Showing 102001 words to 105000 words out of 154779 words
biya ni hakkina."
"Wani hakkin zan ba ka Doctor? Ina ce ba ni na sace Asadullah ba, ban san su waye ba kuma ban san shirin su ba, abu ɗaya na saka ka shi ne ka kashe mani Asadullah shi sai na biya ka, burina na ji labarin mutuwarsa. Ka kasa yin komai lokacin da kake da damar yin komai dai da aka neme shi aka rasa ne za ka zo Mani da zancen banza wai na baka kuɗi akan me? Wallahi ƙwandala ba zan ba ka ba."
Kallonsa Doctor ya yi kafin ya ce
"Zan tona naka asiri idna har ba ka cika Mani alkawarin da ka yi Mani na cewa za ka bani miliyan goma."
Dariya Kamal ya yi kafin ya ce
"Don Allah ka yi sauri ka tona Mani asiri, a ranar da ka tona mani asiri a ranar ina mau tabbatar maka da cewa sai ka tsinci kanka a cikin gidan yarin nan. Kuma tsab zan fitar da kaina na bar ka a ciki. Domin ba ni na kama shi ba n na rufe shi ba ban san inda aka ajiye shi ba. Kuma ba ka da wata hujjar da za ka ce ni na saka ka. Tun wuri ka je nemi mafita ba zai ka nemo duk in da Asad ya shiga a faɗin garin nan.'
Murmushi Doctor ya yi a kafin ya ce
"Me kake ci na baki na zuba wandada suka kama shi har ya samu guduwa suna nan ana neman ruwa a jallo.
Hankalinsu ya yi masifar tashi sosai don gudun tonuwar asirinsu."
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect
*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*
*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*
Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.
Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.
Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩
1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more
Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.
*YAR GIDAN TAFIDA*
Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.
*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.
Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯
Page4️⃣9️⃣
"Me kake ci na baka na zuba? Waɗan da suka kama shi har ya samu guduwa suna nan suna nemansa ruwa a jallo. Hankalinsu ya yi masifar tashi sosai don gudun tonuwar asirinsu."
Tsuki Kamal ya ja tare da cewa.
" Wannan kuma matsalar su ce, ko na ce matsalarku ce, don idan asiri ya tono dole kai ma sai an kama ka. Don kai ma maci amana ne, kana matsayin likitansa amma suka siye ka don ka dinga yi masa alluran da da zai illata rayuwarsa ko? Ba su ne suke cikin tashin hankali ba kai ma kanka kana cikin tashin hankali don na tabbatar ba zai rasa sanin ko kai waye ba."
Cikin Doctor ne ya ɗori ruwa domin ya san tabbas asirinsa zai tonu, dan wasu lokutan ma idan ya je don yi masa alluran yana cikin hayyacinsa, bisa la'akari da kallon da yake jifansa da shi wasu lokutan, sai dai bakinsa da hannunsa suna ɗaure ba halin ya ɗauki wani matakin akansa. Ya ɗauka a hankali alluran za su yi tasiri a jikinsa ne har ya kai ga rasa rayuwarsa, amma abun mamaki sai ga Asadullah garau sai abun da ba'a rasa ba. A zuciyarsa ya ce.
'Wane irin mutum ne shi?'
Sai ji ya yi Kamal ya ce.
"Ni ma tambayar da na sha yi wa kai na kenan, irin sukar da muka yi masa da wuƙa amma bai mutu ba."
Sai a lokcin Doctor ya san cewa maganar zuci ce ta fito fili.
"Ba na da lokacin ɓata wa alƙawari ka yi mani akan cewa za ka biya ni kuɗin..."
Tsawar da Kamal ya daka masa ne ya saka shi dakawa da maganar da yake yi.
"Idan ma ka na mafarki kan cewa zan. Aka kudi ka farka. Domin kuwa na saka ka kashe shi ka saka ba amfanin da ka yi mani, sannan idan har kana son na cika maka alkawarin da na maka to ya zama dole ka nemo in da yake ka kashe shi, idan ba haka ba kada na sake ganinka a in da nake."
Ya ƙarasa maganar cike da gargaɗi.
Wace wa ya yi ya bar Doctor yana bin sa da kallo.
Karshe shi ma ya wuce don barin gidan yarin.
_Zahrah_
Sanye take cikin riga da siket na atamfar, ta yafa mayafi da zai sauka ya rufe jikinta kasancewar rigar ta kama ta, kuma ta san akwai maza a gidan ba muharramanta ba ne. Wayarta ce ta soma ringing ganin Ammar ne ya saki mumrmushi ta zauna bakin gadon tana amsa wayarsa.
kasancewar yau Juma'a kuma dama duk ranar jama'a wajibi ne ilahirin jama'ar gidan su ci abinci a tare. Kamar kowane juma'a yau ma wasu na zaune a dinning wasu na shirin fitowa.
