Showing 123001 words to 126000 words out of 154779 words
Aunti Laila ta juya tana kallon Hilal da ya haɗe fuksa.
"Ka je yanzu bangaren Papa yana son ganinka."
Sai da gabansa ya fadi amma ya dake ya riga ta fita yana gaba tana baya.
Da sallama ya shiga falon, amma ganin dukkan iyayensu a falon ba da yaran gidan ba sai shi kuma ga abinda Sunyi Laila ta aikata ya saka shi shiga tashin hankali, sai dai kasancewarsa yana da jarumta ya saka ba wanda zai kalle shi ya gane tashin hankali ga yake ciki.
A hankali ta taku ya zauna bayan su Abbi kasancewar sune karshe.
"Hilal"
Papa ya kira sunansa, ɗago kai ya yi ya kalli Papa wanda idanunsa suka canza launi zuwa ja, kafin ya ɗauke kai ya ce.
"Na'am."
"Ashe kai mutumin banza ne ban sani ba, Haba Hilal ka yi aure mana idan kana bukatar mace Meye amfanin aikata fasikanci ."
"Ban taɓa aikata fasiƙanci ba, kuma ba zan aikata ba in sha Allah."
Kowa dake falon sai da ya kalle shi jin abinda ya ce.
Papa ya kalli Abbi ya ce.
"Salis ka bashi Camerar nan ya gani."
Abbi ya mika masa ya karɓa yana dubawa .
Ganinsa ya yi dauke da Sury akan cinyarsa.wanda idan ba shi ba ba Wada zai ce ba rumgumar ta ya yi ba.
'Lallai sai na illata yarinyar nan,, wato da na ganta a garden wato hoton mu ta ɗauka, lallai ta tafka babban kuskure don sai na illata ta.'
"Za ka iya rantse Mani cewa wannan ne karo na farko da ka kawo mace a gidan nan?"
Shiru ya yi yana tuna Zahrah ta san cewa ya kawo Alexandra tabbas ita ta fada masa ga kuma hoto ta ɗauka.
Bai gama tunanin ba ya ji Papa na cewa.
"Yau Alhamis gobe juma'a zan zartar da hukuncin da na ga ya dace kuka zai kawo daidaito a cikin zuri'a"
Yana gama fadar haka ya mike ya nufi part ɗin sa kafin ya shiga ya ce.
"Gobe kowa ya shirya karbar hukuncin da zan yanke ko ya yi maku dadi ko kada ya yi maku biyayya dole ne ga umarnina. Kowa ya tashi ya tafi na sallame ku."
A fusace Hilal ya bar part ɗin, burinsa ya yi ido biyu da Zahrah, yadda ta saka ya shiga cikin wannan takaicin kowa ya shiga damuwa musamman kakanninsu suka ji haushinsa sai ya tabbatar ta ji a jikinta.
Cikin sanyin jiki Daddy da Mummy suka mike Mummy na cewa.
"Allah ya wadaranki ki Zahrah."
Dada ta yi saurin cewa .
"Akan me za ki za ki yi kokarin aibata ta, ai godiya ya kamata ki yi mata a dalilin ta aka gano banzar halin da yaron nan yake yi a ɓoye yanzu za'ayi wa tufkar hanci."
Rai s ɓace Mummy ke shirin sake yin magana Daddy ta daga mata hannu ta yi shiru ta fice rai a ɓace, nan kowa ya watse aka bar Dada ita kaɗai a falon.
Ammin Zahrah ta shiga damuwa sosai ba kaɗan ba, da suka shiga cikin falonsu Ammi ta kalli Abbi ta ce.
"Zahrah ta ɓallo mana ruwa."
Ta yi maganar cike da jimami.'
"Ki kwantar da hankalinki ba wani ruwa da ta ɓallo mana, a dalilin haka kowa zai san abun da yake aikatawa a dauki mataki akansa."
"To yanzu wane irin mataki Papa zai ɗauka?"
"Allah masani, sai dai goben mu ji hukuncin da zai ɗauka. Tabbas ban taɓa ganin Papa cikin irin wannan ɓacin rai haka ba, kuma fa alama hukuncin na san ba zai yi wa kowa dad'i ba."
