Showing 51001 words to 54000 words out of 154779 words
har kin yi arzikin da za ki bani mota, to na fi ƙarfin motocinki."
"Na sani Ya Hilal, ba wai za ka duba wannan ba manufar dake cikin kyautar za ka du..."
Kafin ta karasa zancenta har ya bar wajen ya nufi part ɗin su Papa.
Duk yadda ta so tashi kasawa ta yi don bayanta ji take ya rike. Rintse idanu ta yi hawaye na bin gefen fuskarta.
Tana cikin wannan yanayin ne sai Allah ya jeho Yaa Mahmud, ganinta ya sa ya karasa wajen yana tamabayar ta .
"Subhanahi Zahra me ya faru da ke?"
"Faɗowa na yi."
Ɗaukar ta ya yi cak ya nufi part ɗin Umminsu da ita.
Tana zaune a falo hannunta rike da littafin addini tana karantawa.
"Lafiya me ya same ta?"
Ta tambaya tana ajiye littafin kan Centre table dake gabanta.
"Faɗowa ta yi daga upstair, a gasa mata jiki idan ya kama na asibiti ne sai ki kira ni."
Daga nan ya nufi ɗakinta da ita a hannu, har cikin bathroom ya kai ta sannan ya fito. Ummi ce ta shiga don taimaka mata.
Ita ta cire mata kaya ta gasa mata jiki da ruwa ɗumi.
Sai da ta tabbatar ta gasa mata jiki musamman bayanta sannan ta bar ta ta ce ta yi wanka.
Wanka ta yi ta fito ɗaure da towel.
Sai dai ta ji dadin jinkinta sosai, Man zafi Ummi ta bata ta shafa a jinkinta kuma ta ji daɗin ruwan ɗumin.
Magani ta bata ta sha sannan ta kwanta. Ba jimawa barci ya ɗauke ta. Ganin ta yi barci Ummi ta fita ta bar mata ɗakin.
_Hilal_
Ko da ya nufi sahsen kakannin nasa sallama ya yi wanda shi kaɗai ya ji kayansa.
Papa na waya yayin da kuma Dada ta ke yanka fruits a faranti.
Kamar yadda ba su ji sallamarsa ba haka ba su san ya shigo ba. Ganinsa kawai Dada ta yi zaune bayan ta gama yankan fruits ɗin. Papa ko har lokacin bai san da zuwansa ba duk da yana waya idanunsa na kan T.V.
Kallonsa Dada ta yi tare da cewa.
"Kai yaushe ka shigo nan ne, mutum sai ka ce aljani. Ba wanda ya ga shigowar ka sai ganinka."
Papa ya kalli gefen da Hilal yake zaune cikin soyayyar jikan nasa wanda yake jin son sa daban ne idan aka cire Zahrah cikin jikokin nasa ya ce.
"Jarumin soja yaushe ka shigo, ina ta zuba idanu na ganka shiru, kadan ya rage ban bika ba har ɗakinka ba."
"Barka da rana Papa."
Ya faɗa kamar baya son magana. Cikin farin ciki ya amsa da .
"Barka dai jarumina ya kake?"
"Alhamdulillah"
Ya faɗa a takaice. Sannan ya mai da dubansa ga Dada ya ce.
"Ina wuni.?"
Ita ma ta amsa masa cikin sakin fuska tana tsokanarta irin na kaka da jika. Shi dai bai tanka mata ba ya tashi ya bar wajen. Don idan ya yi gaisuwa ya gama kenan ba fira.
Har ya kai ba bakin kofar ya murda handle ɗin kofar zai fita ya ji Papa na cewa.
"Zahrah ta kawo maka makullin mota wai za ta baka ."
"Ba na buƙata."
"Ai ta sani kuma na san duk motocinka sun fi wacce za ta baka, amma kada ka ƙi karba ba'a mayar da hannun kyauta baya. Ta duba kirkin da ka ji mata ne na zuwa har Kaduna ka ajiye komai na ka ka tafi can saboda ita."
"Ban tafi saboda ita ba, don da ace don ita ne ba zan tafi ba."
",Daga nan ya fice.
Kallon juna Dada da Papa suka yi kafin Papa ya girgiza kai tare da cewa
"Allah ya shirya ."
