Showing 12001 words to 15000 words out of 154779 words

Chapter 5 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6261

samu kudin ba.

A ƙafa take tafiya ta yi tafiya kamar kimanin mintuna talatin, a babban tita ta ta tare abun hawa.

Ya tsaya tare da cewa.

"Ina za ki je Hajiya.?"

"Asibiti za ka kai ni, sai dai ba kudi a hannuna sai na shiga ciki zan karbo maka wajen Yayana."
Na

"Amma gaskiya za ki kara Mani kuɗi."

"Ka taimaka mani dan Allah."

"Shiga muje."

Sun fara tafiya ta jikin mirror ya hango Jidderh na goge ƙwalla.

"Hajiya ki yi hakuri sauki na zuwa in sha Allah, waye na ki ne a asibitin?"

"Matar Yayana ce za'ayi wa aiki za ta haihu."

"Ayyah to Allah ya sa ayi a sa'a ki daina mata kuka yau za'ayi aikin ne?"

"Ban sani ba saboda sai an bayar da kuɗin aiki."

"Amma Kada ki ce na cika tambaya, na ga kina cikin damuwa ne kudin aikin ne babu?"

Kai kawai ta ɗaya masa ba tare da ta ce komai ba.

"Amma ina ganin me zai hana ku nemi taimakon Sir Asadullah, saboda mutum ne mai taimakon al'umma musamman marasa ƙarfi, kuma mutane na zuwa wajensa idan suna da matsala, kuma ban taɓa jin wanda ya je bai samu abinda yake so a wajensa ba. Kema ina da yaƙinin za ki samu, in dai kin je duk da ganin sa ba abu mai sauki ba ne."

"Tunda na gaggawa ne ki je kamfaninsa kawai."

"Ban san in da kamfanin yake ba."

"Bari na kai ki. Amma fa security ba za su bari ki shiga ba sai kin samu hanya da taimakon wani."

Godiya ta yi masa kai tsaye ya kai ta har kofar tangamemen kamfaninsa, wanda yake saka ran za ta same shi a wajen.


_Sir Asadullah_

Zaune yake a bayan motarsa motoci biyar ne yau suka fito da su. Biyu gabansa sai biyu a bayan wacce yake ciki. Lafiyayyun motoci ne na alfarma sai ƙyalli suke suna ɗaukar ido.

Jidderh dake can tsaye bayan mai napep ya tafi ta saki baki tana kallon motocin. Ɗaya bayan ɗaya suke cinna hancisu s cikin katafaren kamfanin.

Ganin motar ƙarshe ta shiga ne ana shirin rufe gate ɗin ta ruga a guje za ta shige. Security ne ke ƙoƙarin hana ta shiga yayin da ya dage akan shiga ciki.

"Ke kuma daga ina haka har kike dagewa sai kin shiga ko kamfanin na ubanki ne?"

Wani security dake tsaye yana kallon yadda take artabu da abokin aikinsa ne ya yi maganar.

Wanda ya tare kofar gete ɗin ne ya ce bar ta kawai ko an fada mata yanzu ne lokacin da yake sauraren ƴan maula irin ta, ko tsabar talauci ne ke neman haukata ki kina yarinya da ke?"

Bayan motocin sun tsaya ne ɗaya daga cikin masu tsaronsa ya yi saurin buɗe wa Sir Asadullah murfin motar.

Fararen ƙafarsa ɗaya ya fara zirowa waje, kafin ya fito da ɗayan sai da ya ɗauki sakanni sannan ya fito.

Sanye yake da Suit a jikinsa rigar ciki fara wanda ake hango kwalar rigar sai rigar Suit blue da ya dora sa saman na cikin da wando shi ma blue na Suit ɗin rigar.wuyarsa ɗaure da necktie faru yana da layin blue a jiki. Takalmin ƙafarsa sau ciki baki sai ɗaukar ido suke yi, agogon Diamond dake ɗaure a tsinysiyar hannunsa ya kalla, fuskarsa sanye da farin glass a idanunsa.

Har ya fara taku zai shiga ciki sai ya ji sautin ƙara na mace. Juyowa ya yi yayin da idanunsa suka yi tozali da jidderh dake kokawa tura gate security ya riƙe. Yana juyowa ta ce .

"Yallaɓai!"

