Showing 84001 words to 87000 words out of 154779 words
tare da cewa.
"Mu bar wajen nan."
Daga jin yadda ya yi maganar zai tabbatar maka da cewa a gajiye yake.
"Okay sir Amma wannan fa?"
Ya yi maganar yana nuna Direban.
"Tare za mu tafi."
"Okay mu je ko?"
Asadullah ya kalli Jidderh ya ce .
"Zo mu je."
Bin bayansu take yi har wajen motar, sai kallonta Asad yake yi kamar ba ita ba. Asad ya bude mata bayan motar ta zauna ya zauna gefenta yayin da direban ya shiga wajan me zaman banza.
"Ina za mu je mansion ko?"
Kai ya girgiza sannan ya ce.
"Sabbon gidan da na siya ana gobe zan ɓata."
Kai kawai ya jinjina sannan ya yi wa motar key suka bar wajen.
Doguwar tafiya suka yi sannan suka isa wani gida. Horn suka yi a ƙofar tangamemen gate ɗin gadin ne ya leƙo yana duban motar.
Sai da Asadullah ya ja facemask din dake fuskarsa ƙasa ya Gandhi sannan ya nufi gate ɗin a guje ya wangale masu shi.
Shiga suka yi cikin gidan in da Barrister Haris ya nufi parking space ya yi parking suka fito.
Motoci guda biyu ne a parking lot ɗin.
Maigadi ya zo ya zube yana gaida Asadullah. Shi dai har lokacin bai yi magana ba hannu kawai ya ɗaga masa. Zuwa lokacin Barrister Haris ya fahimci Asad baya son wannan direban da suke tare da shi ya san waye Asad. Don bai yarda ya bude fuskarsa ba da alama baya son Direban nan ya gan shi ne .
Fitwawa suka yi gabaɗaya suka nufi ƙofar da za ta sada su da main falon gidan.
Password ya danna a jikin ƙofar Sannan ƙofar ta bude, juyowa ya yi ya kalle su sannan ya masu alamar su shigo.
Bayan sun shigo ne suka tsaya a babban falon gidan. Nan direba ya baki baki tana kallon Aljannat duniya.
Jidderh dai kamar mutum mutumi haka take.
Ciki Asad ya shiga yayin da Barrister Haris ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun dake falon.
Kallon Direban da Jidderh ya yi tare da cewa.
"Ku zauna mana."
"Direban ya kalli Barrister Haris ya zauna a ƙasa saman Centre Carpet dake tsakiyar falon."
Jidderh dai kallon ƙasa kawai take yi. Kallon Direban ya yi daidai lokacin da Asad ya dawo.
"Tare da yarinyar nan kake ne?"
"A'a Yallaɓai ta dai je tashar mu ta ce tana son na zo na dauke ta ita da wani mutum, ta fada Mani unguwar da lokacin da zanzo. Ya biya ni shi ne na je na dauke su amma ban san ta ba "
Asad bai ce komai ba, ya zauna kan kujerar ya rubuta check cek ɗin kudi ya mikawa Direban.
"Karbi wannan Naira miliyan goma ne, na san za su ishe ka ka gyara motar nan ka mayar wa mai ita , sannan kai ma ka ajiye ta ka ta motar ka cigaba da sana'a."
Zubawa Direban ya yi yana godiya tare da kallon cek ɗin kudin yana kukan farin ciki yana jerowa Asad albarka.
Da hannu ya masa alamar ya tafi don ya kosa ya bude fuskarsa kada wannan mutum ya gane shi kasancewar sa sanannen mutum a garin.
Bayan fitarsa ya zubawa Jidderh idanu na wasu seconds sannan ya cire p cap dake kansa. Ya zare facemask kyakkyawar fuskarsa ta bayyana.
Har lokacin idanunsa na kan Jidderh
"Zauna mana har yanzu kima tsaye, ki zauna kafin mu yi magana na kai ki har gida."
Ya uku maganar a gajiye don har yanzu jikinsa ba ƙarfi.
Ganin duk maganar da yake yi ba ta iya cewa komai ba, kuma har lokacin Idanunta na ƙasa abun ya bashi mamaki matuka.
"Meye ma sunanki?"
Nan ma shiru kuma bata kalle shi ba. Zuwa can ya tuno da sunar ya ce.
