Showing 15001 words to 18000 words out of 154779 words
Umminsu.
Ganin autarsu na kuka ya sa duk hankalinsu ya tashi. Musamman Mahmud da ya fi Sadik sauƙin kai.
"Lafiya Auta?"
Ba ta tanka ba sai kuka, kallon Ummin ya yi wace ta shafa addu'a ya fara gaishe ta, Sadik ma ya gashe ta.
Suka haɗa baki wajen tambayar abinda ya faru da Zahrah.
"Ku tambaye ta da kanku, na dai ji ƙanwar mahaifinku na cewa wai a ɗalin Hilal ta kwana, ta gansu suna fitowa a tare."
"What!?"
Sadik ya faɗa yana cewa sharrin har ya kai haka, wallahi matar nan da ..."
"Ba sharri ta yi ba tunda ba tambaye ta da kaina ta kasa ƙaryatawa."
"Ke!."
Ta san halin Sadik da zafin zuciya yanzu zai iya kai mata duka, don haka ta miƙa da sauri ta koma jikin Mahmud.
"Dakata Sadik akwai wani abu dai, amma ba yadda kake tunani ba, na san ba komai wallahi."
Sadik ya kalli Mahmud ya ce.
"Yaa Mahmud meye hujjar ka?"
"Na sani ka sani tarbiyyar da Ummi ta bamu tarbiyya ce da ba za mu iya aikata wani abun da ba daidai ba. Musamman tarbiyyar da ta yi wa Zahrah da ƙoƙarin da take wajan kula da tarbiyyar ta kasancewar ta ƴa mace ba za ta aikata abinda ba daidai ba."
Kallon Fatima Zahrah ya ji tare da cewa.
"Sanar da ni abinda ya faru bar kika kwana a ɗakin wanda ba muharramin ki ba."
Nan ta kwashe komai da ya faru ta sanar da su. Tun da Dada ta aike ta har ɓarna da ta masa zuwa punishment ɗin da ya bata.
Haƙiƙa ransu ya ɓaci da abinda Hilal ɗin ya yi wa Zahrah, wani irin zalunci ne zai saka ta tsallan kwaɗon na tsawon lokaci ya fita har ya dawo.
Cikin zafin zuciya Sadik ya mike zai fice. Jin muryar Umminsa ya ji tana cewa.
"Dawo Sadik!"
Dawowa ya ji zuciyarrsa na tafarfasa ya ce.
"Ummina abinda ake mana a gidan nan ya fara isa ta, wannan ai zalunci ne. Ta ya ya zai azabtar da yarinya don ta yi masa ɓarna. Ai da ya fadi ko nawa a ne ɓarnar da ta masa sai mu biya. Amma ka yi wa ɗan Adam horo da har ya kasa tafiya, don shi soja ne sai ya gwada ikonsa akanta. Gabaɗaya an tsane mu a gidan nan kamar ba jininsu ba."
Zahrah dai ɗakinta ta nufa tare da faɗawa toilet, gasa jikina ta yi da ruwa mai zafi sanna ta ɗauro alwala ta zo ta saka doguwar riga ta gabatar da sallah. Ba laifi ta ji dadin jikinta.
_Aunty Laila_
Tana zuwa ta part nata ta nufi ɗakin yaranta mata biyu duk suna barci ba sallar asuba.
Duk ta kai wa Nabeela da Kausar ta ce.
"Ku tashi banzaye kun kasa karkato hankalin Hilal zuwa gare ku, to ki tsaya kowacce cikinku ta rasa ga waccen mai kama da aljanar tana neman yi masu sakiyar da ba ruwa."
"Wace ce wanan ?"
Nabeela ta tambaya."
Kausar ta bata amsa da wace ce mai siffar aljanna a gidan nan?"
"Uban me zai yi da wannan figaggiyar yarinyar , ai babban goro sai magogin karfe."
Nabeela ta ce.
"Kema ki hakuri ki bar Mani shi."
"Wallahi ba zan hakura ba kowa ta iya allonta ta wanke. Kuma na san ko Mahifiyarsa da mahaifinsa ba za su bari ya kula yarinyar nan ba, na rasa abinda ya kai ta part ɗin sa amma zan yi maganinta."
_Jidderh_
Washe baki take yi tana dariya har dimple ɗin ta na lotsawa, Inna da isah fuksar kowa da farin ciki anyi nasarar ciro baby boy dake cikin Sa'adatu.
