Showing 99001 words to 102000 words out of 154779 words

Chapter 34 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6269

yi saurin fitowa ya buɗe wa Daddy da Mom bayan motar suka fito.

Sannan ya dauko kakar kayan Dad ya bi bayansu da shi. Bayan ya ajiye jakar a falo ne Mom ke sanar da shi idan wadan nan baƙin sun iso ya yi masu jagora zuwa ciki. Wato su Innar Jidderh kenan.

Yana fita ya hange su suna t waige-waige suna kallon Mansion ɗin mai girma wanda suka kasa gane ko wanne ne za su nufa don su Mom sun ɓscewa ganinsu.

Alama ya masu da hannu daga in da yake hangen su. Don haka suka nufo ɓangaren da suka gan shi.

Jagora ya yi masu har zuwa bakin ƙofar falon.

Bayan ya ce su shiga ne shi kuma ya fice. Shiga suka yi yayin da wani ƙamshi da sanyi ya ziyarci hancinansu. Ba kowa a falon don su Mom da Dad sun wuce falon ciki.

Zama suka yi a saman tattausan Carpet ɗin da ke tsakiyar falon.


Kasancewar Mom ce da girki ba Aunty ba. Don haka ta aiki ɗaya daga cikin masu aikin gidan akan ya je ta kai wa bakin dake wancan falon ruwa da lemu har da abinci.

Fitowar Aunty daga part ɗin ta kenan don yi wa Dad Barka da zuwa. Fauziyya ma ta fito bayan Mom ta kira ta.

Rungume Dad ɗin na ta ta yi cike da farin ciki tana ta dariya.

"I miss you so much Dad."

"Miss you more my Daughter."

Kallon Aunty ya yi ganin bai gan ta tare da ƴart ba."

"Ina Suhailat?"

"Tana ciki."

Ba ki fada mata zan dawo ba ne ko kuma dawowa ta?"

"Ban fada mata ba Abban Asad."

"Saboda ba ni ne mahaifinta ba ko?"

"Ba haka ba ne..."

Ba wani abun da za ki fada na dade da sanin turbar da kika ɗora ƴarki a kai, ki yi yadda kike so na ɗauke ta tamkar sauran yaran da na haifa amma dake ba ni ne ubanta ba ya saka kike mata shamaki da ni, da ma kowa na gidan nan bakya bari ta yi mu'amala da su musamman Asadullah nan san manufarki ba, Alhamdulillah ni ma na haifa."

Kallon Mom ya yi yana cewa.

"Zan shiga na yi wanka."

"To Alhaji a fito lafiya. Bari na taiamaka maka da kayan da idan ka fito za ka saka."

Ta yi maganar tana bin bayansa.

Taɓe baki Aunyi ta yi tana bin bayanta da kallo. Fauziyya kam idanunta na kan wayarta da alama chatting take yi.


Suna nan zaune Mom ta fito tana duba abincin da masu aikinta duka jera.

Ba jimawa shi ma ya fito daidai lokacin da Mom ta fara ƙoƙarin yin savin ɗin sa.

Kai tsaye ya nufi dinning area ɗin.

Bayan ta zuba masa ne dai ga Aunty ta karaso wajen kasancewarsu tare suke cikin abinci in dai yana gari.

Gudun ka da ya sake nuna ɓacin rai akan rashin zuwa. Suhailat ya saka Aunty ta kira wayar ƴar ta ta, shaida mata ta fito ta yi kafin ta katse kiran wayar.

Mom ta zuba wa Aunty sannan ta zuba na ta abincin.

Kusan a tare Suhaila dake part ɗin Aunyi da kuma Fauziyar dake chatting tare suka ƙarasa wajen dinning table.

Mom ta kalli Dad da ya kasa cin abinci ta ce.

"Dad ɗin yara na san meke damunka, ka yi hakuri ka ragewa kanka damuwa, muna muna ta addu'a kuma na saka malamai su yi masa addu'a in sha Allahu Allah zai bayyanar mana da shi ."