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*
Page5️⃣9️⃣
Allah masani sai dai goben mu ji hukuncin da zai ɗauka. Tabbas ban taɓa ganin Papa cikin irin wannan ɓacin rai haka ba, kuna da alama hukuncin na san ba zai yi wa kowa dad'i ba."
Jingina lamarin Ummi ta yi kafin ta ce.
"Tabbas da alamar haka."
_Zahrah_
Horn ta yi a bakin gate yayin da security ya bude mata ƙofar ta shigo da motarta ciki .
Hilal dake tsaye a harabar gidan ya hangi shigowarra. Dama ita yake jira ya hadu da ita.
Kai tsaye ya nufi parking space ɗin, tana gama parking ta turo murfin motar za ta fito. Tana saka ƙafa ɗaya a waje ta ganshi tsaye rike da murfin motar fuskarsa a murtuƙe.
Ɗaga niƙab dake fuskarta ta yi don ya samu damar ganinta yadda ya dace, ita a tunaninta bai gane ta ba ne tun da ko magana ba ta haɗa su, Gaisuwa ma idan ta masa baya amsawa. Hakan ya saka ta yi tunanin bai gane ta ba ne tun da ya zo wajen motarta ya tsaya.
Sai dai tana cire niƙab ɗin fuskarta ta bayyana ya shaƙo wuyan hijabinta ya murɗe. Nan take hijabinta ya shake mata wuya ta fara fafutuka da rayuwarta, Idanunta sun firfito waje, sai da ya ga kamar za ta dauke numfashi sannan ya sake ta ta fadi ƙasa yaraf. Kin yi kuskure na shiga gonata, har kin yi tasirin idanun da za ki ɗauki photo na ki kai wa Papa?"
Ɗago ta ya yi ta mike tsaye tagwayen maruka biyu ya sauke mata a fuska, kafin ya yi jira da ita ta fadi a wajen ta ƙoje sai ga jini ya fara zuba daga hannunta.
Zare belt ya yi daga jikin wandonsa yana cewa .
"Ke ga munafuka ko? Mai kai rahoto wallahi wata rana ko an ce ki shiga harkata ba za ki shiga ciki ba."
Belt ɗin ya rike ya dinga dukanta da shi, ihun azaba da take yi ne ya saka ma'aikatan gidan ƙsrasowa wajen don ganin meke faruwa.
Carko-carko suka yi suna kallon yadda yake dukan Zahrah kamar Allah ne ya aiko shi.
Tausayin ta cika su, don sun san cewa Zahrah ba ta da hatsaniya ko wani abu da zai saka ya dake ta, hasalima tafi sauran yaran gidan nutsuwa, hankali, da sanin ya kamata.
Take jini duk ya ɓata farin hijabin dake jikinta. Ganin da suka yi ba su da zarrar da za su tari gabanshi ne ya saka ɗaya daga cikin direban gidan ya ruga don kiran wani daga cikin gidan.
Zuwa lokacin Zahrah ko motsi ba ta yi jikinta duk ya farfashe da duka ta daina motsi kamar matacciya, sai da ya ga ta daina motsi sannan ya bar ta nan kwance, motarsa ya shiga ya fige ta, da sauri maigadi ya wangale masa gate saboda tsorata da yanayinsa. Ya bar gidan a guje.
A babban falon gidan ya yi sallama sai dai ba kowa a falon, don haka ya karasa part ɗin Dada ya ya yi sallama .
Dada ta amsa tare da bashi izinin shigowa.
"Dada ku kawo ɗauki soja zai kashe Zahrah."
Salati Dada ta saka tana ƙwalawa Papa kira, ba shiri ya fito yana tambayar me ya faru.
"Wai Hilal ne zai lashe Zahrah."
"Suna ina?"
Papa ya tambaye direban.
"Suna parking space don daowarta kenan."
Da sauri suka fita don zuwa parking space, duk da kasancewar su tsofaffi ne amma suna da ƙwarin jiki.
Suna ƙarasowa parking space daidai lokacin motar Mahmud ta karaso. Ganin suna cikin tashin hankali ya saka ya fito daga cikin motar da sauri, ya bude baki da niyyar ya tamabaye su abun da ya faru sai ya yi tozali da Zahrah dake kwance ba ta motsi.
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un."
Shi ne kalmar da ya furta ya karasa wajen da take kwance yana cewa.
"Accident ta yi ne?"