Daga haka ya tafi zuwa part ɗin iyayensa, suka gaisa bayan haka ƙannensa Faisal da Maryam suka gaishe shi , ganin za su dame shi da surutu ya tashi ya bar falon
Part ɗin Abba ya nufa nan ma ya same su duka , ya gaida Abba da Umma yayin ga Mansur da Nadiya suka gaishe shi.
Bayan ya bar part ɗin ne ya nufi part ɗin Aunty Laila. Nabeela da Kausar kamar za su cinye shi. Ganin yadda suke kallonsa ne ya saka shi tsuke fuska.
"Barka da warhaka Aunty."
Cikin jin dadi ta ce.
"Barka dai Son ka dawo?"
"Eh"
Ya amsa a takaice.
Nabeela ta fara gaishe shi ya ce
"Ina wuni Yaa Hilal?"
"Lafiya lau."
Ya amsa ya yin da Kausar ke ƙoƙarin gaishe shi ta ce.
"Ya Hilal ina wuni ka dawo?"
"Eh na dawo."
"Alhamdulillah na ji dadi da ka dawo laflya."
Bai ce komai ba sai tashi da ya yi ya ce.
"Aunty zan tafi."
"Ka zauna mu yi fira mana."
"Aunty na gaji zan kwanta ne."
Daga haka ya wuce, don yana son yin barci dan ya koma part ɗin sa Alexandra za ta dame shi. Don haka ya yi kwanciyar sa a babban falon gida, kasancewar ba kowa a falon."
Bayan kamar awa ɗaya da kwanciyarsa sai ya ding jin hayaniyar ƴa matan gidan, sai dariya sha da shewa.
A fusace ya tashi tare da daka masu wata irin tsawa wanda ya saka hanyar cikinsu kaɗawa.
Nadiya da Maryam har z su gudu suka ji muryarsa yana cewa.
"Kada wacce ta gudu, duk kuwa wacce ta gudu sai na yi mata ninkin wanda zan yi wa Sa'id."
Sanin waye shi da abin da zai iya aikatawa in dai ya furta ya saka suka dawo.
Belt ɗin wandonsa ya zare da ta kan Maryan ya fara, dukanta kawai yake yi, dai d ya tabbatar ta ji laushi kafin ya janyo Nadeey. Ita ma ya fara dukanta sosai kamar Allah ne ya aiko shi.
Ganin Haka ya saka Nabeela gudu wa .
Tsalle ɗaya ya yi ya isa gabanta. Finciko ta, ganin haka Kausar ta kara tsorata. A guje ta nufi ɗakin Mahaifiyarta.
Sunyi Laila da ke kwance ta mike da sauri tana tamabayar Kausar abin da ya firgita.
Nuni take yi da ƙofa ganin haka ya saka Aunty Laila rufe ƙofa ta murza key.
Sai da ya gama dukan Maryam, Nadeeya, da Nabeela sannan ya lura da Kusar ba ta nan. Kuma duk dukan nan ba wanda ya ji ballantana ya fito cetonsu. Don ya hana su kuka wai baya don hayaniya.
Kausar kuwa tana can wajen Aunty Laila tana rarrashinta duk da ba dukan nata ya yi ba. Ƙarin guiwa take bata akan ta daina wanann kukan tun da ta zo wajen ta ai ta tsira bai isa ya ce zai dakar mata 'ya a gabanta ba.
"Wai me kuka yi masa?"
"Wallahi ba abinda muka masa.'
Girgiza kai ta yi tare da cewa.
"Ƙarya ne haka kawai ba yadda zai iya cewa zai dake ku, sai dai da dalili."
"Eh to yana barci a Falo mu kuma muna ta fira shi ne ya farka ya zare bellet daga wandonsa ya fara ta kan ƙanwarsa Maryam, daga ita dai Nadeeya yana zuwa kan Nabeela shi ne na gudu."
"Kuma ai kun san halinsa baya son hayaniya da kuka kan shi kwance a wajen ai da sai ki tafi. Wani Wajan."
"Mun ɗauka ba zai..."
Dukan kofar da ake yi ne ya saka Kusar ƙankame Aunty Laila.
"Ki fito kafin na ɓalle ƙofar nan na zo na same ki ."
Rai a ɓace Aunty Laila ta ce .
"Halal ka fita i idona ko mutuwa na kunyar idon mahaifi a ɗakina za ka zo ka ce zaka ɓalla?"
