Showing 93001 words to 96000 words out of 154779 words

Chapter 32 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6287

ce

"Hope dai ba wata matsala."

"To ai kiransa wallahi ba alkhairi ba ne."

Maryam ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Ba ku sani ba sai kun ke kun tambaye shi za ku san dalili."

"Yaa Faisal me ya saka yau ba ka tsaya ka gyara masa part ɗin sa ba ne?"

Nadiya ta yi maganar kamar za ta yi kuka ita ma.

"Yau da wuri na wuce kasuwa customers na jira na, shi kuma bay tashi barci da wuri da na ga bai tashi ba na tafi bayan na tura masa text message a waya ."

Kausar ta ce.

"Allah ya sa mun masa daidai tsoro nake ji ya ce mu gyara masa part ɗin sa. Mu kuma ba iyawa muka yi ba tun da ba mu ke yi ba masu aiki ke mana, haka nan muka ƙoƙarta muka yi masa."

Sai a lokacin Faisal ya gane dalilin ɓacin rai da ya gani akan fuskarsa. Dariya ce ta taso masa amma sai ya shanye ya ce su je yana jiransu kada su ƙara wa kansu laifi.

Nabeela ce ta fara tashi ta ce su tashi su je su gani.

Suna zuwa babban falon gidan suka ga Mummy da Umma sai Aunty Laila.

Ganin yanayinsu Umma ta ce.

"Lafiya kuwa kuke?"

"Wai Yaa Hilal ne yake kiran mu."

"Okay to ku je ku same shi ku ji."

"Wallahi tsoro nake ji"

Nabeela ta yi maganar tana kallon mahaifiyarta Aunty Laila.

Ganin haka ya saka Sunyi Laila ta ce.

"Ke ba na son rashin hankali daga kira sai ku fata tsoro wata kila akwai abinda za ku yi masa ne?"

"Mu tafi don Allah kada mu yi laifi."

Cewar Maryam ta na yin gaba zuwa hanyar matattakalar stage ɗin.

Mara mata baya suka yi har zuwa falonsa layi suka jera kamar an ce su jeru.

Sallama suka yi suka shiga ƙofar falon ya amsa can ƙasan maƙoshinsa.

Kansa a ƙasa yana kallon ƙasan tile ɗin kamar me karantar wani abu a ƙasan Ɗago kai ya yi ya kalle su, yatsarsa manuniya ya saka ya shafi dogon karan hancinsa wanda ya dace da kyakkyawar fuskarsa.

Ganin yanayin da suka same shi sun tabbatar ransa ya yi ƙololuwar tashi.

Zuba masu rikitattun idanunsa ya yi ɗaya bayan ɗaya yake kare masu kallo kafin ya ce.

"Me na saka ku kafin na bar gidan nan?"

"Gyaran part ɗin ka?"

"Me kuka yi yanzu?"

Nan suka hau bashi hakuri suna cewa wallahi ba su iya ba ne. Cikin mamaki da takaici ya kalle su ya ce

"Shut up!"

Ya daka masu tsawa wanda ya saka suka zube a gabansa saman guiwoyinsu.

"Ko kunya ba ku ji ba, kuna ƴaƴa mata ace ba ku san yadda za ku kula da muhalli ba? Tur da wanan rayuwar ta ku."

Ji ya yi kansa ba masa ciwo ba zai iya dogon magana ba.

"Na baku mintinan ashirin na ga komai yadda ya dace. Idan ba haka ba."

Ya faɗa yana cije laɓɓansa na ƙasa.

Ficewa ya yi ta ƙofar baya da ke cikin part ɗin na su.

Cikin tsoro kowaccensu ta kasa magana sai aiki suke yi ta ko ina.



*Washegari*

_Asadullah_

Yana zaune kan sofa ya jingina bayansa idanusa alumshe kamar mai barci.

