Showing 39001 words to 42000 words out of 154779 words
shirya cikin ƙananan kaya, yana shirin fitowa sai ga Jamilu ya shigo ɗakin tare da sallama.
Ya amsa masa kamar baya son magana.
"Zo ku ci abinci ko?"
"Okay mu je masallaci mu dawo."
Ya faɗa yana saka wayoyinsa a silent ya zuba a Aljihu suka fita zuwa Masallaci.
_Asadullah Mansion_
Dad ya kasa barci har ƙarfe ɗayan dare, Mom ce ta farka ta ganshi tsaye yana zageye ɗakin.
"Alhaji lafiya kuwa?"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa.
"Hajiya lafiya kau ki kwanta kawai."
Tashi zaune ta yi tana kallonsa, ganin haka ya sa ya zauna bakin gadon tare da cewa.
"Gabaɗaya hankali na ya kasa kwanciya ne dangane da tafiyar Asadullah. Dalili na farko bai taɓa tafiya ba tare da ya sanar da ni ba. Amma wannan karon sai na ga text message yana sanar da ni tafiyar. A lokacin na yi mamaki haka, da abinda ya hana ya same ni ya sanar da ni, sannan kuma har tsawon wata ɗaya kenan amma bai kira kowa a waya ba. Sannan suka layukansa na ƙasashen da yake zuwa na gwada kira ba sa tafiya. Ina ji a ajikina akwai wata matsala."
"Gaskiya ne Alhaji ni ma kaina abun ya dame ni, jiya na gama wannan tuninin ina son da safe mu tattauna akan zancen. Kada ka yawaita saka damuwa kasan yanayin ciwonka baya son damuwa."
Jinjina kai ya yi suka kwanta zuciyar kowa cike da saƙe-sake.
Washegari gari da safe bayan yaran sun tafi school masu zuwa aikin sun tafi. Dad ne sai Mom da Aunty. Sun saka mijin nasu a tsakiya
Dad ya kalli Aunty da Momya ce.
"Ina son zan yi tafiya don nemo halin da ɗana yake ciki."
"To Alhaji tun da ba ka san wace ƙasa ya ya tafi ba ta ina za ka fara?"
"Ni ma ban sani ba daidai duk ƙasashen duniya da na san yana zuwa zan je na ji dalilin shirun nasa."
Kallon Mom Aunty ta yi tare da cewa.
"Allah ya kyauta ya wadaran naka ya lalace."
Banzan kallo Mom ta yi mata tare da cewa.
"Alhaji kana jin matarka ko, ka yi Mani iyaka da ita, ban san me yasa kake magana da ita akan matsalar da ta shafi Asadullah ba, ko ka manta irin ƙiyayyar da take masa ne, ko gaisuwarsa ba ta amsa wa da kyau. Ita da shi ba maganar arziki idan ya mata magana ba ta kula shi, sannan ta hana yaranta duk da ta san ƴan uwansa ne amma ta hana su magana da kowa, idan ta ga Suhaila na kiran Asad da Yaya ko tana masa magana sai ta yi mata duka. To wallahi ki zuba idanau idan wani abu ya samu ɗana sai na yi kuka dake."
Dariya Aunty ta yi har da ƙyakyatawa ta ce
"To makira ta nan za ki ɓullo to Ina jira daidai nake da zamaninki"
Abba ne ya nuna wa Aunty ɓacin ransa wanda ya sa dole suka yi shiru Aunty ta tashi ta nufi ɗakinta
Bayan ta tafi ne Kin ta kalli Dad ta ce .
"Wallahi matar nan ba ƙaunarmu take yi ba daga ni har yara na, kuma duk abinda ya samu Asadullahi sai na yi Shari'a da ita."
Dad ne ya kwantar mata da hankali sannan ya fita , kiran amintaccen bodyguard ɗin Asadullah ya yi wato Sulaiman.
Bayan sun gaisa ne Dad ya masa tambayoyi dangane da wuraren da Asadullahi ke zuwa tare da shi. Da kuma wuraren da da yake zuwa shi kadai ba tare da kowane guard ɗin sa ba. Bayan sun tattauna Dad yana ƙoƙarin koma ciki sai ga Uncle Adam ya karaso wajen.