Sa'adatu da baby suna barci suna hutawa, babyn ma sha Allah sai barcinsa yake kan gadon baby yana sanye da Kayan sanyi a jikinsa.
_Fatima Zahrah_
Kasancewar ba ta samu barci a daren jiya ba ya saka tana isar da salla ta kwanta tana barci. Can cikin barcinta sai ta ji ana kiran sunanta a hankali ta bude idanunta ta sauke su akan na Umminta. Da sauri ta tashi zaune ganin idanun Umminta ya naɗa ya yi ja.
"Ummina lafiya ?"
Ba ta ba ta amsa ba ta ce.
"Ki zo falo ana son ganinki."
Daga nan Ummin ta fice, gaban Zahrah ya fadi, don kamar kuka ta ga Umminta na yi .
Da sauri ta tashi ko sanye da hijabi da ta yi sallah ta fito babban falon gidan.
Gabaɗaya ahalin gidan ne suka hadu, tana fitowa kowa ya zuba mata idanu. Kallon yayyunta ta yi Mahmud da Sadik ta ga ransu a ɓace ga Umminta ido ya yi ja.
Kallon kakanninsu ta yi ta ga ita suke kallo, cikin sanyi jiki ta karasa tare da zubewar akan guiwarta.
09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
Ba *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*SADAUKARWA*
_Wannan shafin sadaukarwa ne ga ƙungiyar Jajirtattu writers association Alla ya ƙara mana ƙwarin guiwa fa haɗin kai_🥰🤝
Page0️⃣8️⃣
Kallon Kakanninsu ta yi ta ga ita suke kallo, cikin sanyin jiki ta ƙarasa tare da zubewar akan guiwarta.
Ta kalli Kakannin nata ta ce.
"Barka da safiya kun tashi lafiya?"
Suka amsa mata ba yabo ba fallasa. Daga nan ta kalli iyayen nata maza ta haɗa jam'i wajen gaishe su ta ce.
"Ina kwana?"
Mahaifinta ya amsa amma sauran ƴan uwansa ba wanda ya amsa, ta saba da haka don kullum ba su amsa gaisuwarta sai dai idan sun ga idon Papa da Dada. Wanan karon ma Papa ya kalle su ya ce.
"Ba ku ji tana gaishe ku ba ne, kullum abu ɗaya ya ƙi wucewa wa, yaushe za su haɗa kai ku so juna sai bayan mutuwsata?"
Jin haka ya saka suka amsa mata da lafiya lau daga nan ta juya kallonta ga iyaye mata wanda suka share ta ba su amsa ba har sai da suka ga ɓaci ran Papa sannan suka amsa iya surukan ne suka amsa amma ita kam Aunty Laila ba ta amsa ba. Zahrah ba ta damu ba ta juya wajen Yayyun su maza da suke zaune gefe ɗaya. Bilal, Mansur, Faisal, Mahmud da Sadik. Gaishe su ta yi wanda ba su so amsawa ba idan aka cire Mahmud da Sadik. Hilal kam dama ba ita ba kowa sauran yaran gidan suka gaishe su kallo ba su ishe shi ba ko da kuwa Faisal da Maryam ne wadanda suka fito ciki ɗaya , duka yaran Abba da Umma ne to ba amsa gaisuwar su yake yi ba
Sannan ta kalli gefen ƴan matan gidan Maryam, Nadiya, Nabeela da Kausar. kasancewar duk sun girme ta nan ma ta gaishe su Maryam kawai ta amsa tare da.
"Lafiya lau sister."
Umma kam harara ya ta gallawa ƴarta, don ta tsani halayyar ta.
Gyaran Murya Papa ya yi wanda hakan ya saka kowa ya dube shi tare da kallonsa, idan aka cire Hilal wanda shi tun da ya shigo wajen bai yi wa kowa magana ba, tunda ya tsarin ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan daya yana danne-,danne a wayarsa.
Duban Aunty Laila Papa ya yi tare da cewa.
"Auta faɗa abinda kika faɗa mani gaban kowa."
Ba tare da tuninin komai ba ta fara magana.
"Dama wancan banzar yarinyar da nake faɗa maku cewa tana bin maza kuka ƙi yarda da zance na yau za ku yarda. Don na dade da sanin wannan yarinyar yawon banza kawai take zuwa da sunan makaranta."
