Showing 42001 words to 45000 words out of 154779 words

Chapter 15 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6295

wa Mallamansu da niyyar idan ta koma za ta same su a makaranta ita da iyayenta.

Tafiya take a hankali ta ji mutane na bin ta a baya za su yi photo. Ba musu ta bawa duk masu bukatar daukar photo da iya dama, wasu kuma ita kadai suke dauka saboda su yi posting a a social media.

Jamilu ne ya karaso wajen da suke ya kira ta don ta zo su wuce. Da

Ɗaga kai ta yi suka haɗa idanu da Nihal ya watsa mata mugun kallo.

Ganin haka ya saka ta bar wajen da sauri don wuce wa. Tana tsaka da tafiya ta ji ana mata sallama.

Juyawa ta yi ta kalli mai sallamar. Wani matashin saurayi ne kyakkyawa yana sanye cikin gezna ruwan sky blue ya guard ɗin sa na biye da shi a baya. Murmushi ya sakar mata tare da cewa.

" Hafiza barka da wannan lokacin, don Allah ko za'a jiƙaina a bani lambar waya?"

Shiru ta yi wanda ganin haka ya saka ya yi murmushi tare da miƙa mata wani kati.

Karɓa ta yi ta yi gaba. Tana tafiya cikin sanyin jikinta, wanda har lokacin ba ta daina jin idanun mutane na yawo a jinkinta ba.

Suna ƙarasowa wajen parking motocin sai wani mutum yana sanye cikin Suit ya karaso, tare da miƙawa Hilal da Jamilu hannu suka gaisa.

Kallonsu ya yi tare da cewa

"Na so na ji matakin Shari'a don Allah idan ba damuwa ina son na sani wannan sister naku an yi mata miji ne?"

Da sauri Jamilu ya ce .

"Ƙwarai kuwa nan ba da jimawa ba za'ayi mata aure sai ka yi hakuri."

Cikin sanyin jiki ya masu godiya ya tafi. Ita dai Zahra mamakin Jamilu ne ya kama ta. Gefen motarsa wajen me zama banza ya bude mata.

Shiga ta yi ta zauna wajen me zaman banza. Hilal ya zauna bayan motar kasancewar ya tura direbasa ya dauko massa ALEXANDRA a airport.

"Mallam ina motarka da Direbanka, bai tanka masa ba ya dinga danne-danne a waya.

Har suka karasa gidan bai yi magana ba, Sai Jamilu dake ta jan Zahra da fira yana yabawa baiwar ilimin da Allah ya yi mata.ita dai fage uhm sai umm."

A parking space suka yi parking ta fito shima ya fito yayin da Hilal ya fito daga karshe.

Key ya saka ya buɗe gidan suka shiga. Kai tsaye ta nufi ɗakin da aka sauke ta.

Jamilu ya kalli Hilal ya ce.

"Abokina gaskiya ina son wannn sister ta ka fatan za ku bani aurenta, hakan ya saka na cewa wancan gayen ta kusa yin aure ya haƙura."



Ita ko wayarta ta ɗauka tana kiran Abbi da Umminta, ba su shiga ba don ta lura tun tuni ya dace su dawo amma ba su dawo ba, amma ta ji Yaa Sadik ya ce mata jikin Papa ne ya tsayar da su, amma nan da kwanaki uku za su dawo. Don Papa na asibiti likita na kula da lafiyarsa.

Fitowa ta yi da niyyar ta duba ko akwai aikin da za ta taya matar gidan, fitowarta ya yi daidai da shigowar direban Hilal da wata baturiya a bayansa. Tana ganin Hilal ta ruga wajensa wanda ganinta ya sa ya miƙe tsaye ta rungume shi a jikinta tare da sumbatarsa a kumatu. Mumrmushi ya yi mata yayin da Jamilu ya tsuke fuska yana masu wani banzan kallo musamman ALEXANDRA.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z




*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page2️⃣1️⃣

Fitowa ta yi da niyyar ta duba ko akwai aikin da za ta taya matar gidan, fitowarta ya yi daidai da shigowar direban Hilal da wata baturiya a bayansa wanda ganinta ya sa ya miƙe tsaye ta rungume shi a goshinta tare de sumbatarsa a kumatu. Murmushi ya yi mata yayin da Jamilu ya tsuke fuska ya masu wani banzan kallo musamman ALEXANDRA.