Sallamar Dr Isma'il ne ya dawo da shi cikin duniyar da ya lula. A hankali ya bude idanunsa ƙawayan idanunsa da suka kasance blue ya sake su a kan Jidderh.

Jallabiya ce a jikinsa fara duk wanda ya san shi kallo ɗaya za ka masa ka san ya rame.

"Dr ya jikin na ta ina fatan dai ba wata matsala ko?"

Asadullah ya tambaya cikin tausaya wa

Zama Doctor Isma'il ya yi ba tare da ya ce komai ba.

"Ka yi magana mana akwai matsala ne?"

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kalli Jidderh sannan ya mai da dubansa ga Asad.

"Yallaɓai a gaskiya duk binciken da aka yi ba wata matsala a tattare da ita. Ƙwaƙwalwarta lafiya lau take ba wata matsala.

"Ban gane ba wata matsala ba yarinyar nan ba haka take ba accident muka samu "

"Ban yi maka musun cewa ba accident kuka samu ba, ina mai tabbatar maka da cewa ƙwaƙwalwa yarinyar nan lafiya lau take babu wata damuwa s tattare da ƙwaƙwalwarta. Ko bugawa ba mu gani ba ƙalau take."

"Ba ƙalau take ba!"

Ya faɗa rai a ɓace.

Duk yadda Doctor Isma'il ya so fahimtar da shi ƙi ya yi daga karshe dai hakura ya yi ya masa sallama akan gobe zai dawo.

Kallonta ya yi ta zauna kan kujera ta dubawa TV.

Sulaiman ne ya yi sallama ya shigo. Bayan ya gaida uban gidansa cikin girmamawa ne ya mika masa ledar hannunsa.

Wata kwali ne y ciro daga cikin ledar, waya ce ya fito da ita daga cikin kwalinta.

Har da sim card an yi register an yi komai.

Saka sim card a cikin wayar ya yi ya saita komai.

Har lokacin fuskarsa ba walwala. Sulaiman ne ya ce.

"Sir zancen CCTV Camera na yi yadda ka ce yanzu ba wata matsala in sha Allah."

Ya yi maganar yana kallon Jidderh wacce ba ta san me ke faruwa ba.

"Gud job."

Ya faɗa idanunsa akan wayar dake hannunsa.

"Za'a kai yarinyar nan wani asibiti a ninki matsalar ta."

"Sir me Doctor Isma'il ya faɗa?"

"Wai laflya lau ƙwaƙwalwarta take."

Da mamaki Sulaiman ke kallonta don tabbas ba haka ya san yarinyar.

"To yallaɓai ya kake so ayi yanzu?"

Shiru Asad ya yi kamar ba zai yi magana ba kafin ya ce.

"A canza mata wani asibitin don gano matsalar amma ban gamsu da zancen cewa ƙalau take ban yarda ba."

Jinjina kai Sulaiman ya yi kafin ya ce.

"Ba damuwa zan kai ta asibiti maikyau ƙwararrun likitoci za su duba ta."

Jinjina kai ya yi kafin ya tashi ya haura upstairs.

Kai tsaye bedroom ɗin sa ja shiga. Ya wani na'ura ya danna dake manne jikin bango, take dai ga wata dorowa ta bayyana wanda ba za ka taɓa cewa akwai ta wajen ba. Kuɗaɗe ne a ciki jere daga kan Dollar har zuwa Naira.

Ɗiba ya yi ya zuba a wata ƙaramar jaka kafin ya fita zuwa falo in da ya samu Sulaiman.

Zama ya yi a in da ya tashi kafin ya ce.

"Ya kamata ka nemo mata abun da za ta ci kafin ku tafi zuwa wani asibitn."

Jinjina kai Sulaiman ya yi sannan ya mike tsaye ya nufi ƙofar fita ya fice.



_Hilal_

Tsawon mintuna talatin ya ɗauka a wajen garden ɗin kafin ya bi ƙofar baya ya koma part ɗin sa.

