Showing 69001 words to 72000 words out of 154779 words
Asadullah dake cike da mamaki ya ce.
"Duk da yana gidan yari amma ya fi ka rayuwar jin dad'i. Kalli yadda kake a kulle a daki kuma daure da sarƙa. Sai an baka abinci ko wane iri ne dole ka ci."
Yana gama fadar haka ya fice ya bar Asadullah yana binsa da kallo. Har lokacin yana daure da sarƙa a hannunsa.
Yana kai wa bakin ƙofa ya ya juyo yana cewa.
"Ka san me ya janyo naka haka?"
Murmushi ya yi sannan ya ce.
"Yarda da mutane, da ba don lokaci ya kure maka ba da na baka shawarar cewa ka rage yarda da mutane, domin wani lokacin wadanda ka yarda da su sune za su iya cutar da kai."
Yana gama fadar haka ya fice ya ja masa kofar ya rufe.
_Ummi_
Tana fita daga part ɗin su ta nufo Babban falon gidan ta ga Hilal zaune yana danne-danne a system ɗinsa. Rai a ɓaci ta kalle shi ta tuna yadda Zahrah take kuka da kumburin da fuskarta ta yi sakamakon marukan da ya dinga sabga mata. Domin Ita uwa ce.
"Hilal!"
Ta kira sunansa rai a ɓace, ɗaga kai ya yi ya kalle ta ba tare da ya amsa ba.
"Me Zahra ta yi maka da ka yi mata wannan dukar haka, to tura ta fara kai wa bango. Ba wannan ba ne karo na farko da ka fara dukan ta, ka sha azabtar mun ca yarinya da duka ko punishment har sumewa ta yi a dalilin ukubarka. Sannan duka da haka bai ishe ka ba saboda na kawar da kai ban taɓa nuna ɓacin rai akan abinda ake mata ba wai hakan na nufin ba na ƙaunar ƴata ba ne, kawaici nake yi maku amma tun da ba ku gane wa na gaji ya isa haka nan kada ka sake taɓa lafiyar Zahrah."
Tana faɗin haka ya nufi part ɗin Papa bin ta ya yi da idanu, ita ma ba ta saka ran zai amsa mata ba duk da ta san ya ji ta sarai. Sai dai ya san cewa an ƙure ta ne don shi kansa shaida ne akan ƙiyayyar da ke yi wa Ummi da ƴaƴanta musamman Zahrah sun fi tsanar ta amma hakan bai saka Ummi ta nuna ɓacin rai ba sai yau.
"Ni dai ba zan taɓa zuba idanu na bar ɗaya daga cikin ahalin gidan nan su yi duk abinda suka ga dama ba. Musamman Zahra dake da masoya ga shi yanzu har ta fara zubar da ciki, sannan a ce na ƙyale ta?"
Ya faɗa yana girgiza kai tare da sarrafa na'urar dake gabansa. Wani tsanar Zahrah ne sabo ya dirar masa.
"Zan yi maganin ƴar iskar yarinyar nan, ƙura ce ita lulluɓa da fatar akuya."
*Maman Ihsan ce*✍️ da
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page3️⃣5️⃣
"Zan yi maganin ƴar iskar yarinyar nan, kura ce lulluɓe da fatar akuya.
Da sallama Ummi ta ƙarasa part ɗin Papa. Dada ce a falo tana zuba kwadon zogale cikin bowl. Ta amsa sallamar tare da kallon Ummi ta ce.
"Zahrah ne na ga kin zo da kanku?"
Ta tambaye ne kasancewar ta san idan Ummi ta shigo da safe ta gaishe su ko wani abu ne sai dai ta aiko Zahra.
Murmushi Ummi ta yi tare da cewa.
"Wannan zuwan na wa ne Dada."
Ajiye bowl ɗin da ta zuba zogale ta yi tare da cewa.
"Tun da kin shigo shiga kitchen ki ɗauko plate ki zuba zogale, wancan mai murɗaɗɗen halin ke saka Ni yi masa zogalen nan, ga uwarsa ga masu aiki ya ce ba zai saka su ba na wa yake so."