Bayan sun gaisa ne y ce
" Dama part ɗin ka zan tafi. Ya ake ciki ne har yanzu ba ka ji motsin Asadullah ko labarin ƙasar da ya tafi ba?"
Girgiza kai Dad ya yi cikin damuwa ya kalli ƙanin nasa ya ce.
"Adam har yanzu ba wani labari bai taba yin tafiya ba tare da ya sanar da Ni kasar da zai tafi ba, ko kuma ya tafiay bai yi Mani sallama ba sai dai wannan karon na ga sakon message da ya tura mani ta waya wai ya tafi wata ƙasar sai ɗauki lokaci kafin ya dawo."
Jinjina kai Uncle Adam ya yi tare da kallon Sulaiman ya ce.
"Har da kai bai sanar da kai ba?"
"Bai sanar da ni ba, kuma abun da ya bani mamaki mun dawo daga kamfaninsa ASADULLAH GLOBAL RESOURCES."
"To da kuka dawo sai aka yi yaya?"
"Sai ya shiga gidan sauran guard ɗin suka tsaya a harabar gidan kamar yadda suka saba, ni kuma na ɗauki laptop da wasu file da ya dawo da su na taka shi har part ɗin sa, na ajiye masa a falonsa na fito. To tun daga ranar ban sake ganinsa ba har yau."
Wani banzan kallo Uncle Adam ya masa tare da cewa.
"Wannan ai zance banza ne , ta yaya kuka aikin kula da mutum ku ce b ku san lokacin da ya fito ba, barci kuke yi ko me?'"
"Alhaji ba barci kuke yi ba, sanin kanka ne ko dare yayi akwai security da basa barci, sai dai su yi ta zagaye gidan nan har gari ya waye kafin wasu su karbi aiki. Amma wallahi ba wanda ya ga fitowarsa a cikin gid..."
"Shut up! Me za ka ce kana nufin yana. Kwance a ɗakinsa ne ko me kake nufi? 6)To je ka kira shi."
_Fatima Zahrah_
Fitowa ta yi zuwa dinning area kamar yadda Sumayya ta sanar da ita. Suna zaune su uku, Hilal, Jamilu da Sumayya.
Bakinta ɗauke da sallama ta karasa wajen, tana sanye da hijabi wanda ya rufe mata jiki.
Amsa mata sallamar suka yi ta karaso ta zauna.
Abinci Sumayya ta zuba mata jallop ɗin cuscus da ya ji kayan lambu da kuma lemun ta zuba mata a kofi da ruwa. Sai farfesun kaza.
Kaɗan ta ci ta kasa sake wa ganin irin kallon da Jamilu ke yi mata .
Tashi ta yi bayan ta ɗan ci kaɗan ta sha ruwa, kallonta Jamilu ya yi tare da cewa.
"Me kika ci?"
"Alhamdulillah na ƙoshi."
"Ban yarda ba, nan fa kamar gidanku ne, ina zuwa Katsina fa a gidanku nake sauka kuma ina sake jikina kamar gidanmu. Duk da ban taba haduwa da ke ba, sai dai ina tunanin ke ce mai fita kullum da niƙab ko?"
Murmushi ta yi sannan ta sunkuyar da kai.
"Okay na gane kullum idanunki kawai ake gani, nima yanzu na gane ki ne saboda wannan kyawawan idanun naki."
Wani kallo Sumayya ta masa ya wayance ya cigaba da cin abincinsa.
Wayar Hilal ce ta yi ƙara ya duba ALEXANDRA ce ke kiransa a waya. Ɗagawa ya yi suka fara magana cikin yaren ƙasar Spain. Tun da ya fara magana Jamil dake jin me yake cewa ne yake masa wani mugun kallo da harara. Su kam Sumayya da Zahra ba sa jin yaren sai dai idan ya ambaci Nigeria ko ya ambaci U.S ne suka san me ya kira.
Bayan Hilal ya gama wayar ne Jamil ya kalle shi rai a ɓace ya ce.
"Kana nufin goben nan za ta bar ƙasar U.S ta biyo ka Nigeria?"
