Showing 21001 words to 24000 words out of 154779 words

Chapter 8 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6281

ma zo ku ga farin ciki a wajen wannan family. Ranar suka aka sakawa yaro suna. Abubakar. Ya taso cikin kulawar uwa da uba da kuka Kaka.

Bayan shekaru biyu Dada ta dake samun wani cikin. bayan watanni tara ta sake haihuwar ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Adam.

Umma ke kula da jikokinta nsosai take nuna masu ƙauna dujansu. Shekaru uku ne ke tsakanin Abubakar da Adam. Lokacin da aka yaye Adam a lokacin ne aka saka Abubakar Makarantar boko da ta islamiyya. Kuka a wannan tsakanin ne Dada ta dake samun wani cikin in da bayan watanni tara ta sake haihuwar ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Salisu. Wato sunan mahaifin Muhammad da ya ya rasu ya saka masa.

Yaron da aka nunawa gata da so da kulawa fiye da sauran yaran. Kasancewar sunan mahaifinsa ne d shi wato mijin Ummi.

Daga Muhammad har Dada ba mai kiran sunan Salisu sau suna kiransa da suna Abbi.

Umma kuma mijina take kiransa. So da ƙauna da suke yi wa Abbi ya kasa ɓoyuwa. Dan duk wanda ya so gidan nan dai ya fahimci sun fita soyayyar Abbi fiye da sauran yaran. Ko kukansa suka ji sai hankalin su ya tashi sosai.

Yaran sai suna kiran Muhammad da suna Papa. A ƙa'idar Papa ko ya dawo kasuwa sai ya fara zuwa ɓangaren mahaifiyarsa ya gaishe ta, ya ba ta nata tsarabar sannan ya wuce da nasu ɓangaren su. 'Ya'yan nasa ma anan yake ganinsu ya barshi tare da Kakarsu. Sai dai tun da aka haifi Salis wanda suke wa laƙani da Abbi Dada da Papa suka kasa kawaici akan sa kamar yadda suke yi akan sauran yaran biyu.

Don Papa ko ya dawo kasuwa ba ya ɗaukar yaro daga ɓangaren Dada ya tafi da shi nasu bangaren nan ya ke barinsa. Amma tunda aka haifi Salis ya kasa yi mata kawaicin da yake yi akan Abubakar da Adam.

Don sai ya ɗauke da ya jI shi can ɓangaren tare da su, sauran ƴan uwan kuma sai su natsu tare da kakan.

Ita kanta Dada lokacin da take goyon sauran yaran ko ta ji suna kuka a ɓangaren Ummi ba ta zuwa sai ta yi kawaici har sai Ummi ta kira ta ko da kawo yaran .

Amma ta ɓangaren Salisu wanda suke kira Abbi ba wannan kawaicin, tana jin kukansa zata nufi ɓangaren Ummi cikin hanzari. Ta ɗauke sa ta ta je da shi part ɗin sa bashi mama ya sha .

Kuma wani abu da yake ɗaurewa Umma kai sauran yaran ba sai ta je ta ɗauko su ko ta ce a kawo su ba, Dada da kanta za ta kai su ko Papa zai kai su amma shi wannan Salis da ake goyo ba'a kai shi dai dai idan ita ce da kanta ta je ta ɗauko shi.

Umma ta so ta yi magana amma sai ta bar abun a cewar kika saboda shi ne ƙarami shi ya saka suke nuna masa irin wannan soyayya. Duk da cewa sauran ma ko da suke ƙanana ba'a nuna masa haka ba, ko shi Abubakar da suke ƙarami kuma a kansa aka fara haihuwa ba'a nuna masa wannan soyayyar ba, haka ma Adam.

Ana cikin wannan haka nan ne aka saka Adam makaranta ɗaya da Yayansa Abubakar. Lokacin ne Kum aka yaye Salis wanda ake kira da Abbi.

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har aka yaye Salis.

