Showing 60001 words to 63000 words out of 154779 words
ce ta kone gabaɗaya ta ragargaje, komai ma motar ma ta ƙone san ƙwarangwal na mutane biyu.
Ganin yadda Umma ke kuka ga Abba idanunsa sun rikiɗe zuwa ja ya sa ya karasa wajen yana cewa.
"Umma Lafiya?"
Dubansa ya maida zuwa ga Abba zai yi magana ya ji daga can gefe wani na cewa.
"Allah Sarki Allah ya jikansu ga mijin matar nan ya iso?"
Daidai lokacin idanunsa ya sauka akan zoben dake ƙasa wanda shi ne ya siya wa Ammi da kansa, ya zana dising din da yake so.
Take ya zube wajen a sume. Kukan Umma ne ya tsananta.
A can gidan kowa Mom ba ta san meke faruwa ba, ta gama shirya girki ta zuba a flask, tana ajiye wa a dinning table sai ga Kamal ya dawo gidan yana cewa. Yau bai fito lecture da wuri ba. Fauziyya tana school.
Ganin yadda Ya shigo gidan yana kuka kamar karamin yaro ya saka Zubaida wato Mom ta ƙaraso wajen da yake, tana tamabayarsa. Kuka ne ya ci ƙarfinsaya kasa cewa komai.
Daƙyar ya iya cewa.
"Mun rasa Na'ima."
Daidai lokacin da Fauziyya ke shigowa ta ji cewa ta rasa Ammi matar da ta rene ta kamar ita ta haife ta suka rasa.
Zubewa wajen suka yi a sumammiya. Mom sai kuka take yi take yi. Dad ne y je ɗauki ruwan roba ya watsa mata daidai lokacin ta farfaɗo suka ga Abba da Umma sun shigo wanda suke cikin tashin hankali na fasa ƴarsu ɗaya tilo da suka yi.
A ranar wannan ahalin sun ga tashin hankali sosai. Don tabbas rashin Ammi babban giɓi ne na rayawarsu. Kamar yadda Abba da Umma suka haife ta ita kadai haka ita ma Asadullah kadai ta haifa.
An ɗauki tsawon kwanaki kafin Dad iya cin abinci, rashin Na'ima ba karamin girgiza shi ya yi ba. Ya rame ya yi baƙi.
Mom ma ta shiga damuwa ko walwala da kuzari ta daina yi, gabaɗaya ta sauya ba ta da aiki sai kuka har dai idan ta kalli part ɗin Ammi.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka yi kwana arba'in da rasuwar Ammi. Har lokacin Asadullah na bai san da rasuwar mahaifiyarsa ba. Duk da ya so ya fahimci akwai matsala saboda ko suna waya da Dad ɗin sa ba walwala haka Mom ma ba yadda ya saba jin ta ba. Duk sanda ya tambayi ina mahaifiyarsa number ta ba ta shiga sai dai su sanaar da shi wani uzurin. Ko su ce mahaifiyarsa ba ta jin dadi ya kwanta. Da
Kamal da Fauziyya kam sun daina ɗaukar wayarsa. Saboda sun san dalilin kiran nasa.
Abba ma wanda yake kira da Grandpa da Umma da yake kiranta Grandma ko ya tambaye su za su ce tana lafiya
Saura wata ɗaya ya kammala ya dawo Nigeria, don haka ya bar zancen kan cewa yadda Dad ɗin sa ya faɗa ne Amminsa ba lafiya tana asibiti
ba ta iya magana.
Ɓangaren Uncle Adam ma ƙanin Dad Asad ya yi kiransa ko ya ji daga bakinsa amma kamar hadin baki suka yi. Hatta ƴaƴansa Nasir, Maryam, da Abida sai da ya gargaɗe su akan kada wanda ya sanar wa Asad zancen rasuwar mahaifiyarsa.
Kamfanin Asadullah da Dad ne ya kasance C.E.O na kamfanin baya zuwa don har yanzu bai dawo daidai ba. Ƙanimsa Uncle Adam ne kawai ke kula da kamfanin.
Bayan wata ɗaya Asad bai sanar da kowa zai dawo ranar ba, don ko kiransu a waya bai yi ba ballantana ya sanar da su dawowarsa.
