Showing 30001 words to 33000 words out of 154779 words
ta ta shiga ɗakinta.
Halin da ta bar Asadullah kawai ke damunta. Tana tuna tarin alkhairi da ya yi mata a rayuwa.
A hankali ta fara tuna ranar da ta je kamfanin a karo na biyu da neman aiki.
Wata ranar talata da misalin karfe goma na safe, mai keke napep ya sauke Jidderh a bakin kamfanin Asadullah. Bayan ta biya mai napep kuɗinsa ne ta karasa bakin kofar kamfanin. Cikin ikon Allah sai ta samu wancan security ne a bakin gate. Kallo ɗaya ta yi masa ta gane cewa shi ne mutumin da ranar da ta zo neman taimako za'ayi wa Sa'adatu tiyata ya hana ta shiga. Wanda wurin dagewarta na son shiga ne ta faɗi har kokon da A ta kai asibiti ya zube.
Yana ganinta shi ma ya gane ta, da sallama a bakinta ta karasa wajensa. Ya amsa mata tare da sauraren me za ta ce.
"Don Allah ina son ka taimake ni na hadu da Sir Asadullah ne."
"Ke baiwar Allah ganin Sir Asadullah ba abu ba ne mai sauƙi, bar ganin wancan ranar kin gan shi cikin sauki sa'a kika ci yana isowa kika zo shi ya sa kika gan shi kafin ya karasa ciki, amma da zaran ya shiga ganinsa zai maki wuya. Ko nan bakin gate mutum baya shiga ba tare da an bada izinin shigarsa ba."
Marairaice fuska ta yi tare da cewa.
"Ka taimaka ka barni na shiga."
Ko na barki kin shiga daga gate to idan kin shiga ciki ba barin ki za'ayi ki shiga ba. Don ma'aikatan ma hana ki za su yi ki shiga dole sai sun sanar da shi har sai ya bada izinin shigarki ciki."
"To ai shi ne ya ce duk lokacin da nake bukatar ganin shi na zo kai tsaye."
Ta faɗa tana addu'a Allah ya sa kada ya gane karya take masa.
"Ina shaidar yake dole zai baki katinsa mai ɗauke da saka hannunsa ."
"Eh ya bani ɓacewa katin ya yi, kuma yau in sha Allah sai na shiga nan, ka je ka tamabaye shi mana."
Kallon ta kawai ya yi sannan ya bude mata gate yana cewa
"Ai su ba za su bari ki shiga ba kya dawo."
Tana shiga wajen ta saki baki tana kallon yadda aka narka dukiya wajen ƙera Kamfanin. A zuciyarta ta ce.
'Wannan wani irin gini ne, gaskiya duk wanda ya tsara wannan ginin kamfanin ya iya tsara gini, sai ka ce a ƙasar Turai. Gaskiya duk yadda aka yi turawa suka tsara wajen nan.'
Gabaɗaya jikin bango ginin mirror ne ajikinsa, sannan ga wani wuta ne golding ke fitowa daga jikin mirror ɗin. Da wutar solar yake amfani da shi wanda kudinsa zai iya kai billions naira.
Tana kai wa bakin ƙofar ta ji an ce.
"Hey!"
Tana jin haka ta tsaya tana kallonsa, kallon sama da ƙasa ya mata sannan ta ɗaure fuska ya ce.
"Daga ina kike ko an faɗa maki ana bari mabarata ne su shigo nan wajen?"
"Ni ba mabaraciya ba ce, na zo wajen sir Asadullah ne."
Kallon dyama da ƙasa ya yi mata tare da daka mata tsawa . Lokaci guda ya tuna ita ce wacce ta zo ranar da kuma gargadin da aka yi wa security. Don haka ya ce
"Me kika zo yi?"
"Shi ya ce na zo duk sanda na so."
"Ina katin da ya baki?"
"Yallaɓai na nema ban gani ba "
Haka nan sai ya tsinci kansa da ba ta izinin wucewa. Da kansa ya ce ta biyo shi a baya.
Suna nufar wani ƙafa sai ta ga glass din ƙofar ya zuge da kansa. Suka shiga ckki, taɓa kallo ya yadda komai yake cikin tsari da sha'awa. Ganin idan ta tsaya kallo mutumin zai iya wuce wa ya sa ta ɗauke idanunta daga kalle-kallen da take yi .