Kau da kai Zahra ta yi ya nufi kitchen ɗin, tsawon mintuna biyu suka ɗauka kafin ya zame ta daga jikinsa ya fara magana cikin yaren ƙasar Spain.

"Dama da gaske za ki zo duk in da nake?"

"Ina mai tabbatar maka ko a karkashin ƙasa kake zan bila?"

"Anya za ki iya zaman Nigeria kuwa?"

"Me zai hana idan ina tare da kai."

"Amma da kin jira dai na dawo."

"Gaskiya ba zan iya jira ba domin sanin kanka ne cewa ba zan iya hakuri rashinka har na sati ɗaya ba, ga shi kamar ba za ka dawo ba, don haka tare za mu koma ƙafata ƙafarka."

Sai a lokacin da ta kalli Jamilu don ta san shi tare da Hilal tare da shi suka yi karatu a can ƙasar.

Gaishe shi ta yi ya amsa mata ba wani sakin fuska, duk da cewar ta dade da gane cewa baya son tarayyarta da abokinsa amma ba ta damu ba, saboda shi Hilal yana sonta. Amma duk da ta ji wani irin yadda ya amsa mata sai ta ji wani iri, lakatar hancinta da Hilal ya yi ne ya sa ta lalle shi tan murmushi.

Cikin yaren Hausa Jamilu ya fara magana yadda ya san cewa ba za ta ji shi ba.

"Dalla Mallam ka ɗauke mani wannan abar a cikin gidana, duk da ba yau za ku koka Katsina ba sai gobe tabbas wannan ba za ta kwana a gidana ba, sai dai daga kai har ita ku je ku jama hotel ku kwana, washegari ka zo ka dauki Zahra ku tafi, ko ma da kaina zan iya mayar da ita gidan.

Wani kallon baka isa Hilal ya yi masa ba, sannan ya ɗaura da cewa.

"Tabbas nan gidanka ne amma ba ka isa ka kore mu ba, har sai gobe idan mun tashi tafiya. Da lokacin da na yi niyyar kama hotel me ya saka ka dame ni akan na sauka a gidanka, duk da ba da shawarar son raina na sauka ba saboda yanzu kana da mata, ni kuka nake ganin kamar zan takura har. Kana fushi da ikirarin ba za ka sauka a gidanmu idan ka sake zuwa garin ba. Dole ba da son raina na zo ba. Sannan yanzu ka kawo Mani wani zancen ba ka isa ba."

Yana fadar haka ya ja hannun Alexandra suka nufi bedroom ɗin da y sauka. Muryar Jamilu ya ji yana ce masa.

"Nan gidan Sunnah ne wallahi ko da wasa kuke aikata Mani ɓarna a cikin gidana sai na baku mamaki, tun da ta kasa hakuri ka koma can ku cigaba da iskancin da kuka saba."

Kamar Hilal bai ji shi ba ya share shi suka shiga cikin bedroom ɗin.

"Zahra tana kitchen tana mata goge goge, ta ji maganar Jamilu tana mamaki dama haka halin ya Hilal yake, take ta ji babu dad'i a ranta.



_Asadullah Mantson_

Uncle Adam ya cigaba da yi wa Sulaiman faɗa akan me za' ce ba'a san in da Asadullahi yake ba. Bayan shi ne na hannun damansa. Ya kamata ace duk in da yake yana tare da shi. Ko da cikin falonsa ne.

Jin faɗar ya ƙi karewa ne ya saka Dad yi masa magana akan ya bar shi don yana iyakar ƙoƙarinsa.

Uncle Adam bai saurari Dad ba ya kira duka guard ɗin dake kasance tare da Asadullahi ya masu tambaya, sai dai kowa amsa iri ɗaya suke bashi.

Dole ya ƙyale su don ba abinda zai ce masu kuma.