Kasancewar rana ɗaya suka dawo shi da wani abokinsa mai suna Sagir . Da motar da aka ɗauko Sadik ɗin shima aka ɗauko su tare.
Sai suka fara ɗaukar hanyar gidan Asad bayan sun ajiye shi a ƙofar gidan ne ya fito, Direban Sagir ya fito masa da trolling bag ɗin sa ya nufi gate ɗin gidan. Ƙaramar trolling bag ɗinsa ya ja ƙaramar door din gidan ya tura da niyyar shiga sai ya ji ta a rufe.
Bubbuga ƙofar ya fara yi maigadi ya yana tambayar waye, jin shiru ya bude yayin da ya sauke idanunsa akan Asad dake tsaye yana rike da trolling bag, washe baki ya yi yana masa sannu da zuwa. Ya amsa masa ba yabo ba fallasa.
Amsar trolling ɗin ya yi daga hannunsa yana binsa a baya.
Da sallama ya tura ƙofar falon ya shiga, suna zaune a dinning table suna cin abinci. Jin muryarsa ya sa suka nufo falo don tabbatar wa.
Maigadi ya ajiye masa trolling ya fita. Mamaki da farin ciki ya cika su gabadaya suka nufi wajensa Kamal da Fauziyya har suna rige-rige wajen fara rungumarsa. A tare ya rungume su yana raba idanu don ganin ta in da Amminsa za ta fito. Lura da haka ya saka Mom ta janye su Kamal daga jikinsa ta janyo hannunsa tana cewa.
"Ku bar shi mana sai kun gajiyar da shi."
Zaunar da shi take kokarin yi amma ya tsaya ƙikam yana cewa.
"Inna Ammina?"
Don wani kewarta da ƙawazucinta ya taso masa. Duk da cewar Mom na bashi kulawa tun Ammi na da dai don wanda bai sani ba zai ɗauka ita ta haife shi.
Shiru suka yi ba wanda ya bashi amsa hakan ya saka ya nufi part ɗin Ammi yana ƙwala mata kira.
"Ammina kina ina kin san yadda na yi kewarko kuwa?"
Bata a falon don haka ya nufi bedroom ɗin ta nan ma ba ta nan. Dad ne ya janyo hannunsa yana cewa.
"Muje na yi maka bayani."
Ya yi maganar idanunsa cike da ƙwalla, ganin haka ya saka Asad ya juya ya kalli Mom da ita shigo ganin hawaye a idanunta ya saka ya ji wani jiri na ɗibarsa. Take ya yanke jiki ya fadi ƙasa sumamme.
Mom ta saka kuka ta nufe shi tana kiran sunansa. Dad ya watsa masa ruwa amma ko motsi bai yi ba. Daidai lokacin Kamal da Fauziyya suka shigo hannun Kamal rike da robar ruwa mai sanyi.
Shima ya bude bakin ruwan ya cika bakinsa ya farar da ruwan da ƙarfi akan fuskar Asad nan ma shiru bai motsa ba.
Har aka yayyafa masa ruwa a karo na biyar shiru bai motsa ba.
Kamal ya ɗauke shi tare da cewa
"Dad mu tafi asibiti"
Fita suka yi gabaɗaya, Kamal ya kwantar da shi a bayan mota Dad ya shiga ya zauna baya yayin da Kamal ya ja motar suka kama hanyar sibitin.
Mom da Fauziyya suka fito ganin sun wuce ya daka Mom ta sa Direba ya bi bayansu.
A hanya Dad ya kira Abba ya sanar da shi, hankalinsa ya tashi jin halin da jikan nasa ɗaya da yake tunawa da shi a matsayin bayan Na'ima.
Shi da Umma suka zo asibitin inda isowarsa ya yi daidai da isowar su Mom. Uncle Adam ma ya iso a bayansa don shi ma Dad ya kira shi.
Sai da aka ɗauki tsawon lokaci kafin likitoci suka samu ya farfaɗo.
A ranar dai sai da rasuwar Ammi ya dawo masu sabo, don kuka suke yi sosai.
Ɗaya bayan ɗaya Asadullah yake kallonsu kamar wani zautacce.