Gajeren murmushi Ummi ta yi don ta gane cewa Hilal Dada ke nufi tun da ta ce mai murɗaɗɗen halin.
"Dada na gode ba zan ci zogale ba, wajen Papa na zo."
Tana rufe baki sai ga Papa ya fito daga ɗakinsa. Ya kalli Ummi ya ce.
"A'isha ke ce?"
Ya yi magana yana gyara zaman medical glass dake saman karan hancinsa.
"Eh ni ce."
Ta fada kanta a sunkuye yayin da ta zube a saman guiwarta kamar mai rokon gafara.
Zama Papa ya yi yana fuskantar ta ya ce.
"A'isha lafiya dai ko?"
Hawaye da ya taru a idanunta ta goge.
"Papa wata alfarma nake nema a wajen ka, duk da na san abu ne mai matukar wahala a gare ka, amma dole na tamabaye ka shi don idan ba haka ba wata rana za'a wayi gari bakin ciki ya kashe ni."
"Subhanallah me ya yi zafi haka?"
Murmushin takaici ta yi tare da cewa.
"Papa ina neman alfarma don Allah ka bar mu mu tashi daga gidan nan, mu nemi wani gidan mu zauna ni da yarana, ko ba komai za ku yi rayuwar farin ciki a cikin gidanmu."
Shiru ya yi tare da yin nazarin kalamanta don tabbas ya san irin zaman da take yi a cikin gidan. Yadda ta zama sanayar ware a cikin matan gidan. Duk da ya so a ce ta ƙara hakuri na wani lokacin.
"A'isha me kike son cewa ne?"
"Sama da shekaru ashirin ina zaune a cikin gidan nan, duk da wariya da ƙiyayyar da ake nuna mani haka na kawar da kai. Sakamakon hakuri da juriya da na ga mijina na yi na zama da ƴan uwansa. Ni ma na ɗora wannan aniyar. Zuwa gaba bayan ba fara haihuwa na fahimci tsanar da ake mana ya shafi yaran da muka haifa. A lokacin hankali na ya tashi amma ganin ba zaman kowa nake yi a cikinsu ba, kuma ina samun kulawa daga wajan mijina da iyayensa ya sa na watsar da lamarin kowa na cigaba da mu'amalantar kowa duk da ko na masu magana ba sa amsawa ƴaƴansu ba sa mu'amala da ƴaƴana ban nuna damuwa ba na mayar da hankali wajen tarbiyyar yarana da cusa masu aƙida mai kyau a cikin zuciyarsu, ban koya masu tsanar danginsu ko ƴaƴan cikin gidan ba. Amma na lura sun fi tsanar Zahrah fiye da tsanar da suke muna da sauran ƴan uwanta. Na rasa me ta yi masu a rayuwa sun cusawa ƴaƴansu tsanar ƴaƴana kamar ba jini ɗaya suke ba. To yanzu har ya kai a yi wa Zahra ƙazafin zubar da ciki sannan ayi mata duka har da kumbura mata jiki, gaskiya hakurina ya fara ƙarewa ba zan iya ba."
Shiru Papa ya yi na wani lokacin daga shi har Dada kowa ya kasa magana. Don sun san tsananin hakuri da kawaici irin na Ammi tun fa ta fara kawo ƙorafi tura ce ta kai bango.
"Aisha."
Papa ya kira sunanta. A hankali ta ɗago kai ta kalle shi cikin sanyin murya ta ce.
"Na'am Papa."
"Mijinki ya dade yana burin barin gidan nan saboda halin da ƴan uwansa ke nuna masa. Ni ne na hana shi tashi sakamakon ina ganin ni ne Ummul aba'isin wadan nan abubuwa dake faruwa a cikin zuri'ta gabaɗaya. Yanzu dai don Allah ina rokonki wannan karon in sha Allah za ki ga abinda zan yi. Ki ƙara hakuri in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe."
Ya faɗa yana jinjina mata kai alamar tabbatar wa.
Godiya ta yi masa sannan ta yi masu sallama za ta bar part ɗin.
