Showing 33001 words to 36000 words out of 154779 words

Chapter 12 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6265

Zahrah ya ji kamar ciwonta ya tashi.

Bayan ya katse wayar gajeren tsaki ya yi cike da takaicin yarinyar ya sauko ƙasa.


_Asadullah_

Kwance yake a saman katifar dake ɗakin, tun yana kan kafa har ya fado ƙasa, dafe kansa da yake jin kamar zai fashe. Wani sauti yake fitarwa mai kama da gurnani.

Doctor dake tsaye a kansa ne ya ciro wayarsa a Aljihu tare da lalubo wata lamba. Kira ya dannawa lambar nan da nan aka ɗaga.

Cikin wace irin murya mai kama da rauni ya fara magana.

"Na gama maku aikinku don Allah ku sake mani ƴaƴanta."

Ta cikin wayar ya ji Muryarta tana cewa .


"Gaggawar ne kake yi ai aikinka bai ƙare ba."

"B haka muka yi da ke ba kun saka ni aiki kuma na yi maku me kuke buƙata kuma, amma kin san ba haka muka yi da ku ba?....Wallahi ba za ku ga annabin rahama ba, mutumin da ya yarda da ni yake kyautata mani iyalai na, har yanzu wannan aikin da nake yi ina cin alfarmarsa, wanda bai cancanci haka daga gare ni ba, amma saboda son zuciya da kwaɗayin abun duniya kuna neman kashe shi. Sai dai shi idan ba ku sani ba kainuwa dashen Allah ne shi ba na mutum ba. Don da wani ne yadda kika dinga sakawa ana yi masa waɗan nan alluran da tuni ya bar duniya amma shi har yanzu yana a raye."

Tsawar da ya ji wani ya daka masa ta cikin wayar ya saka shi yin shiru.

"Za ka yi aikin da aka saka ne ko kuma sauratan banza? Kar ka manta ƴaƴanka suna hannunmu ba za mu sake su ba har sai ka kammala mana aikin mu. Idan kuma ka ɗauki lokaci mai tsayi to za mu tiro maka da gawar ɗaya daga cikinsu. Ya rage saura ɗaya wannan gargaɗi ne."

Muryar macen ya ji tana cewa.

"Kada ka bamu matsala fa ba wai mun ɗauke ka aiki ba ne saboda matsala, mun ɗauke ka ne saboda muna neman mafita. Don kai kaɗai ne likitan iyalin dake cikin Asadullah Mantson. Idan aka wani yana shige da fice waɗan nan security za su tsaurara bincike ne, amma kau ba wanda zai damu saboda sun san kai ne mai duba marasa lafiyar, za su yi zaton rashin lafiyar ɗaya daga cikin ahalin ne ya saka kake zuwa. Don haka ka iya takunka."

Ana faɗin haka aka katse kira wayar, kallon Asadullah ya yi cikin rauni ya ce.

"Ka gafarce ni yallaɓai, ƴaƴana guda biyu da Allah ya bani suka kama, saboda sun san cewa suke rauni na. Ba yadda zan yi ina son ƴaƴana."

Yana gama faɗar haka ya harhaɗa kayansa ya fito daga ɓangaren idanunsa cike da ƙwalla.

Kiciɓis suka ji da amintaccen bodyguard ɗin Asadullah wato Sulaiman, kallon Dr ɗin ya yi ganin daga in da ya fito ga shi yana zubar da ƙwalla.

"Hey Doctor daga ina, me kake yi a wancan ɓangaren?"



_Hilal_

Yana saukowa downstairs suka zuba masa idanu daga shi sai farar singileti da dogon wando baƙi. Singileti ya fitar da surar jikinsa na ƙaƙƙarfan namiji jarumi. Kallo ɗaya za ka masa ka san cewa yana yawan motsa jiki bisa la'akari da yadda ƙwanjinsa suka bayyana a fili.

Kausar ta saki murmushi tare da maganar zuci .

'Allah ya nuna mani ranar da za ka zama mallakina ni ma na zama taka.'

Nabeela kam cewa ta yi a zuciyarta

' Yaya Hilal har yanzu ba ka amince da bukatata ba, ko ba ka aure ni ba so nake mu ɗumin juna.'

Kai tsaye part ɗin su Zahra ya nufa, bakinsa ɗauke da sallama.

