Showing 18001 words to 21000 words out of 154779 words

Chapter 7 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6259

ba. Kamfanoni gidajen man fetur hannayen jari duk banda sauran kadarorinsa sai na mallake, kuma duk shekara sai na haihu."

"Na ji ke mai wayo ko to ba zan hakura ba kuma idan kika nuna Mani bakin ciki da hassada to kin san dai wannan gidan da muke ciki gabaɗaya wanann Mansion ɗin mallakinsa ne, abaunda ake ci da sha da sutura da karatu da motoci da muke hawa duka daga cikin dukiyarsa ne ko? To wallahi kika yi wasa idan na sure shi sai na sa an kore ki daga cikin Asadullah Mansion."

A fusace Abida ta yi cikinta suka kacame da dambe.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z





*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page0️⃣9️⃣

A fusace Abida ta yi cikinta suka kacame da dambe.

Uncle Adam mamaki ya kama yaran nasa, daga magana har da dambe akan mutumin da bai ma san suna yi ba.

Mami ce ta daka masu tasowa wanda ya saka suka saki juna kowace na maida numfashi.

"Wani irin hakka ne wannan shi da kuke yi akansa ya san ma kuna yi ba. Kowace ta ɓace mani da gani sai mun yi shawara da mahaifinku akan wacce za'a bashi. Don ko ma wace ce cikinku ai duk ɗaya ne idan ɗaya ta samu arziki ai tamkar ita ce ta samu, saboda kowa ce za ta mori arzikin ƴar uwarta."

A'a Mamy tun da ni ce babba dole ne na fara yin aure kafin ita ta yi, kuma ni nafi dacewa da shi ba ita ba, ki daina cewa ai duk ɗaya ne domin duk shan inuwar gemu bai kai ya maƙogoro ba. Dan sai ta fara gina kanta kafin sai abin da ta ba mu sannan ki ce duk ɗaya?"

Maryam ce ta cigaba da yin magana ran ta a ɓace.

Nan suka fara sa'insa dakyar Uncle Adam ya shawo kan yaran nasa suka watse kowacce ta nufi ɗakinta.


_Fatima Zahrah_

Fitowa ta yi sanye da riga da wando hadi da hijabi har ƙasa, hijabin fari ne yayin da riga da wando na uniform ɗin ruwan toka.

Sanye da niƙab da ta ɗaura a fuskarta wanda idanunta kawai ake gani. Ko k'afarta ta saka Safa.

Sanyayyen ƙamshin turaren ta ke tashi daga jikinta. Ƙarasowa ta yi tana kallonsu ta ce.

"Zan tafi islamiyya sai na dawo."

Ba wanda ya amsa sai Dada da Papa sai kuma yayyun Zahrah. Jin ba wanda ya amsa ne ya saka Papa ya kalle tare da cewa.

"Ba ku ji ana sallamar ku ba ne?"

Ya yi maganar ransa a ɓacewanda hakan ya saka dole suka amsa mata da a dawo lafiya. Girgiza kansa ya yi cikin damuwa ya bar wajen.

Dada ta kalle ta tare da cewa.

"Me ya saka baki son shafa kwalli, sai ki bar fuska haka nan ba kwalliya sannan saka kuwalli ma ya zama Maki wahala.? Ga idanun ki masu matukar kyau da jan hakali sai ki bar su a koɗe ba kwalli."

Kallon ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ta jyi tare da cewa.

"Ke Tani je ki ɗakina ki ɗauko Mani kwalli a gaban dressing mirror."

Cikin girmamawa matar da aka kira da Tani ta amsa wa Dada tare da nufar ɓangaren Dada.

Minti ɗaya ta dawo ɗauke da Kwalli ta zo ta kawo wa Dada . Durkusa wa Zahrah ta yi a gaban Dada, nan Dada ta zizara mata kwalli a idanunta. Sai yaba kyawun idanun take yi kafin Zahrah mike ta nufi hanyar fita don zuwa makaranta.

Tana zuwa parking lot sai ɗaya daga cikin direbobin ya taso, don dama akasari shi ne yake kai ta makarantar.

Har zai buɗe mata bayan motar sai ga Yaa Mansur ya fito. Wani mugun kallo ya yi wa Zahrah kafin ya kalli direban da ya bude mata bayan motar ya ce.