"Don Allah kada ku ce Mani Ammina ta rasu, ta ce mani sai ta ga jikokinta na wa da na Kamal da Fauziyya. Kai na san ba za ta tafi ba ba mu gama rayuwa da ita ba, ba za ta bar ni ba.."
Haka ya dinga surutu da sambatu kowa na ɗakin na kuka saboda yanzu aka yi masu matuwar.
Bayan an sallame su har lokacin Asad na zubar da hawaye sai sai bai yi kuka ba a lokacin.
Haka suka ɗunguma zuwa gida kowa rai a jagule.
A part ɗin Asadullah suka nufa saboda bin sa kawai suke yi a baya.
Kasancewar Mom ta kira mai aikin gidan a waya ya sa aka gyara masa part ɗin.
A falonsa ya zauna har lokacin hawaye ke zuba daga idanunsa. Mamy matar Uncle Adam da yaranta Nasir, Maryam da Abida duk sun zo gidan.
Mom ce ta kawo masa ruwan tea don ta san halin da yake ciki daƙyar zai iya cin abinci. Haka kuwa aka yi ruwan tea ɗin ma bai sha ba, sun yi fama da shi amma sam hakan bai saka ya sha ba.
Nasiha sosai Kakanninsa suka yi masa shi kansa ya tausaya masu, sanin son da suke yi wa ƴarsu ɗaya tilo ga shi sun rasa ta.
Umma ce ta dauki kofin shayin ta kai bakinsa da niyyar bashi a baki, kau da kai ya yi alamar ba zai sha ba, Abba ne ya shafa kansa yana bubbuga bayansa alamar rarrashi.
Sai suka tuno masa da Amminsa don fuskar Umma da ta miko masa shayin sai ya ga Kamfanin ta da Amminsa bai san lokacin da ya sha ruwan tea ɗin ba.
Sai dare sannan kowa ya koma gidansa in da aka bar shi da sauran mutanen gidan. Dad Mom Kamal da Fauziyya.
Daren wannan ranar ya kasance dare mafi muni a rayuwarsa. Kamar yadda ake cewa dare mahutar bawa wannan daren kam bai masa rana. Duniyar ta yi masa zafi. Farin ciki ya ƙaurace a rayuwarsa damuwoyi sun mamaye masa zuciya kamar yadda duhu ke mamaye ɗaki bayan an kashe fitila.
*Rashin comments rashin ganin typing akai-akai*
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page3️⃣1️⃣
Daren ranar ya kasance dare mafi muni a rayuwarsa. Kamar yadda ake cewa dare mahutar bawa wannan daren kam bai masa rana ba. Duniyar ta ya yi masa zafi farin ciki ya ƙaurace a rayuwarsa damuwoyi sun mamaye masa zuciya kamar yadda duhu ke mamaye ɗaki bayan an kashe fitila.
A hankali ya yunƙura ya tashi, kai tsaye bathroom ya nufa don yin wanka. Bayan ya sakarwa jikinsa ruwa ne ya ɗauro alwala sannan ya fito.
Farar jallabiya ya saka a jikinsa , ya dauki sallaya ya fara gabatar da salloli.
Sai ƙarfe biyun dare ya isar sannan ya ɗauki alƙur'arni ya fara karantawa.
A hankali ya ji ya fara samun sassauci. Addu'ar samun rahamar Allah ya yi Amminsa. Sannan ya tashi ya haura gadon ya kwanta.
Har lokacin juyi kawai yake ji yana tuninin rayuwar da ya yi da Amminsa.
Sai da ya dawo sallar asuba sannan barci ya yi awon gaba da shi. Mom da Dad tare suka shigo ɗakinsa ganin yana barci suka koma.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yana samun kulawar Dad da Mom sosai, kuma ya kan ji dadin irin kulawar da suke nuna masa kamar ƙaramin yaro.
Ɓangaren su Umma da Abba wandada yake kira da Grandpa da Grandma, suna bashi kulawa ganin Umma yake kamar Amminsa.
Bayan ya tafi ƙasar Canada ya yi karatun masters ɗin sa ne ya dawo. Dad ya kira Abba da Umma sai Mom da kuma Uncle Adam.