Gabaɗaya ahalin dake falon suka bishi da kallon mamaki ganin in da ya koma.

Dady da Abba ne suka mara masa baya sannan su Aunty Laila da Mummy da Umma suka bi bayansu. Haka yaran ma suka tashi maza da mata.

Yana shiga ɗakin ya tarar da tana kokawa da numfashinta.
Kai tsaye ya nufi in da ya ɗauki maganin ranar da ya saka ta punishment ciwonta ya tashi.

Yana duba wa ba komai a ciki haka ya hau duba maganin ko ina ya birkice ɗakin bai ga magungunan ta ba.

Cikin kufula Umma ta ce.

"Me kake ƙoƙarin yi ne?"

"Maganinta nake nema baya nan."

"Wai me ya sa duk cikin ƴaƴan da na haifa kai kaɗai ne ban isa da kai ba, ina ruwanka da maganinta ko halin da take cikin, shin kana da alaƙa da yarinyar nan ne ?"

"Umma ba wata alaƙa ko wani abu a tsakanina da yarinyar nan, hasalima na tsane ta, wannan ƙoƙarin ceton rai ne. Wanda ko da ba ita ba ko wani ne na hadu da shi a hanya yana cikin halin da take ciki sai na taimaka masa ko da ban san shi ba zan ceci rayuwarsa wanann shi ne."

Cikin takaici Aunty Laila ta kalli Abba ta ce.

"Kana ganin yaronka na shirin ba mu matsala ko, ka faɗa masa ya fita daga harkar yarinyar nan idan ba haka wallahi sai ga abinda zai biyo baya."

"Aunty ba na shiga harkarta yanzu ma Papa ya turo ni wajenta akan ciwonta ya tashi kuma na fada maki ba don ita ba ko maƙiyina ba na masa fatan ya tsinci kansa a cikin mawuyacin hali, aikin ceton rayuwaka da dukiyarsu nake yi rashin imanin nawa ba kai da zan iya ganin ɗan Adam w cikin mawuyacin hali na ciwo na yi fatali da shi ba saboda wata aƙida, ku saka wa ranku ba ita na ce ta ba rai na ceta ko na waye kuwa ."

Abban ya ce.

"Hilal mu ne marasa imani kake nufi ko meye?"

"Ban faɗa ba Abba ka yi hakuri ba nufina kenan ba, ku saka a ranku ban ceci yarinyar nan ba rayuwa na ceta wacce ko a ina ne ko ban san mutum ba haka zan yi."

Cikin ɓacin rai Umma ta ce.

"Hilal ka fita ka bar ɗakin nan yanzun nan."

"Zan fita Ummana amma sai na kammala abun da ya kawo ni, matukar na sa gaba a bi ba na dakata wa har sai na kai ga ci."

Bai saurare su ba ya cigaba da neman maganin ba su yi mamaki ba don sun san halinsa in dai akan gaskiyarsa ne ba zai taɓa sauraren kowa."

Kausar ce ta yi magana ƙasa-ƙasa tana cewa.

"Ka gama wahalarka ba na kwashe magungunan na fita da su, kafin ka kai ta asibiti Allah ya sa ta mutu."

Ba wanda ya ji ta sai shi a fusace ya kalle ta nada sai da hanjin cikinta ya ƙaɗa. Ya nufe ta tare da cewa.

"Ki yi sauri ki kawo mani su duk in da kika kai su."


"Yaa Hilal me zan baka ni fa ban san komai ba."

Ganin za ta raina masa hankali ya sa shi cewa


"Kada ki bari na sake maki tambaya a karo na biyu, ina suke na ce."

Ganin ta masa banza ya saka ya shaƙo wuyarta tare da cewa .

"Za ki fada ko sai na kashe ki kafin ita ta mutu ki riga ta mutuwa?"

Idanunta suka firfito nan da na Yaa Mansur da Yaa Faisal suka fara ƙoƙarin kwatarta, amma ina sun kasa cire hannunsa daga wuyanta . Aunty Laila sai kuka take yi tana cewa zai kashe mata yarinya.



*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Page1️⃣7️⃣

Idanuwanta suka firfito nan da nan Yaa Mansur da Yaa Faisal suka fara ƙoƙarin kwatarta, amma ina sun kasa cire hannunsa daga wuyanta. Aunty Laila sai kuka take yi tana cewa zai kashe mata yarinya.