Ba wanda ya iya magana don Dada da Papa ma sun kiɗime da ganin halin da suka gan ta a ciki.
Mahmud ya durkusa ya ɗauke ta yana cewa.
"A kai ta asibiti mana."
"A'a ka kai ta ɗakinta dake ɓangarena zan kira Doctor ya zo da kayan aiki, zai yi mata duk abinda ya dace."
Daga haka ya yi gaba Mahmud ya bi bayansa suka koma cikin gida.
Ɗakinta dake bangaren Dada ya Mahmud ya kai ta. Akan gadonta ya shimfidar da ita. Har lokacin ba ta motsi.
Daidai nan Papa ya kira Doctor a waya, bayani ya yi masa ya ce ya zo da kayan aiki gida.
Nan Doctor ya ce masa ga shi nan zuwa.
Mahmud ya kalli Papa cikin damuwa ya ce.
"Me ya same ta haka ne?"
"Wai Hilal ne ya yi mata duka ."
Zaro idanu Mahmud ya yi yana cewa
"Wane irin duka ne haka kashe ta ya yi niyyar yi ko me?"
Fita daga dakin ya yi da sauri zuciyarsa na masa zafi, ganin ƙanwar ta sa a cikin wannan halin ba karamin tashin hankali ya saka shi ba, duk da cewar ba ƙaramin abu ba ne idan aka ce Hilal ya yi wa mutum irin dukan nan, saboda yana da zafi, amma ya tabbata Zahrah ba za ta aikata masa laifin da zai yi mata irin wannan dukar ba, Gara kowa a gidan nan idan ya dake su amma ban da Zahrah. Ba za ta yi masa laifin da zai mata haka ba.
Yana shiga part ɗin ya dinga ƙwalawa Abbi Kalifa, da kuma Ammi.
"Abbi Ammi."
Ya fada cikin daga murya.
Ba shiri Abbi da Ammi suka fito daga cikin falon, don su san wannan kiran ba na laflya ba ne, musamman jin Muryar da sun san ba komai yake magana a kai ba saɓanin Sadik.
"Lafiya Mahmud.?"
"Zahrah ce Hilal ya yi wa mugun duka ko motsi ta kasa yi."
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un."
Ummi ta fada cikin tashin hankali.
Gabaɗaya suka fita zuwa part ɗin Dada har dakin Zahrah suka shiga . In da suka tarar da Papa da Dada akanta.
Shigowarsu ba jimawa sai ga ga Daddy da Mummy sakamakon kiran da Papa ya yi masu.
Suna shigowa suka zuba idanu akan Zahrah, sai Ga Umma da Abba sai Aunty Laila a ƙarshe.
Kowa ya kasa yin magana suna ta tambayar kansu abinda ya dame ta.
Gyaran murya Papa ya yi tare da kallon Daddy ya ce .
"Kun ga abinda yaron nan Hilal ya aikata wa yarinyar nan ko? Akan abu da ba t d masaniya akai, lallai sai ya biya bashin abinda ya aikata, sai ya gyara abinda ya ɓata."
Kowa ya kasa magana Ummin Zahrah sai zubar da ƙwallar tausayin ƴarta take yi.
Doctor ne ya shigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama.
Gabadaya suka amsa masa ya shigo hannunsa dauke da kakar kayan aikinsa.
Gaisawa ya yi tare da suka gaisa sannan Papa ta ce sun fita su ba Doctor wuri ya yi aikinsa."
Gabaɗaya suka yi daga dakin Ummi ta nufi part ɗin su da sassarfa ƙwalla na ciko mata idanu.
Ganin haka Abbi da Mahmud suka bi bayanta. Tana shiga ciki ta tarar da Sadik wanda dawowarsa kenan ya ga ba kowa a part ɗin.
Cikin tashin hankali ya nufi mahaifiyarsa yana rike hannunta ya ce
"Subhanallah! Ummina ya aka yi ko mutuwa ce ka yi ban sani ba."
Kasa magana ta yi sai kuka , Mahmud ya rike hannunta yana cewa
"Dan Allah ku yi hakuri Ummi ba cewa aka yi ba za ta tashi ba, in sha Allah yanzu za ta farfaɗo tun da Doctor ya zo ,"
Sai a lokacin hankalin Sadik y je ga Zahrah yana cewa.
"Ina Zahrah ne ya same ta, ba dai ciwonta ne ya tashi ba ko?".
