Showing 114001 words to 117000 words out of 154779 words
kalmar."
"Eh na ji labarin ba ta da lafiya shi ne muka zo ni da ƙanwata don duba lafiyarta."
"Wai wannan yarinyar da suka shigo da Zahrah ita ce Humaira ?"
Cewar Mummy cike da takaici.
",Eh ita ce dama ba ki gane ta ba ne?"
Tsabar takaici kasa magana ta yi, kowa dake wajen ba wanda ya yi farin ciki da jin jin zancen Ammar.
Tashi ya yi yana cewa .
"Bari na gaida Dada "
Bayan tafiyarsa Aunty Laila ta ce
"Sai na bi duk hanyar da zan bai don ganin na hana Ammar auren wannan yarinyar, matukar ina numfashi a duniyar nan ba zan taba bari na wani ya zo neman aurenta ban lalata maganar ba."
Jinjina kai Mummy ta yi tare da cewa
"Ina bayanki ɗari bisa ɗari. Ba za ta taɓa yin rayuwar farin ciki ba daga ita har Iyayenta mu zuba mu gani."
Jinjina kai Umma ta yi tana murmushi tare da masu alamar Jinjina.
A ɓangaren Dada suke a falonta, Dada, Ammar, Zahrah, da Humaira.
Fira suke yi cikin annashuwa da farin ciki,, duk da cewar Zahrah ba ta saki jiki ba saboda Ammar na wajen kunyarsa take ji
An cika masu gaba da kayan ciye-ciye da na sha.
Bayan sun kammala ne Suka tashi suka nufi part ɗin Abbi. Su uku ne Zahrah da Humaira na rike da hannun juna sai Ammar dake bayansu.
Har lokacin jama'ar gidan na falo.suna ganinsu bakin cikinsu ya kafa ninkuwa.
Don sun san in dai Ammar ya auri Zahrah ta huta. Za ta samu duk wani abun da take buƙata na more rayuwa. Su kuma ba haka suke so ba, so suke yi su ga rayuwarta ta tagayyara.
Da sallama suka shiga part ɗin Ummi tana zaune da alƙur'arni mai girma tana karantawa .
Tana kai aya ta ajiye ta tarbe su da fara'a duk da ba ta yi mamakin ganin Ammar ɗin ba.
"Bisimillah."
Suka zauna bayan sun gaishe ta, ta amsa cikin farin ciki da walwala.
Abbi ya fito daga ɗakinsa ya ya karaso falon.
Suka gaishe shi kasancewar weekend ne kowa na gida, Yaa Mahmud da Yaa Sadik ma duk sun fito an gaisa.
Nan ma Ummi ta kawo masu abun sha duk da sun ce sun cika ciki a bangaren Dada.
_Asadullah_
Wayar Sulaiman yake kira baya daga wa. Jikinsa ne ya bashi akwai wata matsala dake faruwa .
Sake kira ya sake yi a daidai lokacin da yake driving yana ƙoƙarin barin layin Asadullah mansion, ɗagawa ya yi tare da kara wayar a kunnensa.
"Yallaɓai zan kira ka ina ƙoƙarin bin bayan wadanda suka zo neman Jidderh ne, da alama Yayanta.
Yana faɗin haka ya katse kiran wayar da alama sauri yake yi sosai.
Asadullah bai san sanda ya saki murmushi ba, saboda ya ji dadin wannan labarin da ba ya ji. Ya kuma yi addu'ar Allah ya bayyana ta.
Kiran waya ne ya shigo wayarsa dubawa ya yi ya ga sunan da ya bayyana akan fuskar wayar.
Inspector Bashir. Shi ne sunan da ya bayyana akan fuskar wayarsa.
Ɗaga wa ya yi tare da yin sallama.bayan ya amsa sallamar daga can ɓangaren ne Asadullah ya ce.
"Ya aiki?"
"Alhamdulillah." Inspector ya amsa sannan ya ce.
"Shi wannan sagir ɗin da ya yi ƙoƙarin kashe ka a baya tare da ɗan uwanka mun gano in da yake."
Da sauri Asadullah ya mike tsaye yana cewa.
"A ina yake yanzu?"