Kallonsa Hilal ya yi kamar baya jin me yake cewa, ya cigaba da danne-danne a wayarsa.
"To ai sai ka bari idan ka koma can Katsina ta je ta same ka, amma ba gidana wacen shegiyar za ta zo ba."
Sai a lokacin ya kalli Jamilu ya ce.
"Gobe za ta zo kuma duk in da nake dole nan za ta zo, ba ka isa ka hana ta zuwa in da nake ba. Don da na yi niyyar kama hotel ai hana ni ka yi ka sa dole na sauka a gidanka. Don haka duk in da nake nan ALEXANDRA za ta kasance baƙuwata ce."
"Baƙuwarka amma ba bakuwar arziki ba ne don haka ka je ka kama maku hotel kai da ita, Zahra za ta zauna a nan har ta kammala abinda ya kawo ta ."
"Wallahi ba ka isa ba, yadda ka hana ni da farko na hanu yanzu ba ka isa ka saka ni ba."
Yana gama fadar haka ya tashi cikin takunsa na ƙasaita ya nufi bedroom ɗin da ya sauka.
Da kallon mamaki suka bishi wanda sam Jamilu bai yi mamaki ba don ya saba da halinsa. Zahara kam mamakin isa da gadara da yake da shi take yi.
Washegari gari kasancewar da safe ne za'a gudanar da musabaƙar ya saka Zahra tun da ta yi sallar asuba ta yi azkar sai ta nufi kitchen. Don ba ta saba da barci safe ba.
Ruwan tea ta dafa da ya ji kayan ƙamshi sananne ta yi farfesun kayan ciki ta soya dankalin turawa da plantain sai ta soya ƙwai .
Lokacin da Sumayya ta fito har ta gama komai ƙamshin da ta ji ne ya bata mamaki
Suka gaisa tana mata maganar ta wahalar da kanta tana girki, murmushi kawai ta yi tare da komawa ɗakinta.
Kasancewar karfe takwas ta yi ne ya saka Zahra ta gama shirinta. Lokacin da Sumayya ta shigo kiranta har ta sanya hijabi.
A tare suka fita in da suka tarar da Hilal da Jamilu suna cin abinci. Hilal kam ya shanye farfesun kayan ciki ya masa dad'i . Don bai ci komai a wajan ba tun da ya ji ƙamshin farfesun.
Jamilu kowa har santi yake zubawa yana cewa.
"Sweetheart wanan girkin na yau na musamman ne, gaskiya ya yi dadi."
"Ba ni ba ce na yi Zahrah ce ta yi."
Cak Hilal ya tsaya tare da ture bowl ɗin gabansa ya bar wajen.
Da kallon mamaki Jamilu da Sumayya suna bishi, Zahra ko kallonsa ma ba ta yi ba, ba ta da riko amma abinda ya mata jiya ya tsaya mata a rai.zama ta yi inda Jamilu ya daga murya yake ce wa Hilal.
"Ba ka birge ni ba har sai ka amayar da abun da ka ci sannan zan san ka yi abin kai."
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page2️⃣0️⃣
"Ba ka birge ni ba har sai ka amayar da abun da ka ci."
Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi ba tare da ta nuna ma ta san yana yi ba.
Nan Jamilu da Sumayya suka dinga jan ta da fira da yaba irin daɗin da girkin nata, har ta saki ta fara dariya.
Ganin saura mintuna arba'in a fara ne ya saka Zahra hankalinta ya fara tashi, musamman da ta ga Hilal baya da niyyar kai ta.
Lura da yanayinta ne ya saka Jamilu cewa.
"Ƙanwata lokacin ya kusa ko?"
Murmushi kawai ta yi ba tare da ta yi magana. Don haka ya cigaba da cewa.
"Bari na yi masa magana ya shirya, ai tare da ni za ku tafi. Don direban nasa na ce ba sai ya kira shi ba, ya bar shi s hotel ɗin za mu tafi da motata."
Yana gama faɗar haka ne ya tashi tare da nufar ɗakin da Hilal yaƙew. Bayan kamar mintuna goma Jamilu ya fito ransa a ɓace. Da alama sun samu saɓani da Hilal ɗin.
Jikinta ne ya yi sanyi ganin yadda ya fito, sai ya yi murnushi tare da cewa.