Murmushi ya yi cikin jin dadin kalamanta. Sai dai ba damuwar Asadullah kawai ba ne a zuciyarsa yanzu har da damuwar Kamal dake prison akan mugayen halayyarsa.

"Ba damuwoyi sun yi Mani yawa, ga ya rashin san in da Asadullah yake ga kuma matsalar Kamal dake gidan yari."

Mom ta kalle shi ta ce.

"Damuwar rashin Asadullah ce kawai a wajena, amma Kamal ba abun da ya dame ni da shi duk da ni na haife shi amma a yanzu na fi kowa tsanarsa ko sunansa ba na so na ji ana ambatar mani, mutumin da ya yi yunkurin kisan kai, kisan ma dai ɗan uwansa da ya zame masa gata a rayuwa? Me ya yi masa? Akan abun duniya wanda duniya za mu barshi gidan aro? Da ya yi kashe Asad da tabbas ya dade da mutuwa. Ko yanzu kamar matacce yake a wajena domin na riga da na rufe shafinsa dag cikin rayuwata."

Taɓe baki Aunty ta yi tare da cewa.

"Uhmm in ji mai ciwon hakori."

Kallonta Mom ta yi tana girgiza kai kawai ba tare da ta ce komai ba.

Dad ne ya kalli Aunty ya ce.

"Zulaihat wai ke ba za ki taba sauyawa ba, har a wannan halin da muke ciki?"

"To me na ce maku ne?"

Tashi ta yi ta bar wajen abincin ma ba ta ci ba, ta koma main falon gidan.

A can ne ta tarar da su Inna, kallon su ta yi sannan ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerar dake falon.

Inna da Isah da Sa'adatu suka gaishe ta. Ta amsa masu ba yabo ba fallasa. Ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta jijjiga ƙafa.

Bayan kamar mintuna goma sai ga Mom ta shigo tana kallonsu Inna da Murmushi a fudkarta .

"Don Allah ku yi hakuri bayin Allah, na ɗan sha'afa ne kasancewar dawowar mai gidan kenan daga ƙasar."

Murmushi Inna ta yi tana cewa.

"Ba komai Hajiya."

Zama ta yi sannan ta kira mai aikin gidan ta ce ta kawo masu abinci. Nan suka ce sun ƙoshi ba za su ci ba. Dole ta bar su don sun dage.

"Me kuka ce yana tafe da ku ne ma?"

Cikin rawar murya irin ta mai shirin kuka Inna ta ce.

"Ƴata Jidderh dake maku aiki muka nema muka rasa tun shekaranjiya"

Da mamaki Mom take kallo Inna, sai ta ce.

"Haba Baiwar Allah tun shekaranjiya shi ne sai yau kike zuwa nemant"

Isah ne ya ce.

"Hajiya kwana biyu ina zuwa ba na samun shihowa saboda masu tsaron kofar ba su bari ba."

Kallon Aunty Mom ta yi kafin ta ce.

"Zulaihat kin ji wai yarinyar nan aka nema aka rasa."

"Allah ya bayyanar da ta."

Ta fada tana tuna turin kai irin na yarinyar.

Mom ta ce.

"Tun ranar da muka yi gobarar nan ta tafi gida ai ba ta dawo ba. Amma. Bari na kira abokan aikinta na ji ta bakinsu."

Nan ta kira masu aikin gidan mata ta tambaye su kowa ya ce tun shekaranjiya na su sake ganinta ba.

Kula Inna ta saka suka tashi suka mike don tafiya. Mom ta basu kudi masu yawa tare da masu addu'a Allah ya bayyana ta.

Sa'adatu ce ga karbi kudin wanda za su iya kai dubi dari ta ciri a cikin jakkarta.

Fita suka yi isah na rike da Inna suka fice daga mansion ɗin.



