Showing 87001 words to 90000 words out of 154779 words

Chapter 30 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6289

cikin mamaki ya ce.

"Wanna ba ƴar aikin nan ba ne, me ya kawo ta nan."

Bai bashi amsa ba sai cewa ya yi ya kara masa Doctor Isma'il.

Ba musu ya ciro wayarsa ya sanar da Doctor Isma'il saƙon uban gidansa. Cikin damuwa yake tamabayarsa ya bar shi kwance ko jikin ne, ya ce masa a'a sai ya zo dai.


Asadullah ya saka Sulaiman ya je ya siyowa Jidderh kaya da Hijab, don yadda take ba zai yiwa ma ta iya sanar da su gidansu ba.

Bayan tafiyar Sulaiman ne Barrister ya masa sallama kan cewa sai ya sake shigowa.

Godiya Asad ya masa sannan ya kalli Jidderh ya yi mata alamar ta tashi tsaye.

A hankali ta mike kamar yadda ya bukata. Ya mata alamar da ta bishi . Tana biye da shi a baya suka nufi wani bedroom dake nan downstairs."

Babban ɗaki ne mai ɗauke da saitin furnitures komai na more rayuwa akwai.

Kai tsaye ya nufi bathroom tana biye da shi a baya.

Sai da ya haɗa mata ruwa mai ɗumi, ya yi mata alama da ta yi wanka. Ya nuna mata towel sabo a cikin ledarsa sabulu komai har ma man goge baki sannan ya fita.


Bayan Sulaiman ya dawo da kayan ne ya karba ya nufi ɗakinta. Ya ajiye kayan saman gado ya duba dogayen riguna ne kala uku da takami da Hijab.

Ƙwanƙwasa ƙofar ya yi ya ji shiru sai ya tuna da yanayinta. Don haka sai ya bude ƙofar a hankali.

Hango ta ya yi tsaye kamar yadda ya bar ta . Da alama ba ta san yadda za ta yi ba.

"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un, me yake faruwa da ƴar mutane?"

Shigowa ya yi yana yi mata body language yadda za ta gane abinda za ta yi .

Bayan ya ƙara ruwan zafi ne sai ya cire rigarsa ya rage daga shi sai singileti. Wandon ma ya cire ya saura daga shi sai gajeren wando.

Karasawa ya yi ya goge baki sannan ya yi wanka yana nuna mata yadda za ta yi wanka yana nuna mata tana kallonsa. Sai da ya gana ya yi tsamo-tsamo sannan ya haɗa mata wani ruwan ya ciro sabon brush ya mika mata yana mamakin yadda cikin ƙanƙanin lokaci komai ya shafe a cikin kanta.

Yana miƙa mata brush ɗin ya ɗauki kayansa da ya cire, sai ta ɗaga rigarta za ta tuɓe a gabansa. Ba shiri ya yi hanyar fita da sauri har yana cin karo da ƙofa.


_Zahrah_

Sanye take cikin doguwar rigar abaya shuɗi. Ta yi rolling da mayafin abayar. Ta yi matukar kyau sosai ba kaɗan ba, duk da ita ba ma'abociyar kwalliya ba ce powder kawai ta shafa sai lips glow wanda ya saka pink lips ɗin ta ke shinning Sanyayyaen ƙamshin turerenta ke tashi daga jikinta. Ta fito daga part ɗin Umminta

A babban falon gidan ta hadu da ƴan matan gidan. Nabeela da Kusar sau harararta suke yi, kausar na cewa

"sai neman mazan tsiya kullun cikin kwalliya da ƙamshi."

Nabeela ta ce.

"Wallahi Ammar ya fi karfinki ba za ki taɓa samun namiji wanda ya kai Yaa Ammar ba, sai dai ku ji labarinsa yana can da amaryarsa a UK wata kila ma idan a gidan nan ne ki ga ana taro."

"Sai dai ayi da ke dan ni kin san na mutu a son Yaa Hilal."

Kausar ta faɗa tana zubawa ƴar uwar ta ta idanu.

Harara ta watsa mata tana cewa

"Idan za ki cire idanunku akan my Hilal ki cire, don na wa ne shi. Ai Yaa Ammar ɗin ma fa ya haɗu duk da bai kai Yasa Hilal ba amma shi ma mijin nunawa sa'a ne."

Nan suka fara sa'insa Maryam dai kallinsu take tana murmushi yayin da Nadeeya ta ce

"Iska na wahalar da mai kayan kara, ku dinga faɗa akan Yaa Hilal wanda ko kallon banza ba ku ishe shi ba. Da ni ma na ɗaurawa kaina son sa amma tun da na ga alamar ba zan samu soyayyarsa ba na cirewa kaina dakon wahala."

