Showing 27001 words to 30000 words out of 154779 words

Chapter 10 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6285

da ke ki koma wajen aikinki ni ma yanzu zan fara nawa aikin.

"Amma me ya saka kika tamabaya?"

Murmushi ta yi tare da cewa.

"Ba komai na dai tambaya ne."

Daga nan Bahijja ta koma wajen aikinta. Ita kuma Jidderh madadin ta mayar da hankali wajen aikinta kawai sai ta tsinci kanta da son zuwa ɓangaren da ta je ta ga an rufe Sir Asadullah ana masa allurai ana son kashe shi.

Dafe kirji ta yi tare da cewa.

"Kar dai a ce har sun ida nufi su akan sa."

Aikin dake gabanta ma ba ta tsaya yinsa ba, ta nufi part ɗin da ta ga wannan Doctor dake don kashe shi ranar ta ga ya je.


Mutane biyu mace da namiji. Da suka je dubansa suna kallonsa sai da sautin murmushinsu ya fito. Maccen ta kalli namijin tare da mika masa wata allura da sirinji da kwalbar ruwan alluran.

Daidai lokacin Jidderh ta tura ƙofar a hankali kasancewar sun juyawa wa kofar baya ya sa ba bayansu take gani, suka ba su san an turo kofar ba kasancewar ƙofar baya ƙara .

Tana kallo ya yi masa alluran a damtsen hannunsa. Ana masa alluran take ƙofofin gashin jikinsa suka miƙe jijiyar kansa ta yi ruɗu-ruɗu ta fito idanunsa suka rikeɗe zuwa ja. Hannayensa biyu dake ɗauke da sarƙar ya ɗaya tare da ɗora su a saman kansa yana wani ihu mai haɗe da gurnani. Take Jidderh hawaye suka wanke mata fuska. Mace ta yi namijin almar jinjina da hannunta . Kuka ne ya ci karfin Jidderh ta sake kofar ta rufe.

Wanda ƙarar rufe ƙofar ya saka suka juyi da sauri. Ita ma sai ta fara waige-waige don ta san idan ta kama hanya za su gane ta. Wani kontena ta gani sai ta durƙusa tare da kwantawa dab kada su hanahe ta. Don yana da girma. Suna fitowa suka fara waige-waige ba su ga alamar wani ya zo wajen ba, don haka suka juya suka bar Wajen.

Tana. Kallonsu sai dai ba su ganinta tasowa ta yi a hankali don ta tabbatar da su waye sai ta ga sun nufi cikin gidan.

Hakan ya tabbatar mata da cewa ƴan cikin gidan ne suke neman kashe Sir Asadullah.

Da sauri ta bi bayansu don ta gano ko su waye amma sai dai ba ta ga kowa ba sun ɓacewa ganinta.

Fridge ta nufa dake fakon ta ɗauko youghurt da cake ta tura cikin hijabi. Cikin sanɗa ta fita ta koma part ɗin da ta fito.

Tura ƙofar ɗakin ta yi yana zaune jingine da jikin bango ya ɗaga kai ya lalle ta. Ƙarasa wa ta gabansa ta zube tare da cewa.

"Yallaɓai barka da safiya?"

Kallonta kawai yake yi kamar wanda ya ga sabon halitta.

"Yallaɓai dan Allah me ka yi masu kuma su waye ke son ganin bayanka?"

Nan ma shiru ya kasa magana.

"Yallaɓai zan so fitar da kai sai dai na san ba abu ba ne mai yiwuwa, don matukar suka gane na san in da kake ba za su barni ba, ga shi Dad ɗinka baya gari ballantana na sanar da shi, amma zan yi shawara ko zan sanar wa Mom ɗin ka."

Kallonta kawai yake yi ko motsin kirki ya kasa yi. Cake ɗin da youghurt ɗin ta ciro daga cikin hijabi. Ganin hannunsa ɗaure da sarƙa ya sa ta bude cake ɗin a cikin ledar da yake ta kai masa bakinsa. Nan da nan ya gutsiri cake ɗin, ganin haka ya sa ta dinga gutsura tana bashi a baki yana ci. Tana kuka bashi youghurt , sai da ya cinye tas ya kuma shanye robar youghurt ɗin sannan ta kalle shi ganin yadda ya rame.