*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z




*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect


*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*



*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*



Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.


Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.



Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩


1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more



Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.


*YAR GIDAN TAFIDA*


Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.



*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.

Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯



Page4️⃣8️⃣

Fita suka yi Isah na rike da Inna suka fice daga mansion ɗin.


_Asadullah_

Fitowa ya yi daga bedroom ɗin ya sauko downstairs. Sanye yake da wando three quarter baƙi da jan shirt. Ya ɗan canza a cikin kwanaki biyu da barinsa wajen da aka ɓoye shi. Kyawunsa da cikar haibarsa sun kara bayyana.

Zama ya yi a saman sofa ya kai hannu ya shafa tattausan gashin kansa wanda ya kwanta ya kwanta luf irin na fulanin usuli ya shafa tare da yin gajeren tsaki.

Daidai lokacin ya ji ƙarar ƙararrawar ƙofa. Ta jikin gilashin ƙofar ne ya ya hango Barrister Haris tare da wata mace a tare da shi, wacce ba za ta wuce shekaru ashirin da biyar ba

Remote ya danna ƙofar ta buɗe kanta suka shigo.

Da sallama a bakinsu suka shigo falon, ya amsa ba tare da ya sake Kallansu ba.

Barrister Haris ya karaso gabansa ya mika masa hannu suka yi musabaha sannan suka gaisa.

"Ga ta nan ita ce ƙanwar Matata mijinta ya rasu ne kamar yadda na faɗa maka.

"Ina wuni ranka ya daɗe?"

Kallonta ya yi ya amsa ba yabo ba fallasa.

Murmushi Anisa ta sake
'

Barrister Haris ya ce.

"An gama yi mata komai na shirin tafiya."

Jinjina kai ya yi tare da cewa.

"Ina fatan kin gane dalilin da ya sa na ɗauko ki, ina bukatar ki kula da iya fiye da yadda za ki kula da kanki."

Kallonsa ta yi sakamakon jin kalaman Asad ɗin, wato ma fiye da yadda za ta kula da kanta.

'So so ne, amma son kai ya fi, kafin na hango abun da zai faranta ran wani dole sai na hango wanda zai faranta mani rai.'

A fili kuwa sai cewa ta yi.

"In sha Allah zan yi fiye da yadda kake bukatar."

"Na wa ne farashin da zan biya ki? Sannan kuma ina bukatar sirri ba ma son kowa ya san wani abu game da ni ko wajen da nake ina fatan kin gane?"

Jingina kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.

"Ba kya ji na ne?"

"Kada ka damu yallaɓai na san kai sanannen mutum ne so ba zan taba fadar komai game da kai ba. Sannan farashi kuma ba sai ka biya ba don ni ka taimake ni ma a haka?"


"Ki faɗa dole ne sai na biya ki kamar yadda na faɗa.

"To ko nawa ne Allah ya sa albarka."

"Account details."

Ya faɗa yana sarrafa wayarsa.

Karanto masa account number ta yi bayan ta gama faɗa take sai ga shigowar saƙo. Tana budewa ta ga 2 million ne ya tura mata

Zare Idanu ta yi tare da cewa.

"Miliyan biyu yau na Mallaka ta wa ta kaina?"

Ta fada har da ihu tana kallon Barrister Haris. Murmushi ya yi tare da cewa.

"Allah ya saka da alkhairi sir."

Nuna mata ɗakin da Jidderh take ya yi sannan ya ce .

"Ga ɗakinta nan, gobe in sha Allah za ku tafi. Tare da wani Doctor ku uku za ku yi tafiyar."

Ba ta amsa ba sai zuba masa Idanu da ta yi kamar za ta cinye shi. Jin yanda Idanu ke yawo a jikinsa ya saka ɗaga kai ya kalle ta, da sauri ta ɗauke idanunta tana cewa.

"Bari na shiga na same ta ."