Maryam suka kalla kasancewar ita ce suka fito ciki ɗaya da Hilal ya sa Nabeela cewa

"Maryam ba ki taba jin ya ce ga wacce yake so ba?"

Taɓe baki Maryam ta yi tare da cewa.

"Wake sanin halin da yake ciki, ko Mummy jiya da ya shigo na ji tana masa fadar cewa yana nuna halin ko in kula da kowa har da ita ba ta sanin halin da yake ciki ta ce dole ya fitar mata a cikin ƴan matan da suke sonsa har da ku ta ambata amma budar bakinsa ya ce shi bai ga maccen da ta masa ba da zai sure ta ba."

Nadeeya ta kece da dariya tana cewa

" ku na jin..."

Ƙasa karasawa ta yi sakamakon ƙamshin turarensa da suka ji, alamar yana kusa da su kenan. Nan kowacce ta yi shiru suka dakar da firan ballantana dariya, kamar ruwa ya ci su haka suka yi tsit.

Jin takunsa kamar yana nufo un da suke ne ya saka kowacd ta juyo ta kalle shi. Ƙananan kaya ne a jikina ya zuba hannayensa a cikin aljihun wandonsa. Fuskar nan tamau ba fara'a kamar kullun.

Kowacce ta kasa ƙwaƙƙwaran motsi. Don sun san halinsa idan ya samu suna hayaniya ba karamin aikinsa ba ne ya zare belt ɗin wandonsa sai kowacce ta ji jiki.

"Kausar ce ya sake kallonsa hararar da ya wurga mata ne ya saka ta sunkuyar da kai da sauri.

"Gyara mun ɗaki."

Abinda ya ce kenan ya nufi ƙofar fita cikin takunsa na mazantaka.

Gabaɗaya suka amsa da to tare da masa a dawo laflya. Bai tanka masu ba ya fice .

Sai da suka tabbatar ya yi nisa sannan Maryam da Nadeeya suka ƙyalkyace da dariya. Maryam ta ce.

"Yanzu kuka gama ciki baki akan son da kuke masa, amma yana fitowa kuka yi kamar ruwa ya ci ku a haka za'ayi soyayyar?"

Nadeeya ta amshime da cewa.

Ni ma haka na gani da sai wata ta tashi ta karasa wajensa tana tamabayarsa fita za ka yi ko na zo na raka ka ne?"

Kausar ta dafe ƙarji tana cewa

"Wace ni, ai sai ya ci ubana la'ada waje."

Nabeela ta ce.

"Na taɓa gwada wa sau ɗaya na tare shi da niyyar ya rage mani hanya zai fita, ai kafin na yi magana kallon da na ga ya mani sai na daburce na rasa ta cewa."

Dariya suka yi Maryan ta ce.

"Ya Hilal kenan shi ake kira kamar maza tana ga mazuru ko ba faɗa akwai mugun kallo."

Dariya suka yi kafin suka su huɗun suka nufi ɗakinsa don gyara masa.


Zahrah da ta shiga Part ɗin Kakanninta ta tarar da Papa yana tsaye a falo yana cewa Dada ta fito su tafi.

Da sallama a bakinta ta shiga Papa ya amsa yana kiran sunanta tare da tambayarta ya karfin jiki. Ta amsa a Alhamdulillah.

Tana shiga ɗakin Dada ta same ta tana yafa mayafinta.

"Dada fita za ku yi ba ki ce na shirya mu tafi tare ba?"

"To tun da kin zo ai sai ki juya mu tafi ."

Ɗakinta ta shiga ta ɗauko facemask ɗin ta ta saka, a tare suka bar part ɗin.

Papa na gaba Dada da Zahrah na baya.

Wata mota ta ga sun nufa wacce ba ta san motar a gidan ba, ba ta yi magana ba tana jiran su ƙarasa.

Papa ne ya buɗe gidan gaba ya zauna gefen mai zaman banza.

Dada ta bude bayan motar ta shiga, Zahrah ma ta shiga ciki. Ƙamshin da ta ji ne ya haifar mata da faɗuwar gaba, da sauri ta ɗaga kai ta kalle shi, suka hada idanu ta cikin madubin dake cikin motar. Gabanta ya tsananta faduwa don ba ta san shi da motar ba, kuma Allah bai bata ikon tambaya ba.

"Ita kuma wannan fa ina za ta je ko akwai sa'anta anan ne da za ta bi mu?"

Papa ya ce.

"Ba ta san in da za mu je ba ka san ta saba fita da kakar ta ku shi ne ta biyo ta."

Harara ya watsa mata tare de cewa.

"Get out!"

Ya faɗa a tsawace. Yunƙurawa ta yi za ta fita Dada ta rike ta tana cewa.

"Wallahi ba za ta fita ba akan me ba na son takura ehe."