Nuna mata wata ƙofa ya yi tare da cewa.
" ki shiga za ki ga wata mata ita ce za ta maki izinin shiga wajensa."
Daga nan ya juya yayin da Jidderh ta kutsa kai cikin office ɗin.
Wata matashiyar budurwa ce sanye da Suit baƙi tana danne-danne a laptop.
Kallo budurwar ta yi mata tare da cewa.
"Ke mahaukaciyar ina ce za ki shigo wa mutane ba tare da an baki izinin shigowa ba?"
Wayar dake gabanta ce ta yi ƙara. Tana dubawa ta ga yallaɓai ne da kansa, tana ɗagawa ta ji muryatsa ya ce .
"Let her in."
"Okay sir,."
Ta fada sannan ya katse kiran wayar.
Tun zuwan ta yake kallonta da yadda suka ji da security na ƙafa har yadda aka yi ta a shigo duk akan idanunsa ne, sai dai yana mamakin karfin hali ir Irin na yarinyar .
Bayan an nuna mata ƙofar da za ta shiga ne ta mike da sauri ta nufi ƙofar .
Tura ƙofar ta yi tare da yin sallama.
Can kasan maƙoshi ya amsa sallamar don shi kadai ya ji kayansa.
Tana shigowa ta saki ajiyar zuciya sakamakon wani sanyin AC da da da ƙamdhin da ya yi mata Barka da zuwa.
Tsaya wa ta ji tana kallonsa shi ma ya zuba mata blue eyes ɗin sa yana jiran me za ta ce.
"Dama na zo ne don na sake yi msla godiya da irin alkahiri da ka yi Mani a rayuwa ta. Ka ce rayuwar matar Yayana ."
Ba tare da ya kalle ta ba ya na ta danne-danne s laptop.
"Don Allah zab samu aiki?"
Dakatar sda abinda yake yi ya yi tare da zuba mata idanu ya ce.
"Wane irin aiki, ne ya matakin karatunki?"
"Ban yi karatu ba aikin goge-goe nake bukatar yi."
"A yanzu muna da isassun ma'aikata, a shekarun ki ya kamata ace kina makaranta ne."
"Eh ina zuwa ina son na hada biyu ne."
"Yanzu ba buƙatar mai'iakata, anan."
"Yauwa to can gidan fa ba buƙatar mai aiki ne?"
Wayarsa ya ɗauka ya kira lambar Mom, bayan ta ɗaga ne yake tambaya ko suna bukatar ƙarin mai aiki, Mom ta ce eh don ɗaya daga cikin masu aikin ta tafi gida wai aure za'a mata.
Ya ce zai turo ta .
Bayan sun gama wayar ne ya bata adireshin ya ce duk mau abun hawannfs ta tare ta bashi zai kai ta.
Sannan ya bata wa i Katin ya ce ta bawa security dake kula da ƙofa idan suka gani za su bari ta shiga ciki.
Godiya ta yi masa ya bata kudi masu yawa ta wuce zuciyarta fara tas. Ta samu aikin da za ta tallafawa iyayenta .
Bayan ta je ne ta ba wa security katin sannan suka bari ta shiga bayan sun duba.
Ta shiga ciki ta samu su Mom da Dady , sallama ta U in suka amsa ta gabatar da kants.
Daga nan Mom ta kira Mama ta ce ya nuna mata aikin da alawiyya ke yi sai ta cigaba da yi.
Bayan ta gama tunanin da take yi ne ya goge ƙwalla. Tana zancen zuci.
'To dai me yasa aka daure shi aka kulle ji kamar dabba, anya iyayensa na tare da shi kuwa? Ba uwar da za ta juri hakan akwai sake.
Ta yaya za'a ɗaure mutum mai daraja kamar Asad ko haukacewa ya yi bai cacanci haka ba.
Daga karshe ta yanke shawarar nemo hanyar da za ta taimaka masa.
Daga karshe ta fita ta samu Inna da Aunty Sa'adatu.