Bai sake magana ba ita ma ba ta jira cewar ta ba don ta ji kunyar kallon da ya mata.

Tana tura ƙofar ɗakin da sallama ta shiga. Jidderh na kwance kan gado na barci take yi ba. Amma jin ƙarar ƙofar ya saka ta tashi zunne.

Yanayin Anisa ne ya canza sakamakon ganin Jidderh cikakkiyar budurwa, kyakkyawar gaske. Ita a zatonta yarjnya ce ƙarama za ta kula da ita. Kuma ta shigo da niyyar yadda za ta samu kusanci da Asadullah ne. Sakamakon son da take masa. Duk da ba ta ji dadin da Barrister Haris ya sanar da shi cewa ta taɓa yin aure ba, ta so ya dauka budurwa ce ita .

Sai dai abin tambaya Meye alaƙarasa da wannan yarinyar?

A hankali ta tako zuwa in da take kwance kan gadon, har lokacin ba ta daina kallon Jidderh ba. Ita ma a ɓangaren ta ta zuba mata dara-daran Idanunta ne tana kallon bakuwar fuskar.

Zama ta yi a gefen gadon, tana kallon Jidderh tare da sakar mata mumrmushi, don dole sai yarinyar ta saki jiki da ita.

Doguwar rigar Material ce a jikin Jidderh, kanta ba ɗankwali. Kitson dake kanta ya fara tsufa.

Rike hannunta ta yi tana murmushi sannan ta ce.

"Sannu ƙanwata."

Ba ta magana illa iya ka ta yi mata murmushin da ita ma shi ta yi mata.

Tashi ta yi ta nufi gaban dreessin mirror ta duba kayan da aka jera a wajen. Komai sabo ne, don haka sai ta ga abun kwance kitso ta ciro.

Zama ta yi bakin gadon sannan ta janyo Jidderh ta kwantar a saman ƙafarta. Ta fara tsefe mata kitson.


Asadullah ne ya shigo tare da sallama. Anisa ta amsa masa ta daga kai ta kalle shi. Shi ko Jidderh yake kallo wacce ke yamutse fuska alamar tana jin tsifar.

Ƙarasa wa ya yi gabansu har lokacin idanunsa na kan Jidderh.

Har lokacin tana ɓata fuska kuma da alama ita ma irin masu jin zafin kai ne da ba sa son ana yi masu kitso ko tsifa. Alama ya nuna hakan bisa la'akari da yadda kitson ya tsufa alamar ya daɗe ba'a kwance shi ba. Sai dai ba datti alamar tana wankewa kitson ne dai ba ta so.

"Ki yi mata a hankali akwai zafi."

Ɗan karawa ta yi kafin ta ce.

"Yallaɓai a hankali nake mata ba zafi."

"Ya za ki ce ba za fi ga shi yanzu tana yi kamar za ta yi kuka."

Ya karasa maganar cikin rashin jin dad'i.

Daga nan ya fita ta bi bayansa da kallo. Har yanzu tana son jin alkarsa da yarinyar amma ba wanda za ta tambaya. Shi dai ba ta ga fuska ba.

Yana komawa falon sai ga Sulaiman ya iso. Bayan sun gaisa ya kalli Asadullah ya ce.

"In sha Allah nan da kwanaki biyu za'a kammala binciken, na jima a can don ban sake shi ba, ko da ya karaso yana da baƙi sai da na jira."

Jinjina kai Asadullah ya yi tare da cewa.

"Okay."

"Sir ya kamata na rage yawan fita da nake yi, wannan zirga-zirga da nake ba na wajenka ba na gida zai iya janyo hankula jama'a ya dawo kaina.

"Haka ne ya kamata ka koma idan da bukatar wani abu zan kira ka a waya."

Sallama suka yi sannan Sulaiman ya bar gidan.


Ko da ya koma Asadullah mansion ya samu security suka gaisa, ciki ya shiga ya fara gaisawa da abokan aikins.