Ƙwallar tausayin sa ne ya zubo mata, ta mike ta bar wajen da sauri don kada wani ya zo ya tarar da ita wajensa.

Ta tafi ta ƙudiri niyyar sai ta yi wa Mama magana, duk da cewar Mama ƴar aiki ce a gidan amma ta dade don ta ji labarin cewa Mama ta reni Asadullah yana yaro ita ke kula da shi. Za ta yi shawara ta sanar mata halin da ake ciki. Don tana tsoron tunkarar ƴan gidan da zancen ya kasance ta saka kanta a cikin hatsari.


_Hilal_

Zaune yake a bayan motarsa yayin da ke gaba yana driving. Wayarsa ce ta yi ruri ya duba. Ganin Papa ne ya ɗaga tare da yin sallama.

"Assalamu alaikum"

Daga can ɓangaren Papa ya amsa tare da cewa.

"Sojana ya kake?"

"Am fine."

"Yauwa dama ƙanwarku ce za su yi gasar karatun Al-ƙur'ani a garin Kaduna. Shi ne nake so a ce ka kai ta."

A tunaninsa Maryam ce da suka fito ciki ɗaya ko Nadiya ƴar wajen Uncle Adam ko ɗaya daga cikin yaran Aunty Laila, sai dai ya san cewa ba damuwa suka yi da karatun Alqur'ani ba ballantana su je wani gasa. Gara ma Maryam duk da ita ba ta sauke ba ya san daƙyar idan ita ce.

"Papa wacce kake nufi? Don na ga dukkansu ba wani nisa suka yi a cikin karatun Alqur'ani ba."

"Ka mance Zahra ta sauke har walima ta yi, to ita ce nake nufi ai."

Haɗe fuska ya yi tare da cewa.

"Kuma ba wanda zai kai ta sai ni?"

"Yayanninta ba sa nan kai ba Yayanta ba ne idan aka cire Mahmud da Sadik. "

"Papa a gaskiya ni ba zan...."

Katse shi ya yi ta hanyar cewa

"Ba na bukatar wani uzuri daga wajenka. Ba wanda zan iya sawa ya kai ta bayan kai, don mahaifinta da mahaifiyar ba sa nan, ko na da ina nan zan bi ta ji tafi duka gidan nan na san ba wanda zai kai ta, don haka ka koma gidan yanzu ka same ta ku tafi can Makarantar ka yi magana da Mallamansu. Don ban yarda ta tafi tare da kowa a makarantar ba ƴa mace ce ita sai da saka idanu da kula. Na san ban isa da mahaifiyaeka ba amma idan ba za ka je ba zan kira ubanka na bashi umarnin da dole sai ya bi. Don haka yanzu na gama magana da Mallamansu suna jiranku kai da ita."

Yana gama maganar ya kashe kiran wayar, ransa a ɓace, wai shi ne zai dauki yarinyar can ya kai ta wani gari

Umarni ya bawa direban ya juya akalar motar zuwa gidan. A parking space ya tsaya, tsawon mintuna biyu da bude basa motar bai fito ba, kafin ya fara fito da ɗayar ƙafarsa waje, sannan ya fito da ɗayan ya fito gabadaya.

A falon ta samu ƴan matan gidan duka suna kallon T.V suna fira.

"Sannu da zuwa Yaya."

"Kausar ta fada tana miƙewa don ta ɗauka saboda messages nata ya dawo da ta sanar da shi ya dawo gidan ta masa girki kuma akwai maganar da za ta masa.

Bai amsa gaisuwar ba ya kalli Maryam ya ce.

"Je ki kira mani yarinyar can?"

Wace yarinya Yaya?"

Harara ya banka mata tare da sauke kai "


"To Yaya ba kowa a nan iyakar mu kenan sai dai idan Zahra kake nufi."

"Eh ita."

Da mamaki suka kalle shi Nabeela ta zaro idanu tana cewa.

"Lafiya?"

Bai tanka mata ba, ba jimawa Maryam ta dawo tare da Zahra Sanye da Hijabi kamar kullum.

"Mugun kallo ya mata sannan ya ce.

"Idan kin shirya ki same ni a mota."

Yana gama fadar haka ya fice ya barsu da ƙamshin turarensa.