"Kai Falalu zo ka ka kai ni wajen aiki na makara."

Kallonsa Zahrah ta yi don ta san da gangan yake yi, duka mazan gidan nan suna da motoci su suke driving da kansu. Yana ji tana faɗa ta yi letti amma yana cewa a kai shi.

Waige-waige ta fara yi don dama direbobin gidan su biyu ne ɗayan ya tafi garinsu ganin gida. Cikin damuwa ta kalli Ya Munsur ta ce.

"Ya dan Allah ka yi hakuri tun da ga motarka nan sai ka hau, ka taimaka ka bar shi ya kai ni na makara."

Wani banzan kallo ya mata kamar ba zai yi magana ba sannan ya ce.

"Kin fi ni sanin da motar ne, ko ubanki Salisu ne ya siya mani motar.?"

Daidai lokacin da Hilal ya fito daga ciki ya nufi motarsa, kallo ɗaya ya yi masu ya kau da kai ya shige motarsa tare da yi mata key.

Maigadi ya bude buɗe massa gate ya shige ya fice.

"Yaa Mansur don na roke ka akan uzurin da nake da shi kake zagin Abbi, amma kai ma ai ɗa ne a wajen sa kamar..."

"Dalla rufe mani baki kafin yanzu na sauya maki kamanni, Salisu Uban Mahmud da Sadik sai ke amma ban da Ni."

Da sauri ta kalle shi tana mamaki ko ba komai ai mahaifinta ƙanin mahaifinsa ne bai isa ya canza shi a matsayin kawunsa ba amma yake kiransa sunansa gatsai ba.

Juyawa ta yi ta nufi bakin gate don zuwa neman abin hawa. Shi kansa Falalu direba bai so haka ba, saboda mazan gidan kowa motarsa yake hawa. Neman ya ƙuntata rayuwar ta yake so.

Wani tunanin Zahrah ta yi ta dawo don ta roki ɗaya daga cikin Yayyunta su kai ta, don kafin ta karasa ta nemi abun hawa za ta ƙara makara.

Da sallama ta koma cikin falon, zuwa lokacin duk sun watse Yaa Sadik ne yana kokarin komawa ciki ya ji sallamarta. Amsawa ya yi tare da cewa

"Shalelen Dada lafiya ko mantuwa kika yi ?"

"A'a Yaa Sadik ban yi mantuwa ba, dan Allah ka taso ka kai ni na makara."

"Ina Falalu yake?"

"Yana nan."

"To me yasa ba ki je ya kai ki ba?"

"Na je har ya bude mani motar zan shiga shi ne Yaa Mansur ya ce wai ya kai shi wajan aiki."

"What, aiki fa kika ce, ina motarsa take ?"

Ba ta bashi amsa ba hakan ya saka ya kalle ta tare da cewa.

"Mu je."

Fita ta yi daga falon ya mara mata baya, suka nufi parking space, daidai lokacin da direban ke ƙoƙarin barin wajen. Da sauri Sadik ya tari gabansa tare da yi wa Falalu alamar tsaya.

Bayan Falalu ya tsayar da motar ne sai ya fito tare da cewa Sadik.

"Barka da safiya yallaɓai."

"Yauwa barka, ya aka yi Zahrah da ta riga fitowa daga gidan amma ba ka ɗauke ta ba, bayan ka san kowace safiya kake kai ta makaranta."

"Eh ina shirin kai ta ne har na bude mata marfin motar sai ga Mansur ya fito ya ce sai na fara kai shi wajen aiki."

Sadik ya karasa tare da bude murfin motar na baya in da Mansur yake zaune ya ce.

"Shiga ki zauna."

Wani kallo Mansur ya yi wa Sadik Sannan ya ce.

"Ba ka isa ba wallahi."

Ganin haka ya saka Zahrah cewa.

"Yaa Sadik ka bari kawai na je na nemi abun hawa idan ba za ka kai ni ba."

Ta yi maganar kamar wacce za ta yi kuka. Ba in da za ki je don neman abin hawa, kamar yadda kika ya saba kai ki zai dauke ki ya kai ki idan ya fara ajiye ki sai ya kai mo ma waye in da zai je."