Nan da nan Abba ya ƙarasa yana kiran sunansa shi da Abba, su ma sun kasa cire hannunsa daga wuyanta.

"Za ki faɗa ko ba za ki fada ba kin fi son mutuwa.?"

Dukansa Aunty Laila take yi tana kuka amma kamar dutse take duka.

Kausar jin ta kusa mutuwa ne kuka ba ta ga alamar zai sake ta ba ne ya sa ta ɗaga masa kai da muryarta da baya fita ta ce.

"Zan faɗa"

Jin haka ya sa ya sake ta tare da fuszar da iska mai zafi ta bakinsa.

Aunty Laila ta rungume ta tana kuka yayin da Kausar ɗin ma ta kasa kuka. Don tashin hankali idan ya yi yawa ma ba ka samun damar yin kuka.

Sai wuyar ta da ta rike take tari.

"Ina suke!?"

Ya faɗa a fusace yana kallonta.

"Yana ɗakinmu a ƙarƙashin gado."

Kallon Nabeela ya yi tare da cewa.

"Ki yi sauri ki kawo Mani."

Ba ta da wani zaɓi dole ta tafi duk da ba da son ranta ba ne, amma tun da tana son shige masa dole sai ta bi yadda yake so.

Ba jimawa sai ga ta ta dawo da jakkar magungunan. Miƙa masa ta yi ya karba tare da juye su kan gadon.

Kallon Zahra ya yi dake kwance kamar gawa, sannan ya mai da dubansa kan magungunan, sanin cewa alluran zai fi mata aiki a yanzu ne ya saka ya ɗauki alluran da sirinjin. Dubawa ya yi ya karanta sannan ya yi mata alluran.

Bayan ruwan alluran sun bi jijiyoyin jikinta ne ta ja numfashi da karfi . A hankali ta buɗe Idanunta tare da sauke su akan fuskarsa dake ɗaure tamau.

Sai ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo, tana mamakin yadda gabaɗaya ilahirin gidan suka cika mata ɗaki. Ta dai san alkhairi ba zai kawo su wajenta ba. Tun da ba ƙaunarta suke yi ba. Hatta idanunsu duk ya nuna hakan bisa la'akari da irin kallon tsanar da suke jifanta da shi.

Abba ne ya fara fita sai Dady, daga nan Umma da Mummy suka fita. Daga nan sai Yaa Mansur da Yaa Faisal, Nadiya da Maryam ma suka fita, ya saura sai Aunty Laila da yaranta.

Aunty Laila kwafa ta yi tare da hannun Kausar suka fice. Nabeela ta rage ta tsaya ganin abinda zai tura wa buzu naɗi.

Zuciyoyin kowa na gidan cike da takaicin Hilal, sai dai ba yadda suka iya da shi. Sun so a ce baya nan hakan ta kasance don damar da suka faɗe suna jira kenan. So suke ta bar duniyar gabaɗaya, don sun san hakan zai dasa baƙin ciki a zuciyar Salis da Matarsa. So suke ya ɗandani bakin cikin fiye da wanda ya yi sanadiyyar saka su a baya. Wanda tun tasowar ɗan uwan nasu ba su taba ganin ya kwashi bakin ciki ba a rayuwarsa sai farin ciki. Amma idan ya ji labarin mutuwar ƴarsa mace tilo da suka fi ƙauna shi da matarsa da iyayensu dole duk za su kwashi bakin ciki.

A falo suka hadu dukkansu cikin takaici Aunty Laila ta ce.

"Kan waccan banzar yarinyar ne yake kokarin kashe Mani ƴa ko?"

Abba ya kalle ta tare da cewa.

Kuyi hakuri Laila."

"Haba Yaya wani haƙuri kawai abin da zai fi dauki ka yi gaggawar cewa ya koma can U.S a bakin aikinsa. Don wani sati mahajjata za su dawo, idan iyayen yarinyar nan fa su Papa suka dawo ba halin shirin mu ya tabbata."

Umma ta cikin takaici ta ce.