Fatima Zahrah ta koma ta dauko wayarta a ɗaki, tana fito Kusar ta ce.

"Uban meye za ki masa meye tsakaninku?"

Ba ta tanka mata ba ta nufi hanyar kofar fita.

Ƙasancewar akwai matattakala kin fita wanda sai kin sauka ta nan. Tana fita Kausar ta bi bayanta ta hankaɗa ta da ƙarfi ta tafi luu idsnunta a rintse ta sadakar dole sai ta illata.


*Maman Ihsan ce*✍️


09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z



*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page1️⃣4️⃣

Kasancewar akwai matattakala ƙoagar fita wanda sai kin sauka ta nan. Tana fita Khausar ta bi bayanta ta hankaɗa ta da ƙarfi ta tafi luu idanunta a rintse ta sadakar dole sai ta illata.

Bayan ta sadakar tana jiran ta ji yadda Allah zai yi da ita Idanunta a rintse ta ji sauka a jikin mutum, don tabbas hannun mutum ne, tabbatar da cewa ba faduwa ta yi ba ne ya sa ya ƙanƙame shi a jikinta.

Jin daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya sa gabanta ya faɗi, saboda tsoronsa da take ji. Tana buɗe Idanunta ta sauke akan idanunsa masu rikita mai kallonsu.

Harara ya watsa mata tare da sakinta ta faɗi ƙasa, ƙara ta saki ta ɗan ji zafin faɗuwar sai dai duk da haka ya gode masa ya ceci rayuwarta. Don da daga can saman matattakalar ne ta faɗo tabbas sai sai ta karye.

Tashi tsaye ta yi tana tura baki tare da goge ƙwalla a zuciyarta tana cewa.

'Ya san dama zai yarda ni na fadi me yasa ya tare ni, ai da ya barni kawai na fado na ji ciwo, bayan na sakankance da cewa ya taimake ni ashe wani sabon muguntarsa zai mani. Sai sai na shi da sauki tun da daga jikinsa ne ya yarda ni da daga matattakalar na fado ba. '

Ɗaga kai ta yi ta kalli ƙofar ta ga Kausar, Nabeela, Nadeeya da Maryam sai kuma su Mama da Aunty Laila.

Mugun kallo suke mata sai Maryam ce kaɗai ke mata kallon tausaya wa.

Ko da ta juya ta ga baya wajen har ya karasa parking space, da sauri ta karasa wajen tana ɗan ɗingisa ƙafa.

Yana zaune a bayan motarsa direbansa na gaba. Tana tsoron ta zauna kusa da shi sai ta tsaya. Don sanin halin mutanen gidan sai su ce ba zasu shiga mota tare da ita ba, mazansu da matan.Cikin takaici ya fara magana.

"Tsayuwar me kike yi a wajen da ba za ki shigo ba."

Da sauri ta bude bayan motar ta shiga. Ba abinda kake ji a motar sai sanyi da kuma daddaɗan ƙamshi wanda ya sa sai da ta yi ajiyar zuciya.

Direban ya ja motar suka fice daga gidan. Tana mamakin yadda wani lokacin Yaa Hilal ya ɗan banbanta da sauran mutanen gidan. Don shi baya hantararta ko kyararta ballantana ya nuna ƙyamarta kamar yadda sauran suke yi. Shi dai idan sun haɗa idanu ya harare ta ko ya mata mugun kallo, amma ko gaishe shi ta yi baya amsawa, sallama dai yana amsawa kamar yadda ya zama wajibi a Addinin Musulunci. Amma sauran mutanen gidan ba sa amsawa ko sallmarta ce.

Direban ya ɗan juyo ya kalli Hilal ya ce.

"Sir ina za ku je?"

"Ka tambayi yarinyar nan ina ne makarantar islamiyyarsu."

Jin haka ya sa Fatima Zahrah ta sanar da shi wajen.

Wayarsa ta kawo haske alamar kira ya shigo.

Ɗaga wa ya yi kafin ya yi magana ya ji Muryar Mama na fada tana cewa.

"Ina za ka je da wannan banzar yarinyar ?"

"Mama Papa ne ya aike ni makarantarsu."

Tsuki ta ji tare da cewa.

"Akan me za ka yarda?"

"Mama cewa ya yi idan ban yi ba ai sai ya kira Abba ya bashi umarni."