Akan idanunsu ya mallaka wa Asadullah na kamfanoninsa, da duk wace kadarorinsa Kasancewar Ammi kafin ta rasu ta yi masa bayanin komai da iyayenta suka mallaka masa. Ta kuma bashi ƙwarin guiwa akan cewa ya tsaya ya zama jajirtacce kada ya basu kunya. Cike da yakini iyayenta suka mallaka masa ƙasancewar ta mace ya saka ba su ba ta ba suka ce sai Allah ya raya shi za'a mallaka masa . Dan a matsayinsa na ɗa namiji babba a wajenta zai tsaya tsayin daka ya zame masu garkuwa har ita sai ya zama wani jigo ne na rayuwarta.
Sannan ya tuna a ranar da Amminsa ke fada masa haka sai ya kalle ta ya ce
"To Ammi da sun mallaka wa mijinki tun da shi namiji ne zai tsaya tsayin daka Kuma Yaya ne a wajenki."
Mumrmushi ta masa tare da shafa lallausan gashin kansa irin na fulanin usuli ta ce.
"Asad kenan, ni ma na yi masu maganar su bashi a lokacin, amma sai suka sanar da ni cewa, ba na da tabbacin cewa ni kadai ce macen da zai aura, zai iya kasancewa ya auri wata mace ko wasu matan bayan ni. Kuma haihuwa za su yi ba za su taɓa yarda cewa dukiyar mijinki ba ma su ba ne na matarsa ce da ƴaƴanta. Shi kansa bayan ran mutum ki ga ayi ta rigima akan gado ko da ya bar wasiyya da shedu ba za ki tsira ba hakan na iya janyo maki wata matsala daga kishiyarki. Wannan dalilin ya sa za mu mallaka wa ɗanki idan ya girma a mallaka masa ita, na sa me da sauran ƙanninsa da za ki haifa masa."
Tunawa da Ammin ya saka shi zubar da hawaye, gogewa ya yi tare da addu'ar Allah ya shige masa gaba.
"Ka adana su da kyau ka da ka yi sakaci da su."
Ya ji muryar Abba na masa magana, sai a lokacin ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula gyaɗa kai ya yi yana kallon Kakan nasa.
Nan aka rufe taro da addu'a tare da masa fatan alheri.
A washegarin ranar Dad ya tafi da shi ya nuna masa manyan filayen da ya mallaka masa takardunsu sannan ya nuna masa kamfanin da Dad ɗin ke jagoranta.
Ya kuma yi masa bayanin wasu guda biyu ɗaya na garin Kano ne ɗaya kuma na garin Lagos.
Kasancewar na garin Kano ne babba kuma yana da ilimin sanin abin ya saka ya yanke shawarar zama garin Kano.
Duk wasu gyare-gyare da za'ayi ya saka an yi an farfaɗo da kamfanin. Hakan ya saka ya koma garin Kano da zama. Ya nemi lafiyayen gida ya siya.
A cikin shekaru biyu kamfanin ya bunƙasa domin Allah ya saka wa ha hannunsa albarka. Kamfanin mai suna *ASADULLAH GLOBAL RESOURCES* Ya yi suna a garin Kano da kewayenta.
Mom ganin Asadullah ya yi masu wuya ya saka ta tashi hankali wai yarinta ya yi nisar da ba za ta iya jurewa ba, sai sai ya dawo. Dad ya ce hakan ba mai yiwuwa ba ne. Da ta kira Asadullah ta yi masa magana ya ce yana shirin dawo da su nan garin ma, saboda shi ma baya jin daɗin rayuwar da yake yi ba tare da su a kusa da shi ba.
Cikin ƙankanin lokaci ya saka aka samar wasa wani tangamemen fili mai matukar girma, ya kai wani ƙaramin unguwar.
Aka yi gini ladiyayye na zamani irin babban gida wanda ya tara family haka aka tsara gidan. Tsaya wa fada maku tsaruwar gidan ɓata lokaci ne, don dai mu cika shafi biyu ina maku bayanin ginin da kayan more rayuwa da aka zuba. Wannan ginin shi ne *Asadullah mansion*
Ya sanar da Dad du dawo, nan Dad da Mom suka dawo da Kamal sai Fauziyya.
Ya so kakanninsa su ma su dawo kusa da shi, amma sun ƙi yarda sun ce za su dinga ziyartarsu lokaci zuwa lokaci.
