Showing 150001 words to 153000 words out of 154779 words
hankali yake bin ta, bai riga ya shige ta duka lokaci guda ba, wani kukan ta saki lokacin da ya shige ta duka.
Kuka take yi tana kiran sunan Yaa Mansur ya zo ya taimake ta.
Sai da ya dauka mintuna hamsin a kanta sannan y saurara mata, zuwa lokacin muryarta har ta dakushe saboda kuka.
Daukarta ya yi ya kai ta bathroom ya haɗa zuwan zafi, zai taimaka mata ta ce zata iya ya fita kawai.
Ba musu ya yi mata sannu ya fita. Shifdar gadon ya canza ya jira fitowarta, yadda take tafiya ya kalla yana yi mata sannu.
Ba ta kalle shi ba, ta zauna bakin gadon tana daure da towel.
Shiga ya yi shi ma don yin wanka, yana shiga ta shige bargon ta kwanta. Lumshe idanu ta yi kamar mai barci. Ko da ya fito ya saka kaya ya ɗauka barcin take yi. Don haka ya ja masu bargo ya rufe su.
Sam bai taba tunanin wannan daren za ta zo ba tsakanin sa da Nadeeya, shi kansa ya rasa dalilin da ya saka ya kasa rike kansa a daren nan.
Barci ya ɗauke su kusan a tare kowa da abinda ke zuciyarsa.
_Faisal_
Tun da suka bar Tafarki Family bayan ya dauko matarsa Kausar, ba wanda ya yi wa wani magana tsakanin shi da ita.
Har suka karasa gidan ba wanda ya yi wa wani magana, kowa ransa a ɓaci yake.
Suna shiga ta nufi wani bedroom ta ga ba na ta bane, sai ta duba dayan ta ga nata ne sai ta shiga tare da banko kofar da karfi wanda sai da Faisal ya kalli kofar.
"Mahaukaciya."
Ya fada yana nufar bedroom ɗin sa ransa a ɓace, don ya san zamansa da kausar akwai matsala, ya san yaran Aunty Laila ba tarbiyya ne da su ba.
A haka kowanne cikinsu ya kwanta dakinsa cike da bakin ciki.
_Mahmud_
Bayan Papa ya bashi umarnin ya rike hannunsa Nabeela su tafi, suna fita ta fisge hannunta tare da cewa.
"Wallahi ka sake taɓa Ni sai na yi maka rashin mutunci ."
Bai ce mata komai ba, ya shiga mota yana zaman jiranta, tsabar wulakanci sai da ta shafe mintuna goma kafin ta shiga ya ja motar suka bar gidan.
Suna hanya sai faman masifa take yi tana zage-zage, bai tanka mata ba, har suka isa gidan ya yi parking. Da
Fitowa ya ya yi ita ma ta fito ta bi bayansa.
Suka shiga tai masa wani banzan kallo sannan ta kalli ko ina ta ce.
"Ina ɗakina?"
Da hannu ya nuna mata yana cewa .
"Ga shi can."
"Yunwa nake ji kuma kaza zan ci, na ga a farkon layin nan ba nisa akwai mai gasashshen kaza ja je ka siyo Mani."
Banza ya yi mata ya nufi kofar dakinsa.
Da sauri ta tari gabansa tare da cewa.
"Mahmud magana nake yi maka, don ba zan iya laƙaba maka kalmar Yaya ba. Wallahi wa billahillazi idan ba ka siyo Mani kaza ba ai ba za ka taba rintsawa a cikin gidan nan ba. Idan kuka kana ganin ƙarya ne bisimillah."
Baya son tashin hankali ne ya saka ya fita ya siyo mata kazar, har ya dawo tana falon sai dai ta zauna .
Yana miƙa mata ta fisga ta wuce dakinta rana murguda masa baki.
Wanka ya yi ya yi alwala ya kwanta.
Sai da ya raba dare yana Sallah kafin karfe uku ya yi shirin kwanciya barci. Da karfi aka buga kofar kamar za'a ɓalle ta.
"Waye?"
Ya fada yana nufar kofar?"
"Uwar da ka ajiye ce."
Tsaye ya ganta ta rike kugu tana jijjiga.