"Ki faɗi a abinda kika faɗa mana kai tsaye."
"Wannan yarinyar tana zuwa ɗakin Hilal idan ga tara mazajen waje, hakan ya saka na ga ya kamata a taka mata burki na san bayan Hilal za ta iya bin wasu mazan na gidan nan don ga wasu samarin nan a gidan."
Fatima Zahrah ta fashe da wani kuka mai cin rai da ƙunar zuci. Jin sharrin da ake mata .
Papa ya kalle ta tare da cewa.
"Kina da tabbacin cewa maza take bi a waje za ki iya rantsuwa akan haka?"
"Papa me ya kawo zancen rantsuwa fa, na rassa waye zan yi wa sharri sai wannan ƴar yarinyar duk cikin yaran gidan nan."
"Me zai hana idan ita kaɗai kika tsana."
Dada ta yi magana tana kallon ƴarta wacce ta tsani halinta, shi ya saka ba sa shiri sai ta ce sai ba ta son ta.
Kallonta mahaifinta ya ji tare da cewa.
"Kina da tabbacin akan abinda kika faɗa?"
"Ƙwarai kuwa da asuba kafin ayi sallar asuba na ganta tana fitowa daga ɗakin Hilal da alama nan ta kwana, sun fito tare da shi hijabinta a hannu
Sautin kukan Fatima Zahrah kawai ke tashi a falon, shi kuwa gogan Hilal har yanzu yana yadda yake sai sarrafa wayar hannunsa yake yi cike da ƙwarewa. Ko a jikinsa bai nuna alamar cewa yana jin me suke faɗa ba, ko a jikinsa.
"Za ki iya rantsuwa akan zargin da kike masu cewa sun yi lalata a ɗakin Hilal?"
"Ba zan rantse ba amma na san tabbas wani al'amari y faru a tsakaninsu."
Kallon Hilal Papa ya yi tare da cewa.
'Hilal ka sanar da mu abinda ya faru."
Tsawon minti ɗaya kafin ya bude baki ya ce
"Dad ku tambayi yarinyar mana,."
Ya yi magana har lokacin idanunsa kan wayarsa, kamar ba shi ne ya yi yi maganar ba. Daga karshe ya ce
"Ku faɗa wa ƴar ku shaidar zina wuya ne da shi ta kiyayi hakan matukar ba tana da juriyar da za ta iya jure bulala tamanin ba."
Yana gama fadar haka ya tashi ya nufi upstairs ɗin.
Binsa da kallo suka yi Aunty Laila ta fara masifa tana cewa
"Hilal rashin mutumcin naka har ya kai haka, to ka zo ka ka yi mani bulala tamanin ɗin mara kunya."
Dada ce ta janyo Zahrah ta zaunar a gabanta tana goge mata hawaye ta ce
"Ki yi shiru Shalelen Dada, ki wanke ka ki ta hanayar fada mana gaskiya abinda ya faru na yarda da ke."
Nan ta goge hawayenta sannan ta basu labarin komai da ya faru tun daga kan aiken da Dada ta yi mata har zuwa ɓarnar da ta masa da punishment da ya saka ta duk ta sanar har ya zuwa kasa tafiya wanda hakan ya saka ba ta da zaɓi ta kamata a wajen.
Shiru falon ya ɗauka ba abinda ke tashi sai sautin kukan Zahrah. Dada ce ta janyo ta a jinkinta ta rungume ta tana rarrashinta.
"Ki yi hakuri shalele na san dama sharri ne kawai aka maki."
",Ke Laila ki kiyaye ni ba za ki kaso aurenki ki dawo mani gida kina wargaza mani zuri'a ba. Akan me za ki bayar da shaidar da ba ki ta tabbacin faruwarsa, za ki bi ki tayar wa mutane da hankali ki ƙuntata rayuwar baiwar Allah Saliha na rasa me yarinyar nan ta yi maku da kuka bi kuka ɗora mata karan tsana. Kun tsane ta daga ita har sauran ƴan uwan ta da iyayenta. Na ji kokarin ganin na gyara komI amma hakan ya ci tura so kuke bakin ciki ya kashe ni?"
Papa ya yi maganar idanunsa sun canza launi saboda ɓacin rai da yake fama da shi na tsawon shekaru.
Ganin lokaci na tafiya ne ga yaran gidan akwai masu zuwa aiki da masu zuwa school ne ya saka Papa cewa .