Lokacin da aka yaye shi Ummi ba ƙaramin mamaki ta yi ba, ganin uban jibgin kayan wasa da aka siyo masa, ɗaki guda aka cika da kaya. Wasa. Ga kuma kayan yaye da aka siyo masa sakamakon yaye shi aka yi. Kama daga kan kwalim biscuits, kwalim chocolate da Sweet da wasu snack da lemun roba da na kwali duk an siya masa. Ga motar wasan yara jirgi da keke da jita da kayan wasan yara kala-kala.

Umma ta kira Papa ta ce masa

"An ya kuna adalci a tsakanin ƴaƴanku kuwa ? Me ya saka kuka fifita soyayyar Salisu fiye da sauran ƴan uwansa?"

Kallonta Papa ya yi tare da cewa

"Ba fifita shi muka yi ba Ummi, duk da cewa idan n kalle shi sai na ji dadi saboda Sunan Mahaifins ne da shi."

Wannan ba dalili ba ne sai dai zan fada maka ku ji tsoron Allah ku yi adalci a tsakanin ƴaƴanku. Ba ni ce na fada ba fadar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne. Za ka iya tafiya."

Tashi ya yi har ya kai bakin ƙafa ya juyo jin tana cewa.

"Kada ku janyo ƙiyayya a tsakanin ƴaƴanku matukar kuka cigaba a haka. Idan ka fita ka siyo Mani maganin zazzaɓi kai na ciwo yake yi."

Jinjina kai ya yi sannan ya fita don zuwa siyo mata magani.



*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z




*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page1️⃣1️⃣

Jinjina kai ya yi sannan ya fita don zuwa siyo mata magani.


Bayan kamar mintuna ashirin ya dawo hannunsa rike da ledar magungunan da ya siyo mata .

Tana kwance a saman doguwar kujera ya shigo da sallama a bakinsa kallo ɗaya ya yi mata gabansa ya faɗin, a guje ya ƙara da gabanta tare da kiran sunanta.

Shiru ba ta amsa har sau uku yana kiran ta shiru ba amsa, hakan ya saka ya fito a gigice ya koma ɓangarensu. Wayarsa ya ɗauka ya kira wani abokinsa mai suna Dr Ibrahim ya sanar da shi halin da ya zo ya samu mahaifiyarsa.

Dada ma ta nufi ɓangaren Umma cikin tashin hankali. Ganin ta ta yi kwance rai ya yi halinsa. Durƙusawa ta yi tana kuka a wajen.

Har Dr Ibrahim ya zo da kayan gwaje-gwaje ya karasa gaban kujerar da Umma ke kwance.

Bayan ya yi gwaje-gwaje ne ya girgiza kai tare da abokin nasa wanda Papan ma shi yake kallo.

"Abokina sai dai da mu yi hakuri Inna ta riga mu gidan gaskiya."

Wani jiri ne ya so ɗibar Papa wanda hakan ya saka shi zubewar bisa guiwoyinsa.

Sai nanata kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yake ta nanata wa. Kafin zuwa can hawaye suka fara bin fuskarsa. Zani ya dauko a bedroom ɗin ta ya zo ya lallube ta har fuska.

Dada ma sai kuka ta ke yi sosai don ta ji mutuwar Umman . Dr Ibrahim ya fita tare da sanar da su yana zuwa

Nan fa labarin ya fara karade unguwar mutune suka fara shigowa.


*Bayan shekaru biyu*

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a wajen wannan iyalan na Papa. Yana kyautatawa iyalansa sai dai ya fifita soyayyar Salis a cikin ƴaƴansa uku. Don komai na Salis na musamman ne iyayen su ke masa .

Kullun Papa idan zai dawo kasuwa sai ya yi wa Salis tsaraba wanda ba ya yi sa sauran yaran. Kama daga kayan sawa har kayan maƙulashe. Don har yanzu ya kai Abubakar wanda a yanzu yake da shekaru takwas a duniya ya fara fahimtar cewa iyayen nasa na nuna masu wariya a tsakanin yaransu. Ko Adam da yake da shekaru biyar ya fara gane cewa an fi son Salis fiye da su.

