Showing 126001 words to 129000 words out of 154779 words
duk wajen ba wanda ya kalla, bude baki ya yi ya ce
"Morning."
Daga nan bai sake magana ba ya dauki wayarsa ta hau danne-danne.
Ƙannensa suka hau gaishe shi da ina kwana ba wanda ya kalla a cikinsu ballantana a saka ran zai amsa wa ko mutum guda ne.
Wato saboda yana fushi ne ba zai yi wa kowa magana ba, ya masu gaisawar jam'i wai Morning.
Kwafa Papa ya yi don har yanzu shi ma ransa a ɓaci yake da abinda ya faru. Don haka dama ya gama shan shayi kawai ya iya sha
Har Papa zai bar dinning area ɗin ya juyo ya kalle su ya ce.
"Wannan sallar juma'a da za'ayi yau ɗin nan ba na bukatar a ce kowa ya tafi da motarsa yadda kuke yi ku shirya akan lokaci kuma ba wai daga wajan aiki ko kasuwa za ku tafi ba, ku tabbatar kafin lokacin sallar ta yi kun dawo gidan an tafi tare, ba na bukatar wani ya kawo Mani wani uzuri."
Yana gama fadar haka ya juya ya cigaba da tafiya zuwa part ɗin sa.
*Maman Ihsan ce*
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page6️⃣0️⃣
Yana gama fadar haka ya cigaba da tafiya zuwa part ɗin sa.
*LAGOS*
Wata bakar mota ce ta yi bakin daidai ƙofar wani madaidaicin gida. Fitowa mamallakin motar ya yi sanye da rigar mai hula sai bakin Glass da ya sanya wa fuskarsa hular ta rufe kusan rabin fuskarsa.
Kasancewar safiya ne ba yawan jama'a dake kai kawo a unguwar. Wayarsa ƙarama ya fito da shi daga aljihun wandonsa. Wata lamba ya dannawa kira, bayan an daga kiran wayar ne ya ce.
"Ki fito da sauri ina son zan bar garin nan yau ne?"
Yana fadar haka ya katse kiran wayar.
Bayan kamar mintuna uku sai ga wata budurwa ta fiti daga cikin gidan. Sanye da riga da siket na atamfa, sai mayafin da ta yafa a kanta madadin Ɗankwali.
Yamutse fuska take yi Aalamar daga barci ta tashi .
"Assalamu alaikum."
Ta yi masa sallama ya amsa da.
"Wa'alaiki Salam "
"Sagir wai wannan sammakon na tafiyar ne?"
"Eh ina sauri ne."
"Wai me ya saka kullum cikin sauri kake ne, sai ka dinga yin abu. Kamar mara gaskiya wani lokacin."
Kallonta ya yi kafin ya ce.
"Sadiya na yi maki kama da mai laifi ne?"
"A'a ba haka nake nufi ba, na ga dai kullum idan ka zo ƙasar nan sai ka yi ta ɗari-dari, ba ka sakin jiki sosai, da zaran ka zo ba ka dadewa kake barin Wajen nan, sai ka yi ta kalle-kalle kamar bai neman wani abu, gabaɗaya ba ka da sukuni ne. Ko ja zo ba ka dadewa."
"Eh saboda yanayin aiki na ne ba na da lokutan kaina, amma fa zaran mun yi aure na dauke ki mun bar ƙasar nan, za ki samu isasshen lokacina yadda kike so."
Kuɗaɗe masu yawa ya miƙa mata sannan ya yi mata sallama ya shiga motarsa ya bar unguwar.
Jinjina kai Safiya ta yi ta dubu yawan kuɗin da ya bata sannan ta ce.
"Sagir kenan."
Komawa ta yi cikin madaidaicin gidan na su, gidan ne mai ɗauke da ɗakuna guda uku. Ɗaya na Mamanta sai ɗaya na mahaifinta sai ɗayan kuma na ta. Watanni biyar kenan da rasuwarsa.
Ɗakin mamanta ta shiga da sallama a bakinta, Mama na barci ta ci Sallamar Sadiya. Ta amsa tana tashi zaune, ganin ta ajiye kudi a gefen filon ne ya saka Maman tashi zaune ta ce.