Wani mai suna Auwal ne ya ce.

"Ina kake zuwa ne kwana biyu kuma sai ka fita, wani lokacin ma sau daya ko biyu ba. Alhaji ya dawo har ya tambaye ina ka je."

Da sauri ya kalle shi jin Dad ya dawo.

"Yanzu ya dawo?"

"No ba yanzu ba ya jima da dawowa."

"Okay."

Ya nufi part ɗin Dad don yi masa sannu da zuwa, sannan yana addu'a Allah ya ba ba zai dame shi da tambayar kwakkwafi ba.

Dad, Mom Aunty. Duka suna zaune a falon Sulaiman ya ya shigo bayan ya masu sallama sun amsa.

Cikin girmamawa ya gaida Dad

Ya amsa masa cikin sakin fuska da walwala. Sannan ya dora da tambayar sa.

"Wai ya ake ciki ne zancen uban gidanka har yanzu ba wanda ya ji labarin ko an gan sa a wani wajen?"

Girgiza kai ya yi kafin ya ce.

"Har yanzu muna ta kokari kuma muna addu'a in sha Allah Zai bayyana mana da izinin Allah.

Kallonsa Aunty ta yi kafin ta ce.

"Na lura kwana biyu ba ka zama kamar yadda ka saba, ina kake zuwa "

"Ba in da nake zuwa sai dai idan wani uzurin ne ya fitar da ni."

"Wani uzuri ne zai fitar da kai wanda a baya ba ka fita?"

Kafin ya bada amsa Dad ya ce.

"Haba Zulaihata tun da ya ce uzuri ne dole sai ya faɗa maki?"

"Hmm amma ai ɗaukarasa aiki aka yi kuma biyansa ake yi, duk da uban gidan na sa baya nan, ai an biya su ko last month duk da uban gidansu baya nan. Ni da kuɗin da ake kashewa na ciyar da waɗan nan ƙartin da salary na su ban ga amfanin su ba dan..."

Dad ne ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.

"Ya Isa haka."

Kallon Sulaiman ya yi sannan ya bashi izinin tafiya. Ya fita jiki ba ƙari don kalaman Aunty sun masa zafi."

Bayan ta fita ne Dad ya ce.

"Hajiya Zulaihat bakya kyutawa abun da kike yi."

"Dama ai ba abinda za ka goyi bayana saboda ba matarso ta faɗa ba ."

"Allah ya kyauta."

Mom ta faɗa tana mikewa don komawa part ɗin ta. Aunty ta bi bayanta da harara.



*Prison/ Gidan yari*

Kasancewar yau ranar ziyara ce ga duk ilahirin ƴan gidan yarin. Wasu an kawo masu ziyara suna cikin nishaɗi.

Wasu iyayen su ne suka zo masu wasu kuma abokansu ne suka zo masu, wasu kuma wasu daga cikin danginsu .

Ɓangaren Kamal ma haka ne, an zo masa sai dai ba danginsa ba ne Family Doctor ɗin su ne ya zo masa.

Suna tsaye a ƙafar da z ta sada su da in da Kamal yake.

Kallo ɗaya za ka masu ka fahimci ran kowa a ɓace yake a cikinsu. Wani banzan kallo Kamal ya yi wa Doctor kafin ya ce.

"Idan ma kana mafarkin cewa zan kara ba ka wasu kudi ne to ka farka. Me ka tsinana mani da zan ɗauki wasu kudade na baka?"

Cikin ɓacin rai Doctor ya ce

"Au haka ma za ka ce butulu, ko da yake ban yi mamaki ba, tun da har ka iya yunƙurin kashe Ɗan uwanka da kuka fito tsatso ɗaya Asadullah, mutumin da ya dauki so da yarda ya baka ka ci amnarsa ai ba abinda ba za ka iya aikatawa ba, aiki ka saka ni kuma na yi maka dole ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login