Zai yi magana Papa ya ce .

"Ka ja mota mu tafi ka san gaba za mu je daga nan."

Kasancewar baya yi wa Papa musu akan komai ya saka ya yi shiru . Zahra kam shirin fita take yi Dada ta ce ki zauna ba inda za ki je."

Ita kanta ba ta so ba don da ta san ba direba zai kai su ba ko da wasa ba za ta biyu Papa ba

Kunkuni take yi kuma ya ganta ganin facemask din da ta sa yana motsawa.

Kwafa kawai ya yi tare da yiwa motar key yana cewa.

"Idan kika shiga hannuna sai kin faɗa mani abin da kike cewa."

Ba abinda ta ce ba na son sharri."

Dada ta faɗa cikin fada.

Tafiyar mintuna talatin suka yi kasancewar a a hankali yake tuki.

Wani tangamemen gate ya tsaya remote ya danna dai gate ɗin ya wangale kansa, ya danna hancin motar a ciki.

"Ma sha Allah."

Shi ne abinda Dada da Papa suke faɗa, Zahra ma haka ta ce a zuciysryarta. Don babban gida ne mai girma wanda ya ƙawatu da abubuwan more rayuwa.

Dada ta ce

"Gida ya kammala saura a ajiye iyali, ba a abinda ya rage maka yanzu tun da ka kammala burina na ga auren wannan tuzurun."

"Haba Dada ni ne tuzuru?"

Kafin su shiga zagayawa suka fara yi har suka iso wani garden, wajen gwanin sha'awa ha waken hutawa nan ga kayan marmari nan daga gefe can kuma ga swimming pool, gafe ga wani gado na kwanciya yana ɗan kaɗawa.


Ciki da suka shiga a babban falon wanda ya gaji da haɗuwa.

Cikin tsautsayi Rigar abayar Zahra ya ɗan harɗe mata ƙafa lokacin da za ta bi su upstair, kifawa ta kusa yi wanda cikin ikon Allah ba ta faɗi ba sai dai ta ture wani glass da fulawa masu kyau ne ciki, wanda hakan ya saka suka tarwatse, ƙarar ya janyo hankalin su suka kalli abinda ya fashe wanda aka ajiye shi a gefen benen.

Kallon Hilal ta yi ta ga ya zuba mata rikitattun idanunsa masu firgita ta , yana aika mata da wani kallo. Gabanta ne ya fadi ta fara ja baya za ta shiga cikin fasassun glass ɗin


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z






*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️





❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect

*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*



*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*



Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.


Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.



Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩


1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more



Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.


*YAR GIDAN TAFIDA*


Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.



*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.

Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯





Page4️⃣4️⃣


Kallon Hilal ta yi ta ga zuba mata rikitattun idanunsa masu firgita ta, yana aika mata wani kallo. Gabanta ya faɗi ta fara ja baya za ta shiga cikin fasassun glass glass ɗin.

Ba abinda take tunawa sai ranar da ta shiga ɗakinsa Dada ta aike ta sai ta ga wani frame an zana butterfly cikin tsautsayi ta taɓa wanda hakan ya saka frame ɗin ya faɗo. Da ya ga ɓarnar da ta yi har ya saka ta punishment wanda tsabar azaba dai da ciwon athma ɗin ta ya tashi ta sume don wahala. Ga shi yanzu ta sake masa wata ɓarnar wacce tafi waccen ta san halinsa dole sai ta yabawa a aya zaƙinta.

Hawaye ke bin fuskarta tana sake ja da baya. Dada da Papa na cewa ta dakata kada ta ji wa kanta ciwo za ta taka kwalba. Amma ina ba ta ma san me suke cewa ba tsoron Hilal ne fal a zuciyarta wanda ta san ba raga mata zai yi ba. Ta masa ɓarnar da ba ta kai wannan ba ya sumar da ita wanda har ta kasa tafiyar da ƙafarta ballantana wannan .

Zame facemask dake fuskarta ta yi za ta bashi hakuri ganin yana matsowa in da take

Ɗaga ƙafar da zata wanda idan ta aje ƙafar za ta ɗora shi ne akan wani tsinin kwalba da ke tsaye a sama, cikin zafin nama ya janyo ta da ƙarfi ta faɗo jikinsa. Bakinta ya mannu da ƙirjinsa. Tsabar firgita ba ta san ta ƙanƙame shi da hannayenta duka biyu ba. Idanunta a rintse suke gabanta na faɗuwa jiran hukuncin da zai ɗauka akanta kawai take jira.

Kalaman da ta ji a ƙunnenta ne suka firgita ta ta zare idanu tare da sakinsa ba shiri .