Haka y jera masu tambayoyi, yana kallonsu cikin tashin hankali. Mahmud ne y yi karfin halin cewa.
"Yaa Hilal ne ya yi wa Zahrah dukan mutuwa ga ta can ɓangaren Dada ko motsi ta kasa yi."
"What's!"
Kai Mahmud ya jinjina masa alamar tabbatar da cewa maganarsa haka take .
Ciki. Fusata Sadik ya fara magana.
"Wannan wani irin cin zali ne, na tabbatar da cewa Zahrah ba za ta shiga sabgarsa ba, na ji shaidar cewa Zahrah ko mu fa muke uwa ɗaya uba ɗaya ba za ta aikata mana abun da za mu dake ta ba, ballantana shi da yaran gidan ne tsoronsa."
Nisawa ya yi kafin ya ce .
"Yanzu wane mataki akan ɗauka akan abinda ya yi wa Zahra.?"
"Kai ma ka san ba wani matakin da za'a dauka akansa tun da ya zaba hukunta yaran gidan sai dai a ce wannan karon ya uku tsauri da yawa."
Da mamaki Sadik ke cewa .
"Ai ko wannan bai dace a yake shi ba, don na ga alamar gabadaya gidan nan shakkar sa ake yi, ba mai iya dakatar da shi . Zan same shi na fada masa gaskiya duk abinda zai faru ya faru."
Yana gama fadar haka ya ce.
"Ina za ka je?"
"Zan je na samu Hilal ne sai na fada masa duk maganar ta zo bakina, tunda anan gidan ba mai iya magana , ka duba yadda ya saka Mahaifiyar mu kuka ba zan ƙyale ahi ba. Sai dai ya kashe ni."
'idan ka fita a nan sai ranka ya ɓaci "
Cewar Ummi tana goge hawayen fuskarta, kafin ta cigaba da cewa
"Na tabbatar da cewa Papa da Dada ba za su bar shi ba har shi ba."
Nan da daina kuka sabida sanin zuciyar zuciyar Sadik , kuma ba su fada masu komai abinda ya saka ya dake Zahrah. Sai da Ummi ta saka wa ta ya Zahrah na warkerwa zata kwshe yaranta su bar gidan ne ta gaji.
_Hilal_
Bayan ya bar gidan kai tsaye sabon gidansa ya nufa, zuciyarsa a cunkushe yake, abinda Zahrah ta yi masa ya kunyata yau, tun da yake a rayuwarsa bai taɓa jin kunya irin na yau ba, sannan Papa yana cewa zai yanke hukunci akan wannan al'amari to wane irin hukunci yake shirin yanke wa akan sa oho.
Ummi duk juriya da kawaici yau sai ta kasa hakura, don haka ta koma part ɗin Dada dan ta dubo halin da Autarta take ciki.
Kamar wacce aka tsikara ta nufi kofar fita, Abbi dake cikin damuwa shi ma ya kalle ta ya ce.
"Ina zuwa kuma yanzu?"
"Am zan je na duba ko ta farka ne."
Jinjina mata kai kawai ya yi, ta nufi hanyar fitowa, a babban falon ta ji muryar su Umma da Aunty Laila sai Mummy suna tattaunawa. Aunty Laila na cewa.
"Duk da ban ji dadin abinda Hilal yake aikata wa ba, amma na ji dadin dukan mutuwar da ya yi wa shegiyar yarinyar nan."
Umma ta daura da cewa
"Dama ai sakamakon abinda ya kamata ayi mata kenan."
"Ba ku kai ni tsanar yarinyar nan ba wallahi."
Ran Ummi ya ɓaci da jin yadda suke aibata mata yarinya suna zaginta akan abun da ba laifinta ko da sanin ta ne ta aikata ba. Cikin ɓaci rai ta ce.
"Don Allah me yarinyar nan ta tsare maku a duniyar nan ne, Meye laifinta akan abinda ya faru? Ita kanta ba da saniya ne ta aikata wannan abun na daukar photo ba. Ga ɗanku nan da ya kamata ku mayar da hankali wajen bincikar lamuransa da mu'amalarsa da mutane don ku gane me yake aikata wa ba, shi ne Idanun ku ya rufe ba ku ga laifinsa ba sai na Zahrah ko?"
Murmushin takiaci ta yi tare da cewa.