_Hilal_
Suna isa makarantar direbansa ya yi parking motarsa. Ya fito ya budewa Halal bayan motar ya fito. Zahrah ma ta fito ta ɗaya bangaren.
Kusan rabin jama'ar dake harabar makarantar zuba masu idanu suka yi. Don motar ta burge mutane sai ɗaukar idanu take yi. Ga mamallakin motar ya haɗu duk wanda ya kalli Hial sau ɗaya sai ya ƙara kallonsa.
Ballantana yau Fatima Zahrah ta zo babu niƙab a fuskarta, don duk zuwa islamiyarsu da take yi sai ya sanya niƙab. Idan ko ta fito haka nan to sai ta tsargu da irin kallon da ake yi mata, ba maza ba hatta mata ma shagala suke yi da kallonta.
Dan tamkar ita ta halicci kanta haka take. Don duk yadda kuke ji ana faɗin tsantsar kyau da ta wuce haka nan, idanunta ma ɗaukar hankalin mutane suke yi ga ƙaramin pink lips ɗin ta dai shinning suke yi. Sai dai ba ta da ƙiba siririya ce sosai kamar za'a hure ta ta faɗi ƙasa.
Wani Mallami ne wanda yake son Zahrah don shi ya san fuskarta wata rana da ciwonta ya tashi a abinsa. Da fara'arsa Mallam Usman ya karaso wajensu. Sai dai yana kallon idanun Hilal ya ji kwarjininsa ya masa yawa. Sai da ya daure ya yi masa sallama tare da mika masa hannu suka yi musabaha.
Bayan sun gaisa ya zubawa Zahrah idanu ba ko ƙyaftawa, sai da Hilal ya ji gaba sannan Zahra ta take masa baya.
Mallam Usman ya yi gaba tare da yi wa Hilal jagora zuwa office ɗin shugaban makarantar.
Da sallama suka shiga bayan sun gaisa da Hilal ne Zahrah ta gaishe shi.
Bai san Fuskarta ba, amma ganin kyawon idanunta ya sa ya gane ta, murmushi ya yi tare da cewa.
"Fatima Zahrah Salis Tafarki ko?"
Kai ta gyada masa tare da sunkuyar da kai ƙasa. Ya sake cewa.
"Yau ba niƙab ne?"
Murmushi ta yi wanda har sai da dimple ɗin ta suka lotsa.
Hilal ne ya lalle shi tare da cewa.
"Na ji an ce gobe ne za'ayi tafiyar ko?"
"Eh haka ne."
"To ya tsarin naku yake?"
"Eh iyayen yaran sun ba da yaran da za'ayi da su akwai motar makaranta da za'a tafi da su, akwai masauki da abinci kyauta da za'a basu. Sai dai akwai wasu iyayen yaran da ba yarda su bayar da yaransu, kamar ku kenan to ba za mu ce dole sai kun bayar da yaranku ba sai dai za mu baku adireshin wajen da za'a gudanar da karatun sai ku kawo su akan lokaci."
Takarda mai ɗauke da adireshin wajen ya ɗauko ya bawa Hilal sannan ya sanar da shi jibi da misalin karfe tara na safe za'a gudanar da karatun don haka idan son samu ne sai a kawo ta zuwa karfe takwas da rabi."
Amsar adireshin ya yi tare da yi masa sallama ya mike ya fice.
Da sauri Zahra ta bi bayansa yayin da Mallam Usman ya bi ta bayanta don yana son magana da ita.
Ko da ta ƙarasa har ya shiga motar yana jiran fitowarta. Har ta kai hannu za ta bude murfin motar sai ga Mallam Usman ya zo yana kiranta, hakan ya saka ta karaso wajensa tana jiran me zai ce.
"Mallama Zahrah bai dace na kebe ina magana dake a titi ba, amma zan zo neman izini wajen iyayenki, akan amincewar su na zo ko Allah zai sa mu fahimci juna don ina ƙaunarki fisabilillah."
Hilal ganin ta tsaya tana magana da wani yana zaune a mota yana jiranta, sai ya bawa direban damar ya tayar da motar su wuce su barta wajen.
Hakan ya saka direban ya figi motar suka bar wajen, don dama Hilal ya ga yadda Mallam Usman ke yi wa Zahrah kallon ƙurilla.