Har ta dawo babban falon gidan Hilal na nan in da ta bar shi.
Tana wuce wa ya tashi ya shiga ɓangaren su Papa. Ciki-ciki ya yi sallama wanda shi kaɗai ya ji kayansa, don su ba wanda ya ji sallamarsa ballantana su amsa masa.
Kuma shi ma bai sake yin magana ba, ƙarasa wa ya yi gaban Centre table ya dauki bowl ɗin da Dada ya haɗa masa kwaɗon zogale.
Bai yi magana ba saboda ya san shi ta haɗawa. Har ya kai bakin ƙaofa ya ji Muryar Dada tana cewa.
"Kai kam matarka tana da aiki mutum sai bakin hali. To uwarka ce ta dafa maka zogalen da za ka ɗauka babu sannu da aiki ballantana ka yi Mani godiya ko? To ƙaniyar gobe, don ba za ka saka ni aiki na yi ba."
Ya juyo ya kalle ta dai ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba.
Kallon Papa ta yi tare da cewa.
"Kana ganin wannan yaron jikan naka abun da yake mani ko? Ba za'a taɓa yi masa abu ya nuna ya ji dadi ba, kuma an alhalin abin da yake so ne aka yi masa shi, amma jin kai da mishkilanci irin nasa ba zai nuna ba. Yo ba don shi ba kaf jikokin gidan nan idan aka cire Zahrah ai ba wanda zan yi wa bauta. Don ba zai yiwa na yi wa ubansa shi ma na masa ba, sai dai shi ba zan iya ba."
Papa kallonta ya yi yana murmushi don ya san irin son da take yi wa Hilal da Zahrah na daban ne a zuciyarta. Kamar yadda shi ma haka yake jin su a ransa. Gara Zahrah tana yawan shigewa Kakannin nata har kwana ɓangaren su tana yi wasu Kayanta ma suna ɓangaren kamannin na su ne sai in da ta ga dama za ta ci ta sha ko ta kwana. Duk da akasari ta fi kwana a bangaren Umminta.
*Bayan sati ɗaya*
Zahra ta warke ta warware ta cigaba da sabgarta. Kuma har lokacin ba ta sake saka Hilal a Idanunta ba. Don ko zuwa part ɗin Dada ba ta yi ballantana ta hadu da shi.
Ranar Ummi ta gama abincin rana ta aiki Zahra ta kai wa Dada. Duk da kasancewar suna da masu aikin girki a gidan da suke abinci gabaɗaya amma Ummi ta kan yi abin Marmari da ta san tana so kitchen ɗin ta da ke part ɗin ta. Ɗanwake ta yi ta san Dada na so ta zuba don a kai mata.
Zahara ta ɗauki abincin ta nufi part ɗin Dada don kai mata.
Bayan ta kai mata ne ta samu tana aiki a kitchen tana dafa zogale, ganin Zahra ta zo sai ta saka ta daka mata yajin ƙuli.
Bayan ta gama daka mata ta zubawa Zahra na ta ta zuba wani a wani bowl ta zuba yajin ƙuli da yanka su tumatir da albasa. Ya
Mika wa Zahrah ta yi tare da cewa.
"Kar bi ki kai wa Yayanku wannan a ɓangarensa."
Rass gabanta ya faɗi.
Ƙasa amsa ta yi ta tsaya tana kallon bowl ɗin.
"Karbi mana ki je ki dawo ga naki."
Tura baki ta yi tare da cewa.
"Da ban shigo ba waye zai kai masa?"
"To kin san ina da ciwon ƙafa ba iya hawa bene nake yi ba, kuma sauran yaran ba sa shigowa saboda wai ke nake so ba na son su duk da na san hudubar iyayensu ne saboda sun san kina zama a nan wajena. Dama shi ne idan ya shigo ya dauka amma tun da ga ki ba wanda zan aika don ya hana masu aiki zuwa part ɗin sa ballantana na aika su kai masa."
"To ki jira ya zo ya ɗauka, ba zan je ya ci zalina ba tunda shi mugu ne ba imani a zuciyarsa."