Daidai sanda ta fadi ledar hannunta ma ya bugu a ƙasa, kokon ya malale a wajen.

Kuka ta sake tana cewa.

"Yallaɓai ka taimake ni!"

Glass din idanunsa ya cire tare da zuba mata blue eyes ɗinsa.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page0️⃣6️⃣


Glass ɗin idanunsa ya cire tare da zuba mata blue eyes ɗinsa.

Kuka ne kawai take yi idanunta a kansa, mai da dubansa ya yi a wajen security da ya ture ta ta faɗi, kallon garhaɗi da ya masa ne ya saka ya rusunar da kai alamar ban haƙuri kafin ya ce.

"Sir ita ce ta janyo na hana ta shiga na sanar da ita cewa ba yanzu ne lokacin da kake bayar da taimako ba, amma ta kafe sai ta shiga tana ƙoƙarin nuna mani ƙarfi a bakin aikina."

Kallon Jidderh ya yi tare da yi mata alamar ta taso da hannunsa mai rike da glass.

Da sauri ta tashi ko ta kan ledar da kokon da ya zube ba ta bi ba. Ƙarasawa ta yi gabansa sannan ta zube akan guiwarta.

Kallont ya yi ga ta dai kyakkyawar yarinya doguwa fara fuskarta mai ɗauke da dara-daran idanunta da zankaɗeden hanci da ƙaramin bakinta. A daidai wannan lokaci kamata ya yi a ce tana makaranta ba nan ba.

"Me ke tafe da ke?"

Ta tsinkayi muryarsa ya jefa mata tambaya.

"Taimako muke nema yallaɓai ka taimake mu ka rufa man asiri kamar yadda Allah ya rufa maka."

"Me kike so?"

"Yallaɓai matar Yayana ce take kwance s asibiti ana bukatar kudi kimanin Naira dubu ɗari ga shi ba mu da..."

Kafin ta karasa maganar sai ta ji takun takalmin ƙafarsa ya fara tafiya.

" Yallaɓai ka saurare ni don..."

Kafin ta karasa maganar da za ta yi ta ga ɗaya daga cikin mutane da yake tare da su ya ciro bandir na 1k guda biyu, wato dubu ɗari biyu kenan ya ce mata.

"Ga wannan ya ce a baki."

Tsabar ruɗewa da ganin kudin da ba ta taɓa rike irinsu ba ko da ba nata ba sai yau. Ta ɗauka Sir Asadullah share ta ya yi ba ta san ya yi wa ɗaya daga cikin mutanensa alamar ya bata dubu ɗari biyu ba.

Tashi ta yi a guje cikin farin ciki nufi inda ta ga ya bi don ta yi masa godiya, sai wasu dake ciki da alama security ne suka yi mata alamar ta koma . Dube-dube ta fara ko za ta gan shi ba ta gan shi ba kuma ba ta san wace kofar ya shiga ba.

"Allah ya saka masa da alkahiri ya baka a inda kake nema duniya da lahira ya jikan Magabata."

Da sauri ta fice ta kwashi kayan da ta zubar ɗumamen tuwon na nan amma koko ne ya zube. Ta dauka jug da ledar ta zuba cikin ledar kudin ta dukunkune su a hijabi.

Fita ta yi in da ta samu mai nepe ta shige tare da sanar da shi inda zai kai ta.


_Asadullah mansion_

Mom ce ta nufi part ɗin Asadullah don ta lura wasan ɓuya yake son yi da ita, tun lokacin da ta ce dole sai ya auri Fadeela ƴar ƙawarta

Duba wa ta ji gabaɗaya ba ya ɗakin don haka ta fito tana tamabayar ma'aikatan da suke falo.

"Kun ga fitar Asad ne?"

"Eh Hajiya ya yi mintuna talatin da fita."

Jinjina kai ta yi tana shirin komawa part ɗinta sai ta ga an banko ƙofar an shigo. Mami ce fuskanta ba walwala.

"Dama wajenki na zo."

Mumrmushi Mom ta yi tare da cewa

"Sannu da zuwa, ga wuri ki zauna."

Kallon ma'aikatan dake ta gyaran falon ta yi tare da cewa.

"Ku ba mu wuri."

Kowace ta ajiye aikin da take yi ta basu waje."

Dubanta ta mai da ga Mami dake cika tana batsewa ta yi tare da cewa

"Ki zauna mana Hajjaju."