Saboda ƙiri-kiri suna kallo za'a siyo masa kofin gwangwani da yawa a jera wa Salis a ɗaki bayan ƙwai da ake tar masa a ɗaki din zuwa lokacin bai wuce shekaru biyu ba ko daa ka siyo masa tsire da nama ba iya ci su yake ba . Haka za'a loda masa a gabansa sauran yi sauran ƴan uwansa na kallo ba'a ajiye masu ba kuka ba'a tsammu su ba. Suna kallo da halin su ci

Lokacin ne kuma aka yaye shi.

Bayan yaye shi ne Dada ta sake samun wani cikin, bayan watanni tara ta haifi ƴa mace. Sun yi farin ciki da samun ƴa mace sosai. Ranar suna yarinya ta ci suna Laila.

Zuwa lokacin an saka Salis makaranta, sai dai ko a makaranta ma an fifita shi za sauran ƴan uwansa. Don makaranta da aka saki shi ya fi wanda aka saka sauran ƴan uwansa kudi, don makaranta ce ta kuɗi sosai tana da tsada.

Kullun da safe idan Suka shirya zuwa makarnata za'a girka wa Abubakar da Adam abinci su je da shi makaranta yayin da shi kuma Salis za'a soya masa ƙwai da dankalin turwa wata rana ya kai ƙwai da indomie da lemun kwali ko na gora da sauransu. Ko da sun ce wa Papa ya siya masu abinda ya yake siya wa Salis ba ya siya.

Makarantar su Abubakar da Adam ya fi nisa, makarantar Salis a kusa yake amma kullun safiya sai Papa ya kai Salisu makaranta a motarsa sannan ya wuce kasuwa.

Su kuma sauran ƴan uwansa sai su tafi makarantarsu a ƙasa.

A haka rayuwa ta yi ta tafiya ana nuna masu banbanci da fifiko wanda har hakan ya kunna wa Ababakar da Adam wutar ƙiyayyar ɗan uwansu. Don haushinsa suke ji a cikin zuciyarsu.

Don ko Laila dake ƙanwa ce a wajen Salisu ba'a nuna mata soyayyar da ke ji nunawa Salis .

Ko da ta cika s shekaru uzu makarantar da suke aka haɗa ta a cikinsa. Kuma sai a siya wa Salis abu amma ita a barta haka nan ba komai. ko Makaranta ce tana gani za'a kai Salisu da mota yayin da ita kuma ba ta damuwa ba saboda karancin shekarunta a lokacin.

Yau da gobe har ita ma ta yi wayo ƴan uwan suka fara cusa mata tsanar Salis, don ida za su je makaranta a hanya suke zancen yadda iyayen suke nuna banbanci a tsakanin yaran ta hanyar bata labarin abubuwan da ke masa wanda su ba'ayi masu da yadda kullun Papa ya dawo kasuwa sai dawo masa da tsaraba.


*Bayan shekaru goma*

Abubakar ya gama karatun secondry school yayin da Abba ya nema masa girbi a jami'ar Bayero in da y fara karatunsa na digiri . A lokacin kuma Adam na s.s. 2 a secondry school yayin da Salis yake j.ss 2 ita kuma tana primary 5 ne a lokacin.

Bayan Abubakar ya fara karatun jami'a ne sai ya zama Adam ne ke zuwa tare da Laila makaranta, har lokacin Papa bai daina kai Salisu makaranta a motarsa ba, kuma har lokacin bai daina siyo masa kaysyyskin da yake siyo masa ba, kama daga na ci da na sha har zuwa na sakaws.

Don a ɗinkin Dada an yi masa jere da kifin gwangwani da sauran kayan maƙulashe da su lemukan kwali. Dan ko girki idan aka gama sai a saka masa naman da ya fi na ƴan uwansa. Ranar da ba makaranta Papa ya kan ɗauke shi ya tafi da shi kasuwa wurin kasuwancinsa.