Mumrmushi Dada ta yi tare da cewa.
"Tun da ba mahaukaci ba ne shi ai ba zai dake ki haka kawai ba."
"Ni fa ba zan je part ɗin nan ba."
"Ku ji mani ja'irar yarinya ko ubanki Salisu na aika bai isa ya faɗa Mani haka ba, ballantana uwarki A'isha."
Ganin ida idanunta ya ciko da ƙwalla ta ce.
"Ki yi hakuri je ki dawo ƴar albarka kin ji, ba na son kina ɓata rai je ki dawo in ba ki labari mai daɗi tatsoniya zan maki."
Sanin Zahrah na son tatsuniya idan tana ba ta ta yi ta dariya ya saka ta ce haka. Nan da nan ta amsa har tana murmushi.
_Hilal_
Yana komawa part ɗin sa ya tarar Alexandra ta kammala haɗa kayanta a trolley bag ɗin ta. Don yau za ta koma ƙasar US. Duk da burinta bai cika akan Hilal ba, don har yanzu sai dai ya yi romancing ɗin ta bai taɓa gigin yin sex da ita ba. Duk iya hanyoyin da za ta bi don ta ja hankalinsa ya kai in da take so ya kai ta kasa. Da sun yi zurfi wajen wasannin su da juna ya fahimci yana neman wuce iyaka take zai raba ta da jikinsa ya je ya sakarwa kansa ruwa. Wata rana ma sai ya sha magani.
Ita mamakinsa take yi yadda zai ce ba zai yi sex da ita ba amma zai yi wasa da ita son ransa ya kuma sarrafa ta yadda ransa yake so.
Kamar dai yadda ta ji labarinsa a wajen wasu ƴan matan da suke cewa shi ne kaɗai namijin da suka ga zai yi wasa da mace son ransa duk yadda ta so ya yi sex da ita ba ya yi sabanin sauran mazajen da idan sun fara ba su dakatawa sai sun kai ga biyan buƙatarsu ta hanyar sex da su. A lokacin ta ƙalubalance su akan cewa su ne ba su iya janyo hankalinsa ba. Ta ce ita za ta gwada basirar ta sai dai ita ma kamar su ta kasa.
Yana shigowa ya ajiye wayoyinsa saman wani table dake cikin bedroom ɗin sa.
Ƙarasawa ta yi gabansa ta ɗora hannunta a daddaɗen ƙirjinsa. Cikin harshen ƙasar Spain ta fara magana.
"Ni zan tafi na yi kokarin zama a wannan ƙasar ta ku, saboda soyayyar da nake maka na mallaka maka komai na wa dukkanin jikina da kuka zuciyata. Amma kai ka kasa yi Mani haka.
Sanin abinda take nufi ne ya saka shi share ta a hankali ta matso da fuskanta saitin na sa ta tallabo fuskarsa ta fara kissing lips ɗin sa. Take shi ma ya mayar mata da martanin abin da take masa zazzafar kiss yake yi mata wanda ta fara zaucewa. Ganin yadda ƙafarta ke rawa ya sa ya dauke ta ya dora akan doguwar kujera dake kusa da su.
Cikin kiɗima ta zame yololuwar rigar dake jikinta tana kara shige masa. Boturan gaban rigarsa ta fara ballewa bai hana ta ba, bayan ta balle rigar ne ta yi ƙasa da hannu wajen wandonsa. Rike mata hannu ya yi tare da zare bakinsa daga nata ya ce.
"Na sha fada maki ba na bukatar haka daga wajan ko wata ƴa mace ko?"
"Ni ina ne ba ka sani ba ko ba ka ƙalla a jikina ba? Sai sai ne za ka ce ba wacce za ta kalle ka?"
"Tun farkon haduwa ta da ke na fada maki haka don haka ki tsaya iya matsayin duk ranar da kika sake ƙoƙarin aikata Mani abinda irin haka to hannun da kira kokarin kai wa wajen zan karya. Kuma zan rabu da ke har abada."
Cikin kuka ta fara roƙonsa da magiya.
"Don Allah ka taimake ni ko sau daya ne ka yi sex da burina kenan."