"Ya kamata kowa ya tashi ayi breakfast lokaci na tafiya kada su makara."
Gabaɗaya kowa ya mike maza da mata zuwa wajen yin breakfast.
Babban dinning table ne wanda ke zagaye da kujeru guda ashirin. Ma'aikatan gidan ne tsaye sun kai su huɗu suna jiran a basu umarnin abincin da za su zuba wa kowa."
Nan kowa ya fadi abin da ransa yake so a zuba masa. Umma ce kaɗai ta kasa cin komai, don ta lura Sam huɗubar da take yi wa yaranta da alama Hilal baya ɗauka.
Maganar zuci take yi tana cewa.
'Anya ba yaron nan ba ne ya ceci rayuwar yarinyar nan, duba da yadda yarinyar nan ke bayar da labarin cewa ciwonta ya tashi da alama har suma ta yi, to idan ba shi ne ya yi mata magani ba babu yadda za'ayi har ta wanke ta iya tashi har ta fita daga ɗakin sa ƙafafunta, shin ina ma ya samu maganin da ya mata amfani da shi! ? Ta sha fada masu ba ta yafe ba duk wanda ya taimaka wa Zahrah akan ciwonta, idan ya tashi sai dai su barta har numfashinta na karshe ya iso gare ta. Amma Hilal baya jin maganar ta shi ne har da yi mata magani ko, wanda nake tunanin zai iya ƙarasa ta lahira ne ya ceci rayuwarta. Dole na tashi tsaye akansa.'
Jin Abba ya taba ƙafarta ne ya saka ta lalle shi tare da fara cin a abinci.
Hilal ne ya fito sanye da shigar kananan kaya sa sai zuba ƙamashin turarensa mai daɗin ƙamshi yake yi .
Zama ya yi tare da kallon mug ɗin da ruwan shayi ke ciki, wanda hakan ya tabbatar wa da mai aikin ruwan shayi zai sha. Zuba masa ta yi ya ɗauka ya fara sha ba tare da ya haɗa da komai ba.
Suna bama cin abinci ne Papa ya lalle su ya ce.
"In sha Allah ranar Asabar Fatima Zahrah za ta yi walimar saukar alƙu'ani mai girma. Don haka ranar ba aiki ba zan karbi uzuri daga wajan kowa ba dole kowa ya je wannan walimar in sha Allah."
Ba wanda ya tanka a wajen ballantana su ce Allah ya sa Albarka ko su yi mata murna. Don bakin ciki ne ya bayyana a kan fuskarta .
Kallon sauran ƴan matan Dada ta yi tare da cewa
Nabeela da Kausar Allah ya sa ma kun iya karatun sallah, ga ƙanwar bayanku nan ta sauke kuma nan kuma sakarci uwarku ta daure maku gindi."
kallon Maryam da Nadeey ta ji tare da cewa .
",Ku kuna zuwa amma kun kasa hada ko da izu goma Allah ya shirye ku."
Zahara ta mike tare da cewa.
"Bari na je Dada na shirya zan makara fa."
"To Shalele a dawo lafiya Allah ya maki albarka."
Da amin ta masa ta tashi ta nufi part ɗin su.
Dada ta kalli Ummi ganin duk jinkinta a sanyaye yake ta ce
"A'isha kada fa wannan abun ya dame ki."
Murmushi ta aro ta yafa a fuskarta sannan ta fara kokarin yin breakfast.
A can ɓangaren su Jidderh kuwa yanzu damuwarsu ta kau, ba abinda ke damunsu yanzu, tunda an yi nasarar ciro yaro a cikin Sa'adatu kuma duk suna cikin ƙoshin lafiya. Tana samun kulawa sosai daga wajan likitoci da kuma dangi. Don iyayenta ma suna zuwa asibitin sai yamma suke komawa gidan.
Inna a asibitin take kwana Jidderh ke tashi da asuba ta girka masu abincin breakfast. Don kudin da Asadullah ya ba ta da shi duka siyen kayan abinci, idan ta yi shirin zuwa school sai ta dauki abincin idan ta kai asibiti daga na za ta nufi school.
_Asadullah_
Saukowa yake yi daga upstair ɗin Zuwa downstairs. Da sallamarsa ciki wanda ba wanda shi kaɗai ya ji sallamar da ya yi ya ƙaraso dinning area.
Gabaɗaya sun dinning table suna yin breakfast.