"Bayan mun yi bincike mun gano cewa yau satin sa ɗaya kenan da ya dawo ƙasar, kuma yana garin Lagos ne a yanzu haka."
"Da kyau."
"Mun gano cewa akwai yarinyar da yake nema a garin ne, ta hanyar ta za mu fara bi, ita ce tsanin da za mu bi ta kai mu zuwa gare shi.
Don yanzu yana taka tsan-tsan da mutane ba zai saki jiki yadda zai kamu cikin sauki ba."
"Okay"
"Yanzu ka jira za ka ji daga gare ni, don akwai abubuwan da nake bukatar ji daga gare ka."
"In sha Allah."
"Kada ka damu zai shiga hannu kamar yadda Kamal ya shiga hannu yana prison, wata kila ma yana da saka hannu a abinda aka yi maka na rufe ka tsawon lokaci. Bisa la'akari da ya zauna a cikin mansion ɗin tsawon lokaci ya san komai na ciki."
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page5️⃣5️⃣
Kada ka damu zai shiga hannu kamar yadda Kamal ya shiga hannu yana prison,watakila ma yana da saka hannu kan abin da aka maka na rufe ka tsawon lokaci. Bisa la'akari da ya zauna a cikin mansion ɗin tsawon lokaci ya san komai na ciki."
Ɗan jim Asad ya yi kafin ya ce.
"Ta iya kasance wa haka ne, amma abun da hankalina ya fi karkata wani ne daban ba Sagir ba."
Ta iya yiwuwa haka ne, ta iya yiwuwa ba haka ba ne, amma bincike zai tabbatar mana da ko waye ya aikata wannan laifin. Ku shi ne ko kuma wani ne daban daga gefe".
"To shi kenan inspector Bashir Na gode sosai."
Daga haka suka yi sallama ya kashe kiran wayarsa.
_Zahrah_
Wunin ranar yin shi ta yi tare da Ammar da kuma ƙanwarsa. Ta yi shi ne cikin farin ciki da jin dad'i. Don Ammar ya shiga ranta duk da idan ta tuna da zantukan mahifiyarta jininta yana sanyi sosai. Don ta ga alamar cewa su Mummy ba za su bari Ammar ya aure ta ba. Ko da ba su san waye iyayen Ammar ba za su yi iyakar kokarinta ganin sun ɓata komai. Ballantana akwai mutunci da zumunci a tsakanin Mahaifiyar Ammar da mahaifiyar Hilal ɗin
Sai kusan magrib Ammar ya ce wa Humaira ta tashi su koma gida.
Don lokacin sun bar part ɗin Ummi sun koma na Dada. Wata shaƙuwa ce ta shiga tsakanin Humaira da Zaharah a cikin yini guda . Tamkar Wadanda suka shekara da sanin juna
Dama sun yi wa su Ummi sallama don haka suka yi wa Dada sallama a lokacin da za su tafi.
Ko da suka karaso main falon gidan ba kowa. Da alama kowa ya koma part ɗin sa kenan.
Kallon Humaira Ammar ya yi kafin ya ce.
"Ya kamata na shiga na gaida Mummyn Hilal, idan na tafi ban shiga ban kyauta ba."
"To ka shiga ka dawo mana."
"A'a tare da ke za mu je."
Da mamaki take kallonsa.
"Ni kuma wallahi Yaya bana son zuwa na ga take-taken mutanen gidan nan ba su da mutumci. "
"Eh ba da da shi amma dole sai mun je mun gaida mahaifiyar Hilal."
Tura baki ta yi kafin ta kalli Zahrah ta ce.
", Sister mu je ki raka ni."
Da sauri ta girgiza kai, don ta san matuƙa ta ke part ɗin Mummy sai ta gwammace dama ba ta shiga ba.
Don haka ta ƙaƙalo murmushi ta ta ce.
"Ku dai je ku dawo."
Zata sake wata magana dai Ammar ya ja hannunta suka nufi part ɗin Mummy, ba tare da ya ba ta damar sake magana ba .
Da idanu Zahra ta taka su tana murmushi.
Da sallama suka shiga kofar part ɗin.