"Ba abinda ke ɓata mani rai da Hilal kamar taurin kansa sam baya tanƙwasuwa, idan ya kafe ya kafe kenan ba mai saka shi ba mai hana shi. Ina ga idan ya ƙure ni akan waɗan nan mutanen dai na gifta kalmar tsinuwa sannan zai dawo cikin hankalinsa."

"Kul!"

Abba ya dafa yana kallonta.

"Abban Hilal ba ka ganin yadda muna hana shi abu baya hanuwa?"

"Yana hanuwa mana, duk muka bashi umarni baya taba tsallake wa, sai dai na lura da shi in dai akan gaskiyarsa ne baya mana biyayya, matuƙar ya san cewa shi ne mai gaskiya to fa baya sauraren kowa."

Cikin takaici Umma ta sake cewa

"To zan nuna masa mu ne muka haife shi ba shi ya haife mu ba."

Aunty Laila ta ce.

"Ina ga ayi masa aure kawai shi ne mafita, ya ɗauki matarsa su tafi can U.S sai idan sun zo mana ziyara. Don haka ha ƴan uwansa nan ya zabi daya daga ciki, idan bai zaba na mu za mu zaba masa da kanmu."

Jinjina kai Abba ya yi cike da gamsuwa. Dady ya ɗaura da cewa.

"Ƙwarai kuwa a cikin Nadiya, Kausar da Nabeela cikin su uku ba zai rasa wacce yake so ba."

Aunty Laila ba ta so ya hada da ƴarsa Nadiya a ciki ba, taso cikin ƴaƴanta biyu don haka ta ce.

"Ai Kausar da Nabeela suna son sa ne ita Nadiya ta ce tana sonsa ne?"

Kowa ya kalle ta dake ba kunya ce da ita ba ta ce.

"To wace mace ne za ta kalli cikakken namiji irin ya Hilal ta ce ba ta so, wallahi ina son sa ."

Maryam sai taka ƙafarta take don ta yi shiru amma ko a jinkinta .

Abban Hilal ya ce .

"Shi kenan, za mu bashi zaɓi cikin su uku , idan ya ki haƙiƙa za mu sura masa duk wacce muka ga dama."

Daga haka suka watse kowa ya yi part ɗin ta sai Aunty Laila da ta zauna zaman jiran fitowar Hilal.

A can cikin ɗakin kuwa bayan ta dawo daidai ne ta yunƙura da niyyar tashi amma ta kasa.koma ta yi ƙasa ta kwanta.

Sanin sanyin tile zai iya kawo barazana ga lafiyarta ya saka shi ɗaukar ta cak ya ɗaura a saman gadon. Sannan ya kalli Nabeela ya ce.

"Ke kuma fa akwai abinda kike jira ne?"

Taɓe baki ta yi tare da cewa.

Magana nake so mu yi da kai."

Kallonta ya yi na sakan sakan uku ya ce.

"Ina jin ki."

"Sirri ne."

Jin haka ya sa ya juya dan ficewa daga ɗakin. Cikin sanyin murya irin nata ta ce.

"Na gode da ceton rayuwata da ka yi, Allah ya saka maka da gidan Aljanna."

Bai amsa ba sai ce mara ya yi

"Ki shirya ƙarfe bakwai na safe za mu tafi.

Da mamaki Nabeela ta lalle shi tana cewa.

"Ina za ku je tare?"

Fita daga ɗakin ya yi ba tare da ya ce mata komai ba.

Haka ta dinga binsa a baya har ya haura upstairs, ya shiga falonsa ta bishi, yana ƙoƙarin shiga bedroom tana ƙoƙarin binsa.

Dakata wa ya yi ba tare da ya juyo ba ya ce.

"Lafiya?"

"Magana da nake so mu yi da kai."

"Ina jinki."

"Ina za ku tafi da waccan yarinyar ne?"

"Wata yarinya?"

Sai da ta yamutse fuska sannan ta ce.

"Zahrah "

"Kaduna"

Ya bata amsa sannan ya saka hannu a handle ɗin ƙofar zai shiga.

"Yaa Hilal me za ku je yi da ita?"

Bai ba ta amsa ba ya yi shigewarsa ciki, kai tsaye ita ma ta kutsa kai ta shiga bedroom ɗin nasa.

Singileti dake jikinsa yake ƙoƙarin cirewa ganinta ya saka shi dakata wa tare da ɗauke fuska tamau.

"Ke meye kuma?"