"To idan ba haka kike so ba ki miƙo Mani yarinyar nan"
"Wace yarinyar? Yarinyar da za'a aura makan ne za ka daka, so kake ta tsotsa da kai ta ce ta fasa?"
Tsuki ya yi cikin takaici ya ce.
"Kausar wallahi idan ba ki kawo mun kanki ba har kika bari na ɓalle ƙofar nan dukan ki sai ya ninka na su."
"Ƙofar za ka ɓalle mun saboda ba ka ..."
Kafin ta ƙarasa zancen nata ne ta ji wani ƙara take Kum ƙofar ta faɗi ƙasa, sakamakon duka ɗaya da ya yi wa ƙofar Bature sai ga ga ƙasa.
Haka ya nufi Kausar da na ta ƙara tsorata don dama akwai ta da taron duka.
Ƙanƙame Aunty Laila ta yi tana cewa .
"Mum ki taimake ni."
Yana zuwa ya finciko ta tare da hankaɗa ta ƙasa ya hau dukanta da belt ɗin hannunsa. Duk yadda Sunyi Laila ta yi kokarin ƙwatar ta amma ina ta kasa. Don wajen ƙwatar ta har ita ma ta samu rabonta ba shiri ta yi gefe tana duba hannunta da ya daka.
Sai da ya tabbatar ya mata lilis sannan ya bar ɗakin yana huci.
_Fatima Zahrah_
Bayan ta tashi daga barci ne sai ta ji dadin jinkinta sosai. Tashi ta yi ta nufi bathroom ta yi wanka da wani ruwan ɗumin. Sannan ta ɗauro alwala ta zo ya gabatar da sallah.
Bayan ta yi addu'a ta fito ta samu kowa nata a falon. Abbi, Umma, Yaa Mahmud da Yaa Sadik.
Yayyun nata ta bawa keys din motar, Mahmud ya ce.
"Ta ya ya za ki bamu ai kece aka ba."
"Yaya wallahi ba na so ɗaya ta ishe ni"
Ba yadda suka iya dole suka karba suna mata godiya. Dubanta ta mayar kan Abbi ta ce.
"Abbi sauran kujerar Hajji ka bawa wandanda ka ga sun dace, musamman masu bukata da ka san ba su taba zuwa ba sai ka basu, don ka ga mu kam Alhamdulillah Allah ya hore ana zuwa duk shekara."
Sanya mata albarka kawai suke yi tare da yaba kyawun zuviyarta, don duniya ba ta dame ta ba.
Washegari tun a school take jin Mararta na mata ciwo, dakyar ta iya fitowa daga lecture ko Amini da A'isha yau ba ta tsaya sun yi sallama ba ta nufi motarta.
Gudu take yi wajen yin driving ɗin sauri take ta ganta a gida. Ikon Allah ne kawai ya kawo ta gida lafiya.
Tana parking ta fito ko wayarta da jaka ba ta tsaya ɗauka ba ta fice daga motar.
Tana shiga falon sai ta zube kan dogon kujerar ta kasa ƙarasa wa .
Dama haka take fama a duk lokacin da za ta yi period, shi ya sa Ummi ke hana ta yawan shan zaƙi da take yi.
Haka ta dinga murƙususu na azaba ga shi ta kasa, ga shi ta bar wayarta a mota.
Tana cikin wannan yanayi sai ga Aunty Laila ta shigo ita da Mummy. Da alama daga unguwa suke. Kasancewar tana zubar da jini sosai ya saka Kayanta ya ɓaci don haka juyawa da ta yi kuma Abaya ruwan madara ta saka wanda jinin ya nuna a rigar sosai.
Dama tana shan wahala sosai idan za ta yi baƙon wata. Daidai lokacin nan Hilal ya shigo falon, ganin yadda Zahra take ya saka ya kalli su Mummy da sauri ya ce.
"Lafiya kuwa?"
Buɗar bakin Aunty Laila ta ce
"Ciki ta zubar shi ne ta zo ta kwanta wa mutane a nan."
Da mamaki ya kalle ta tare da cewa.
"Ciki kuma?"
", Kwarai kuwa ai wannan kana ganinta ne kawai baka san mugun abu da take aikatawa ba."
"Waye ya faɗa maku ciki ne?"
Mummy ta kalle shi a fusace ta ce
"Ina ruwanka ne wai ma da kake tamabayar mutane, wannan jinin ya wuce jinin haila kam."