Daddy, Mummy, Faisal, Maryam duk suna falon, amsa masu sallamar suka yi yayin da suka karaso ciki.
Cikin girmamawa suka gaida Dad da Mom. Suka amsa masu ba yabo ba fallasa. Faisal da Maryam ma suka gaishe su
"Dama har yanzu kuna gidan nan ne?"
"Eh Mummy wannan karon kun ga ban zo lokacin da Hilal kenan ba ko, wannan karon zuwan na Zahrah ne."
Amma tun wancan zuwa Laila ta baka shawarar cewa ka fita harkar Zahrah domin ƴar iska ce bin maza take yi ko?"
Shiru ya yi kafin ta cigaba da cewa.
"An fada maka bar cikin shege ta yi ta zubar shi ne ba za ka nemi yar mutunci ka aura ba sai ita ko? Idan ma ya zama dole a cikin wannan family na Tafarki kake neman aure ga ƴan mata nan muna da su da yawa sai wacce ka zaɓa, why not ka zaɓi ɗaya ka mance da Zahrah."
Ɗago idanu ya yi ya kalle ta kokarin ita ma shi take kallo ya ce.
"Mummy wallahi zuciyata Zahrah take so, bayan ita ban ga wata ƴa mace da ta kwanta Mani a rai ba, Mummy ana zuwa gidan ƙaruwai a auri mace jihadi ne domin an tairatar da ita daga halaka. Wallahi duk yadda Zahrah ta kai ga lalacewa ina son ta a haka , kuma in sha Allah kafin na bar garin nan zan tura a nema mani aurenta."
Sakin baki suka yi suna kallonsa, yayin da ya ce wa Humaira.
"Tashi mu tafi."
A tare da ita suka mike suna masu sallama ba wanda ya amsa sai Maryam.
Mamaki da al'ajabi ya hana Humaira da Ammar magana har suka karaso in da Zahrah take.
Ƙoƙarin daidaita kansu suka yi don kafa ta fahimci komai. Sai ma murmushi da suka yi mata lokaci guda.
"Kun fito?"
Ammar ya ce
"Eh mun fito, jibi xan dawo ni kadai don yau wannan yarinyar ta takura Mani, ba ta bari mun samu isasshen lokacin da za mu yi zance ba, ta cika ku da surutu."
Humaira ta yi saurin cewa
"Ai ko za ka dawo ba biyo ka zan yi ba, na zo na ga Zahrah, dama ai ni ka kawo na ganta . Idan ka sake dawowa Sai ku ci soyayyarku."
Umarnin ɗauko sakon da suka zo da ji ya ba Humaira. Ta karbi key ɗin motar ta fita don dauko sakon.
Manyan kedoji ne guda biyu shaƙe da kaya, ta ajiye tare da cewa
"Ga su."
Kallon Zahrah ya yi tare da cewa
"Ga tsarabar ki nan gimbiyata."
Kallon kayan ta yi tare da cewa.
"Yaa Ammar don Allah ka bari na dauki ɗaya sun yi yawa, dayan ma na don Ummi ma sai ta yi faɗa. "
Duk yadda ta yi akan su rage kayan ba su saurare ta ba suka fice suna mata sallama.
Ba ta da wani zaɓi ta ɗauki kayan niƙi-niƙi ta nufi part ɗin Dada, don tana tsoron Ummi, saboda Ummi ta hana ta karbar komai daga hannun wani ɗa namiji.
Da sallama ta shiga wajen Dada, tana kokarin shiga bedroom ta ga Zaheah da kaya niƙi-niƙi a hannunta.
"Wadan nan kayan daga ina haka?"
Kamar za ta yi kuka ta fara magana.
"Yaa Ammar ne ya bani, kuma Ummi za ta yi Mani faɗa ya sa na kawo nan, na ce ya rage kayan amma ya ƙi."
Shiru Dada ta yi kafin ta ce.
"Umminki ba ta yi laifi ba gaskiya, domin babu amfanin ki yi ta karɓar abun samari bayan ba aurensa za ki yi ba."
Da sauri ta kalli Dada jin zancen ta, Allah ya sani tana don Ammar har cikin zuciyarta.