Dad, Abba, Mummy, Umma ne a dinning table ɗin.
Abbi ya karaso wajen bakinsa ɗauke da sallama. Ba wanda ya amsa masa cikinsu kamar kullum. Ba sa amsa wa kuma baya fasa yi masu, sai dai idan suna ganin Papa da Dada ne suke masa masa sallama har da gaiswa na ganin Idanu.
Zama ya yi bayan ya ja kujera ya zauna. Zamansa kenan sai ga Ummi ta karaso wajen sanye take da doguwar rigar Abaya.
Sallama ta yi ita ma haka ba wanda ya amsa sai mijinta Abbi yana sakar mata mumrmushi.
Kafin ya zauna ne sai ga Yaa Mansur da Faisal sun fito daga part ɗin su. Fira suke yi suna dariya.
Suka karaso wajen suka gaida Dad da Abba, sai Mom da Umma. Ba su gaida Abbi da Ummi ba kamar yadda iyayensu suka ɗora su a tafarkin gaba da ƙanin na su da iyalansu.
Sunyi Laila ma ta yafi daga part ɗin ta tana waya da wata ƙa ƙawarta. Bayan ta zauna ne ta yi wa kawarta sallamarsa ajiye wayar.
Kallon Dad, ta yi ta ce.
"Yaya ina kwana?"
Ya amsa mata cikin walwala kamar kullum. Sannan ta kalli Abba ta ce.
"Yaya Ina kwana."
"Lafiya lau Autar Dada ya kike?"
"Alhamdulillah"
Suka gaisa da su Mummy da su Mummy da Umma.
Mansur da Faisal suka gaishe ta, ta amsa tana saka masu albarka.
Abbi duk da kasancewar sa Yaya ne ne ga Sunyi Laila amma hakan bai hana shi ce mata.
"Ina kwana Laila?"
"Auhm mutum dai ba Zuciya kamar ya yar kare ya ɗauka. Ko dole ne sai na yi maka magana.
"Wai Abbi ka dole ne sai ka shiga sabgar su ne, ko a wajen Allah ba ka da laifi ka fita hakkinsu . Ka yi masu magana sau daya biyu uku ba sa amsa maka to meye amfanin ci gaba da gaishe su. Ka yi rayuwrka da Ummi da Yaa Mahmud ga Auta Zahrah mun ishe ku don Allah ku fita daga harkar mutanen nan. Wanda ya ce baya yi da kai ka manta da shi ka ɗauka cewa sun mutu."
"To fitsararre mara kunya, dama na san sai kai da ka fita Zakka."
Ta karasa maganar tana yi wa Sadik wani banzan kallo. Taɓe baki ya yi da niyyar zai sake mayar mata da martani Ummi ta daka masa tsawa. Dole ta saka ya yi shiru.
"Ƙanwar mahaifinka ce ita ce abikinyar sa'insa a gare ka?"
"Ummi don ki bar ni na fada masu gaskiya. Ita da take masa rashin kunya ai Yaya ne a wajen ta. Me kuka yi masu a ce kuma jini ɗaya uwa ɗaya uba ɗaya amma ku ware mutum ɗaya ku ɗora masa karan tsana bisa wani banzan dalilin ku da bai da tushe."
Abba ya tashi a fusace ya ce.
"Za ka rufe wa mutane ba ki ko sai na saka yanzu an koya maka tarbiyyar da iyayeka suka ba ka?"
"Ai a gidan nan ban ga mai tarbiyyar da zai koya mani tarbiyyar da aka kasa ba ni ba."
"Ka iya bakinka Sadik wallahi yanzu zan kwaɓe riga mu daku a nan a banbance tsakanin aya da tsakuwa."
Mansur ne ya yi maganar yana tashi tsaye yana huci.
Dariya Sadik ya yi tare da cewa.
"Oh ashe ba dad'i ka ga ana cin mutumcin iyayenka ka ƙyale, da ake yi wa Mahaifina ina kallo har da murnushi kake, yanzu da na mayarwa mahaifinka da martani ka ji zafi ko?"
Yaa Mahmud ne ya rike hannun ƙanin na sa Sadik yana cewa
"Ya isa haka Sadik."
Zai yi magana amma ganin kallon da Abbi da Ummi ke masa ya saka ya yi shiru. Don da ido sukan tsawatar da yaransu kuma su hanu.
Daidai lokacin Maryam, Nadiya, Kausar, Nabeela suka fito daga kitchen hannunsu rike da food flask. Kasancewar Hilal ya saka su yin girkin dole tun daga ranar tare da su ake girki kuma suke service ɗin mutanen gidan dokar da Hilal ya saka masu kenan.