Ko da ya shiga tsaye ya same su dukkansu kowacce a tsorace take .

Falon ya fara dubawa ya ga ba abinda suka gyara da alama iya iyawarsu kenan ba su iya komai ba.

Idanunsa ne suka sauka akan home theater da ruwa ke ɗiga daga sama na shi zuwa ƙasa. T.V ma haka, Centre table ma haka.

Bedroom ya koma ya ga sun gyara shimfidar zanin gadon amma lillubashi suka yi filon ma a karkace.

Cikin ɓacin rai ya karasa in da suke yana zuwa kan Maryam dake ita ce farko ya ɗauke mata wani lafiyayen marin da sai da ta ji ji da ganinta ya ɗauke. Kafin ta ankare ya saka ƙafa ya harɗe mata ƙafa tare da zubar da ita ta fadi ƙasa wanwar.

Haka ya yi masu dukkansu sai da suka zube suna ihu.

Daga nan ya saka su tsallen kwaɗo suna yi suna kuka.

Har sun gaji amma sun kasa tsayawa wa, sai da ta tabbatar sun gaji kafin ya dakatar da su.

Kuka da majina suke yi iya jigatuwa sun yi. Kafin ya ce.

"Kodayake ba laifin ku ba ne, saboda an sabgarta ku ba'a koya maku ba kasancewar ku mata waɗanda za su je gidan wani. Ko wane namiji ne zai yarda a ce yar aiki ke masa aikin gida?"

Shiru ya yi kafin ya ce.

"Ku tashi ku fice mani daga nan."

Sun kasa tashi da rarrafe suka fice. Sai dai zuwa wajen matattakalar ya saka kuka don ba za su iya taka ƙafar ba.

A zaune suna jan mazaunai suka sauko har lokacin kuka suke.

Mummy, Umma, Aunty Laila da suke falon suka taso cikin tashin hankali jin kukan yaran na su.

Cikin tashin hankali suka taso suke tambayar abinda ke faruwa. Ba su iya amsa masu ba, shi kuma Hilal ya hangi ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ta fito bangaren Aunty Laila.

Kiranta ya yi ya sanar da ita cewa ta kira masa duk ma'ikatan gidan, ta wuce jikinta na rawa .

Cikin ƙufula Mummy ke kallon su Kausar kafin ta ce.

"Me suka yi maka ne haka kana neman illata su?"

Kafin ya yi magana masu aikin gidan suka karaso wajen . Kallonsu ya yi kafin ya ce .

"Su waye ke gyara masu part ɗin su?"

Ya yi maganar yana nuna su Nabeela dake jigace.

Wasu ƴan mata masu suna Saude da Lami suka ce su ne. Jinjina kai ya yi kafin ya ce

"Daga yau ba ƴanta ku daga yi masu aiki, kuma idan na ji labarin cewa kun gyara masu part kai ko tsinke idan kuka kawar sai kun bar gidan nan."

Da sauri suka bashi hakuri suna cewa za su kiyaye.

Mai da dubansa ga wata dattijuwar mata ya yi wacce suke kira da Baaba ya ce.

"Mama duk sanda za ki yi girki a cikin gidan nan ki tabbatar yaran nan suna cikin kitchen kina koyar da su girki. Idan gari ya waye za ki shiga kitchen ki aika a kira su haka da rana ko yamma sai dai idan sun je school wannan ba matsala. A cikin sati biyu da koyon nake son su fara gwada wa. Idan wata ta yi maki rashin kunya ko cin mutunci ki sanar da ni."

Jinjina kai Baaba ta yi sannan ta ce .

"In sha Allah za'ayi yadda ka ce."

Sallamar su ya yi suka fice, har lokacin su Maryam na kuka .

A ƙufule Mummy ta sake magana .

"Akan me za ka yanke irin wannan hukuncin sai ka ce ba na gaba da kai. Akan me za ka ce su za su dinga aiki sai kace Kai?"