Barcin da bai samu ya runtsa ba kenan, don yana idar da sallar daren kenan zai kwanta ta buga masa ƙofar.
Masifa da bala'i ta fara yi masa idan ya shiga dakin ta dinga buga kofar yadda ba zai iya barci ba.
Har kafe biyar ne asuba ba ta bar shi y runtsa ba, alwala ya yi ya nufi masallaci don yin sallar asuba.
Sai karfe bakwai ya dawo gidan, yana dawowa ya ya shiga kitchen don zai tafi aiki.
Ruwan tea ya dafa ya zuba a flak ƙwai ya soya ya ɗauko kayan ya ajiye a falo saman Centre Carpet.
Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin bakin Suit, ya sa Black cover shoe sai kamshi yake yi .
Fitowa ya yi don yin breakfast. Nan ya tarar da Nabeela tana kallon kayan da ya jera na breakfast.
_Mansur_
Ko da ya tashi da asuba ya tayar da ita suka yi sallah, ta koma barci akan gado , shi kuma bayan ya dawo masallaci ya shiga ya shirya mata breakfast, ya kai har bedroom ya ajiye mata a kan tebur.
Baya son tashin ta daga barci don haka ya ajiye mata takarda da lambar wayarsa ya ce ta kira shi idan ta tashi.
Barin gidan ya yi yana tunanin halin da ɗan uwansa yake ciki, don ya san Aunty Laila ba za ta bar Nabeela ta bari Mahmud ya kwana lafiya ba. So yayje yi ya je ya ga ya ɗan uwansa yake ciki.
Mahmud na zaune a kan Centre Carpet dake tsakiyar falon, tea ya haɗa a cup yana sauraren zai je aiki, ga soyayyen ƙwai da ya zuba a plate sai ya debi yankakken bread biyu.
"Au ni ma yunwar nake ji ki ka kawo Mani abinda zan ci ne?"
Bai ce komai ba ya ɗauki wani cup ya haɗa mata shayi, ya zuba Milo ya tura mata plantain da ƙwai ɗin da ya soya.
Ɗaukar kofin tea ɗin ta yi ta masa wani kallo sannan ta ɗauki kofin shatin ta wasa masa a jiki.
Kallonta ya yi da idanunsa da suka rikeɗe zuwa ja ba.
Daidai lokacin aka yi knocking, kafin su yi wata magana Sadik ya tura kofar ya shigo. Kallon Yayan nasa ya yi ya ga yadda ruwan shayin ke ɗiga tun daga fuskarsa har zuwa jikinsa.
Ransa ya ɓaci zuciyarsa har tafarfasa take yi ya karaso wajen, Ganin yanayin Sadik ya firgita Nabeela, don ta san shi baya daukar raini. Cikin ɗakiya ta ce
"Kai kuma uban wa ya ce ka shigo wa mutane ba izini da safiyar nan?"
"Ubanki ne?"
"Wallahi ba dai ni ba."
Ganin yadda gefen fuskar Yayansa ya yi ja lokacin da ya goge fuskarsa alamar tea ɗin da zafi.
Sadik ya ɗaga hannu a fusace zai kai wa Nabeela mari, Mahmud ya yi saurin mikewa tare da rike masa hannu.
"Yaya kana kallo wannan yarinyar na yi maka wannan cin kashin za ka ƙyale ta?"
"Ai da ka bar shi ya mare ni, wallahi sai ya yi nadama."
"Haka aka koya maki rashin tarbiyya?"
"Kana mamaki ne?"
Murmushin takaici Sadik ya yi kafin ya ce
"Ban yi mamaki ba, domin idan ba ki aikata haka ba, ai ba ki amsa sunan Laila ta haife ki ba?"
"Sunan mahaifiyar tawa kake kira gatsai?"
"Ko za ki ki rama ne?"
Ya yi maganar yana ƙoƙarin kwace rikon da Yaa Mahmud ya yi masa.
Wayarsa ce ta yi ruri, ya kalli Mahmud ya ce .
"Sake ni na amsa waya."
Jin haka ya saka Mahmud ya sake shi.
Ciro wayar ya yi ya duba mai kira, True caller ta nuna masa sunan Nadeeya Adam Tafarki. Hakan ya sa ya gane ita ce don bai da number ta.