Dady da Mom, sai Hajiya Zulaihat, Kamal Fauziyya da Suhailat.
Kasancewar ba wanda ya ji sallamarsa ballantana ya amsa masa. Sanye yake cikin Suit blue black with white inner sai necktie blue white ƙamshin turarensa ne ya tabbatar masu da isowarsa.
Kallon Dadynsa ya yi tare da cewa.
"Gud morning Dad "
"Morning my Son ka tashi lafiya?"
"Alhamdulillah."
Ya amsa yana mai da dubansa ga Mom ɗinsa wacce ke masa kallon kake ya yawo da hankali ko.
"Mom Barka da safiya sai yanzu na ga kiranki."
Taɓe baki ta yi tare da cewa .
"Ka gama duk abinda za ka yi aure ba fashi sai ka yi shi anan kusa kuwa."
Kallon matar mahaifinsa ya yi wacce ko kallonsu ba ta yi ba ya ce.
"Hajiya ina kwana?"
Hajiya Zulaihat ta kalle shi kamar ba za ta amsa ba sannan ta ce.
"Lafiya."
Idan ba wa da ya kalli bakinta ba ma ba za su gane Hajiya Zulaihat ta amsa gaisuwar ba. Ƴarta Suhailat ce ta gaishe shi cikin farin ciki ya amsa mata cikin kulawa tare da tamabayar ta ya school.
Kamal ne ya mike tare da rike hannun Asadullah ya ce.
"Big bros ƙafata ƙafarka."
Nasir wanda shigowar sa kenan part ɗin ya rike ɗaya hannun Asadullah shi ma yana cewa.
"Big bross ni ma ƙafata ƙafarka."
Dariya suka yi in banda Hajiya Zulaihat da ta tsuke fuska.
Mansur ya gaida su Dady da Mom da Hajiya Zulaihat wacce ta masa kamar dole. Asadullah ya lalle Mansur ya ce
"Uncle ya tashi kuwa?"
"Eh na barshi yana breakfast."
Sallama suka yi duk da Mom ta so Asadullah ya yi breakfast amma ya ce zai yi a kamfani.
Ɓangaren ƙanin mahaifinsa ya nufa wato Uncle Adam mahaifin Mansur ɗin.
Nasir ne ya masu jagora zuwa ciki. Da sallama a bakinsu suka shiga. Duk suna zane a dinning table Uncle Adam Mami da kuma Maryam da Abida.
Gaida Uncle Adam ya yi sannan ya gaida Mami, ta amsa masa cikin sakin fuska tana tamabayar sa aiki. Ya amsa da Alhamdulillah.
Abida da Maryam suka taso zuwa gabansa suna gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska da walwala. Kowacce na na ƙoƙarin jan hankalinsa cikin salo Abida ta ce.
"Mu da Yayanmu amma ganinsa na mana wahala sai dai a jaridu da gidan T.V ko?"
Murmushi ya yi ya ce
"Abida aiki suna Mani yawa ba na da lokaci sai dare wani lokacin nake dawowa kuma a gajiya."
Maryam ta yi saurin cewa .
"Ya ya a bamu lokaci mana a cikin satin nan mu yi fira sosai."
"Ba damuwa zan duba na gani ko zuwa Friday da yamma ."
Cikin jin dadi suka ce
"Promise"
Jinjina kai ya yi tare da yi masu sallama suka fice Kamal da Nasir suka yake masa baya.
Body guard ɗin sa na tsaye ƙikam suna jiran fitowarsa, yana fitowa hana ɗaya suka karasa in da motocinsa suke.
Uncle Adam ya kalli Mami ya ce .
"Wai cikin yaran nan wace ce za'a bawa Asadullah??"
"Maryam mana ita ce babba "
"To ai ni kam Abida na ce masa amma ba matsala sai a canza da ita."
Abida ta mike tsaye tana cewa.
"Wallahi ban yarda ba akan meye za ku ce haka bayan kun san za'a bashi auren ne saboda kwadayin dukiyarsa, kuma Maryam ba ta da wayon da za ta kwashi dukiyarsa. Don na fi ta gohewa da wayewa da zan san banyar da zan kwaso maku dukiyarsa. Kar ku manta Yaa Asad fa ba karamin attajiri ba ne yaro ne da kuɗi. An ce fa shi kansa bai san iya adadin dukiyar da ya mallaka