"Ke Sadiya wai Sagir ne ya baki kudi masu yawa haka ?"
"Eh Mama."
"Wai yaron nan ɗan albarka ne akwai son kyauta."
"Uhm."
Sadiya ta ce tare da tashi ta barwa Mamanta kuɗaɗen.
_Hilal_
Saukowa yake yi daga upstairs ɗin sakamakon kiran wayar da Papa ya dame shi da ita.
Sanye yake cikin ɗanyar shadda fara, ya sanya bakin hula da bakin takalmi. Sai kamshi ke tashi daga jikinsa.
Ya rasa dalilin da ya saka Papa cewa yau sai dai gabaɗaya familyn Tafarki su haɗu zuwa babban Masallacin juma'a na garin. Bayan ba tare suke zuwa ba, wasu ba nan masallacin sune sallah ba. Dan Yaa Mahmud masallacin da ke kusa da bakinsu su yaje zuwa. Haka Faisal Masallacin juma'a dake kusa da kasuwa yake zuwa kasancewar sa dan kasuwa. Amma yai Papa ya tsiro cewa yau da ƴaƴansa da jikokin sa tare za su tafi sallar juma'a.
Ko da ya sauko Downstairs ɗin nan ya tarar da kowa da kowa. Sun hallara da alama saukowarsa ake jira.
Yana saukowa Papa ya yi gaba kowa ya bi bayansa suka nufi parking space.
Papa ya kalli Sadik wanda shi ne karami a cikin jikokin ya ce.
"Ku tafi a motarka dukakkan ku."
Mansur ya bude baki zai yi magana sai ya faɗa sakamakon kallon da ya ga Papa ya jefa masa.
Ba wanda ya iya magana don fuskar kakan na su kamar zai yi aman wuta haka yake.
Sadik ya shiga mazaunin direba yayin da Mahmud ya zauna gefensa. Hilal dake jin kansa wani iri ya bude bayan motar ya shiga don baya da wani zaɓi. Ganin ya shiga ya saka Faisal ya shiga Mansur ma ya shiga.
Papa ya zauna gefen direbasa wato wajen me zaman banza, ya ce wa su Daddy duk su shiga baya.
Daddy ya shiga sai Abba sannan Abbi ya shiga bayan suka zama su uku a baya.
Daga haka motocin suka bar gidan.
_Zahrah_
Koda ta fara da safe jikinta duk ya yi mata tsami sosai.don ko ina ciwo yake yi mata a jikin na ta, ga wani zazzaɓi da take jin ya rufe ta.
Daƙyar ta iya buɗe idanunta da suka yi mata nauyi sosai. Da taimakon Dada ta tashi zaune, har bathroom ta raka ta,sannan ta tabbatar ta haɗa masa ruwan zafi ta yi wanka da shi ta gasa jikinta da ya yi mata tsami sosai.
Tana wanka tana kuka tana tuna irin dukan da Hilal ya yi mata wanda ita har yanzu ba ta san laifin da ta yi masa ba da ya yi mata irin wannan dukar har ta fita hayyacinta.
Bayan ta gana wanka ta ɗauro alwala, haka ta tako a hankali tana jin ƙirjinta na bugawa da karfi. Fargaba ne ya shige ta wanda ba ta san dalilin da ya saka take jin faɗuwar gaba ba.
Doguwar riga ta janyo daga cikin Kayanta ta zira a jikinta bayan ta fesa turaren jiki a sassan jikinta, duk da ba ta da lafiya amma ba ta iya zama ba ƙamshi a jikinta.
Hijabi ta saka sannan ta shimfida sallaya, salloli da ake binta ta rama. Sannan ta yi sallar asuba.
Tana kishingide taba azkar Dada ta shigo da kofin shayi da soyayyen ƙwai dai bread ta jera su a faranti.
Duk yadda ta so Zahrah ta ci ƙwai da bread ƙi ta yi sai dai ta ɗan sha ruwan tea shi ma kadan ta sha.
Sai magungunan da Doctor ya bayar Dada ta ba ta , bayan t karba ta sha ne ta sake kwanciya. Yayin da gabanta ta tsananta faduwa, sai ta dinga karanta innalillahi wa'inna'ilahi raji'un a zuciyarta.
Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita .
Bayan sun yi parking a in da aka tanada don ajiye motoci dukkansu suka fito daga cikin motocin. Sai dai abu ɗaya da ya ɗaure wa su Daddy kai su ne. Ganin surukansu sun ƙaraso wajen wanda ba su taba ganin su a wannan masallacin ba.
Wato kakan Hilal mahaifin Mummy kenan, da kuma Kakan su Mansura mahaifin Umma da kuma Modibbo mahaifin Ummi da kuma wasu daga cikin dangin mahaifiyarsu. Sai kuma mahaifin su Kausar da Nabeela.
Bayan an gaggaisa suka shiga cikin masallaci don ba damar su yi wata tamabya, suka bar Papa yana gaisawa da su Modibbo suka shiga cikin masallaci.
Bayan an idar da sallar juma'a an yi addu'a aka sanar da ɗaurin aure da za'ayi a masallacin.
Daga bayan motar ɗin motar Papa aka dinga fito wa da goro dabino da ai drinks da ruwa daga motar Sadik wanda ba wanda ya san da su .
Kamar daga sama aka ji sanar da ɗaurin auren. *Hilal Abubakar Tafarki tare da Fatima Zahrah Salis Tafarki.* Hilal ya ɗago kai a firgice yana kallon wajen da su Papa suke, suna farin ciki har da kakansa mahaifin Mummy da wasu dangin mahaifiyarsa. Wani abu ya ji ya tokare masa ƙirji mai nauyi ya sunkuyar da kai yana kallon darduman dake shimfide a masallacin. Sai kuma aka ji sanarwar ɗaurin auren *Mahmud Adam Tafarki tare da Nabeela Nasir Isah* daga nan kuma *Mansur Adam Tafarki tare da Maryam Abubakar Tafarki* sai kuka *Sadik Salis Tafarki tare da Nadeeya Adam Tafarki*
*Sai kuma Faisal Abubakar Tafarki tare da Kausar Nasir Isah* dukkansu akan sadaki Naira dubi ɗari biyu.
Gabaɗaya angwayen da suka ji wannan sanarwar ɗaurin auren na su tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskarsu. Duk wanda ya kalle su zai shaida hakan, ya san hankulansu a tashe yake .
Hilal ne kawai idan ka kalla ba za ka iya gano rashin hankali a tattare da shi ba, domin yana da wuya ka gane halin da yake ciki ko ka iya karantar abun da ke ransa, da yake yana da jarumtar da zai iya shanye ko wane irin tashin hankali ba tare da kowa ya san halin da yake ciki ba, don haka, ko da Papa ya kallo in da jikokin na sa suke duk suna cikin tashin hankali sosai mai da dubansa ya yi ga Hilal wanda bai hango tashin hankali a tattare da shi ba, sai sai ya san cewa dole zai ji shi kasancewar ba sa jituwa da Zahrah hasalima ya tsane ta, amma da yake namijin duniya ne shi ba wanda ya iya hango hakan a fuskarsa ko a yanayinsa .
Goro da dabino aka dinga rabawa dai drinks da ruwan roba. Ana ta Allah ya sanya alkhairi da fatan zaman lafiya a tsakanin ma'uratan.
*Ku yi hakuri da wannan*
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug?mode=ac_t
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE*
Page6️⃣1️⃣
Goro da dabino aka dinga rabawa da drinks da robar ruwar roba. Ana ta Allah ya sanya alkhairi da fatan zaman lafiya tsakanin ma'uratan.
_Mom_
Zaune suke a dinning table sana cin abinci, Dad ne a gefenta sai Aunty Zulaihat dake fuskantar su. Gefe kuma Fauziyya ce da Suhailat suna yin breakfast. Mom sai juya cikali take yi a cikin ruwan shayi. Ta yi tagaumi tana tunani. Dad ya kalle ta ya ce.
"Hajiya lafiya na ga ba ki wani ci abincin kirki ba ga kowa na cin abinci."
Ajiyar zuciya ta sauke cikin damuwa kafin ta ce
"Ba komai Dad ɗin Asad ."