Haka kawia sai ya tsinci kansa da jin farin ciki da nishaɗi.
Yana daukan wayar ta saka masa kukan shagwaɓa.
"Haba Baby kukan ya isa haka mana kada kanki ya yi ciwo, kuka tun jiya har yau, ki yi hakuri na tuba ba zab sake wahalar dake ba kin ji baby?"
Nabeela ta kalle shi tana mamakin da wa yake magana, ta dai san tare aka yi masu huduba da Nadeeya to me ta aikata haka, ganin yadda Sadik ya koma wani iri ya tashi hankali jin kukanta ya sa ta gane mai afkuwa ta afku."
"Kin ga ki kwantar hankalin ki daina kuka, yanzu ki daure ki sake shiga ruwan zafi, magani na nan na ajiye maki da tare da breakfast, ba zan dade ba zan dawo."
Mumrmushi ya yi ya kashe kiran wayar. Nabeela mamaki da takaici ya cika ta.
Muryar Mahmud ya ji yana cewa
" Bari na sake shirya wa sai mu fita tare."
Mahmud na nufar bedroom ɗin sa Sadik ya mike rai a ɓace ganin ya tunkaro Nabeela ya sa ta ruga a guje ta shiga bedroom ta rufo kofar. Don ta san yanzu ba Mahmud da zai dakatar da shi kuma ta lura da ɓacin ran dake fuskarsa.
Fita ya yi harabar gidan ya shiga motarsa yana zaman jiran Yayan nasa ya fito.
_Aunty Laila_
Cike da tashin hankali ta nufi ɓangaren Mummy, don tana da tabbacin Umma na can yanzu .
Ganin yanda ta shigo ne ya saka Umma ta mike da sauri. Mummy dake kwance ba lafiya da ido ta bi ta.
"Laila laflya me yake faruwa?"
Umma ta yi tambayar cike da damuwa.
"Komai ma ya faru, yanzu ƴarki Nabeela sai da ta bamu matsala ta wargaza mana shiri duk jan kunnen Da aka yi mata?"
"Me ta yi?"
"Ta bawa wannan mara mutunci kanta mana."
"No hakan ba zai faru ba, yaushe suka samu fahimta da wani abu zai shiga tsakaninsu?"
"Nabeela ta kira ni wai Sadik ya je wajen Mahmud ta kara shi a waya, sai lallaɓa ta yake yi yana ce mata ta shiga ruwan zafi ya ajiye mata magani."
"Idan kuwa haka ne tabbas Nadeeya ta cuce mu ta wargaza komai, kai ba zai yiwa ba."
"Tun da kina kokwanto zan je gidan yau ɗin nan, sai na saka ta ta kwanra na duba ta kafin mu yanke mata hukunci, duk da na ga baki yarda ba."
Ƙarar mota suka ji ta shigo gidan, ta window Umma ta leka, ganin Mahmud da Sadik ta ce.
"Ga su nan sun zo gaida uwarsu."
Kallo ɗaya suka yi wa Mahmud suka gane yana cikin tashin hankali. Sunyi Laila ta saki uwar dariya tana sawa Nabeela albarka.
Sadik ne ba za ka iya karantar yanayinsa ba tashin hankali ko akasin haka, don cikin farin ciki yake ganin halin da ɗan uwansa yake ciki ya gurguntar da farin cikin da ya tsinci kansa a ciki.
"Zan je na duba Nadeeya don ga tashin hankali a tattare da wanna mai taurin kai da zuciyar ba."
Part ɗin Dada suka je suka gaishe da Papa da Dada, in da suke kara masu nasiha da sanya albarka sannan suka nufi part ɗin Umminsu.
Hankalin ta ya tashi ganin Mahmud a firgice, ya sa Ummi ƙwalla ya cika idanunta, sai ta dauke da sauri. Don ta san halin Mahmud da Sadik ne ba za ta damu ba. Albarka ta sanya masu suka shiga sauka gaida Abbi suka tafi.
_Zahrah_
Tun bayan da Hilal ya ja mata bargo ya ya tafi yake kuka. Duk da ba ta san dalilin da ya saka ya bar ta yana mata kallon mamaki ba, ta lura jikinsa ya yi sanyi ya yi mata kallon da bai taɓa yi mata ba a rayuwarsa.