Har ya kai Dr Ibrahim abokin Papa ya yi wa Papa magana akan yadda yake fifita son ɗan sa Salisu fiye da sauran wanda har Dada ma ta fifita soyayyar Salisu fiye da sauran duk da kasancewar Laila ƴa mace ƙarama a cikinsu kuwa. Don dukkansu uku a jami'ar Bayero university suka yi karatun digi yayin da Salisu aka tura shi ƙasar Ingila ya ƙarasa karatunsa har matakin masters ɗin sa.


Papa ya sour babban fili wanda ya yi gini ɓangare ɓangare a cikin gidan. Bayan ya san cewa ƴaƴansa Abubakar da Adam suna neman aure. Don ya ce baya son yaransa su yi nisa da su. Don zuwa lokacin arzikinsa ya ƙara bunƙasa sosai. Abubakar yana aiki a jami'ar Bayero University ne yayin da Adam ke aiki a kamfanin Papa dake nan garin Kano.

Duk da cewar Salisu baya ƙasar sai dai idan ya dawo yake zuwa amma sam ƴan uwansa nasa mu'amala da shi. Ko fira suke yi da zaran ya zo cikinsu ya zauna za su watse su bar wajen. Wannan ƙiyayyar ta yarinta sun gina ta a cikin zuciyarsu. Sam ba sa ƙaunarsa a cikin zuciyarsu. Don ko motoci da Papa ya siyaasu na sa ya ninka kudin ta su motar sau uku.

A hankali bikin Abubakar da Adam ya ƙarato don rana ɗaya za su yi auren. Ana saura sati ɗaya bikin Salis ya diro a ƙasar don sauran masa shekara ɗaya ya kammala haɗa masters ɗin sa.

An saka ranar auren Laila ita ma nan da wata ɗaya mai zuwa. Bayan kammala bikin su Abubakar.

Ko da Salisu ya dawo garin ana ta a hidimar biki in da ya cire kuɗaɗe masu yawa ya bawa ƴan uwansa do su ƙara wajen hidimar biki amma tsabar tsanar da suka masa ko abin hannunsu ba sa son karɓa. Da ya same su duka su uku Abubakar da Adam da Laila ya masu magana akan abinda ya masu da suka tsane shi basa son ya rabe su sai suka nuna masa cewa ai shi dama daban yake ba a cikinsu yake ba. Shi ai daban ne su uku suke abu ɗaya shi dama an nuna masa ba ɗaya suke ba.


Wata ranar juma'a jama'a suka shaida ɗaurin auren Abubakar Muhammad Tafarki tare da amaryasa Maimuna Ibrahim, sai kuka aka ɗaura auren Adam Muhammad Tafarki tare da amaryarsa Amina Abdullahi.

Bayan an gama shagulgulan biki aka kawo amare a ɓangarensu da ke nan c cikin gidan Papa kowacce ɓangareta daban.

Suna zaune lafiya ba wata matsala a tsakaninsu. Har aka yi bikin Laila in da aka ɗaura auren ta da angonta Aminu in da aka kai ta gidansa dake garin Zaria.


Ba dade wa Maimuna matar Abubakar ta haifi ɗanta namiji ranar suka yaro aka sakawa yaro suna Hilal. Lokacin cikin Amina wata biyar, kuma a wannan lokacin. Daidai wannan gaɓar ne Salisu ya dawo daga ƙasar waje. Ya so ya yi aiki a can saboda wani kamfani sun ɗauke shi aiki, amma. Papa ya hana don ba zai iya nisa da ɗansa mafi soyuwa a gare shi ba.

Bayan dawowarsa Papa ya ce shi ma ya yi aure, ya ce baya da wacce yake so hakan ya saka Papa ya nema masa auren ƴar abokin kasuwancinsa, Alhaji Garba. Abokin Papa ne shi ma kuma mutum ne kamili ganin tarbiyyar yarinyar ya sa Papa sha'awar aura wa Salis ita. Ko da Papa ya dawo ya tura Salisu ya je ya gana da ƴar abokinsa, bayan ya ke kuka suka fahimci juna aka tsaida rana nan da wata ɗaya mai zuwa.