"Jidderh ko?"
Nan ma shiru. Kallonta yake yi da alama ba ta jin me yake cewa.
Kiran sunanta yake yi ta yi shiru ba ta ɗaga kai ta kalle shi ba ballantana ya saka ran tana jin sa.
Cikin mamaki ya karasa yana kallonta . Ita ma shi take kallo a lokacin da ya tsaya gabanta. Alamar ta zauna ya yi mata akan kujera.
Kallonsa ta yi ta gane yana nufin ta zauna ne sannan ta zauna.
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un. Lafiya fa muka fito daga mansion tana magana tana komai amma yanzu kamar an canza ta."
"Wai me ke faruwa ne kuma wace ce ita ?"
"Barrister na gaji yanzu ina bukatar hutawa. Ka kira Mani Doctor Isma'il ya zo ya duba ni, kuma bai san gidan ba, ko za ka iya sauko mani shi daga nan ka yi muna order na abici."
"Ina Doctor ɗin ka yake ?"
"Ba na son kowa ya san ina nan, ga gane ko?'
Jinjina kai Barrister Haris ya yi sannan ya ce
,"Ba ka da matsala bari na je na dawo."
Yana fadar haka ya fice.
Asad ya tsaya tana ƙare wa Jidderh kallo sannan ya ce.
"Bari na shiga na yi wanka kin ji.,?'
Nan ma ba alamar ta ji shi, sama ya nufa ta bishi da kallo.
Bayan kamar awa ɗaya da fitar Barrister Haris ya dawo bayansa tare da wani mutum na sanye cikin Suit.
Mamaki ta kama Doctor yana kallon Asad dake saukowa ƙasa. Da alama ya yi wanka ne don ya sanye yake da riga JC Red colour sai wando three-quarter black colour sai ƙamshi yake yi .
"Sir dama kana nan?"
Murmushi Asad ya sake sannan ya ce.
"Ina nan amma ba na din kowa ya sani sirri ne."
Jinjina kai Dr Isma'il ya yi tare da y.
"Sirrinka ba wanda zai ji dai dai idan kai ne k fitar da kayanka."
Barrister Haris ya ajewa Jidderh leda ɗaya na takeaway da ya yo masu .
Asad ya bude mata fry rice ne da siyayarn naman kaza, sai Lemu mai sanyi da ruwa.
Alama ya mata da ta ci, sai ta fara ci shi kuma ya ajiye ɗyar ledar a Centre table dake gabansa.
"Barrister za ka iya komawa wajen aikinka amma ina bukatar ganinka zuwa dare karfe takwas. Yanzu zan shiga Dr ya duba ni don har ruwa sai ya ƙara Mani."
"Ina nan tare da kai Asad ba in da zan je."
Tare suka shiga su uku wani ɗaki sai Jidderh dake zaune tana tsakuran abinci tana ci.
Gwaje-gwaje Doctor Isma'il ya yi masa sannan ya bashi magunguna ya masa ƙarin ruwa a jikinsa.
Take barci ya ɗauke shi don ya masa allurar. Ganin ya yi barci ne ya saka Dr Isma'il cewa.
"Barrister kana tare da shi ko?"
Jinjina kai ya yi tare da cewa.
"Ina sha Allah."
"Idan ruwan ya kare ka cire masa, in sha Allah idan ya tashi zai ji karfin jikinsa. Na ga jininsa ma ya hau sai dai abinda ke bani mamaki yaushe ya fara amfani da abubuwan da suke gusar masa da hankali ya shiga cikin wani hali kamar wanda baya cikin hayyacinsa?"
Shiru Barrister Haris ya yi kafin ya ce.
"Kana nufin Asad yana shaye-shaye ne?"
"Ba zan ce ba gaskiya, amma yanayin halin da yake ciki tabbas wani lokacin hankalinsa na gushewa ya zama kamar yana cikin maye."
Shiru Barrister ya yi kafin ya saki wata ajiyar zuciya ya ce.
"Aikinka ne kuma ba zan ƙaryata ka akan abokinka ba, sai dai ina da yaƙinin cewa Asad ba zai taɓa ta'ammali da kayan maye ba, sai sai akwai wani ɓoyayyayen al'amarin da ya faru da shi wanda mu ba mu sani ba "
"Allah ya kyauta, ni zan tafi."