Lallaɓawa ta yi tana bin bango ta rufe kofar ta da sakata. Tana kukan abubuwa da ya yi mata. Goge bakinta ta yi tuna yadda ya dinga tsotsan bakin ta kamar ya samu sweet.
Bathroom ta shiga da jin bango ta dauki brush da toothpaste ta dinga wanke bakib tana tofar da miyau cike da ƙyankyami.
*Saura page ɗaya na kammala book 1 wacce ta shirya siyen Book 2 zata tura kuɗinta ta wannan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 09065327995*
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page7️⃣0️⃣
*LAST FREE PAGE*
Bathroom ta shiga da bin bango, ta ɗauki ta ɗauki brush da toothpaste ta dinga wanke ta dinga wanke baki tana tofar da miyau cike da ƙyanƙyami.
Sau uku tana saka toothpaste tana wanke baki kamar za ta canza haƙoranta da harshe take ji.
Wanka ta yi da ruwa mai ɗumi sannan ta fito ɗaure da towel, wankan da ta yi sai ta ji jikinta ya ɗan yi mata ƙarfi. Sai dai har lokacin yunwa na ɗawainiya da ita jin ta take yi tamkar fanko.
Riga da wando na barci ta saka farare, wandon da kadan ya wuce guiwarta, ji ta yi ba za ta iya yin barci ba yadda yake jin yunwa don duk yai sau daya ta ɗan sha ruwan tea kaɗan, ga yanzu dare ya yi bata san ya za ta yi ba.
Hawaye ne ke bin fuskarta ta Kudundune ta cire wuri ɗaya hannayenta a cikinta wanda take ji har ciwo yake yi mata.
_Hilal_
Sai faman Safa da marwa yake yi a cikin ɗakinsa. Ransa a ɓaci idanunsa sun sauya launi zuwa ja kamar zai su fitar wuta.
Yana tuna yadda mahaifiyar sa da ƙanwar mahaifinsa ke ta aibata Zahrah da zancen lalata da cikin da aka ce tana zubarwa. Ƙarin abunda ya saka ya yarda da cewa maganarsu gaskiya ce ranar da ya ganta kwance cikin jini ya kai ta asibiti likita ya sanar masa da zubar da ciki ta yi. Ga shi kuma Family Doctor na su ne wanda suka yarda suka saba da shi tsawon lokaci. Sannan ga shi ya tabbatar da cewa yarinyar cikakkiyar budurwa ce. Shin me ya saka suka yi mata haka sun saka ya tuna Abba, Ummi, Mahmud, Sadik, Zahrah. Yadda ake nuna masu wariya a cikin gidan, kullum sai nufar su da sharri ake yi wanda su kuma har yau bai ga wani aibu ko mugun balin da aka ƙakaba masu ba. Cikin ƙaraji ya ce.
"Meye dalilin da za ku yi wa ƴar mutane shaidar zina? Mummy, Aunty Laila da Doctor dole za ku amsa mani tambayoyin da zan yi maku, tabbas ba na jin zan iya saurara wa kowa. Musamman yadda na cutar da ƴar mutane ba tare da hakkinta ba."
Ya tuna ranar da ya kai ta asibiti aka ce ciki ta zubar ya tuna maruka da dukan da ya yi mata akan laifin da ba ta aikata ba. Da sauran abubuwan da ya yi mata cikin takaicin halin ta yana mata kallon kura lulluɓe da fatar akuya."
Ƙofar fita ya nufa don ya ga halin da take ciki
Zuwan lokacin karfe biyun dare ya yi. Tana nan tana tausayin sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta sai ta ji ƙamshin turarensa.
Cikin faduwar gaba da firgici ta kalli ƙofar sakamakon jin ƙamshin turarensa.
Tsaye yake jikin bango yana sanye da wando 3-quater da farin singileti ƙirarsa na ƙaƙƙarfan namiji ne bayyane a jikinsa saboda yawan motsa jikin da yake yi. Hannunsa ɗaya a cikin aljihunsa ɗayan kuma yana rike da handle ɗin kofar. Ya zuba mata rikitattun idanunsa.
Gabanta ne ya faɗi ta kara matsawa can ƙarshen ta ƙara Kudundune jikinta, gani take yi kamar zai yi mata wani abun.