"Ba zama ya kawo ni ba."

"To meke tafe da ke?"

"Na ji an ce kin samar wa Asad matar aure ko?"

"Eh haka ne, ƴar gidan ƙawata Hajiya Lubna ba zaɓa masa."

"Saboda me ye kika zaba masa?"

Murmushi Mom ta yi tare da cewa.

"Saboda duk macce da na kawo masa baya so yake cewa, na kawo masa ƴan mata sama da guda biyar yana bijire wa zancen."

"Amma gida bai ƙoshi ba ai ba za'a kai dawa ba, ga ƙanninsa nan Abida da Maryam duk suna masifar son sa, amma kika tsallake su saboda son zuciya irin ta ki."

"Ba son zuciya anan saboda bai ce yana son su na hana shi ba."

"Kenan shi ya ce yana son matan da kike kswo masa su suka ce suna son sa?"

"Ni ce na ga dacewarsu tare."

"Okay su bawa ƴaƴan da kika tsallake su me suka rasa kyau ne ba su da shi ko ilimi.?"

"Kin ga mu bar zancen nan kawai tunda na riga na zaba masa kuma wannan karon bai Mani gardama ba. Ina ga ki yi hakuri kawai."

"Hakuri fa kika ce, ai ke ce zan ba hakuri don wallahi sai na ɓallo maki ruwa, idan har baki janye zancen auren Asad da wata mace ba ɗaya daga cikin ƴaƴana ba to ki na mai tabbatar maki da lokacin nadamarki ya kusa zuwa.

Kallon mamaki Mom ke bin Mami da shi.


_Fatima Zahrah_

Gabaɗaya ta kasa barci sai hawaye dake tsiyaya daga idanunta. Ga shi ba saman carpet take ba saman tiles ga ƙarfi da ya mata ga sanyi dake ratsa ta banda sanyin AC da ya mata yawa, ba komai da za ta iya lulluɓa da shi, hijabi da ta sanya lokacin da ya saka ta tsallen kwaɗo ba ta san in da ta jefar ba yanzu.

Takure wa ta ji waje ɗaya wanda da ba don alluran da ya yi mata ba da ba abinda zai hana ciwonta tashi.

Shi kam hankalin sa kwance yake barcinsa cikin lallausan bargonsa. Da zarar ta bude baki za ta yi kuka sai ya tuna da gargadi da ya mata sai ta haɗe baki.

Dare mahutar bawa in ji masu iya magana, lokacin da kowa ke barcinsa a gidan cikin kwanciyar hankali amma ita ya sam ba haka ba don kasa barci ta yi.

Har karfe hudu na asuba ba ta yi barci ba. Misali karfe hudu da rabi ya farka. Sakamakon haka ya saba dama.

Hasken ɗakin ya kunna yayin da haske ya gauraye ɗakin. Can ya hango ta kudundune ta juya baya. A tunaninsa barci take yi don haka tashi ya yi ya shiga bathroom. Wanka ya yi tare da ɗaro alwala. Cikin closet din kayansa ya shiga ya shirya cikin jallabiyarsa blue mai gajeren hannu.

Zuwa lokacin ƙarfe biyar ta yi don haka ya ɗauki sallaya don zuwa sallar asuba a masallaci.

Ƙarasa wa ya yi kusa da in da take kwance a ƙasa ya ce

"Ke!"

A hankali ta mike zaune don dana idanunta biyu.

"Tashi ki tafi."

"Miƙewa ta yi a hankali ta fara tafiya, ƙarasa wa ta ji wajen in da hijabinta ke ajiye a ƙasa ta ɗauka ya rike a hannu.

Ya riga ta isa bakin ƙofar ya bude ƙofar ya fita tana bayansa suka fito.

Jinkinta da sauƙi sai zai tsamin da jikinta ke mata.


Suna saukowa Downstairs suka ji ana tafka salati da tafa hannu. Tsabar tsoron da Zahrah ta ji ba ta san lokacin da ta ƙanƙame Hilal ba.



_Jidderh_

Cikin farin ciki ta shiga asibitin fuskarta ɗauke da jin dad'i. Daga nesa ta hango Inna da Isah fuskarsu dauke da damuwa Isah har da ƙwalla yake goge wa

Tana ƙarassa gabansu ta ciro Naira dubu ɗari ta mikawa Isha tana cewa.