Tsuki Mama ta ja tare da katse kiran wayar.

Kallon Aunty Laila da Mummy ta yi tare da cewa.

"Kin ji wai mahaifinki ne ya tura su wani wajen."

Aunty Laila ta ce.

"Gaskiya ba na son kusancin wannan yarinyar mai ƙirar aljanna kusa da Ajmal, ga Nabeela da Kausar suna mutuwar sonsa."

"Kwantar da hankalinki matar Yaya matuƙar ina raye ai ko da wasa n hakan ba zai taba yiwuwa ba kar ki saka Ni ma na shata masa dogon layi akanta "


*Prison Gidan yari*

Sanye yake da kaya irin nasu na ƴan gidan yarin, sai faman Safa da marwa yake yi a cikin falon.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan yarin ya shigo tare da sallama. Bai amsa masa sallamar bs sai da ya karaso ya ce.

"Yallaɓai wadannan jaridun da n kawo maka iya su ne waɗanda aka fitar yau.da sauri y kalli ma'ikacin ya ce.

"Ka tabbatar ba wani jaridar bayan wandada aka kawo mani da za'a iya rubuta abun da nake bukatar ji?"

Cikin tabbatarwa ya amsa masa da

"Ƙwarai kuwa."

Dunkule hannu ya yi ya naushi iska yayin ma'aikacin ya ce.

"Yallaɓai zan tafi bakin aiki na."

Kuɗi dake kan kujerar ya yissa nuni da hannu, ɗauka ya yi yana yin godiya ya fice.

Dunƙule hannu ya yi ya dakin bangon ɗakin yana cewa.

"Dole ka mutu Asadullah ba zan taba samun kwanciyar hankali ba sai na ji labarin mutuwarka zan samu nutsuwata. Tura ni gidan yarin da ka yi shi ne kuskure mafi munin da ka tafka a rayuwarka. Tunda likitan ya gagara kashe ka to ni zan ɗauki mataki da kaina. Don a duk lokacin da na ganni a cikin gidan yarin nan na tuna kudanci da dangantakar mu amma ka iya aikata Mani haka sai zuciyata ta yi ya tafarfasa. Me ya da ka kasa yafe mani kana da iko da alfarma na fitar da ni ka kasa. To an zo wajen da na ƙasa jurewa da gatana ka kawo ni nan."

Haka ya dinga surutu shi kadai karshe ya fice daga ɓangaren ya nufi wani ɓangaren na gidan yarin.


Wasu maza hudu ne suke shan sigari dai busa hayaƙi suke yi. A hankali ya karaso wajen, kallo ɗaya suka masa suka ɗauke kai.

Shi ma shiru ya yi bai yi magana ba, don tsabar jin kai irin nasa yafi karfin ya masu sallama ko ya gaishe su.

Ɗaya daga cikin su ne ya kalle su ya ce.

"Mallam lafiya ka zo ka wani tsaya wa mutune akai?"

"Kai ka damu da shi ni dama ban cika shiga sabgar ƴaƴan manyan nan ba."

Wani ya faɗa aji bayan ta yi gama busa hayaƙin sigari. Kallon banza ya yi masu tare da cewa.

"Waye madurguji?"

Da sauri suka kalle shi tare da cewa.

"Me yasa kake nemansa mutum ne shi mai hatsari."

"Sanin haka ya sa nake nemansa don zai mani amfani."

"Ka zagaya bayan dutsen nan za ka same shi da shi da muƙarrabansa."

Suna fada masa haka ya juya ya bar su ya nufi bayan dutsen da suka kwatanta masa.

Tafiya yake yi yana murmushi tare da girgiza kai.

Wasu mutane ne kimanin du biyar a bayan dutsen, ɗaya daga cikinsu wanda alama ya nuna shi ne oga yana shan sigari, zaune yake akan dutsen yayin da sauran mutane huɗu suke zaune a ƙasa.

Yana zuwa wajensu ya tsaya akansu yana cewa

"Waye madurguji a cikinku?"

Kallo ɗaya madurguji ya masa ya zuƙi hayaƙi tare da kallon ɗaya daga cikinsu ya ce.

Wanda aka kalla ne ya tashi ya kwashe ƙafar mai tambayar tare da cewa.

"Ka rage tsawonka sannan ka san waye a gabanka ko kai waye."