"Kada ki damu ki yi addu'ar Allah ya zaba maki mafi alkhairi a gare ki, idan Allah ya sa Ammar mijinki ne sai kin aure shi."
Jinjina kai ta yi tare da cewa.
Ki kai kayan ɗakinki daga wannan ɓangaren ba ɓangaren Umminki ba, zan yi magana da ita in sha Allah."
Daga haka ta kai kayan bedroom ɗin ta dake kusa da bedroom ɗin Dada, sannan ta yi mata Sallamar za ta koma part ɗin Ummi."
"Ba nan za ki kwana ba ne?"
"A'a wajen Ummina zan kwana sai da safe."
Daga nan ta fice Dada na cewa.
"Yarinyar nan ƴar ganin dama ce, sai in da kika dama za ki kwana ko? To Allah ya tashe mu lafiya."
Daga haka ta koma part ɗin Umminta.
*Washegari*
Kamar yadda Ammar ya ce zai zo bayan kwana biyu kasawa ya yi, sai ga shi ya zo a ranar. Ko da ya kira ta a waya lokacin tana part ɗin Dada.
Don cewa ya yi ta fito ba zai shiga ciki ba, don baya son Mummy ko Aunty Laila su sake ɓata masa rai ko su ɓatawa Zahrah rai.
Sanye take da hijabi har ƙasa onion colour ya mata kyau.
A hankali take tafiya wanda tun da ya hango ta ya fito daga cikin motar.sanye yake cikin ɗanyar shadda fara, ɗinkin daidai jikinsa na zamani wanda ya dace da shi. Sai baƙar hula da bakin takalmin dake ƙafarsa, ƙamshin turarensa ke tashi a jikinsa ya rungume hannayensa a ƙirjinsa yana sakar mata sanyayyar murmushinsa.
"Assalamu alaikum"
Zazzaƙar muryarta ta daki don kunnensa. Sai da ya lumshe Idanu ya bude a kanta kafin ya amsa mata.
"Ina wuni Yaa Ammar."
"Lafiya lau. Ya ƙarfin jikin?"
"Alhamdulillah na warware."
"Yau ba zan shiga ciki ba"
Hakan ya saka ta nufi wajen kujerun da aka tanada dan zaman shan iska daga can gefe.
Bin bayanta ya yi suka zauna suna fuskantar juna. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle.
*America/New York City*
Dawowarsa kenan gidan ya ɗauko ruwa a fridge, tsiyaya wa ya yi a kofin glass zai sha. Wayarsa ce ta soma ringing, ya duba ya ga Mummy ce.
Ɗaukar wayar ya yi ya kara a kunnensa, ya dauki kofin ruwa ya riƙe.
"Hello Mummy dawowa na kenan, ina son idan n huta na kira ki."
"To ya kake ya aiki?"
"Alhamdulillah Mummy."
"To ma sha Allah."
Ta fada kafin ta ce.
"Wai abokinka nake son ka ba shawara."
"Wane abokin kike nufi Mummy."
"Ammar mana."
Ruwan da ya zuba a kofi ya sha kafin ya ce.
"Okay."
Ya ce yana jiran jin abun da za ta ce
"Wai shegiyar yarinyar Zahrah zai aura, kuma ya samu goyon bayan Kakarku."
"To ni me zan yi akai?"
Ka bashi shawara yarinyar nan fa Yar iska ce bin maza take yi, ta sha zubar da ciki, ja bashi shawara ya rabu da ita ya nemi wata ya aura."
"Mummy saboda wannan dalili ya saka kika kira ni?"
"Eh mana, Hilal na san Ammar ba ka da wani abokin sama da shi zai ji maganarka."
"Mummy ki mai da wajen abun da yake gabanki. Na gaji yanzu zan huta sai mun sake magana."
Bai jira cewarta ba ya katse kiran wayar.
Daga can ɓangaren kuwa Mummy kallon wayar take yi tana mamaki.
Kallon wayar kawa ta yi tare da ajiye wa.
"Dama na sani yaron nan ba zai taba saurara ta ba, duk maganar da zan masa, ya fifita waɗan can tsofaffin akan kowa, su kadai za su yi masa magana ba zai tsallake ba, ba zai yiwu ba dole na yi wa tufkar hanci. Idan ba haka ba ina ji ina gani zai fi karfina."