Kallon mahaifiyar ta sa ya yi tare da kallon Aunty Laila daidai lokacin da Zahra ta saki jiki ta mirgino za ta faɗo ƙasa.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page2️⃣6️⃣
Kallon mahaifiyar ta sa ya yi tare da kallon Aunty Laila daidai Lokacin da Zahra ta saki jiki da ta faɗin.
Cikin zafin nama ya nufi wajan da take kwance da niyyar ta tare ta kafin ta faɗo ƙasa. Tsawar da mahaifiyarsa ta daka masa bai saka ya fasa abinda yake yi ba.
Tare ta ya yi ta fado akan hannunsa.
Cikin fusata Mummy ta daka masa tsawa ta ce.
"Hilal ba da kai nake magana ba ko?"
"Ku yi hakuri Mummy kin ga yanayin da take ciki ga shi iyayen nata sun fita zuwa ta'aziyyar abokin Papa, Yayyun ma basa gidan idan wani abu ya faru da Ita ku da kuke gidan za'a tuhuma."
A fusace Aunty Laila ta ce.
"Uban waye zai tuhume mu ko akwai wanda ya sa ta yin cikin shege be ballantana ta zubar?"
"Kuna da Hujja kan hakan?"
Ba wacce ya bashi amsa, ɗaukar ta ya yi ya nufi kofar fita, Mummy za ta dakatar da shi Aunty Laila ta mata alama ta bar shi. Ta yi murmushi mai cike da ma'anoni.
Yana fita harabar gidan sojojinsa suka taso alama ya masu da su koma, haka ya saka suka koma ya nufi daya daga cikin motocinsa.
Direbansa ya bashi key ɗin motar ya karba sannan ya yi wa motar key a guje ya bar gidan.
Asibiti ya kai ta in da ya yi parking ya fito ta ɗauke ta zuwa ciki. Aka karbe su cikin gaggawa kasancewar an san su a asibitin.
Doctor ne tare da nurses suka rufa akan ta don zuwa lokacin a sume take.
Jini ne ya ɓata masa amma bai damu da hakan ba. Yana nan zaune sai ga Dyoctor Ahmad ya fito ya ce masa ya biyo shi a office ɗin sa.
Tashi ya yi ya bishi bayan sun gaisa yake cewa.
"Amma na yi matukar mamaki da abin da idona ya gane Mani."
Kallonsa Hilal ya yi ba tare da ya ce komai ba. Doctor Ahmad ya cigaba da cewa.
"Maganin zubewar cikin da ta sha ne ya saka ta a cikin wanann halin."
Wani kallo Hilal ya masa wanda har sai da Doctor ɗin ya tsorata. Don shi bai yarda ba.
"Ka tabbatar da abun da ka faɗa?"
"Ƙwarai kuwa ba abinda zai saka na fadi abin da ba haka ba, yaushe Zahra ta yi aure ne ban sani ba, kuma ban jima da zuwa gidan ba. Kai ne mijinta?"
Banza ya yi masa zuciyarsa kawai yake jin yana masa zafi. Kai tsaye ya shiga ɗakin da aka kwantar da ita ya samu tana barci an saka mata ƙarin ruwa.
Kallonta yake yake yi cike da ƙarin tsanarta a cikin zuciyarsa. Haka ya nufi motarsa ya nufi gida
Tsuki yake ja lokaci zuwa lokaci .
"To wai ma meye na wa na damuwa akan abun da ta aikata?"
Wata zuciyar kuma ta ce masa, 'Ai dole ka damu don ko kana so ko ba ka so ita ɗin jininka ce, kuma idan ta zubar da mutuncinta tamkar ta zubar da Mutuncin ahalinku ne.'
Yana shiga falon ya samu Mummy da Umma sai Aunty Laila suna zaune a Babban falon gidan a kan kujera.
Suna jin karar ƙofar suka juya suna tambayarsa meke damunta. Yanayin ɓacin rai da yake ciki ne ba zai iya magana da kowa ba, don haka bai ce masu komai ba ya haura sama.
Ko da ya shiga falon Alexandra ne zaune a falon. Don sai da ya saka key ya bude saboda baya son a san da zamanta ya saka yake rufe part ɗin da key.
Tana ganin ya dawo rigarsa da jini ya tashi take tamabayarsa cikin tashin hankali. Ce mata ya yi ba komai mai ciwo ne ya ɗauka zuwa asibiti.