Mansur ya fito ransa a ɓace yana yi wa Sadik wani kallo kafin ya ce.

"Ba ka isa ba wallahi me kake takama da shi ne da har za ka nemi rai na Mani wayo ko Mahmud zai yi Mani wannan iskancin ne ballantana kai?"

" Yaa Mahmud ka ce idan shi zai iya ɗaukar wulakancin da kuke yi ni ba zan iya ba. Akan me za'a kai yarinya makaranta za ka hana sai ka ce kai ne ka siya motar ko kake zuba man da ake amfani da ita, Papa ne ya siya ya ke zuba mai kuma ya ɗauki direban da zai dinga kai yara makaranta wanda saboda su ne aka siya motar. Don kai yara ba saboda mu dinga zuwa aiki da ita ba. Ba ka da hujjar hana ta a kai ta makaranta sai dai ka fito ka shiga taka motar ka je aiki?"

"Saboda ubanka Salisu ya siye motar?"

"Ba shi ya siya ba kamar yadda kai ma ba ubanka Adamu ya siya ba?"

Cikin ɓacin rai Mansur ya ce.

"Mahaifin nawa kake kira gatsai haka?"

"Oh ashe ba dad'i kake kiran nawa maihaifin kai tsaye, ai uba bai fi uba ba."

A zafafe Mansur ya fito daga cikin motar tare da cakumar Sadik shi ma Sadik kamar jiransa yake ya kai masa naushi a baki nan da nan bakinsa ya fashe.Mansur ma ya kai masa naushi ya fasa masa baki. Suka fara dukan juna suna dambe sosai.

Cikin tashin hankali Fatima Zahrah ta nufi cikin gidan aguje tana kuka.


_Asadullah_

Yana cikin kamfaninsa mai suna ASADULLAH VENTURES. Yana tsaye a ofishin sa yana kai da kawo wa.

Staff dake aiki a kamfanin suka ji ƙarar ringing bell. Ƙarar karaarrwar ne ya saka kowa ne ma'ikaci tunanin ko kiran me yau ake masu. Don da sun ji karar ƙararrawa sun san abu mai mahimmanci ne ya saka ake neman su.

Sai suka ji magana daga cikin kowace na'ura dake cikin ko'ina na kamfanin na cewa.

"The C.E.O of Asadullah ventures wants see us at the staffs comperene now."

Nan fa kowa ya mike suka tsaye tsaye daidai saitin wani glaass. Chief of staff meeting ya danna wani remote, bangon glass dake gabansu ya zama lifter haka kowa ya dinga shiga sai suka tsinci kansu a wani waje a ƙafarsa an yi rubutu ta cikin glass din sai shinning yake yi an rubuta . CONFERENCE ROOM.

Komai na wajen abun sha'awa ne. Ciki suka shiga su hamsin ne maza da mata, kowa yana sanye cikin shigar suits baƙi.

"ASADULLAH AHMAD THE CEO ASADULLAH VENTURES is coming closer to the comperene room."

Nan da nan dukkansu suka mike tsaye kafin ya ƙaraso wasu na gyara zaman Suit ɗin su wasu na gyara zaman necktie ɗin su .

Ƙamshin daddaɗen turarensa ne ya riga shi isowa gare su.

Zama ya yi ya yi sannan ya basu izinin zama.

Ko gaisuwa da suka yi bai amsa masu ba

Sakatarensa ya yi wa alama da hannu wanda hakan ya saka ya fita. Ba jimawa ya dawo tare da security dake kula da gate. Kallonsa ya yi tare da cewa.

"Kai ne ka ture yarinyar da ta zo neman taimako har ta faɗi ƙasa abincin ta ya zube kasa tana kuka ko?"

Wani wahalallen yawu securitn ya haɗiye tare da bude baki da niyyar yin magana Sir Asadullah ya ɗaga masa hannu alamar dakatarwa.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z






*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


*SADAUKARWA*

Wannan shafin sadaukarwa ne ga JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION. Haƙiƙa ku Jajirtattun ne kuma haziƙai, marubuta ƴan baiwa Allah ya ƙara mana ƙwarin guiwa.



Page1️⃣0️⃣

Wani wahalallen yawu securitn ya haɗiye tare da buɗe baki da niyyar yin magana. Sir Asadullah ya ɗaga masa hannu alamar dakatarwa.