Papa da Dada ne suka fito tun daga nesa suka hango Mansur da Sadik suna yi wa junansu kallo mai cike da gargaɗin juna.
Gyaran murya Papa ya yi wanda ya saka kowa shiga taitayinsa. Don ba wanda baya baya shakkar Papa a familynsu gabaɗaya.
Kowa ya nemi wurin zama. Sai dai masu zuba abinci ne kawai a tsaye suna serving ɗin su.
Kowa ya gaida Papa da Dada cikin girmamawa. Ganin ba Zahrah ne ya sa Papa cewa.
"Ina Zahrah?"
Ummi ta ce.
"Na barta ta fito wanka ta ce tana zuwa ga ta shiru har yanzu."
"Idan ta ji yunwa ai za ta fito da kanta, yunwa ba ƙanwar uwa ba ce uwa ce da kanta."
Aunty Laila ta yi maganar tana tura soyayyen ƙwai a baki.
Kafin kowa ya yi magana sai ga Zaharah ta ƙaraso da sallama. Kasancewar ta gaida iayakinta da yayunta shi ya sa da ta yi sallama ta suka amsa gabaɗaya, don su Papa na wajen ne kowa ya amsa mata.
Cikin girmamawa ta durkusa ta gaida Papa da Dada. Suka amsa mata cikin sakin fuska da walwala cike da so da ƙaunar da suke mata. Kuma ba komai ya saka suke son ta ba sai don halayyar ta da ɗabi'unta wanda ya sha banbanci da sauran yaran gidan.
Daddy ta fara gaisar wa, ya amsa mata kamar an yi masa dole. Daga nan ta gaida Abba shi ma haka ya amsa mata.
Daga nan ta gaida su Mom suka yi kamar ba su ji ba, sai da Papa ya yi fada suka ba shi haƙuri wai ba su ji ba ne.
Kallon su Mansur ta yi da niyyar gaishe su duk da ta san ba amsawa za su ba Sadik ya dakatar da ita ta hanyar watsa mata harara, tura baki ta yi ta zauna. Zaman ta ke da wuya sai ga kiran Ammar ya shigo wayarta.
Ɗauka ta yi tare da yin Salma ta ce.
"Assalamu alaikum, Yaa Ammar zan kira ka anijma."
Gabaɗaya kowa ya kalle ta, Nabeela da Kausar na sakin tsuki a tare.
Ruwan shayi kawai ta ɗiba sai bread. Don ba z ta iya cin girkin su ba, don ba dad'i yake yi mata ba. Dada da aka zuba mata farfesu kasa ci ta yi, Papa ne ya ɗan ci dankalin turawa ya ɗan ci, nan ma ya ji bai soyu ba. Haka ya ajiye .
Yaa Mahmud da Yaa Sadik da suka saba da daddaɗan girkin Ummi da na Zahrah. Ba za su iya cin wannan ba.
A baya suna cin na masu aikin, amma tun da yanzu ƴan matan ba sa yarda masu aikin su nuna masu yadda za su yi komai, take za su fara masu masifa.
Abincin dai ga shi nan haka dai kowa ya ɗan tsakura ba su iya cin na kirki ba.
Haka dai a hankali kowa ya watse da wajen masu zuwa office suka tafi.
_Asadullah_
Fitowa ta yi daga bedroom ɗin sa zuwa falon. Daidai lokacin da kukunsa ya ke jera abinci a dinning table. Kasancewar yau Barrister Haris ya nemo masa kuku da zai dinga dafa masu abinci a gidan.
Sualaiman ne ya shigo kasancewar sun yi magana ya ce masa ya ƙaraso. Hakan ya saka ya fito.
Bayan kukun ya gama jera abincin ne ya karaso wajen su yana cewa
"Barka da dare Yallaɓai."
Kai ya jinjina masa ba tare da ya ce komai ba.
"An kammala jera komai a dinning table."
"Okay sannu da aiki."
Ya amsa yana barin wajen.
Asadullah ya kalli Sulaiman ya ce.
"Idan Allah ya kai mu da safe za su tafi tare da Doctor Isma'il. Sai dai mu yi mata addu'ar Allah ya bata lafiya. Na san duk in da iyayenta suke hankalinsu ya tashi sakamakon rashin sanin halin da take ciki ba."
Jinjina kai Sulaiman ya yi sannan ya ce.
"Gaskiya ne, da irin wannan gara ko gawar ɗanka ne ka gani ka san cewa ka rasa shi da rashin sanin halin da yake ciki."
"Ka gwada yin bincike ko Allah zai sa a samu bayanin in da iyayenta suke."
"Okay sir."