Bedroom ya wuce har ya shiga ya dawo ya rufe kofar da key don gudun kada wata ta shigo ta ga Alexandra.
Bayan awanni biyu Abbi da Ummi suka shigo falon bakinsu ɗauke da sallama. Daga Umma har Mummy da Aunty Laila ba wacce ta amsa.
"Ummi ta ce barkanku da gida Ina wuninku?"
Aunty Laila ce ta yi tsuki sauran ko ba su ma kalle ta ba ballantana su amsa. Don dama sun san ba amsawa za su yi ba Amma kullum sai sun yi masu sallama sun gaishe su duk da sanin ba amsa wa suke ba.
Har yanzu Handbag ɗin Zahra na tsakiyar falon sai dai sun kira mai aikin ta goge hanci jinin.
Ganin Handbag ɗin Zahra Ummi ta dauka ta shiga da shi tana cewa.
"Zahra kenan ta ajiye jaka ta shige ciki ko?"
"Abbi ne yake cewa.
"Ta gaji ne shi ya sa ta ajiye anan."
"Haba wani gajiya sai ka ce Jakar nauyi ne da ita?"
Haka suke tafiya suna magana har suka karasa part ɗin su.
Bedroom ɗin Zahra suka fara zuwa amma ba ta ciki.
Ummi ta karasa jikin kofar bathrobe ta ji ba motsi, knocking ta yi shiru. Hakan ya saka tura ƙofar ba ta ciki.
Abbi ya ce.
"Ina ta shiga kuma mai baro Dada da Papa wajen ta'aziyya ballantana ace tana can."
Kiran wayarta Abbi ya yi suka ji wayar a handbag ɗin ta.
Mamaki suke ina ta shiga don ba ta fita sai ta nemi izinin iyayen ta.
_Hilal_
Koda ya koma asibitn ya samu har ruwan da aka ƙara mata sun ƙare, Tana zaune ita kadai a ɗakin, tagaumi ta yi tana tunani waye ke tare da ita a nan.
Ƙamshin turarensa da ta ji ne ya haifar mata da faɗuwar gaba. A hankali ta da ɗaga kai tana kallon ƙofar.
Sakin kofar ya yi ya shiga fuskarsa a murtuƙe, ita kanta ta tsorata da ganin yanayinsa.
"Ba za ki daina kallona ba da wannan shegun idnaun naki kamar na mujiya ba?"
Da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa. Munafuka kawai Musa a baki Fir'auna a zuci ana maki kallon mutumiyar ƙwarai ashe ba haka ba kura ce ke lulluɓe da fatar akuya."
"Ya Hilal me na..."
Katse ta ya yi cewa.
"Tun yaushe kika fara wannan harkar a ƙarancin shekarunki?"
Kallon rashin fahimta ta yi masa ta ce.
"Harka?"
"Tambayarki nake yi waye abokin fasiƙancin na ki?"
Shiru ta yi yayin da ƙwalla ke kwaranya a idnaunta. Ba ta yi aune ba ta gan shi a gabanta sai huci take.
Shaƙo wuyanta ya yi ta fara zaro idanu tana kakari.
"Na ce waye ya yi maki cik?"
_Jidderh_
Ko da ta koma gida yau sam ta ƙi cin abinci kuma ta ƙi magana da kowa. Da Inna ta tamabaye ta sai ta ce mata ba komai.
Tana cikin wannan yanayin ne sai ga Yaya isah ya dawo gidan. Kallo ɗaya ta mata ya gane tana cikin damuwa.
Ƙarasa wa ya yi wajen yana cewa.
"Subhanallah Autar Inna lafiya?"
Kuka ne ya kufce mata ta ce.
"Yaya tausayinsa nake ji."
"Waye kike jin tausayinsa?"
"Yaya wa ka sani bayan Asadullah da kullum nake maka zancensa."
"Allah ya kawo masa ɗauki?"
"Yaya ka taimake ni mu fitar da shi daga wannan halin da yake ciki."
Kallon baki da hankali ya yi mata kafin ya ce.
"Kin san me kike fada kuwa?"
"Na sani Yaya."
"Babban mutum ne fa ta Yaya kike tinanin fitar da shi, kada ki je ki saka rayuwarki a hatsari da."
Mumrmushin takaici ta yi tare da cewa.
"Matarka da ɗan ka suna raye