"Ban taɓa sex da kowane mace ba kuma ba zan fara akanki."
Kasancewar ba komai a cikinta ya sa ta kalli jikinta tun daga kirji har zuwa ƙasanta, ita da take ja wa maza rai saboda jikinta amma shi yana mata wulakanci ta bar ƙasar ta da kowa ta zo wajensa amma ya kasa yi mata abinda take so.
Ganin ta bude baki za ta yi magana ya sake hada bakinsu tare da aika mata zazzafar sumbatar da ke mantar da ita kanta. Yana yawo da hannayensa a jikinta yana shafa duk in da hannunsa ya taɓa.
Har lokacin bakinsu na cikin na juna.
Zahra ta shigo part ɗin don kawo masa zogalen da Dada ta aiko ta kawo masa.
Sallama ta yi ba kowa a falo, ajiye wa ta yi a saman Centre table dake falonsa. Har za ta juya za ta za ta koma sai ta ji wani sauti kamar Muryar mace kamar kuka haka take ji . Gabanta ya fadi ita a tunaninta ko cikin yan matan gidan ne suka masa mafi yake punishing din ta. Sai ta yanke shawarar ta fada masa abinda Dada ta aiko ta kawo masa.
Tura ƙofar ta yi tare da yin sallama. Abinda ta gani ne ya girmi tunaninta.
Ƙara ta saki tare da cewa.
"A'uzubillahi minash shaiɗani raƙumi!"
Sai ta saki ƙarar da ya ankarar da su da zuwanta. Kallonta suka yi Idanunta a rintse. Ita Alexandra ba ta damu ba yayin da Hilal ya dafe goshi tare da cije leɓensa na ƙasa.
Zahra cikin tashin hankali ta ruga a guje ta fice, ganin haka ya saka shi ma ya tashi ya mara mata baya a guje.
*Maman Ihsan ce*✍️
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: G*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*Sanarwa*
Wannan ƙirƙirerren labari ne ban rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali ya zo ɗaya to arashi ne. Mai kashe auren wawa.
*Sadaukarwa.*
Wannan shafin sadaukarwa ne ga JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATIO Allah ya ƙara mana ƙwarin guiwa.
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page3️⃣6️⃣
Zahrah cikin tashin hankali ta ruga a guje ta fice, ganin haka ya saka shi ma ya tashi ya mata mata baya.
Abu ga dogon mutum taku uku ya sha gabanta wanda hakan ya saka ta faɗa jikinsa, da sauri ta ja baya tare da furta kalmar.
"A'uzubillahi minash shaiɗani rajim"
"Ke wa kike yi wa ta'awizi, waye sheɗanin?"
Ɗaga kai ta yi ta kalle shi da sauri ta kau da kanta haɗi da rintse idanu. Sakamakon arba da ta yi da faffaɗan ƙirjinsa mai ɗauke da kwantaccen gashi.
Wani banzan kallo ya watsa mata ya ce.
"Uban me ya kawo ki part ɗina?"
Bakinta har rawa yake yi ta ce.
"Dada ce ta aiko ni na kawo maka kwaɗon zogale."
"Dan rashin hankaki shi ne kika shigo mani har cikin bedroom ɗina? Nan bai isa ki ajiye ki koma ba, wato ke ga munafuka shi ya sa kika shiga kiga abinda nake aikatawa ko?"
"Wallahi ba haka ba ne, na ji kamar muryar mace na kuka ne a bedroom ɗin shi ne na duba."
"Da kika leƙa uban me kika gani?"
Tuna yadda ta ga suna yi da Alexandra ta yi. Wani yawu mai ɗaci ta haɗiye ta kasa faɗa masa abinda ta ga suna yi.
Wani tsawa ya daka mata tare da cewa.
"Me kika gani!"
"Ban ga komai ba, ni ba abinda na gani."
Jinjina kai ya yi tare da cewa
",Gud"
Kunnenta ya rike da ƙarfi wanda ya saka ta saki wata ƴar ƙara.
"Kin ceci kanki da kika ce ba ki ga komai