"A'a akwai komai."
"Alhaji damuwa ta ɗaya ce rashin sanin halin da Asadullah yake da kuma rashin sanin in da yake."
Ta yi maganar tana goge ƙwallar dake cikin idanunta, zuba mata idanu Dad ya yi cike da tausayinta, ya san tabbas akwai Shakuwa tsakanin ta da Asadullah, kusan a hannunsa ta ya tashi, ɗan ɗakinta ne shi.
"Hake ne, amma in sha Allah yana cikin ƙoshin lafiya, ki rage damuwa don Allah, fatana ki yi ta yi masa addu'a Allah ya kare shi ya toni asirin waɗan da suka yi masa wannan aiki."
Da sauri ta kalle shi taɓa mamakin jin kalaman sa kafin ta ce.
"Ban gane Allah ya bayyanar da shi ya toni asirin wadanda suka yi masa haka na, don Allah ka faɗa Mani me aka yi masa kuma su waye suka yi masa, kada ka ce an cutar mana da Asadullah don Allah."
Ta karasa maganar tana hawaye. Cikin kokarin boye mata gaskiyar abinda ya sani ya ce.
"Kin ga ki kwantar hankalin ki ba haka nake nufi ba ina nufin Allah ya bayyanar mana da shi a duk in da yake ba tare da wasu sun cutar da shi ba."
"Dad ɗin Asad ni fa ba yarinya karama ba ce, kada ka ce za ka boye mani komai, ka faɗa Mani wani hali ɗan mu yake ciki walalhi ina cikin damuwa na rashin sanin halin da yake ciki .
Nan Dad ya dinga ba ta baki da kwantar mata da hankali, kafin ta saki ranta amma duk da haka ta kasa cin abincin kirki a cikin ta.
Tausayi ta ba Dad don ba don ya yi wa Asadullah alkawarin cewa ba zai fada wa kowa ba da ya sanar da ita halin da Asadullah ke ciki. Don baya zargin za ta iya cutar da shi, bisa la'akari da a hannunta ya tashi akwai kauna a tsakaninsu tun mahaifiyar Asadullah na raye.
Tashi ta yi ta koma bedroom ɗin ta cikin damuwa.
Fauziyya ta tashi ta bi bayan mahaifiyarta ranta a ɓace.
Tana shiga ta samu Mom ta haɗa tagumi ta kalle ta cikin ɓacin ran da mahaifiyar ta su ke nuna halin ko in kula akan Yayanta ta ce.
"Mom yanzu ɗan kishiya ya fi ɗan da kika haifa a wajen ki?"
Kallonta Mom ta yi ba ta yi magana ba ta share ta kamar ba ta ji komai ba ta ce.
"Mom Asadullah ba ke kika haife shi ba ɗan kishiyarki ce shi, duk kin bi kin daga hankalinki akan sa kin damu kin saka rashin wakawlaa tun lokacin da aka rasa ina yake. Amma ke ce kika haifi Kamal ɗanki ne ga shi can yana rayuwa a gidan yari rayuwar rashin ƴanci da ƙasƙanci ba ki damu da hakan ba , ko sau daya ban ji kina magana akan sa ba shi ki da yake prison, amma kin damu da wanda ba ka ke kika haife shi ba wa ya sani ko ya guje mu ne yana..."
Tsawar da Mom ta daka mata ne ya saka ta yin shiru ta fice rai a ɓace, don Allah ya sani tana tsananin ƙaunar ɗan uwanta Kamal. Duk da cewar Asadullah ma tana son sa, saboda yana kyautata mata sosai, amma Kamal da suka fito ciki ɗaya ta fi jin sa a ranta fiye da Asadullah.
_Papa_
Gaisawa yake yi da jama'a dake taya shi murnar aurar da jikokinsa,bakinsa ya ki rufuwa fatan shi Allah ya sa wannan auren ya zama sanadiyar haduwar kan Family ɗin sa. Suka kebe shi da surukan na sa wato iyayen matan ƴaƴansa, da kuma mijin Aunty Laila suka dan yi magana kafin ya masu sallama.