"Ƙanwata muna ina zuwa please."
Jinjina kai kawai Zahra ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Suna nan zaune ita da Sumayya sai ga Jamilu ya fito, sanye yake cikin wata yadi mai ruwan ƙasa, sai zuba ƙamshi yake zubawa. Kallon Zahra ya yi tare da cewa.
"Fatima Zahrah ta shi mu tafi Yayanki baya da niyyar tashi kada ki makara."
Kamar ba za ta je ba sai kuma ta yi wani tunani, saboda Ya Hilal na gidan ta san ko zuwa ya yi ya cutar da ita ko aka rasa ta dole shi za'a tuhuma tun da ya san shi. Don haka sai ta miƙe ta ce.
"Yaa Jamil ina zuwa, ɗakinta ta koma ta ta ɗauko ƙaramin handbag ɗinta da niƙab, sai ta tuna a ce kada su saka saboda a san su. Don haka ta ajiye ta fito bayan ta rataye ƙaramin handbag ɗin ta.
A tsaye ta same su shi da Sumayya suna rike da hannun juna. Don haka gaba suka yi tana biye da su a baya.
Ɗaya daga cikin motocinsa dake parking space suka nufa. Ya shiga mazaunin Direba, Zahara ta kalli Sumayya ta ce
"Auntu ke ba za ki je ba ne?"
Murmushi ta sakar mata tare da cewa.
"Sister ta ce ta haihu yau ake suna, can zan tafi ku yi haƙuri."
Murmushi ta sakar mata tana cewa
"Allah ya raya."
Da Amin ta amsa mata yayin da ta buɗe mata murfin motar, ta shiga ta zauna gefen Jamilu. Ɗaga masu hannu ta ta yi yayin da ya yi wa motar key maigadi ya wangale masu gate suka bar gidan.
Wajen harabar in da za'a gudanar da gasar karatun Al-ƙur'anin ya cika da mutane. Suna parking kiran waya ya shiga cikin wayarta. Ba kowa ba ne face Mallam Usman, Mallamin islamiyarsu da ke sonta.
Ɗaga wa ta yi baya ta yi sallama take sanar da shi sun iso.
Wajen da aka tanada saboda parking motoci ya nufa. Bayan ya yi parking suka fito. Mamakin cikar jama'a dake wajen ta yi, duk da an sanar da su da yadda komai zai gudana a wajen, amma ba ta yi tunanin yawan jama'ar sun kai haka nan ba.
Taro da ya ƙunshi manyan mutane tun daga kan ƙusoshin gwamnatin zuwa hamshaƙan ƴan kasuwa da ƴan siyasa, sarakuna. Da masu matsayi a gwamnati. Jami'an tsaro kuwa ga su nan cike a wajen suna gudanar da aikinsu. Don an saka matakan tsaro sosai ba waje ne da za ka je kai tsaye a bar ka ka shiga ba, sai an bincike babu wani abu na cutarwa a tattare da kai.
Cikin sanyin jiki ta ƙarasa in da ta hango tawagar ƴan jiharsu. Yayin da Jamilu ya zauna ɗaya daga cikin kujeru da aka tanada don baƙi su zauna.
Tana ƙarasawa ƴan tawagar su da Mallamansu suka nuna jin daɗinsu da isowarsa.
Nuna mata wajen zaman da aka tana da dan su aka yi. A hankali ta fara taku cikin nutsuwa ta nufi wajen zamansu , taka step ɗin take yi cin nutsuwa yayin da ta kasa ɗaga idanunta. Saboda idanun. Mutane da take ji yana mata yawo a jiki.
Ɗaya daga cikin kujeru uku da suka rage ba mutane ta nufa. Kowane kujura an rubuta sunan state, kai tsaye ta nufi wanda ta ga an rubuta Katsina state. Saura na Adamawa da Niger state. Su ne da alama ba su ƙaraso ba. Zaman ta ba jimawa sai ga ƴar jihar Niger ta iso Salma Usman Isma'il. Daga kashe sai ga na jihar Adamawa namiji ne shi ma ya ka karaso wajen.