Sannan abu na biyu, ina son duk in da family Doctor na mu yake, ka tabbatar ka kawo Mani shi a cikin gidan nan, saboda duk da wani lokacin ba na sanin abin da ke faruwa amma tabbas ba zan mance fuskarsa ba, kamar yadda na baka labarin komai."
"Bayan shi ba za ka iya tuna komai ba?"
"Ba abin da zan iya tunawa, sai dai yakan yi waya a gabana, da alama umarni yake karba, bayan ya yi Mani allura ba na sake sanin komai."
"Kar ka damu zan kamo shi zai yi bayanin wadanda suka saka shi wannan aiki."
"Ka tashi ka je ka ci abinci."
Tashi ya yi ya nufi dinning area.
Asadullah kuwa ya nufi ɗakin da su Jidderh suke. Sai da ya yi knocking Aninsa ta amsa sannan ya shiga .
Jidderh na zaune tana kallon TV kamar Idanunta za su fito, Anisa na zaune a gefenta tana danne-danne a waya.
"Barka da dare."
Anisa ta faɗa tana ajiye wayarta.
Zama ya yi gefen Jidderh yana sakin murmushi.
"Kallo ne haka kamar za ki fitar da Idanun waje?"
Kallonsa ta yi ganin yana mumrmushi ita ma ta masa tana kallonsa.
"Gobe da safe za ku tafi Allah ya baki lafiya."
"Amin."
Cewar Anisa tana murmushi, kallonta ya yi ya ga shi take kallo fuskarta dauke da murmushi.
"Ku fito ku ci abinci."
"To za mu fito."
Ya fita ya bar su. Yana fita Anisa ta dauki waya ta kira Barrister Haris.
Yana ɗagawa suka gaisa .
"Wai Yaya Haris Meye tsakanin Asad da yarinyar nan, ina nufi alƙarsu da ita?"
",Aiki ya kai ki ko binciken dangantakar su da yarinyar?"
"Aiki mana."
"To ki tsaya iya abinda ke gabanki."
Tura baki ta yi kafin ta kashe wayarta.
Tashi ta yi tana sake zaman riga da siket dake jinkinta, wanda kamar za ta yi nishi su yage. Don sun bayyanar da surar jikinta sosai.
Ba tare da mayafi ko hijabi ba ta tashi tana jan hannun Jidderh wacce ke zaune sanye da doguwar riga kanta ba ɗankwali. Gashinta da Anisa ta gyara mata ya sauka a kafaɗarta da ta tufke mata shi.
Jin kishin yarinyar ta yi don haka ta dauki hula bayan ta nannaɗe mata gashin ta saka mata hula don kar ma ya birge Asadullah idan suka je.
Tare suka fita tana rike da hannunta suka fito daidai lokacin da Sualaiman zai tafi, Asadullah na sake tabbatar masa gobe ya tabbatar ta zo da Family Doctor na su ko ta halin yaya.
"Okay sir, good night."
Ya faɗa ya fice.
Asadullah na zaune a dinning chair yana shan shayi, Anisa ta zaunar da Jidderh kan kujera sannan ta zauna ka. Kujerar dake fuskantar Asad.
Zuba wa Jidderh jollop ɗin cuscus ta yi sannan ta zuba na ta, sai farfesun kazar da ta zuba masu. Nan suka hau ci bayan ta zuba masu ruwa da lemo.
"Yallaɓai na zuba maka ne?"
"No need."
Ya faɗa. Yana kallon Jidderh dake cin abinci.
"Amma na ga ruwan shayi ba abinda zai maka."
"Haka nake buƙata."
Ganin yadda hankalinsa ke kan Jidderh ya saka Anisa ba wa Jidderh kulawa na musamman har tana ba ta abinci a baki. Hakan ba karamin daɗi ya masa ba. Har ya saki jiki suka fara fira da Anisa kuma duk akan Jidderh.
Tana ƙoƙarin bugun cikinsa don gane dangantar dake tsakanin su. Amma bai ba ta damar jin abinda take son ji ba.
Sai dai ta gane cewa ta hanyar Jidderh ne kawai haƙanta za ta cin ma ruwa. Don haka sai nata saki murmushi da ita kadai ta san ma'anarsa.
Kati ya mika mata mai ɗauke da lambar wayarsa.
"Idan kun je can sai ki nemi ni bayan an saka maki kayi na can ƙasar."
Tashi ya yi yana yi masu sai da safe ya haura upstairs. Anisa na masa murmushi har ya ɓacewa ganinta.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
*Albishir! Albishir!! Albishir!!!*
Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku.
Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇
Flasks
Cups
Dinnerset
Kitchenware
Pot
Jugs
Food processor
bedsheet lamps
Second hand gas
Duk wani kitchens items