"Babu wani uzuri da za ka bani wannan ne karo na ƙarshe da za ka sake wulaƙanta mutane da suka zo neman taimako. Ka sanar da su lokacin da nake sauran mabuƙata."

Risinar da kansa ƙasa ya yi alamar ban haƙuri tare da cewa.

"An gama sir."

Kusan mintuna ashirin ya ɗauka yana masu magana sannan ya ba wa kowa damar fadar wani ƙorafin idan suna da shi. Daga bisani ya sallami kowa ya koma bakin aikinsa.


_Fatima Zahra_

Sautin ihun da take yi ne ta nufi part ɗin Papa ya saka hankalin mafi yawan jama'ar gidan hankalinsu ya ɗan tashi. Don sun san akwai wata matsala. Papa dake zaune a falo yana karanta jarida ya jefar da jaridar take da miƙewa cikin tashin hankali yake kallonta. Dada na dake bedroom da sauri ta fito ta tarar da Papa rike da hannun Zahrah yana tamabayar ta abinda ke faruwa.

Ta kasa sanar da su saboda tsabar kuka hannun Papa ta janyo yana bin ta da sauri yayin da Dada ta take masu baya.

A babban falon duka suka hadu da sauran mutanen gidan. Gabaɗaya suka nufi harabar gidan. Tun daga nesa Yaa Mahmud da ya hangi cewa da Sadik ne ake dambe sai ya ya ruga wajen a guje kafin su isa, ya shiga tsakaninsu ya raba daidai lokacin da sauran mutanen gidan suka ƙaraso.

Ganin yadda lokacin guda suka ji ma junar su ciwo jina-jina. Cikin ɓacin rai Papa ya fara magana.

Wani wani irin rayuwa ne kuke yi a cikin gidan nan, kuna ƴan uwan juna amma kuke yi kamar za ku kashe juna? To wannan abun ya ishe ni, ku zo ina son ganin kowa a falo yanzu ba sai an jima ba. Ina nufin kowa dake cikin zuri'ar nan. Har wanda baya gidan a kira shi ya zo ina son ganinsa."

Daga nan ya yi shigewarsa ciki, Mahmud ya ja hannun Sadik suna shiga su ma suka shiga ciki.


_Jidderh_

Tattara kaya take yi cikin wata jaka, Inna na zaune akan kujera rike da baby. Aunty Sa'adatu tana zaune kan gado sanye da hijabi.

Yaa Isah ne ya shigo ɗakin tana cewa.

"Inna kun gama shiryawa ga shi nan n tsayar da mai abun hawa ku zo mu tafi."

Inna ta kalli Jidderh wacce ta gama shirya kayan a jaka ta ce.

"Kin gama Jidderh?"

"Eh Inna na gama."

Ta fada daidai lokacin da take ɗaukar jakar. Isah ma ya shigo ya dauki wasu kayan ya fice .

Inna ta kama hannun Sa'adatu ta tashi yayin da Jidderh ke daidaita mata takalminta. Bayan ta saka takalmin ne suka nufi hanyar fita.


A bakin asibitin suka tarar da Isah da mai napep din suna jiransu. Shiga ciki suka yi Inna da Jidderh da Sa'adatu suna baya, yayin da isah ke gaba gefen mai napep din.


Har ƙofar gida ya kai su, in da Isah ya biya shi kudinsa sannan suka fito da kayan suka shiga cikin gidan.


*Waye Alhaji Muhammad Tafarki?*

Muhammad Salisu shi ne cikakken sunan Papa, mahaifinsa mau suna Salisu mutumin jihar Katsina ne. Shi kaɗai ne a wajen iyayensa. Wato Salisu da Hauwa'u.

Bayan auren Salisu da Hauwa'u sai da suka shekara goma ba su samu haihuwa ba. Wanda har zuwa lokacin Hauwa'u ta fara shiga cikin damuwa, musamman ganin waɗanda suka yi aure lokaci guda da wadanda suka yi aure bayanta daga mai yara uku sai mai huɗu. Shi dai Salisu sai ya yi ta ba ta hakuri tare da tunatar da ita cewa Allah ne ke bayar da haihuwa kuma lokaci ne in sha Allah wata rana za ta samu.