_Jidderh_

Tun daga ranar kullun sai ta faki idanun mutane ta nufi ɓangaren da Asadullahi yake, ta je ta bashi abinci ya ci ta bashi ruwa. Sannan take samun nutsuwata a rayuwarta. Kuma kullum sai ta yi masa kuka, musamman ganin yadda ya rame duk da shi ba mai yawan cin abinci ba ne amma ta lura duk ta saci jiki ta kai masa abin da zai ci. Duk da shi ba mutum ba ne mai yawan cin abinci ba ne, amma ta lura kullum idan ta je kai masa abinci sai ya dinga rawar jiki wajen cin abincin. Da alama yunwa yake ji. Hawaye take yi idan tana kallonsa.


Su kansu waɗan da suka tsare shi a wajen dau ɗaya sauke bashi abinci.

Su kansu sun fara mamakin ganin kwana biyu baya galabaita da yunwa. Don haka suka fara tunanin saka ido a bangaren da kuma mutanen cikin gidan, don sun san tabbas akwai wani abu a ƙasa.

Don haka yadda suke barin ɗakin da suka barin ɗakin Asadullah ba tare da sun saka key ba, saboda sun san cewa sun ɗaure shi da sarƙa, ba iya tashi zai yi ba, kuma bugu da ƙari ba wanda yake zuwa ɓangaren da aka aje shi. Don haka ya faɗa tunanin su rufe.


Kamar kullum yau ma ko da ya shiga part ɗin bayan Doctor ya tafi ne, ta shigo ɗakin.

Sanye take cikin wata doguwar riga baka, ta sanya p cap 🧢 a kanta, sannan ta saka facemask da ban n gallass. Ba wanda ya zai iya gane ko wace ce saboda ta yi shigar ɓadda kama.

Tura ƙofar ta yi ta ji ta a buɗe. Jidderh wacce ta gana ba shi meet pie ta tashi da sauri jin motsi ta nufi toilet. Tana. Shiga ana gama shigowa ɗakin jin kamar motsi ya saka ta waige-waige ganin ba kowa ya saka ta nufi toilet ɗin ta tura ƙofar da sauri ta shiga ciki.


_Zaharah_

Ganin har yamma ta fara gabatowa Sumayya ba ta dawo ba ne ya saka Zahra ta shiga kitchen bayan ta idar da sallar la'asar ta shiga kitchen

Fried rice ta girka masu ta wanda ya ji kayan haɗi da hanta. A dinning table ta jera komai. Daidai lokacin da Jam'i da ya fita ya dawo, don haka nuna jin dadinsa ya yi mata godiya.

Tuna cewa Alexandra na gidan ya saka Jamilu canza fuska, kallion Zahra ya yi tare da cewa.

"Ƙanwata ki kai wa Yayanki da baƙuwarsa na su a daki, saboda ba na son ta fito, ɗin a zahirin gaskiya ba na ƙaunar ganinta."

Ya ƙarasa faɗa yana yin tsuki

Ba musu Zahra ta samu madaidaicin flask ta ta zuba masu na su, ta haɗa da soyayyar naman kaza. Sai Lemun kwakwa da ta haɗa duka ta jera su a tire. Ta saka plate da cokula.

Kai tsaye ta nufi ɗakin da ta san ya sauka. Sallama ta yi ba'a amsa ba, har sau uku shiru. Hakan ya saka ta shiga kai tsaye tun da ta san ba ɗakin ma'aurata ba ne, kai tsaye ta shiga ciki.

Kanta a ƙasa ta ajiye tire a saman table dake ɗakin. Ɗagowa ta yi ta sauke idanunta akan su.

Zaune yake akan doguwar kujerar mai zaman mutum uku, yana sanye da wando dogo babu riga a jikinsa. Alexandra tana zaune a saman cinyarsa babu kaya a jinkinta daga ita sai pant ko bra babu a jikinta. Suna tsotson bakin junansu.

Zaro idanu Zahra ta yi tare da furta kalmar.

"A'uzu billahi minash shaiɗani raƙumi."

Da sauri ta fito cikin yanayin firgici. Jamilu dake falon ya kalle ta . tafe da cewa.

"Zahra lafiya?,"

Ba ta iya cewa koma ɗakin ta sauka

Da hanzari ya nufi ɗakin ganin abin da koro Zahrah, shi ma ganinsu ya yi kamar yadda Zahrah ta gansu .