Ƙamshin daddaɗen turarensa ne ya daki hancinta. Wanda ya haifar mata da faɗuwar gaba, kamar an ce ta ɗaga kai sai kuwa ta sauke su akansa lokacin da yake shigowa cikin taron. Da
Sanye yake cikin wata ɗanyar shadda fara sa sai ɗaukar idanu yake yi, yana sanye da baƙar hula sai bakin takalimi hannunsa ɗauke da tsadden agogonsa. Duk da fuskar nan a tsuke take babu sassauci amma hakan bai hana kyawunsa da cikar haibarsa bayyana ba.
Jamilu ne ya karaso wajensa yana masa nuni da in da za su zauna, kamar ba zai zauna ba sau ya bishi suka zauna.
Nan Sheikh Muhammad bin Ali shahararren Mallamin da ake alfahari da shi ya yi sallama, tare da bude taro da addu'ar ya gabatar da abinda ya tara su . Tare da yi wa manyan baƙi da kowa barka da zuwa, in da ya gabatar da sunanyen wasu manyan baƙi da suka halarci taron. Governor bai samu zuwa ba amma ya turo Wakilinsa ya halarta.
Cikin nutsuwa aka fara gabatar da komai, tamabayoyi ne ake masu na alƙu'arni. Maza da mata ana tambayarsa cikin sura kaza aya ta kaza ka karanto su. Ko kuma a yanko aya a tsakiyar surorin al-ƙur'ani a ce ka karanta , har sai ka kai yadda suke so sai a dakatar da kai a sake shiga cikin wata surar a ce a ce cikin sura kaza aya ta kaza ki karanto su. Kina gama kai in da ake so sai a dakatar da ke a sake tamabayarki wata aya cikin wata sura ki karanto su. Kuma an soma kowane harafin ki bashi hakkinsa don ko kaɗan kika yi kuskuren harshe sai na gyara maki.
Tun ana yi wa ƴan wasu state har aka zo kan Katsina state in da Zahra ke wakiltar ɗaliban jiharsu.
Kowace tamabaya aka yi mata cikin kowane sura aka fada mata lambar ayar kai tsaye za ta fara rero karatunra cikin zazzaƙar muryarta mai saka nutsuwa a cikin zuciyar ma'abota saurarenta.
Ta burge mutane da yawa saboda karatun na ta ba'ayi mata gyara ko ɗaya ba, kowane harafin tana bashi hakkinsa. Kuma duk surar da aka yanko mata za ta fara babu tsayawa har sai an dakatar da ita.
Ta burge mutane da yawa ga yan jarida da yan gidajen rediyo suna ɗauka, bayan masu ɗauka da wayoyinsu.
Tsawon lokaci aka ɗauka ana gudanar da komai gwanin sha'awa, yayin da Zahra ta shiga ran mutane da yawa, yadda duk in da aka aka ce ta karanto za ta karanto take ba tare da sai ta tsaya nazari ko tinani ba.
Hakan ya saka jaharta Katsina ta ci wannan gasar. Ita ce ta zo ta ɗaya a cikinsu. In da ta samu manyan kyaututtuka na ban mamaki. Don kujerar Hajji sai da ta samu guda biyar da mitoci biyu. Ga masu ba ta kyaututtukan kuɗaɗe.
Tsabar farin ciki kuka ta yi sai hawaye ke bin fuskarta. Sauran ma sun samu kyautar amma ba ta kai ta Zahra ba, ta biyu zuwa na biyar ne suka samu kyautar kujerar Hajji.
Farin ciki a wajan Mallaman makarantar ta su ba'a magana. Don sai washe baki suke yi.
Haka aka tashi taron cikin farin ciki, yayin da ƴan jarida ke ta ƙoƙarin sun ji ta bakin Fatima Zahrah Salis Tafarki amma abun ya ci tura. Don ta kasa magana sai kuka take yi. Gashi sai hasken Camera ke ta haska ta ta ko ina, wasu saboda ƙwazonta yayin da wasu kuma saboda kyawun da Allah ya yi mata.
Kamar yadda tsarin su yake sai an koma state ɗin ta kafin a damƙa wa iyayenta kyaututtukan da aka bata. Haka ma ta kasance.
Sallama ta yi