Sallama suka yi ya fice ya ja masa kofar.
A can *Asadullah mansion* kuwa sai da aka samu nasar kashe gobarar sannan hankalin kowa ya kwanta. Sai sai abun da ya ke ba kowa mamaki shi ne yadda wutar ya tashi a part ɗin da ba kowa a ciki. Ta ya ya hakan za ta faru?"
Tamabayar da Uncle Adam ke ta yi kenan.
Nasir ya kalli mahaifin nasa cikin damuwa ya ce
"Dad wallahi ni ma abun ya ɗaure mani kai matuka, da akwai mutane sai a ce ko ko sun kunna electronic ne ko makamancin haka."
Mom cikin damuwa take cewa.
"Allah ya san ko mene ne, kuka a godewa Allah tun da ba'ayi asarar rai ba."
Nan kowa ya dinga jinjina lamarin, Sulaiman da dawowarsa kenan ya tarar da wannan tashin hankali. Don dama shi tunda aka nemi ubangidansa aka rasa bai cika zama mansion ɗin ba. Da ka ganshi ka san yana cikin damuwa.
Kallon abinda ke faruwa ya yi sannan ya nemi karin bayani daga wajan ɗaya daga cikin abokan aikinsa. Nan aka sanar da shi komai.
Jinjina kai ya yi tare da cewa.
"Wannan ba gobara ba ne na haka kawai ba, shirya shi aka yi da wata manufa."
Jinjina kai ya yi alamar tabbatar wa, sannan ya cire bakin glass dake fuskarsa.
"Ko shakka babu ba yadda za'ayi wurin nan ya kama da wuta sai dai idan saka wutar aka yi. "
"Meye hujjar ka na cewa haka kuma Meye amfanin saka wutar?"
Naseer ya tambaya yana kallon Sulaiman da ya ji tambayar
"Kada ka damu zan samo hujja akan haka matukar an bar wata wata hujjar, sai sai idan mai aikin yana da matukar wayau bai saki layi ba."
Yana fadar haka ya zagaya in da wutar ya kama don neman hujjar da zai gani.
*Washegari*
Ammar ya shirya don komawa UK, ya so a ce ya saka Zahrah a idanunsa amma hakan bai samu ba, ga shi kiran gaggawa ne aka yi masa. Don lokacin ko da ya shiga part ɗin Ummi wanda Dada ta tabbatar masa da cewa can ta kwana.
Ko da ya gaida Ummi yake tambayarsa jikin Zahrah ta sanar da shi da sauƙi tana barci.
Sallama ya mata ya tafi, sai da ya shiga kowane part ɗin gidan ya masu sallama sannan ya ya tafi in da Hilal ya yi masa rakiya har airport.
Sai da jirginsu ya tashi sannan ya dawo.
_Sulaiman_
Yana zagaye a wajen da abun ya faru sai ya hago wata jarka da aka jefar. Ƙarasawa ya yi wajen tare da sunkuyawa ya ɗauki galan ɗin fetur da Jidderh ta jefar. Shinshina wa ya yi ya tabbatar da fetur ne ya juyo kenan sai ya ji ya taka abu. Ɗaga ƙafarsa ya yi ya duba , ashana ce da ta ƙyasta bar shi a wajen.
Ɗauka ya yi ya dawo in da sauran mutanen suke, ɗaga galan ɗin fetur ya yi tare da ashana ya ce
"Ga hujjar da za ku yarda cewa wannan shiryayyen al"amai ne."
Gabaɗaya kowa ya zuba masa idanu ana kallon galan da fetur.
"Waye ya kawo wannan a nan?"
Kowa ya yi shiru zuciyoyinsu cike da mamaki ne hakan ya ke nufi.
Ɗaya daga cikin security dake gate ɗin ne ya ce.
"Tabbas akwai wacce ta shigo da da wannan cikin masu aikin gidan nan."
Kowa ya juya yana kallonsa, Uncle Adam ya ce
"Duk wanda aka kama da aikata wannan al'amarin sai ya yi nadama. Don sai na tabbatar ya tafi gidan yari."
Sulaiman ya ce
"To yanzu ta hanya daya za'a ga wanda ya shigo da shi tabbas za'a iya gane ko waye ta hanyar CCTV Camera."