A hankali ya ƙaraso bakin gadon, fuskarsa babu walwala.
"Are you okay?"
Banza ta yi masa kamar ba ta ji shi ba, kallo mata ya yi na mintuna biyu kafin ta ɗauke idanunsa ya ce.
"Meke damunki."
"Ni wajen Ummina za ka mayar da ni, ba na son auren."
"Auren ne ba ki so ko kuma ni ne ba ki so?"
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.
"Talk to me, ni ne ba ki so auren ne baki so?"
"Ba na son ka."
Shiru ya yi tare da cije lips ɗin sa na ƙasa. Kafin ya yi wata magana ne ya ji tana cewa.
"Don Allah ka sake ni ba zan iya zama da kai ba."
Bai yi mamaki don ta ce ba ta son sa ba, saboda shi ya gina mata tsanarsa a cikin zuciyarta, sai dai bai taba tunananin za ta bijire wa auren ba.
"To yanzu wa kike so."
Ba tare de jin shakkar sa ba ta ce "Yaa Ammar."
Sai da rintse ido ya buɗe sannan ya ce.
"Okay ki daina kuka."
"Don Allah ka taimaka ka sake ni, wallahi yanzu ni kadai na san me nake ji a cikin zuciyata, matukar na ci gaba da zama da kai tabbas sai an ɗauki gawata a cikin gidan nan."
"Me za ki ce wa su Papa dangane da mutuwar auren idan kika koma gidan.?"
"Zan fada masu ni ce na nemi ka sauwake Mani."
Yana tunani ta ina zai fara sai ya ji tana cewa.
"Ka yi Mani alkawarin za ka sake ni."
Kai kawai ya jinjina ya fita daga ɗakin. Ba jimawa sai ga shi ya dawo da cup ɗin tea da biscuit a hannunsa.
Mika mata tea ɗin ya yi Wanda ya haɗa mata shi da kauri.
Kauda kanta ta yi don ko kallonsa ba ta son yi, tsuke fuska ya yi cikin dakiya ya ce.
"Za ki karba ko sai na baki da kaina?"
Kallonsa ta yi ta ga ya koma mata asalin Hilal ɗin da ta sani. Kamar ba yanzu shi ne yake yi mata magana cikin taushi ba.
Ganin kallon da ya yi mata ne ya saka ta ɗauke idanunta da sauri ta karɓa tana maganar zuci."
'Mai hali ba zai taɓa canzawa ba, duk macen da ta zauna da shi za ta sha wahala, a haka Aunty Bilkisu ke cewa sai yadda na yi da shi?'
A hankali take tauna biscuit ɗin tana shan ruwan tea ɗin. Kallonta yake yi har lokacin fuskarsa a tsuke, ta ci rabin biscuit ɗin ta shanye ruwan shayin ta ce masa ta ƙoshi.
Karba ya yi ya fita daga cikin ɗakin da cup ɗin a hannunsa.
Sai a lokacin ta ji yunwar da take ji ta ragu da kashi hamsin ta fara jin daidai. Hamdala ta yi tana mamakin yadda ya hado mata tea ya kawo duk jin kai da isar sa.
Dawowa ya yi ya kalle ta ya ce.
"Akwai abinda kike bukata ne kuma yanzu?"
"Takardar sakin da na roke ka nake so zuwa safiya sai na tafi."
Shiru ya yi yana kallon ta kafin ya ce.
"Zan baki tun da haka kike bukata ki bani nan fa zuwa jibi idan na kammala abinda na saka a gaba."
"Ton na gode."
Bai ce komai ba ya ja mata kofar bayan ya kashe switch ɗin ɗakin.
_Asadullah_
Zaune yake a falo shi da Jidderh da Mallamin dake mata addu'o'i. Ruwan zamzam da ya tafa addu'a a ciki take sha .
Tun da aka fara yi mata magani ba ta da abun yi sai barci. Kowane lokaci cikin barci take, da Asad ya yi wa Mallamin complain na yawan baecin ya ce ya ba damuwa alamar nasara ce. Anisa na zaune a gefen kallinsu kawai take yi, ganin yadda Asad ke bata magani da kansa tun da Mallamin ya zo shi