka je can ka koyo mugun hali."

Bai ce mata komai ba ya miƙe ya nufi hanyar fita ya fice. Taɓe baki Dada ta yi tare da cewa.

"Wannan kam matarka na da aiki wallahi, a ce ma magana sai ka ga dama kake yinsa, idan. Ka ga dama ba ka yi kamar kurma, dubi yadda ya shigo ya zauna mani ko magana babu, ai ko kurma ne ya ɗaga mani hannu zan san ya gaishe ni. To Allah ya kyauta."da


_Jidderh_

Tana shiga cikin ɗakin ta dade kai tare da furta kalmar.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"

Jakar makarantarta ta saki ganin matar Yayanta kwance a cikin jini da alama naƙuda take yi.

"Aunty Sa'adatu garin ya kika zauna har hakan ta faru?"

Sa'adatu wacce ta gama galabaita na naƙudar da take yi ta saka magana.

A guje Jidderh ta fito daga ɗakin ta nufi hanyar fita, kai tsaye ta nufi titi duk da sam ta mance wata gajiya da yunwa da ta kwaso. Sai da ta kai bakin titi sannan ta tsaya daga gudun da take yi. Wani mai keke napep (adaidata sahu) ta tare ta shiga.

"Mallama don Allah ka yi sauri mu tafi nan za ka bi matar Yayata ce ba lafiya."

Ta karasa maganar tana nuna masa layin da ta fito, don haka ya bi in da ta nuna masa. kai tsaye har kofar gidan suka sauka. A guje ta fita ta shiga gidan ta same ta har lokacin a kwance. Wani zani ta ɗauko ta ɗora mata ta cire mata wannan da ya ɓaci. Dakyar ta iya taimaka mata ta tashi tare da jingina a jikin bango. Hijabinta ta saka mata shi a jiki ta taimaka mata duk da ba wani iya tafiya take yi ba, amma Jidderh ta taimaka ta rike ta har suka fito ƙofar gida. A cikin napep ɗin ta saka ta ita ma ta shiga suka bar ƙofar gidan.


General hospital ta nemi ya kai su, don can ne take da yakinin sauƙin kashe kuɗi.

Suna shiga harabar asibitin wasu ma'aikata suka hange su shi ne suka ɗauko keken da aka ɗaukar marasa lafiya suka saka ta a ciki. Mai keken na ganin Jidderh za ta wuce ya ce .

"Kud'ina da?"

Sai a lokacin ne ta tuna cewa ai ba ta ko sisi.

"Mallama don Allah ka yi hakuri Wallahi ban da kuɗi."

"Fitowa ya yi daga cikin napep ɗin ya lalle ta ya ce.

"Amma ke ba karamar ƴar rainin hankali ba ce, ta ya ya za ki kira ni ki ce baki da kuɗi, wanann I zancen banza ne, fitsari na zuba a cikin keken ne ba fetur ba, wallahi ko ki bani kud'ina ko na tafka maki rashin mutumci a a wajen nan."

"Ka ga Mallam meye na rashin mutunc, ba na cikin nutsuwata ce, duk na bi na rikice ba ka ga a halin da muka kawo ta ba ne, kai ba ka da tausayi ne idan ƴar uwarka ce ya za ka ji?"

Wata ma'ikaciyar asibitin ce ta zo ta ce.

"Ke koyi sauri ana jiranki."

"Ba in da za ta je sai ta biya ni kuɗina."

"Nawa ne kudin naka?"

Matar da ta zo kiran Jidderh ta tambaya.

"Naira ɗari biyar ne."

Ta mika masa kudinsa yayin da Jidderh ke mata godiya.

Da sauri suka karasa ciki inda ya hangi Aunty Sa'adatu zaune a keken da aka ɗauko ta kuma ko numfashi ba ta yi.

"Nurse a kai ta kan gado a ajiye a duba ta mana, dubi yadda kuka barta cikin wannan halin."

"To ai sai ki ɗauke ta ki kai ta a gadon ki yi mata abinda ya dace."

Ɗaya daga cikin nurse ɗin ce ta faɗa.

Jidderh ta kalle ta da mamaki za ta yi magana sai ta ji Muryar nurse ɗin da ta bayar da kuɗin napep ɗin su ta ce.

"Ki kawo takardar awonta da kayan da ake rubuta masu idan za su zo haihuwa su kawo."

Shiru Jidderh ta yi kafin ta ce.

"Ba ta zuwa awo ai."

Gabaɗaya suka kalle ta tare da kallon Sa'adatu da ba ta san ma me suke cewa ba.

Wata ce .

"To sai ki kwashe ta ku tafi ku bamu waje, duk wayar da kai da ake yi wa mata akan mahimmancin zuwa awo ga masu ciki a banza ne wajenku. Ya ya ya mace da ciki za ta zauna ba ta zuwa asibiti ana yi mata awo a duba lafiyar Babyn a bata magunguna, sannan kun bar ta ta gama galabaita kun kawo ta idan ta mutu ku ɗora mana laifi ko?"

"Duk abinda za ku faɗa ku faɗa amma daga baya na yanzu ba, saboda tana cikin wani hali ku taimaka yi abinda ya dace don Allah."

Haka Jidderh ta dinga roƙonsu tana magiya da taimakon wanan nurse da ya biya masu kudin nape suka ta saka baki suka karɓe su.

Bayan an shigar da ita ɗakin haihuwar ne aka lissafa wa Jidderh kayayyakin da za su yi amfani da su wajen karbar haihuwar da bayan ta haihuwar. Lissafin dubu goma suka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login