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page4️⃣3️⃣
"To yanzu ta hanya daya za'a ga wanda ya shigo da shi, tabbas za'a iya gano wa ta hanyar CCTV Camera."
Gabaɗaya sun ji dadin jin hakan sosai, musamman Mom ta ce .
"Ko ma waye sai na tabbatar ya tafi gidan yari , wani irin ta'addaci kenan?"
Mami ce ta taɓe baki tana cewa.
"Ai wannan ma ya zama dole a gano don ku waye shirin yin kisan kai ya yi, don idan ba don Allah ya tsare ba ai sai sai dai aji labarin mutuwar mu. Don me ne ke kusa da part ɗin da abun ya faru.
Aunty ce ta ce.
Sai dai wani hanzarin ba gudu ba, Alhaji fa ɗan lelensa ne ai za su iya wannan aiki, don na ga su ne suke binciko duk abinda ya faru daga cikin ɗakinsu.,"
Idan suka ji an ce ɗan lelensa sun ɗan Asad take nufi, kai Sulaiman ya jinjina alamar haka ne.
In da Aunty ta cigaba da cewa .
"Sai dai a jira Alhaji daga tafiyar da ya yi, don ba zai yiwu a shiga ɗakinsa kai tsaye ba."
Ta yi maganar tana jan hannun ƴarta Suhailat suka koma ciki. Kowa ya bita da kalli.
Wayar Sulaiman ne ya yi ruri, yana dubawa ya ga lauyan uban gidansa ke kira.
Ya ɗaga tare da yin sallama.
Barrister Haris ya amsa tare da cewa.
"Idan kana cikin mutane ne ka koma gefe."
Jin haka ya saka shi komawa gefe.
Bayan sun gaisa ne Barrister ya sanar da shi in da zai zo ya same shi.
Jin wajen ya saka Sulaiman tambayarsa lafiya don ya san su biyu ne kawai suka san Asad na da gidan.
Don haka ya ce.
"Ko dai an samu cigaba ne ta hanyar ka?"
Ka dai zo kawai ka same ni yanzu ba tare da ɓata lokaci ba
Yana jin haka ya faki idanun mutanen gidan ya fice bai tsaya ɗaukar mota ba, don ya san yanzu Uncle Adam zai fara tambayarsa.
_Zahrah_
Ko da ta tashi daga barci Ummi ke sanar da ita cewa Ammar ya zo sallamarta ya koma. Sai ta ji ba dad'i don ta so su yi sallama da shi ta gan shi ya gan ta. Ko don kulawar da ya nuna mata.
Kasancewar rana cin abinci Ummin ke sanar mata, don haka sai ta faɗa duniyar tunani ta cigaba da juya cikali a cikin ruwan tea.
Ganin daga fada mata ta faɗa duniyar tunani ne ya sa Ummi kiran sunanta.
"Zahrah"
Ɗaga kai ta yi tana kallon Ummi sannan ta ce.
"Na'am Ummina."
"Meye tsakaninki da shi ne?"
"Ba komai Ummi?"
"Ban gane ba komai ba bayan na san haka nan kawai ba zai dinga shigowa nan ba, kasancewar abokinsa da yake zuwa gidan don shi bai taɓa shigowa nan da sunan gaishe su ba ballantana abokinsa.
Sau ɗaya Ummi ta ga Hilal ya shigo part ɗin ta, lokcin da ya saka Zahrah punishment tsabar wahala sai da ciwonta ya tashi ta ga cikin dare ya shigo part ɗin. Duk da ba ta ga shigowar sa a lokacin ba amma ta ga fitarsa bayan ya ɗauki alluran ciwon Zahrah, kuma har yau bai sake zuwa ko bakin part ɗin na su ba.
"Meye sunansa?"
Ummi ta tamabaya yayin da ta kafe Zahrah da idanu.
"Ummi wai so na yake yi?"
"Hmm na san za'a rina, gaskiya ba na son matsala ina zaman zamana. Yaron nan abokin Hilal ne kuma sanin kanki ne cewa Hilal da iyayensa ba za su goyi bayan ya aure ki ba. Musamman Gwaggon ku Laila da sai ta san yadda ta yi ta wargaza komai, kuma na san za ta samu goyon bayan Mahaifiyar Hilal da ta kasance kamar ƙawa ce a wajen mahaifiyar Ammar sakamakon abotarsu. Don haka kin fi kowa sanin ƙiyayyar da suke maki ba za su taba bari iyayen Ammar su yarda ɗan su ya aure ki ba, baki da mugun tabo amma sai sun yaɓa maki. Don haka lna mai shawartarki kada ki saka soyayyarsa a zuciyarki ballantana ya zame maki ƙalubale a gaba."