"Sunyi Laila ta ce.

"Hilal me kake yi haka ne?"

Daidai lokacin da Papa da Dada suka shigo bayan direba ya dauko su.

Cikin damuwa suka karasa wajen in da Dada ke cewa

"Meke faruwa haka me ya same su?"

"Dada ki bar su tarbiyyar da aka kasa ba su ne nake ƙoƙarin ba su shi a matsayin wa tun da iyaye sun gaza ba su gatar da ake bawa kowace ƴa mace."

Jin haka ya saka suka fahimci komai Papa ya ce wa Hilal ya rabu da shi haka, kafin ya nufi part ɗin su Dada na biye da shi a baya.

Mummy ta sake ɓata rai ganin tana mahaifiyarsa bai saurare ta ba.

"Ba da kai nake magana ba Hilal mu kake cewa ba mu ba wa yaran nan tarbiyyar ba sai kai ne za ka basu? To ka fita daga idanunna ba wanda ya isa ya saka yaran nan aikin da ka ce su yi tun da ba jakai ba ne, akan me me za ka wahalar da shi Allah ya hutar da su to wannan karon dole na taka maka birki."

Mumrmushin takaici ya yi, Aunty Laila ta ce

"Akan me za ka mayar da yara kamar marasa gata har da aikace-aikace ba za su yi ba."


"Shikenan ku kuma mu zuba ni da ku wanda ya fasa."

Cikin rawar murya suka hada baki wajen cewa za mu yi aiki.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z




*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect

*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*



*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*



Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.


Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.



Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩


1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more



Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.


*YAR GIDAN TAFIDA*


Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.



*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.

Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯





Page4️⃣6️⃣


Cikin rawar murya suka haɗa baki wajen cewa za mu yi aiki.

"Gud"

Ya faɗa yana amsa kiran wayar da ake masa ya fice daga falon.

Nan suka saka masu aikin suka taiamaka wa su Kausar zuwa part ɗin su.


Zahrah bayan ta samu yi nutsuwa ne ta na zaune tana karatun Alkur'ani da kanta kasancewar ta haddace ta .

Suratul Maryan take ƙarantawa cikin muryarta mai zaƙin sauraro.

Kitchen ta nufa da niyyar taya Umminta aiki, sai Ummin ta fito take sanar da ita yau abincin gidan za su ci su ma, ta je ta yaya Dada girkin.

Fita ta yi ta nufi part Dadar da sallama a bakinta. Suka amsa kafin Dada ta cigaba da cewa.

"Ban ga laifin Hilal ba daidai kenan, iyayensu ba son gaskiya suke yi ba."

Sannu da dawowa Zahrah ta yi masu kafin ta ce.

"Dada me za ki girka ne, ko na gidan gabaɗaya za ki ci?"

"Eh saboda yau na gaji ba zan iya girki nan ba, amma tun da kin zo shiga ki sama mana abu mai sauƙi."

Kitchen ɗin ta nufa Daidai lokacin da Sunyi Laila ta shigo da sallama.

Amsa mata suka yi ta shigo ta zauna tana cewa .

"Barka da warhaka Papa. Dada ina wuni?"

Ba wanda ya amsa mata, ita ma sai ta tsuke fuska.

Tabbas ba sa jin daɗin abinda Aunty Laila da su Mom suke yi. Sai dai Aunty Laila ce suka haifa ita ce ƴarsu. Su Mummy da Umma surukai ne hakan ya saka ba su cika matsa masu ba sai Aunty Laila.

Papa ne ya yi gyara murya ya ce.

"Laila."

"Na'am."

Ta amsa bayan ta daga kai ta kalle shi.

"Ba na sanar da ke cewa ki kwashi su Nabeela da Kausar ki mayar da su gidan ubansu ba?"

Kara ɓata rai ta yi tana cewa.