Ƙarasowa ya yi wajen motocinsu in da ya tarar shi suke jira, don hatta ƴaƴan na sa bai yi shawara da su ba wajen aurar da jikokinsa, don ya san ba za su taba amincewa da wannan hadin ba, don haka sai dai suka ji ɗaurin auren daga sama. Daddy, Abba, Abbi, ba karamin tashin hankali suka shiga ciki ba saboda ba su taba tunani ba. Babban tashin hankalin su yadda dukkansu uku aka haɗa aure a tsakanin ƴaƴan Abbi da na su. Sam ba sa da hadin kai da Abbi cikin yaran Papa huɗu shi kadai suka ware a cikinsu . Amma yau Papa ya kulla igiya mai daraja sun hadu a matsayin surukan juna. Girgiza kai Dad ya yi a zuciyarsa yake magana .
'Wato dukkan mu da muka ware Salis a cikin mu sai da Papa ya haɗa yaran dukkanin mu da yaran Salis, a tunanin Papa wannan zai kawo masalaha kenan, to ai yaran ba sa son junansu na tabbatar Papa ya ƙara ruguza a halinsa wajen kokarin ya kawo sauyi. Musamman Hilal na san da wahala ya yarda da wannan auren.'
Papa ya karaso wajen fuska cike da farin ciki, ya kalli angwayen yana cewa.
"Angwaye kun sha ƙamshi."
Ko wa ya sake tsuke fuska ba wanda ya kula shi sautin murmushin sa ta suka ji ne ya saka suka kalle shi amma ban da Hilal
'
Papa da ya karaso wajen kallonsu ya yi ɗaya bayan ɗaya duk sun yi cirko-cirko kamar wadanda aka aiko wa sakon mutuwa suka yi.
Ku shiga mota mu tafi, kuma idan mun koma gida ina son ganin kowa a part ɗin na."
Ya yi maganar yana shiga gefen direba, cikin sanyi jiki su Daddy da Abba suka shiga bayan motar yayin da Abbi ya shiga daga karshe.
A can kuwa wajen angwaye kasancewar motar Sadik suka shiga wajan zuwa kamar yadda suka zo, sai dai kowa a cikinsu kamar baya da laka a jikinsa. Sadik kasa driving motarsa ya yi, ganin haka Hilal ya fito daga bayan motar ya bude gefen Direba tare da yi wa Sadik alamar ya fito ba tare da ya yi magana ba, ganin haka ya saka Sadik fitowa daga cikin motar ya koma baya.
Hilal ya yi wa motar key tare da fisgarta da ƙarfi ya bar wajen.
Har ya wuce su Papa da suka riga su tashi, gudu yake yi kamar zai tashi sama, su kansu sun lura da irin Yulin da yake yi. Amma ba wanda ya iya yin magana har suka ka ce karasa.
Danna horn yake yi ba kakkautawa. Mai gadin ya leƙo ya bude da sauri.
Ko parking din kirki bai yi ba ya fito ya shiga cikin gidan.
Kamar wakjiya su da suke falo ba su ga shigowarsa ba, sai dai suka jin takun hawa steps da ƙamshinsa da ya bar masu. Har tsallaken stage ɗin yake yi ya haura zuwa ɗakinsa.
Su kuwa cikin sanyin jiki suka shigo, sai dai tunawa da maganar Papa da ya ce su wuce Part ɗin sa su same shi shi ya saka shi ya sa ba su wuce Part ɗin su ba, kowa kowa ya nufi part ɗin Papa kamar yadda ya sanar da su.
Mutanen dake falon suka ga yanayinsu take jikinsu ya yi sanyi, don haka suka bi bayansu ba da kallo.
Kafin su yi wani yunƙuri suka ga Papa ya ba shigo su Daddy na biye da shi a baya.
Kallonsu Papa ya yi tare da cewa.
"Ina son ganin kowa a part ɗi na."
Ya kalli Abbi tare da cewa.
"Salis ka kira matarka don na ga ita kadai ce ba ta nan."
Da to Abbi ya amsa sannan ya nufi part ɗin sa don kiran Ammi.
Haka suka bi shi daga su har yaransu su matan da ba su san meke faruwa ba kansu a daure yake .
Bayan kowa ya hallara gabadaya,