Papa ya saka aka gyara masa ɓangaren dake kusa da nasa. Komai na ɓangaren na musamman ne don ya fi sauran duka ɓangarorin gidan kyau.

Hatta Maimuna da Amina sun san cewa an fifita soyayyar Salis fiye da na mazajensu. Don haka suka suka biyewa mazajensu.

Anyi bikin Salis da Amaryarsa Aisha lafiya in da ga tare a ɓangaren da aka tanadar mata

A'isha ba ta da matsala mace ce mai tsananin kyau da sura idan ka ganta za ka rantse daga jinsin Larabawa ta fito. Ha tsabta da son kwalliya. Mace ce mai son zaman lafiya ba ta da hayaniya.

Tun da aka yi auren Dada ce ke aika mata da abinci daga ɓangarenta. Har sai da ta cewa Dada ta huta haka nan za ta dinga girkawa da kanta.

Tana girkawa kullun ta aikawa Dada da Papa na su, har ta fara kai wa Maimuna da Amina suka ce ba za su ci ba kada ta sake kawo masu abun ci.

Don ta lura ba da sonta ita da mijin don ko gaishe su ta je yi da ƙurar suke amsawa amma ba ta fasa ba. Har ta yi wa Salis magana ya nuna mata kada ta damu haka suke ya saba da hainsu daga su har mazajensu.

Papa da Dada sun zaunar da su don sasanta su amma ba abinda ya canza.

Har Amina aka samu jikoki biyu in da Maimauna ta haifi Hilal yayin da Amina ta haifi Y Mansur, ko da Aisha ta shiga yin barkar haihuwa ba'a bari ta dauki yaron jariri ba ko sakar mata fuska ba su yi ba don dama ba a gidan ba ne kasancewar haihuwar fari ne sai bayan kwana arba'in ne aka dawo da su ɗalibai

Hakan ya da ta yi zamanta ba ta sake zuwa ba . Don lokacin ma tana da ciki Dada ce kawai ta sani.

Kwanci tashi cikinta ya kai wata tara in da ta hafi ɗa namiji sai dai Dada ta hana ta koma gidan ta ce ai duk ɗaya ne, iyayen suke bar ta wajen Dada. Ranar suna yaro ya ci suna Mahmud.

A haka rayuwa ke tafiya daga sakanni zuwa mintuna daga mintuna zuwa awanni da awanni zuwa kwanaki daga kwanaki zuwa satittika daga satittika zuwa watanni har zuwa shekaru. Yanzu haka Maimuna na da yara uku. Hilal, Faisal, da Maryam. Amina kuma yara biyu take da su Mansur da Nadiya. Yayin da kuma A'isha ke da yara Uku Mahmud, Sadik da Fatima Zahrah.

A can ɓangaren Laila tana da yara biyu mata kasancewar ta dade ba ta samu haihuwa ba, Nadiya da Kausar.


Har lokacin ba jituwa don ƙiyayyar ta shafi jikokinsu nasa shiga sabgar yaran Salisu. Musamman Hilal da yake da wani bakin hali da mishkilanci don ko kakannin ba su ishe shi kallo ba tun yana yaro.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z



*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page1️⃣2️⃣

Har lokacin ba jituwa don ƙiyayyar ta shafi jikokinsu nasu ba su shiga sabgar yaran Salisu. Musamman Hilal da yake da wani baƙin hali da mishkilanci don ko kakanninsu ba su ishe shi kallo ba tun yana yaro.

Ko sauran ƴan uwansa nasa ma baya cika kula su, ko da irin yara suna zaune suma wasa ya baya shiga cikinsu. Duk da kasancewar Faisal ƙaninsa ne uwa ɗaya uba ɗaya amma baya wasa da shi ko Maryam ma fa take mace kuka ƙaramar ƙanwarsa baya shiga sabgarsu. Ko yana zaune a wajen suka je wajen kusa da shi sai dai suyi ta wasansu iya su ƙaɗai. Idan ma ya ji sun dame shi da hayaniya tun da baya son hayaniya zai tashi ya bar masu wajen ne ya koma wani wajan ya killace kansa. Mansur da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login