Ba yadda ya iya haka ya hakura ya bar su, sai dai ya nemi ƙanin mahaifinsa wato Uncle Adam ya ce su dawo kusa su zauna a nan cikin mansion ɗin.
Haka kuwa aka yi bayan su Mom sun tare da a ɓangaren su da ya tanadar masu.
Kowa da part ɗinsa a nan ɓangaren, part ɗin Dad daban na Mom daban haka na Kamal da Fauziyya. Sai shi uban gayyatar na shi ma daban ne a upstairs.
Haka can ɓangaren da ya ware na Uncle Adam ma daban ne sai dai bai kai girman na su ba.
Ga part ɗin ma'iaktan gidan ma daban, ga su gidaje can daban sun fi biyar kuma duka a cikin mansion ɗin. Don Dad ma ya masa maganar cewa cewa filin da ginin ya yi girma da yawa haka unguwa guda kuma iya su ƙaɗai.
Harkokin Asad sai kara bunƙasa suke yi arziki na ta cigaba da haɓaka. Sunan Asadullah ya zagaye arewa saboda kasuwancinsa da kuma taimakon al'umma da yake da shi.
Ga ƴan mata sai kawo masa hari suke yi, ƴaƴan manyan mutane, daga cikin gida kuma ga yaran Uncle ɗin sa Maryam da Abida. Sai dai ba wacce yake kulawa da sunan soyayya. Sai dai yana basu kulawa a matsayin Yaya a wajensa.
Duk wani abu da ake kaiwa a cikin mansion ɗin nan daga aljihun Asadullah yake fitowa. Tun daga kan ɓangaren Dad har bangaren Uncle Adam. Kama daga abinci da abun sha har zuwa kan suturar sakawa duka shi yake yi masu da motocin da suke hawa da man fetur da suke zubawa a motocin duk daga wuyansa ne, don gidan man fetur ɗin sa suke zuwa a cika masu tankin motarsu.
*Bayan shekaru biyu*
A wannan lokacin Dad ya ƙara aure, in da y auri wata bazawara mai suna Zulaihat mijinta ya rasu tana da yarinya mace mai suna Suhaila, yarinyar ba za ta wuce sa'ar Fauziyya ba. Da farko Zulaihat wacce suke kira Aunty,da ta shigo cikin gidan suna zaune lafiya ita da Mom. Ba wata matsala a tsakaninsu, ta ɗauke su yan uwa Kamal da Fauziyya ma ta ɗauke su kamar ƴaƴanta, hatta Asadullah da bai cika Zama gidan ba ta na nuna masa kulawa.
Sai dai daga baya lokaci guda ta ja jiki da kowa na gidan, ba ta shiga harkar kowa kuma ba ta bari wani ya shiga nata.
Ƴarta Suhailat ma ta mata shamaki da kowa na gida. Ko da Dad ya tamabaye ta ko an mata wani laifi ne ya ce ba komai haka ta zaɓawa rayuwarta.
Kamal da Nasir ɗan wajan uncle Adam duk a kamfanin Asadullah suke aiki.
Yana sanye cikin Suit black with white inner sai necktie Black mai layin fari a jinkinsa. Ƙafarsa na sanyi cikin Black shoe ƙafa ciki sai ɗaukar idanu yake yi. Fuskarsa na sanye da farin glass. Sai agogon Diamond dake ɗaure a hannunsa.
Ƙamshin turarensa na shumukh luxury scent ya ringa shi isowa falon, wanda gabaɗaya ilahirin jama'ar dake falon sai da kowa ya saki ajiyar zuciya.
Dad, Mom, kamal da Fauziyya su ne zaune a falon. Sai Uncle Adam da ya shigo yanzu fuska ba walwala. Ko gaisuwar da su Kamal da Fauziyya ke masa bai masa ba.
Su dai gabaɗaya hankalin su ya tafi kan Asadullah. Mom ta ce
"My son har ka fito, ina fatan ka kira ta ka sanar da ita da zuwanka, ni ma na yi waya da mahifiyarta da safe na sanar da ita zuwanka. Don Allah wannan karon ma kar ka bani kunya kamar yadda ka saba. Ƴan mata hudu kana bijire mani, to wannan karo na hudu ba ja da baya, ko kana so ko ba ka