Shiru ta yi Allah ya sani tana son Ammar, sai dai Ummi ta yi gaskiya da ta tunatar da ita haka, ga shi dama akan Idanunta Aunty Laila ta fara ɓata da mugayan kalamai amma ya ce ya ji ya gani."
Ƙwalla ne suka cika mata idanu ta kauda kai tana gogewa. Ummi dai ta tashi ta bar ta a dinning area.
_Asadullah_
Tare da Barrister Haris suka sauko Downstairs. Har lokacin Jidderh na zaune, abincin da aka ajiye mata tsakura kawai ta yi. Idanunsu a kanta.
Da sauri Asad ya karaso wajen da take ya sunkuya a gabanta.
"Me ya saka baki ci abinci ba?"
Kallonsa kawai take ko motsawa ba ta yi ba.
"Me kike so ki ci?"
Nan ma shiru, sai da ya yi magana sau uku ba ta tanka ba kuma ba alamar tana jin me yake cewa.
Cikin damuwa ya kalli Barrister Haris tare da cewa
"Akwai matsala fa?"
"Na me?"
Ya tambaya idanunsa akansa yana neman ƙarin bayani.
"Tana magana fa lokacin da muka taho tare, amma yanzu ba ta magana da alama ma ba ta ji?"
Shiru Barrister ya yi tare da cewa.
"Wai daga ina kuke?"
"Daga mansion mana?"
Da mamaki yake kallonsa tare da cewa.
"Duk wannan abun dake faruwa kana cikin ƙasar nan kuma a garin nan a cikin Asadullah mansion?"
"Yanzu ba ta wanan nake ba, zan sanar da kai komai, yanzu ƴar mutane da ta yi kasada saboda ni nake so na ga ta dawo daidai."
Har Barrister Haris zai tambaye shi wace kasadar sai ya fasa, don ya ce zai sanar da shi, duk da abun ya ɗaure masa kai.
"Ina tunanin ko accident da muka samu ya sa yarinyar nan ta shiga cikin wani hali. Da na ga da waya a hannunta muka bar can amma yanzu ba waya a tare da ita ko ta yar da wayar a mota ne?"
Jinjina kai Barrister ya yi sannan ya ce.
"Amma ai accident ɗin da sauki na ga dukanku uku ba wanda ya ji ko ƙwarzane Allah ya kare ku, ba na tunanin accident da kuka yi zai iya saka ta cikin condition ɗin."
"Ta ya zaka ce haka bayan lafiya lau take."
Sulaiman ne ya danna ƙararrswa, ta cikin glass suka hango shi. Don na ciki yana ganin na waje, amma na waje baya ganin wanda ke ciki. Wani remote ne Asad ya ɗauka akan Centre table ya danna. Take ƙofar ta buɗe Sulaiman ya shigo.
Baki sake da mamaki Sulaiman ke kallon Asadullah.
"Sir kai ne?"
Jinina masa kai ya yi tare da cewa.
"Ni ne?"
"Sir saukan yaushe a ƙasar tafiya ba sanarwa, har ina ƙaryata masu cewa ka bar ƙasar na ce ban ga fitanka ba."
"Daga kai sai Barrister Haris wato lauyana ku biyu ne kuka san ina da wannan gidan, wanda na mallake shi ko mahaifina bai san da shi ba, ba wai ba boye masa ba ne sai dai na so na kawo shi ne bayan komai ya kammala Allah bai yi ba aka neme ni aka rasa. Don haka ba na son kowa ya san da ma dawo sai lokacin da na bukata."
Da mamaki Sulaiman yake kallon uban gidan nasa, a hankali ya ce.
"Sir ba za ka koma can mansion ɗin ba ne, kuma na ga Dad da Mom sun nuna damuwa na rashin ka har da su kar a sanar da su?"
"Eh."
Ya faɗa a takaice. Sai a lokacin Sulaiman ya lura da Jidderh,