Take ya tsuke fuska ya fito ransa a ɓace, zama ya yi a Wajan cike da takaicin Hilal.

Bayan m
Kamar muintuna ashirin sai ga kiran sallar magrib. Jamilu ya mike kenan sai ga Hilal ya fito sanye da farar jallabiyarsa da alama alwala ya zai je masallaci.

Kallo ɗaya ya shi ma Hilal ya masa ya ɗauke kai .

Masallaci ya nufa yayin da shi ma Jamilu ya ɗaura alwala ya nufiadallaci don gabatar da sallar magrib.




_Zahrah_

Tun da ta shiga ɗaki ba
abinda take dai sai aikin kuka, kuka ba take yi sosai don hankalinta ya tashi da abun da ta gani, mace kusan tsirara tana zaune a saman cinyar Yaa Hilal tana tsotson bakinsa. Dama haka halin Yaa Hilal yake ba ta sani ba.

"Yaa Hilal me ya saka ka zaɓe wannan ƙazamar rayuwar ne? Dama da gaske ne da nake ji cewa wai sojoji suna da neman matan banza da shan giya? Shin kai ma kana shan giyar ne?"


Haka ta dinga riskar kuka kamar ranta zai fita.

Jin har an tayar da Sallah ya saka ta tashi da sauri ya nufi bathroom. Wanka ta yi sauri-sauri ta ɗauro alwala, rigar barci ta saka riga da dogon wando farare. Ta sanya Hijabi har ƙasa ta fara gabatar da sallar magrib.

Tana nan zaune ha tana addu'o'i har aka kira sallar isha'i. Sai da ta yi sallar sannan ta hau kan gadon bayan ta naɗe sallayar da hijabi ta ajiye.

Kwanciyar ta ke da wuya sai ga Sumayya ta turo ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Amsa mata Zahra ta yi tare da yi mata sannu da zuwa. Amsawa ta yi cike da jin dad'i tare da yi mata godiyar girki. Murmushi ta yi tare da cewa.

"Ba komai kada ki damu."

""Na sha Allah Allah, ina ganin girki har yawu na tsinke wa Sai da oga ya ce kafin na ci sai na kira ki kema kin ci."

Gaskiya na ƙoshi yanzu."

"Me kika ci?"

"Ba komai ba na jin cin komai ne."
.
"Akan me gaskiya ban yarda ba tashi mu tafi "

Duk yadda ta so ƙin fita Sumayya dai da ta takura mata suka fito.

Jamilu na zane a dinning table yana jiransu, daidai lokacin da Hilal ya dawo daga masallaci. Sallama ya yi wanda idan ba wanda ya kalli bakinsa ba zai san ya yi wata sallama ba. Kasancewar sun kalli kofar ya sa suka amsa.

Sumayya ce ta gaishe shi cike da kulawa, ya masa mata a takaice ya nufi bedroom ɗin da yake ciki. Jamilu da Zahra ba wanda ya ce masa uffan.

"Ka kira abokinka mana ya zo ya ci abinci. Ko ƙanwarsa ta kira shi ne?"

"Kada ki damu an kai masa nasa a ɗaki kasancewar yana tare da baƙuwarsa."

"Baƙuwa ya yi ?"

"Eh"

Ya bata amsa a takaice.

"Okay ai da ta fito mun yi dinner tare."

Tsuke fuska ya yi tare da cewa.

"Ki bar su kawai."

Ita ta yi sevin nasu suka fara cin abinci, Zahrah dai abin da ta gani ya tsaya mata a rai. Duk da yau ranar farin ciki ne amma abin da ta gani ya shafi farin ciki da walwalar da take ciki.

Har Allah take gari ya waye su kama hanayar komawa gida.

Nan suka dinga cin abinci suna jan ta da fira suna ta yaya ta murna na samun nasara tare da mata fatan alkhairi.


Bayan sun kammala ne ta yi masu sallama ta shiga cikin, duk da sun so a ce ta tsaya sun yi fira da ita.

Kwanciya ta yi ta bayan ta ɗauro alwala ta yi addu'ar kwanciya barci.

Ƙarfe biyu na dare ta farka ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallar nafilfili.