Ganin sun tafi ya saka hankalinta ya tashi.
"Ya Salam Ya tafi ya bar ni."
"Na ɗauka Yayanki ne."
"Eh Yayana ne."
"Me ya saka zai tafi ya barki?"
"Ban sani ba Akaramukallah."
"To yanzu ki yi gaggawa ki koma kada na jawo maki wata matsala, tun da kin ga ya yi fushi ya tafi, dama ba wata dogon magana ba ce zan nemi izinin ki ne kawai . Amma ko za ki shiga motata na kai ki gidan.?"
"Ka bari kawai zan samu abun hawa."
Sanin hakan zai iya janyo mata matsala duba da yadda Yayanta ya tafi ya barta ne ya saka shi ƙyale ta.
Karasawa ta yi zuwa bakin titin don neman abin hawa.
Tana tsaye a bakin titi wata mota ta tsaya a gaban ta, mamallakin motar ya fito yana mata magana ko kallonsa ba ta yi ba , har ya gaji ya tafi. Wani m ya tsaya shima bai samu fuska ba ya tafi. Ganin yadda ake kallonta ne ya saka ta yi nadamar fitowarta ba niƙab, don ko a school ma sai ta saka hijabi da niƙab.
Tana tsaya ne don ba ta san ma yadda za ta tsayar da abun hawa ba. Wata motar ce ta tsaya kallon motar ta yi sosai ta tabbatar motar Mansur ne cos mate ɗin ta ne da suka karatu a University tare, wanda ya suka zo suka kai ta asibiti shi da A'isha.
Yana zuge Glass din motar suka hada idanu, sanyayyar murmushinsa ya sakar mata,ita ma murmushi ta yi tare da karasawa wajan motar, murfin motar ta bude ta shiga.
"Aminiya ya na ganki akan titi ke ɗaya ina motarki take?"
"Hmm ba komai Aminin ƙwarai."
Kasancewar su uku haka suke kiran junansu, daga Zahra har A'isha Aminiya yake kiransu su ma suna kiransa da Amini."
Haka ya dinga jan ta da fira ita dai ba ta iya amswa masa ba, daga uhm dai um um.
A ƙofar katafaren gidan na su ya yi parking daidai lokacin da Hilal ke fitowa daga gidan waya na kare a kunnensa.
Cire wayar ya yi daga kunnensa tare da ƙarasawa wurin motar kasancewar glas ɗin motar bakin Glass ne na waje baya hangen na ciki.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*Eid Mubarak to you my fans, Allah ya maimaita mana da alkhairi*
Page1️⃣6️⃣
Cire wayar ya yi daga kunnensa tare da ƙarasawa wurin motar, kasancewar glass ɗin motar baƙin glass ne na waje baya hangen na ciki.
Knocking ɗin glass ɗin motar ya yi. A hankali Zahra ta kalle shi tare da cewa.
"Amini bari na fita ka bar wajen nan da sauri."
Kallon ta ya yi tare da cewa.
" To laifin me na yi da zan bar wajen da sauri?"
A hankali ya zuge glass ɗin motar tare da kallon Hilal. Wani banzan kallo Hulal ya yi masa sannan ya maida kallonsa kan Fatima Zahrah wacce ta sunkuyar da kai. Ɗagowa ta yi ta kalle shi sai da gabanta ya faɗi, ganin irin kallon da yake jifanta da shi. Ya tabbata ba wancan malamin da ya bar su tare ba ne, wannan kuma daban ne, wato ita kowa take kulawa kenan.
"Ke fito ki shiga gida!"
Jinkinta na rawa ta fito daga motar ta tsaya tana kallon Amini.
"Kai ja motarka ka tafi kada na sake ganinka a ƙofar gidan nan."
Wani kallo Amini ya masa yana don ya tanka masa sai Zahra ta yi magana a hankali yadda Amini ne kawai zai ji.
"Don Allah ka tafi mutumin nan fa ɗan yawa ne zai iya tarfa ka a wajen nan"
Ta yi maganar cikin sigar rarrashi. Don haka ya ja motar ya bar Wajen.
"Zo nan!"
Ya faɗa ransa a ɓace yana kallon Zahrah, sanin abinda da abun da zai biyo baya ba zai masa dad'i ba ya sa ta ruga cikin gidan a guje.