"Ban yi mamaki ba tunda kin saba bin maza kina haɗa jiki da su, to ni ba ƴan iskan samarinki ba ne da kika saba haɗa jiki da su kuna iskanci, kuma sai kin faɗa mani uban da ya maki ciki kika zubar a kwanakin baya."

Ca baya kawai take yi tana kallonsa hawaye na wanke mata fuska tana girgiza masa kai.

Kasancewa tana jikinsa ya yi maganar kuma a hankali ya yi hakan ya saka Dada da Papa ba su ji mugayen kalaman Hilal ɗin ba .

"Zaharah lafiya kuma?"

Dada ta tamabya ganin yadda take girgiza kai tana kuka. A tunanin su Papa sun ɗauka rumgumar Hilal da ta yi ya saka take ja baya tana tsoronsa kamar yadda yaran gidan sun tabbatar kowa na tsoronsa.

"Ki kwantar da hankali Fatima Zahrah ai tsorata kika yi ba komai ba ne."

Cewar Papa lokacin da ya karasa ya riko hannunta. Cikin kuka ta ce.

"Papa wallahi ni ba ƴar iska ba ce ban taɓa aikata fasiƙanci ba."

"Kada ku damu mun sani ku kwantar da hankalinki."

"Zo mu shiga ciki mu ga ni ko?"

Girgiza kai ta yi alamar ba za ta shiga ciki ba, rarrashinta suke yi ta yi shiru ta ce.

"Zan jira ku a nan."

Ganin ta kafe Papa ya ce .

"Ba za ki shiga ki ga gidan Yayanki ba?"

Murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo ganin yadda Kakannin na su suka damu don haka ta ce .

"Zan biyo ku yanzu bari na kwashe fasassun glass ɗin nan."

Tana dube dube-dube idanunta suka sauka akan abun shafa har da kwandon zubawa ta hanga a wani corridor da za ta sada ta da wata hanya wanda ba ta san hanyar ina ba ne.

"Papa mu je?"

Ya faɗa yana masu jagora zuwa sama yayin da Dada ke ta mitar cewa ƙafarta na mata ciwo ya kawo ta in da za zata wahala.

Zara kuka take yi tana share wajen zuciyarta na mata zafin Kalaman da Hilal ya faɗa mata.

Tambyar kanta take yi shin me ta yi wa Ahalinta ne da zafi haka, gabaɗaya kowa na mata kallon ƴar iska watsatstsiya Kakanninta ne kawai ta san cewa ba sa mata wannan kallon sai iyayenta da yayunta.

Da farko Aunty Laila wacce ta kasance ƙanwar Mahaifinta uwa ɗaya uba ɗaya ce ta fara jifarta da kalmar ƴar iska. Sai Mummy mahaifiyar Hilal da ita ma ta bi bayan Aunty Laila suke kiranta da karuwa. Haka ma Umma , Hawaye Masu zafi suka zubo mata.

Sai da ta share wajen tass ta kwashe fasassun glass ɗin da kwalaben ta samu wuri ta rakuɓe ta kasa haurawa saman.

Takunsa ta ji yana saukowa kafin ta ankare har ta gan shi a gabanta.

"Ba ke kin iya barna kamar ɓera ba, to wannan karon ba ƙyale ki zan yi ba, albarkacin idanun du Papa kika ci ya saka ban maki komai ba, amma ina mai tabbatar maki sai kin biya ɓarnar da kika yi."

Murya na rawa ta ce.

"Nawa ne zan biya?"

"Au har kina da kudin biya ne? Oh na manta ko wace ce ke kin sani kuɗaɗe wajen gasar karatun Alkur'ani ko? Sannan ga na samari da ake baki. To sai dai wannan ba da kudi za ki biya ba."

Da sauri ta kalle shi ta ce.

"Da me zan biya?".

Shiru ya yi kamar ba zai ce komai ba kafin ya ce.

"Ba kuma da jikinki za ki biya ba, domin kamar yadda kika..."

Kuka me sauti ta sake wanda ya saka ya dakata da zancen da yake yi

"Kukan uban me kike yi ƙarya aka yi maki ne, ina a gabana Aunty Laila ta ce ciki kaka zubar na dauke ki na kai ki asibiti Doctor ya sake tabbatarwa ƙwayoyin zubar da ciki kika sha ciki ya zube. Dan an yi magana ki dinga yi wa mutane kuka ƴar iska mai fuska biyu ana ana maki kallon nitsatstsiya mai kamun kai saboda ilimin addini da kike da shi alhakin bakya aiki fa duk Musa a baki ne Fir'auna a zuci."

Sautin kukan ta ne ya ƙaru wanda ya saka har ta ji numfashinta baya fita daidai.

"Uban me na maki kike kuka? Na dake ki ne, yanzu zan maki dukan tsiya a wajen nan kiyi kuka mai dalili."

Ya yi maganar yana ɗora hannunsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login