Sai asuba ta idar tare da yin addu'o'i. Har aka yi assalatu ta yi sallar asuba. Azkar ta yi sai da garin ya fara haske ta fito zuwa kitchen.



_Hilal_

Akan hanyarsa ta dawowa daga masallaci suka jero tare da Jamilu. Bayan Jamilu ya bashi hannu sun yi musabaha ya kalle shi ya ce.

"Hilal"

Bai kalle shi ba amma ya san ya ji shi. Don haka ya cigaba da cewa

"Nan fa Nigeria ne ba U.S ko London ba, irin rayuwar da kake yi a can kada ka ce za ka yi shi a nan. Domin Addininmu da Al'adar mu ya sha banban da ta su. A can don ka rungume mace ka sunmbace ta ko yi abinda ya fi haka ba wanda zai kalle ka. Amma anan ba haka ba ne. Yanzu har ya kai ka kira ɗaya daga cikin matan da kake harka da su don su zo su same ka a ƙasar ka?" Yau za ku tafi ina za ka kai ta?"

"Gidanmu."

Da mamaki ya kalle shi don ya san in dai ya fadi abu sai ya aikata. Don haka ya ce.

"Allah ya kyauta. Amma da zan baka shawsra ka ɗauka ko da sai na ce . Ka auri yarinyar nan Fatima Zahrah."

Wani banzan kallo ya yi masa tare da ɗauke kansa.

"Na yi maka kwaɗayin samun nagartacciyar matar aure ne ya da na baka wanann shawara. Don idan ka aure ta to tabbas ka nema wa yaranka uwa ta gari abun alfahari ga...."

Ɗaga masa hannu ya yi alamar baya son maganar, don haka ya yi mumrmushi tare da cewa.

"To ni zan yi ta biyu da ita in sha Allah ba zan bari ta kufce mani ba."


_Zahrah_

Tana shiga kitchen ɗin sai hayaƙi da ƙauri ya turnuke ta. Sakamakon manja da Sumayya ta bari a wuta ya ƙone ta fita zuwa ɗakinta don ɗauko green pepper da ta dawo da shi jiya daddare sai ta ajiye a bedroom ba ta kawo shi kitchen ba.

Zahra na shiga ta shaƙi hayaƙin, da sauri ta kai hannu ta kashe gas ɗin cikin ƙarfin hali.

Tana fita ƙofar kitchen ɗin numfashinta ya fara ɗauke wa. Kafin ka ce ne har ta zube a wajen. Ƙoƙarin tashi take yi don ta je ɗaki amma ta kasa.

Cikin wannan halin Sumayya ta rugo da gudu sakamakon tuna Abinda ta bari a wuta. Ganin halin da Zahra ke ciki ya saka ta yi ihu daidai lokacin da Hilal da Jamilu suka iso .

Wajen suka nufa in da suka yi kanta, cikin tashin hankali Jamilu ya ce.

"Meke faruwa?"

Cikin kuka Sumayya ta ce ba ta sani ba.

Halal dake tsaye hannunsa a cikin aljihun wandonsa ya ce

"Ina ga wanann hayaƙin ya saka ciwonta ya tashi."

"Wane ciwo?"

Jamilu ya tamabaya ciki n damuwa.

"Athma"

Ya faɗa yana kallonta. Juyawa ya yi ya nufi ya nufi bedroom ɗin da ta sauka. Handbag ɗin ta ya buɗe, ya duba Inhelar ya ciro daga cikin jakkar ya fito.

Fitowa ya yi ya nufi in da take durƙusawa ya yi a gabanta ya shaƙa mata Inhelar ɗin. Zuba mata idanu suka yi suna kallonta. Numfashinta ya fara daidaita.

"Ki yi hakuri don Allah ban sani ba "

Sumayya ta faɗa cikin rauni. Sannan Jamilu ya kalle ta da cewa.

"Gaskiya duk wanda zai suna da ke sai ya kiyeye abinda zai iya jefa rayuwrki cikin hatsari, shawarar da zan bashi kenan ko?"

Ya faɗa yana kallon Hilal.

"Ko ba haka ba abokina?"

Taɓe baki Hilal ya yi tare da cewa.

"Ko kuka ka bashi shawarar ya nemi gida kusa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login