"Yaya ga kuɗin na samo."

Ta fada tana saka ɗaukan kudin cikin leda a ta cikin hijabi. Cikin mamaki suke kallonta suka hada baki wajen cewa.

"Jidderh ina kika samo wadannan kuɗaɗen?"

"Yaya zan maku bayani ka je ka biya a fara shirin yi mata aiki."

Da sauri ya nufi kofar ofishin Dr.

Kallont Inna ta yi tare da cewa.

"Jidderh ki faɗa in da kila samo maƙudan kuɗaɗe masu yawa?"

"Ba ni aka ba iyakar su kenan ba rabi ne."

Wani kallo Inna ta mata tare da cewa

"Jidderh kada ki sa zuciyata ta tarwatse mi fada gidan uban da kika samu wadan nan zunzurutun kuɗi haka?"


*Maman Ihsan ce*✍️


09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





.*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page0️⃣7️⃣

Jidderh kibsa zuciyarta ta tarwatse ki faɗa mani gidan uban da kika samu waɗannan zunzurutun kuɗi haka "

Shiru ta yi ta ma rasa ga in da za ta fara yi wa Innarsu bayani. Sai da Inna ta daka mata tsawa cikin fusata ta ce.

"Ba tambayarki nake yi ba?"

Wata nurse ce ta zo ta ce.

"Don Allah nan asibiti ne akwai makiyayata ba mu bukatar hayaniya."

Inna ta fita ranta a ɓace Jidderh ta bi bayanta har waje in da Inna ta zauna akan baranda. Durƙusawa Jidderh ta yi a gabanta tana cewa.

"Mama ashe akwai ranar da za ki iya zargi na, akan zan aikata wani abun da ba daidai ba. Ke fa kika bani tarbiyya kuma...."

Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga mata hannu.

"Ba abinda nake son ji daga gare ki ba kenan, wa ya baki baki kuɗi?"

"Wani mutum ne."

Da sauri Inna ta kalle ta tare da cewa.

"Wani mutum ne a zamanin nan zai ɗauki kudi kimanin Naira dubu ɗari biyu ya baki?"

"Inna na san kin san shi ko ba ki san shi ba na san kina jin labarin da a gari, ba kowa ba ne illa Sir Asadullah ."

Kasancewar ba ɓoyayyen mutum ba ne ya saka Inna ta gane shi, don ko a gidan rediyo da gidan TV da jaridu tana jin labarinsa sosai. Da kuma yayyukan alkhairi da yake yi wa al'umma.

"Ina kika gan shi?"

Nan ta bawa Inna labarin komai tun shigarta nape da yadda ya kI ta kamfanin komai ta faɗa mata.

Shiru Inna ta yi tare da cewa.

"Allah ya saka masa da alkhairi."

Da Amin ta amsa daidai lokacin da Isah ya dawo. Shi ma tambaya ya yi daga in da kuɗin suka fito, nan ta bashi labari kamar yadda ta bawa Inna, shi ma addu'a ya yi masa Sannan y yi Jidderh godiya bisa jajircewarta wajen samo kudin, sannan ya ɗaura da cewa.

"Na na biya kudin komai, shi ainihin tiyata da za'ayi mata dubu arba'in da biyar ne, sai kuɗin gadon jariri kowane rana dubu goma sai kuɗin magunguna shi ne ya saka suka ce mu nemo dubu ɗari.

"To Allah ya sa ayi a sa'a ai ta sha wahala sosai ."

Cewar Inna cikin tausayi take maganar.

Sauran dubu ɗarin da ya rage Jidderh ta miƙawa Isah.

"Ya ga sauran kudin na ga ko rigar jarirai ba ku siya ba, ka siyo kayan baby da pampers da man shafawarsa, powder da flask na zuba ruwan zafi, abinda ya rage sai a siya kayan abinci a ajiye tunda ga mai jirgo bai kamata a cigaba da manejin abinci ba."

Karba ya yi yana farin ciki tare da godiya .


_Fatima Zahrah_

Tana ƙankame da rigar Hilal ta rike jallabiyar jikinsa ƙam tana kallon Aunty Laila da ke zare idanu akansu. Don tana tsoron ƙanwar mahaifin nata sosai, saboda ba ta raga mata, ko kaɗan, tun tana yarinya abu kadan za ta kai mata duka tun tana yarinya har yanzu kuwa da ta balaga ta zama cikakkiyar budurwa kuwa.