"Fin ƙarfinki na nawa kuma ?"
Da sauri ya juya ta kalli Aunty Laila dake tsaye a bakin ƙofa.
"Ai Hilal dama tun can baya jin maganarki ko na Mahaifinsa, mutum daya ke masa magana ya ji shi ne Papa sai kuma Dada, su yi iko da ɗa sannan su yi da jika."
Jikin Mummy ne ya yi sanyi, sai jin muryar Aunty Laila ta yi ta sake cewa.
"Na tabbatar da Papa ne ko Dada suka ce ya dakatar da Ammar wallahi da ya dakatar da su. Don su ya dauka uwa da uba, shakuwar dake tsakaninsa da su baya tasaninki da shi ko wani shawara da su yaje yi me kika dauki hakan?"
Shiru Mummy ta yi kafin ta ce.
"Na ɗauka shakuwa ce saboda kin san shi ne jika na farko a gidan nan, kuka tun da aka yaye shi ya fi zama da su Papa ya kan fita da shi ko Dada ma na fita da shi ko abinci ya fi cin na su na ɗauka shakuwa ce. Sai bayan ma da aka haifi shegiyar yarinyar can Zahrah na ga sun raba kaunar da suke masa gida biyu sun ba ta gida ɗaya shi na gida ɗaya. Tun lokacin da na ga Zahrah ta shaƙu da kakanni suna sonta hankali na ya tashi amma da na tuna yadda suka nunawa mahaifin ta kauna da fifiko ya sa na gane hakan ya saka ita ma soyayyar mahaifinta ya shafe ta. Na so janye Hilal daga wajan su don kada shakuwa ta shiga tsakaninsu da yarinyar amma bai saurare ni ba. Sai sai na yi nasarar cusa masa tsanar yarinyar a cikin zuciyarsa. Kuma Alhamdulillah ya tsane ta wanda na lura ba sa zama inuwa ɗaya."
Mumrmushi Aunty Laila ta yi kafin ta ce.
"Da sauran rina a kaba."
Daga nan ta juya ta bar Mummy tana aikin fashin baki akan kalmar Sunyi Laila.
Duk yadda Sulaiman ya yi kokarin ganin ya samu yayan Jidderh ya kasa. Don da ya hau titin ma bai ga mai kama da mashin ɗin da ya gan su da shi ba
Wunin ranar haka ya dinga yawo amma bai gan su ba, cikin takaici ya koma mansion ɗin.
Wanka ya yi ya canza kaya ya ɗan yana son komawa wajen uban gidansa ya sanar da shi halin da ake ciki.
Yana fitowa Falo wayarsa dake cikin aljihu ya fara ringing ɗauka ya yi tare da cewa.
"Hello Yallaɓai ban same su ba, amma gani nan zan sanar da kai komai, ka gafarce ni mai gidana na kasa cika maka burinka. Amma in sha Allah sai na samo maka su a duk in da suke, gani nan zuwa .
Yana ajiye wayar suka yi Idanu biyu da Dady da alama tun kafin ya fito yake nan, kuma alamu sun nuna ya ji duk maganar da ya yi a wayar.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
*Albishir! Albishir!! Albishir!!!*
Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku.
Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇
Flasks
Cups
Dinnerset
Kitchenware
Pot
Jugs
Food processor
bedsheet lamps
Second hand gas
Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887
Page5️⃣6️⃣
Yana ajiye wayar suka yi Idanu biyu da Dad da alama tun kafin ya fito yake nan, kuma alamu sun nuna ya ji duk maganar da ya yi a wayar.
Murmushi Sulaiman ya yi kafin ya ce.
"Dad yau..."
Dakatar da shi ya yi ta hanayar daga masa hannu.
"Rainin hankalin ya ishe ni haka Sulaiman, tun yaushe kake ɓoye Mani gaskiyar abun da ke faruwa?"
Shiru Sulaiman ya yi ya kasa cewa komai, in da Dad ya cigaba da cewa.
"Dama na yi tunanin abin da kake boye mani, domin na ga canji a tattatre da kai. A lokacin da Asad ya