"Maganar da zan maka ne ai ban yi ba ka shigo ɗaki."

"Ina jinki."

Juya baya ta yi yadda ba za ta kalli idanunsa ba ta ce .

"Ya Hilal ina son ka don Allah ka aure ni, na maka alkawarin kasancewa duk yadda kake so."

Ransa a ɓace ya juyo yana kallonta.

"Ke!"

Sai da ta firgita da ganin yanayinsa.

"Sa'anki ne ni?"

Sunkuyar da kai ta yi ta kasa hada idanun da shi, saboda tsoron da idanusa suka bata. Cikin ɓacin rai ya sake cewa.

"Duk san da kika dake tara ta wannan maganar sai na karairaya ki."

Ƙofar fita ya nuna mata da fice a guje tana kuka.


Washegari tun da Fatima Zahra ta yi sallar asuba ta yi azkar da karatun Alqur'ani, ta gyara gyara ko ina a ɗakin duk in da ya dace sannan ta yi wanka.

Riga da siket ta saka na leshi, kalar purple an yi masa ado da kalar zare pich colar ɗinkin sun ɗan kama ta amma sun zauna mata ɗagwas a jiki. Ba ta yi wata kwallaiya ba powder kawai ta shafa.

Kasancewar safiya ne ba ta yi tunanin ganin kowa a falon ba, don haka ta fito kanta a buɗe gashi kanta ta tufke shi ta sake shi a gadon bayanta.

A hankali take tafiya kanta tsaye ta nufi hanayar kitchen, jin idanu na yawo a jinkinta ne ya saka ta juya nan ta gan su gaba daya s dinning table suna cin abinci.

Mamaki ya kama ta ganin yau sune da sammako wajen breakfast, sai kuma ta tuna da cewar saboda Hilal zai yi tafiya ne, don haka suka fito don suna ji da shi, in dai zai yi sammako zasu tashi da wuri saboda shi. Ko da ba su ci abinci ba za su kasance da shi a dinning table.

A hankali ta ƙara so don ta gaishe su. Cikin sanyi ta durkusa ta gaida Abba bai amsa mata ba, haka Dady shi ma shiru bai amsa ba. Ta gaida Umma da Mummy da Aunty Laila. Ba wacce ta yi mata kallon arziki.

Ta kalli Yaa Hilal ta ce.

"Ina kwana Yaa Hilal?"

Bai amsa mata ba shi ma, ba ta hakura ba ta kalli Yaa Mansur ta ce.

"Yaa Mansur ina kwana?"

"Wallahi na sake jin sunana a bakinki sai na sauya maki kamanni mayya kawai."

Murmushin takaici ta yi ta kalli Yaa Faisal ta kalle shi ta ce,

"Yaa Faisal ina kwana?"

Idanunsa akanta ya kada ko ƙyaftawa, sanyayyar murmushinsa ya sakar mata tare da jinjina mata kai alamar ya amsa.

Duk da ta fito neman abin da za ta saka wa cikinta ne, kuma da alama an gama an jera a dinning table, sai dai tun da iyayenta suka tafi zaman cin abincin gidan ya gagare ta, don ƙiri-kiri za ta hana ta cin abinci sai dai ta shiga ta girka nata ita kaɗai.

Kallon agogon hannunsa Hilal ya yi ya ga bakwai saura mintuna goma sha biyar.

Tana shiga kitchen ta dafa ruwan zafi ta soya ƙwai ɗaya, ta haɗa tea ta ɗauki bread ta zauna a falon ta fara ci da sauri ganin lokaci ya kusa.

Nan da nan ta gama ta je kitchen ta wanke kayan da ta ɓata.

Ta koma ɗaki. Wayarta ta ɗauka tare da ƙaramar jakkar da ta zuba mata kala uku sai na barci.

Wayarta ta saka a handbag ta ɗauki dogon hijabinta ta saka pich colour ta saka ta fito zuwa Babban falon gidan.

Ba kowa a falon ta nufi parking space a can ta hango su duka. Tana ƙarasa wa ta kowa ya fara mata mugun kallo, bata ce komai tana ƙoƙarin shiga motar ashe ta taka ƙafar Kusar ba ta sani ba, don sun cika wurin da ƙyar ta kutsa ciki ba wanda ya bata hanya.

A fusace Kausar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login