"Ba yadda za ku yi da mu sai dai cikin..."
Abbi ya kira sunanta da ƙarfi wanda hakan ya saka ta kasa karasa maganar da take da niyyar yi. Duk abinda suke yi ko suke cewa akan ta da yaranta ba ta taɓa cewa komai ba sai yau , yau din ma don ranta a nace yake ne, tana ƙoƙarin ganin ta bi ra'ayin Abbi da ya hana ta tanka masu a kan duka abinda za su ce akan ta da yaranta . Don haka ta yi shiru ta nufi part ɗin Dada yayin da shi kuma ya bi bayanta.
Ko da suka shiga ɗakin Zahrah sun tarar tana barci, an yi mata ƙarin ruwa, Dada na zaune a gefenta cikin damuwa .
Kallonsu ta yi ba tare da ta iya cewa komai ba, ta san suna hakuri da zaman gidan nan, da ba don Papa ba da tuni sun bar gidan nan, don sau tari Abbi na yunkurin tashi daga gidan Papa na hana shi.
"Kada ku damu ta farfaɗo za ta samu lafiya in sha Allah."
*Washegari*
Yau ne ta kama ranar juma'a, kuma rana irin ta yau jama'ar gidan Alhaji Muhammad Tafarki wajibi ne su ci a abinci a tare, ko Dada da Papa da sukan yi na su a part to ranar juma'a gabadaya suke cin abincin a tare.
Kamar kullum yau ma sun hadu a babban teburin cin abincin dake dinning area. Papa, Dada, Daddy, Mummy, Abba, Umma, Abbi Ummi, da kuma Aunty Laila duk sun haɗu. Haka jikokin gidan ma duk sun haɗu sai sai ban da mutane biyu. Wato Hilal da Zahrah wacce ke kwance taba barci sakamakon rashin lafiyar dukan da Hilal ya yi mata. Faisal, Mansur, Mahmud, Sadik sun hallara. Nabeela, Kausar, Nadiya, Maryam duk suna nan.
Masu aikin na tsaye in da suke zubawa kowa abinda ransa ke so. Papa ya kalli Faisal ya ce.
"Je ka kira mani Babban Yayanku."
Faisal ya tashi ya nufi stairs ɗin, ɗakin Hilal ya shiga, kasancewar kofar ɗakin a buɗe yake . Ganin baya falo ya saka ya nufi bedroom ɗin sa. Lokacin ya fito daga wanka yana sanye da bathrobe a jikinsa.
"Assalamu alaikum warahmatullah"
Muryar Faisal ya ji tana sallama.
Ciki-ciki ya amsa masa sallamar iya ƙasan maƙoshinsa wanda shi wanda ya yi Sallamar bai ji ba.
'
"Barka da safiya Babban Yaya."
Bai amsa masa ba ta fara ƙoƙarin shafa man shafawarsa a jikinsa bayan ta tsane ruwan dake jikinsa da kansa.
Har lokacin fuskarsa a murtuƙe take tamau, don ko barcin kirki bai yi ba, karfe dayan dare ya dawo gidan.
Faisal ya ga ko gaisuwarsa bai amsa ba ya share shi fuska a murtuƙe ya ce.
"Allah ya huci ran maza gu..."
Ɗaga masa hannu ya yi alamar dakatarwa, sannan ya nuna masa kofar fita.
Murmushi Faisal ya yi kafin ya ce
"Zan fita, dama Papa ne ya ce na kira ka."
Yana fada masa haka ya fice.
Shi kuma ya cigaba da ƙoƙarin shafa man shafawarsa da yake yi.
Ko da Faisal ya koma a dinning area ya sanar da Papa cewar yana zuwa .
Jingina kai kawai Papa ya yi yana shan ruwan shayin dake gabansa.
Bayan kamar mintuna goma sannan Hilal ya sauko zuwa downstairs
Ƙamshin turarensa na Armani Georgia hade da Valentino ke tashi a jikinsa, ƙamshi ne ya fara yi masu sallama, wanda ko bai fesa turaren ba ƙamshin na nan a jikinsa.
Ciki-ciki y yi sallama wanda ba wanda ya ji shi, ƙarasowa ya yi kan kujerar dake gabansa ya ja ya zauna suna fuskantar juna da Papa. Sai dai bai kalle Papa ba