Rufa mata baya ya yi shi ma ya koma ciki.
Kamar daga sama suka ha an jeho ta. Gabaɗaya suna zaune a falon iyaye da ƴaƴansu.
Gabaɗaya suka juyo suna kallonta, sallama ta yi masu ba wanda ya amsa a cikinsu, sai Abba da Dady su ma ciki-ciki suka amsa mata sallamar.
Jin yadda ya banko ƙofar ya shigo ne ya saka ta juyawa da sauri ta nufi part ɗin su.
Rufa mata baya yayi da sauri abu ga dogon mutum tana ƙoƙarin rufe ƙofar ya banko ƙofar da ƙarfi wanda hakan ya saka ta yi baya ta faɗi.
Wuyan hijabinta ya cakumo ta miƙar da ita tsaye. A fusace ya fara magana cikin kakkausar murya.
"Gabaɗaya ke ce kika fita zakka a cikin gidan nan, na tsani macen da ke kuka kowane kare da jaki, kin taɓa ganin wani namiji ya zo ajiye wata a cikin gidan nan? Wato sai ke ko? To bari ki ji ba wai na damu da ke ba ne ko ina da matsala da ke ba, babu ruwana dake matsalata ɗaya shi ne zubar da kimar ahalinmu.Don da zaran kin aikata wani abun da zai zubar da Mutuncin zuri'armu. Dama Abin da Aunty Laila take faɗa aka ki gaskiya ne yau na gani da idona. Sai dai zan maki gargaɗi duk sakaran da kika gayyato zuwa gidan nan ni na san abin da zan masa. Duk shashancin da za ku yi ku yi shi a waje amma ba gidan nan ba. Idan kuma ba haka ba ko?"
Kwafa ya yi tare da barin ɗakin bayan ya sakar mata wuyan hijabi. Yana komawa falo ya same su zaune kamar yadda ya bar su. Aunty Laila ce kawai a tsaye, tana ganinsa ta ce.
"Son meye haɗinka da wanan yarinyar ne?"
Ciwon kai ya fara ji saboda dogon maganar da ya yi saboda shi baya so ya yi magana mai tsayi. Don haka bai ce mata komai ba ya nufi upstairs.
Jin mahaifinsa na magana yana sake tambayarsa ne ya sa ya ce.
"Dama na ga da muka tafi can lokacin da za mu dawo ta tsaya da wani saurayi. Na taho na bar su a wajen. Yanzu kuma wani daban ne ya kawo ta ba wancan ba."
"Dama na fada maka yarinyar nan bin maza take yi, ai yau ka gane wa idanunka ai, yarinyar nan har cikin shege ta yi ita da munafukar uwarta suka zubar."
Umma mahaifiyarsa ce ta faɗi haka, Cikin takaici ya ce.
"Dole na ɗauki mataki akanta kafin ta zubar mana ƙimar gidan nan, don koma mene ne sai dai a ce ɗaya daga cikin familyn Muhammad Tafarki."
Yana gama fadar haka ya haura sama har yana tsallake steps.
Ɓangaren Zahra kuwa tun da ya shaƙe wuyar hijabin dake jikinta ta fara jin numfashinta na barazanar ɗauke wa. Haka ta fara komawa da mumfanin nata wanda yake jin ba ta da wata hanyar shaƙar iska. Ko da ya gama faɗarsa ya fice duk ciwon nata ya fara tashi.
Madadin ta tashi ta nemi maganinta sai ta zauna tana ta riskar kuka duk da yadda take numfashi daƙyar. Don kalaman sa sun yi mata ciwo. Tana tunanin me Aunty Laila ta fada masa akanta ne ya har yake cewa gaskiya Sunyi Laila take faɗa.
Yana haurawa sama direct ɗakinsa ya nufa, yana shiga ya fara cire rigarsa, ya saura daga shi sai singileti da dogon wandon dake jikinsa .
Wayarsa ta soma ruri ya duba ya gani Papa ya sa ya ɗaga tare da yi masa sallama. Muryar tsohon ya ji yana cewa ya sanar da Zahrah sammako za su yi sannan ya kira wayar