"Me nake gani haka, karuwancin naki ya bar waje har cikin gida za ki fara bin maza ɗaki kina lalata da su?"

A lokacin ne Hilal ne ya kalli ƙanwar mahaifin nasa ya ce.

"Take your correction Anty, ni ba fasiƙi ba ne ban aikata komai da ita ba."

"Hilal rashin kunya za ka yi Mani?"

"Ba haka ba ne Aunty na ga kina zargin na aikata wani abu ne kina son ɓata Mani suna a cikin family."

"Ai ba da kai make ba wanan ƙaruwar da ta biyo ka har ɗaki nake tuhuma, je ka sallah kada ka rasa jami'i"

"Aunty ki bar yarinyar nan ta tafi duk yadda kike tunani ba haka ba ne."

'To jeka ɗan albarka."

Ganin zai iya rasa jami'i ya sa ya wuce da sauri, fitarsa ke da wuya Zahara har ta kai bakin part ɗin su ta ji an finciko ta tare da sauke mata tagwayen maruka wanda ya sa ta sakin ƙarar azaba."

Ummu dake shirin tayar da Sallah ta ji ihun ƴar ta , da sauri ta fito ta ƙaraso bakin part ɗin. Daidai lokacin da Aunty Laila ke shirin ƙara saukewa Zahrah mari Ummi ta riƙe mata hannu tare da cewa.

"Kul!"

Da mamaki Aunty Laila ke kallon ta tana mamakin matar da a baya ba ta iya tanka mata ko me za ta yi wa ƴarta kuwa, ta sha dukan Zahrah ba ta hana ta ba amma yanzu har tana mata tsawa.

"Okay ni kike dakatarwa akan na daki Zahrah, to wannan kuma kin yi kaɗan, baki isa ki hana ni na daki Zahrah ba matukar ta yi ba daidai ba sai na ɗora ta a hanya na ba ta tarbiyyar da ta dace."

"Ƴata a tarbiyyancen ta take, 'ya'yanki ke bukatar tarbiyya, kin kasa basu tarbiyya sannan ki ce za ki bawa ƴaƴan wasu? Wanda take da shi ya ishe ta."

Wani kallo mai cike da tsana da ƙiyayya, kafin ta ce.

"Ai duk cikin tarbiyyar ne yasa kike tura ta karuwanci ba ta kwana gida, yanzu tarbiyyar ce ta saka kika tura ta ɗakin Hilal ta je ta kwana yanzu za ta dawo maki ko?"

"Oh ta nan kika ɓullo to ba abinda zai kai ƴata part ɗin Hilal ballantana ta shiga ɗakinsa. Kada ki sake danganta Fatima Zahrah da wannan ƙazamin kalma na karuwanci."

Dariya Sunyi Laila ta yi tare da cewa.

Yadda na ga na gansu sun fito yanzu a jere daga part ɗin sa hijabinta a hannu tana tafiyar tana cije baki idan karya ne kada Allah ya barni na bar wajen nan lafiya."



Kallon mamaki Ummi ke yi wa Fatima Zahrah kafin ta ce.

"Zaharata ki ƙaryata abinda na ji yanzu, a ina kika kwana ba tare da Dada kika kwana ba?"

Kuka ne ya suɓuce wa Zahrah kasa magana sai kuka.

"Zahrahta ina kika kwana?"

Ba ta ce komai ba sai kukan da take yi

"Da gaske ɗakin Hilal kika kwana?"

Kai ta ɗaga alamar eh.

Kasake Ummi ta yi tana kallonta galala ta kasa magana. Juya wa ta yi ta koma ɗakinta.

Tana jin Aunty Laila na cewa

"Ba bakin magana ne?"

Fatima Zahrah ma ɗakin Ummanta ta shiga tana kuka.

Umma wacce dama Sallah za ta yi don haka ta juya gabanta gabas ta tayar da Sallah.

Zahrah ta kasa tashi tana nan durƙushe sai risgar kuka take yi ganin yadda aka mata sharri tana ji tana gani.

Har Ummi ta idar da Sallah daidai lokacin da Yayyun Fatima Zahrah Mahmud da Sadik suka dawo daga masallaci. Sun shigo gaida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login