A haka har wata rana Hauwa'u ta samu ciki farin ciki a wajen Salisu da Hauwa ba'a magana da ma duk wani makusantarsu.

Bayan watanni tara Allah ya sauke ta lafiya in da ta haifo ɗanta namiji tabarakallah. Ranar suna yaro ya ci suna Muhammad.

Ya taso cikin so da ƙaunar iyaye, suna yi masa duk abin da yake so. Ya yi karatun boko da islamiyya.

Bayan ya samu karatunsa daidai gwargwado don ya sauke al-ƙur'ani ya yi karatu har matakin digiri.

Daga nan sai ya fara kasuwanci daga Kano zuwa Katsina. Shaguna biyu ya haɗe waje guda ya fara sana'ar atamfofi.

Cikin ƙankanin lokaci arziki ya ƙara bunƙasa. Dan shaguna biyu da ya bude sai kara haɓaka suke yi. Ana cikin wannan yanayin ne Allah ya yi wa Mallam Salisu rasuwa. Wato mahaifin Muhammad. Ya yi kuka sosai wanda har saboda mutuwar ta shiga jikinsa ko fita baya yi sai da ya kwashe wata ɗaya.

Yaron shgonsa ke kula da komai kafin ya fara zuwa.

Haka suka cigaba da zama da shi da mahaifiyarsa a cikin gidan. Wanda daga baya ne ya siye babban gida wanda ya fi wanda suke ciki. Yayin da wanan da suka ciki kuma suka zuba ƴan haya a ciki.

Daidai wannan gaɓar ne kuma Hauwa'u wanda Muhammad ke kiranta da Ummina ta matsa masa akan yi yi aure. Tun da Allah ya rufa masa asiri yana da arzikin da zai iya rike mata biyu ma ba ɗaya ba.

Wata rana yana zaune a shagonsa yana lissafin kuɗi. Wata matashiyar budurwar kyakkyawa da kin gan ta kun ga cikakkiyar bafulatana. Dukkanin Yola ce ita mahaifinta ya bar ƙauyen bayan ya siyar da shanunsa ya dawo nan garin Katsina .

Ta zo siyen zannuwa a kasuwar ne Allah ya jefo ta shagon Muhammad.

Tun da ya kalle ta ya ji ta kwanta masa a rai. Kudin siyayyan da ta yi ya sanar da yayansa kada su karbi kuɗinta.

Haka kuwa aka yi ta ƙarasa wajen shugaban tana masa godiya sai ya nemi ta yi masa kwatancen gidansu. Ba tare da ɓata lokaci ba ta sanar da shi, wanda a washegarin ranar ne ya zo gidansu.

Bayan sun gaisa ya bayyana mata kudirin sa akanta, don zancen aure ne ya kawo shi ba wani abu ba.

Ta amince da zancen suka fahimci juna.

Daga nan soyayya ta ƙullu tsakanin Muhammad Tafarki da kuma Amina wacce ake kira da suna Dada. Kasancewar sunan mahaifiyarta ta ci ya sa iyayenta basa kiran sunanta sai dai a kira ta da Dada.

Cikin ƙaƙanin lokaci manya suka shiga in da Muhammad ya tura abokin mahaifinsa da abokinsa aka nema masa auren Dada. Wanda aka saka rana biyu masu zuwa.

Ummi kuwa sai shirye-shirye, take yi sosai don dama burinta ta ga auren Muhammad. Nan gidan da ya suye wanda suke zaune tare da Ummin ya siya.

Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗa ta ji kunya. An ɗaura auren Muhammad da Dada in da ta tare da gidansa ɓangarensa daban na Dada ma daban.

Zama suke na amana da juna don wata matsala ba ya taɓa shiga tsakaninsu ba. Haka ma da Ummi. Don Dada tana shiga cikin ɓangaren Ummi ta yi mata aiyuka, sannan ita take dafa abinci kowane lokaci ta kai ma Ummi.

Ana nan har Dada ta samu ciki wanda ya sa familyn suka kasance cikin farin ciki. Dada tana samun kulawa sosai daga wajan uwar mijinta.

Bayan wata tara ta haifi ɗa namiji, nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login