"Mutumin nan fa ya sake ni ya dauki matarsa sun bar ƙasar nan. Zan taho gidan ubana ne bar su wajen waye tun da bai damu da yaran ba. Kuma nan gidan Kakansu ne ai gidan Mahaifina ne. Ba na da inda zan kai su bayan nan Papa ka duba lamarin nan."

Shiru ya yi kafin ya ce

"Duk in da za ki kai su bai fi a ce suna gidan mahaifinsu ba ai da uba ake ado ba uwa ba."

"Amma a baya lokcin da mahaifiyar Zahrah ta ce za ta tafi gida ta gaji ai cewa kuka yi ba za ta tafi da Zahrah ba don ba ta da in da ya fi nan. To ita kun yarda za ku rike ta ballantana yara na Kausar da Nabeela a ce su bar gidan nan."

"Zahrah nan ne gidan mahaifinta ba ta da in da ya fi nan don nan ne adonta ba dangin uwarta ba."

Nan ta basu haƙuri tare da cewa za ta mayar da su, amma a. Zuciyarta ta ayyana ba abunda zai raba ta da yaranta.


Zabarah na kitchen tana jin duk tattaunawar da suke yi ta cigaba da aikinta.

Shinkafa dafa duka na gargajiya ta yi, na manja ne ta zuba Daddawa da da busashshen kifi ya ji kayan miya amma ban da tumatir.

Sai da ta kammala ta fito Daidai lokacin da ake kiran sallar magrib.


_Isah_

Cikin damuwa ya yi sallama ya shigo cikin gidan, Inna da Aunty Sa'adatu ne ke zaune a tabarma tsakar gidan.

Kallo ɗaya za ka yi masa ka san cewa suna cikin damuwa.

Amsa sallar suka yi Inna ta mike tsaye da sauri tana cewa.

"Isah ya ake ciki sun sun bar ka kuwa ka shiga cikin gidan?"

Girgiza kansa ya yi cikin damuwa.

Kuka Inna ta fashe da shi tana zubewa bisa gwuiwarta.

"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un, ina yarinyar nan ta shiga ne, na yarda da ƴata na san ba za ta gudu zuwa wani wajen ba. Sai dai ban san hannun da ya faɗa ba bisa la'akari da zamanin da muke ciki."

Sa'adatu ce ta kalli Mijinta wanda shi ma dauriya kawai yake yi, idanunta cike da ƙwalla ta ce .

"To yanzu ina ya kamata a ke neman ta kuma?"

"Duk in da nake tunanin ta je na je ban gan ta ba, hatta ƙawayenta ba su san in da take ba."

"Gidan da take aiki fa ka sake zuwa ne?"

"Ban sake zuwa ba Inna, waɗan nan security da nake daga masu ina neman ƙanawata dake aiki a gidan na masu kwatancen ta sun ce ba ta kai wa yamma take tafiya. Na nemi su bari na shiga ciki na gana da masu gudun ba su bari ba. Sai wata buduwarwa mai suna Suhailat it ce ta tabbatar mani da cewa Jidderh ba ta gidan su yake wa aiki."

Ba karamin tashin hankali suka shiga ciki ba. Inna ta saka wa ranta za ta koma mansion ɗin ta nemi jin ta baki iyayen gidan Jidderh.


_Hilal_

Ba shi ya dawo gidan ba Sa ƙarfe goma na dare .

Har lokacin ransa a jagule yake. Bai nufi part ɗin sa ba ya nufi part ɗin Dada, kasancewar yunwa yake ji kuma har ga Allah ba ya son abincin masu aikin gidan. Kuma Mummynsa ba girki take yi ba sai dai Dada ba kullum take cin abincin masu aikin ba ita da Papa sai part ɗin su Abbi kuma.

Da sallama ya shiga part ɗin wanda b wanda ya ji sallamar shi kaɗai ya ji kayansa.

Zama ya yi a kan kujera mai zaman mutum ɗaya.

Ganin yanayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login