Murmushin takaici ya yi tare da kallon jikinsa yadda aka kwashe masa ƙafa har sai da ƙura ya ɓata masa jiki, yana duƙe akan guiwarsa ya ce.

"Da kun san waye da matakin da na taka a rayuwa da za ku san cewa na fi ƙarfin wulakancin tantirai irinku."

Dariya Madurguji ya kece da shi sannan ya bushi hayaƙin ya hura a fuskarsa sannan ya ce .

"Mu tantirai ne kuma na sani amma duk tsiya ba na butulu ba ne, ka koyi halarci a Rayuwarka, ina da tarihinka da butulcin da ka yi wa ɗan uwanka uban gidansa wanda ya zama garkuwa a gare ka lallai kai babban maci amana ne."

Tsuke fuska ya yi tare da cewa .

"Wannan bai shafe ka ba aiki na kawo maka kuma zan maki biya mai tsoka idan za ka yi."


_Jidderh_

Bayan ta kammala aikinta ta nufi ɓangaren ma'aikatan gidan, kai tsaye ta nufi ɗakin Mama. Da sallama ta shiga, Mama ta amsa tare da ba ya izinin shigowa.

Shigo wa ta yi t tarar da Mama na ninke kayan z ta wanke.

"Jidderh ke ce?"

"Eh Mama ni ce."

"Na ɗauka kin tafi gida lokacin tashin ki ya yi."

*Ban tafi ba Mama dama ina son magana da ke."

"To ki zauna mana Jidderh."

Ta yi maganar tana nuna mata kujera mai zaman mutane uku. Zama ta yi tare da cewa.

"Barka da warhaka Mama."

"Barka dai Jidderh ina fatan dai lafiya."

"Lafiya lau dama ina son na sani yaushe Dad zai dawo?"

Kallon ta Mama ta yi tare da yin ɗan jim sannan ta ce.

"Ni ina zan sani ai wannan ba hurumina ba ne."

"Haka ne amma dan Allah ina son na tamabaye ki ko ka kin san in da Sir Asadullah ya tafi?"

Kallon mamaki ta yi mata tarar da cewa.

"Jidderh wannan amsar ban san amsar da zan ba ki ba."

"Am dama na gan shi a cikin gidan nan ne?"

Da mamaki ta kalle ta tare da cewa.

"Ban gane yana gidan nan ba, bayan kowa na gidan nan ya tabbatar da cewa baya nan, a ina kika gan shi ?"

"Shiru ta yi tana nazari don da alama masu neman kashe shi suna cikin gidan da alama ma na kusa da shi ne, kada yanzu magana ta fita ga shi baya cikin hayyacinsa kada ta ɗaure kanta. Don haka ta canza zancen da cewa.

"Shekara nawa kika dauka Mama kina masu aiki a gidan nan?"

"Zan kai shekaru talatin ina aiki a gidan nan, akan idanuna aka haifi Asadullah da sauran yaran."

"Mama idan ba damuwa zan so ki bani tarihin wannan gidan."

Murmushi Mama ta yi tare da cewa

"Ba damuwa yanzu ina da aiki idan ki ka sake zuwa zan baki tarihin wannan bahagon gidan."

Kallon mamaki ta yi mata tare da cewa.

"Bahagon gidan kuma Mama."

Murmushi irin ta su manya sannan ta ce.

"Ba za ki gane ba, wannan gidan ya wuce sanin tunaninki , Allah ya kyauta."

Ta so jin wani magana daga bakin Mama amma ba yadda ta iya haka ta yi wa Mama sallama ta bar gidan zuciysrta cike da saƙe-sake.



*Kuyi hakuri da wannan*


Maman Ihsan ce✍️

09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z



*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page1️⃣5️⃣

Ta so jin wani magana daga bakin Mama amma ba yadda ta iya, haka ta yi wa Mama sallama ta bar gidan zuciysrta cike da saƙe-sake.

Ko da ta koma gidan sallama ta yi ta shiga, Inna na zaune bisa tabarma a tsakar gidan tana yi wa yaron Sa'adatu. Sa'adatu na tuƙa tuwo a saman murhun gawayi.

Amsa mata sallamar suka yi tare da mata sannu da zuwa. Amsawa ta yi sama-sama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login