Showing 108001 words to 111000 words out of 154779 words
fice ya bar su. Nasir ya mike don shirin zuwa kamfanin ASADULLAH GLOBAL RESOURCES.
Nasir shi ne Head of marketing department, na kamfanin Asadullah global resources.
_Zahrah_
Tana kwance sume bayan su Nabeela sun tafi sun bar ta da kimanin mintuna goma sai ga Yaa Mahmud ya dawo gidan.
Ganin halin da ƙanwarsa take ciki ne ya saka ya karasa wajen da take kwance da hanzari.
Ganin ta suma ne ya saka ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauke ta ya nufi part ɗin su da sauri tana kiran sunan Umminsu.
"Ummi! Ummu!!
A tare Ummi da Abbi suka fito daga cikin ɗakin, ganin halin da Zaharah ke ciki ne ya saka hankulansu ya tashi sosai da sosai.
"Me ya same ta?"
Abbi da Ummi suka tambaya a tare cike da tashin hankali.
Cikin tsantsan damuwa Mahmud ya ce.
"Wallahi ban sani ba, na dawo kenan na ganta a sume, sai dai da dukkan alamu karatu take yi ciwon na ta ya tashi. Don na ga takardu a gabanta.
Inhelar Ummi ta dauko daga ɗakinta aka shaƙa mata, amma bai yi mata amfani ba don ko motsi ta kasa. Sai Abbi ya umarci Mahmud da ya kwantar da ita a kan doguwar kujerar haka kuwa aka yi sai ya kwantar da ita yayin da Abbi ya yayyafa mata ruwan don ba ta farfaɗo daga sumar da ta yi ba.
Ga shi ba ta cikin hayyacinta ballantana a ba ta magani ta sha.
"Mu tafi asibiti kawai."
Yayin da Mahmud ya yi maganar yana nufar kofar fita.
Kasancewar dama Hijabi ne a jikin Ummi ya saka ta bi bayansu da sauri. Abbi ma ya fito su uku ne Yaa Mahmud na ɗauke da Zahrah.
Ba kowa a babban falon gidan. Sai dab da za su fita suka ji dariya, a tare suka juyo suka ga Nabeela ce da Kausar.
Ba su bi ta kansu ba suka fice har zuwa parking space. Direba ya nufo su da sauri yana cewa.
"Alhaji asibiti za mu tafi."
"Bar shi kawai Sa'idu zan kai ta da kaina."
Ya faɗa yayin da ya nufi motarsa, cikin sauri Sa'idu ya bude masa bayan motar. Ya saka ta.
Ummi ce ta shiga baya gefen Zahrah ta zauna tare da ɗora kan Zahrah akan cinyarta. Yayin da Mahmud ya zauna mazaunin direba Abbi na gefensa suka fice daga gidan bayan ya figi motar da ƙarfi.
Ma'ikatan da suka ga lokacin da aka shigar da ita motar ko motsin kirki ba ta yi.
Lokacin da aka kai ta asibitin emergency room aka kai ta saboda ganin halin da take ciki.
_Asadullah_
Wayarsa ce ke ruri ya duba ya ga Doctor Isma'il ne ke kiransa daga India. Cikin rawar jiki ya ɗaya kiran wayar ya yana addu'a Allah ya sa Jidderh ta samu lafiya.
"Doctor ina fatan wannan karon an samu nasara."
Ajiyar zuciya Doctor Isma'il ya sauke sannan ya kasa magana.
Cikin kaguwa da son jin halin da Jidderh ke ciki ya ce.
"Ina fatan an samu nasara a wannan karon."
Ta cikin wayar ya ji Muryar Dr Isma'il ya na cewa.
"Duka sakamakon ɗaya ne, ina nufin ba wani abu da ake gani. Bincike da gwaje-gwaje da aka yi an tabbatar ƙwaƙwalwarta lafiya lau take kamar yadda sauran asibitoci suka tabbatar."
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un."
Shi ne kalmar da ya fito daga bakin Asadullah. Cikin sanyin jiki ya zauna akan kujera yana dafe kansa.
*Ku yi hakuri ba na jin daɗin jikina ba zan iya dogon typing ba*
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
*Albishir! Albishir!! Albishir!!!*
Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku.
Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇
Flasks
Cups
Dinnerset
Kitchenware
Pot
Jugs
Food processor
bedsheet lamps
Second hand gas
Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887
Page5️⃣2️⃣
Shi ne kalmar da ya fito daga bakin Asadullah, cikin sanyi jiki ya zauna akan kujera yana dafe kansa.
"Ya Salam."
Ya faɗa a zuciyarsa. Yana tausaya wa yarinyar nan da kuma halin da iyayenta za su shiga.
Jin shiru ne ya saka Doctor Isma'il sake magana.
"Yallaɓai kana tare da ni kuwa?"
"Ina tare da kai Isma'il hakika hankalina ya tashi sosai ba kaɗan ba."
"Ka da ka damu in sha Allah za ta samu lafiya a ci gaba da yi mata addu'a."
Jinjina kai ya yi tare da cewa.
"Yanzu ba wata ƙasar da kake ganin za su iya wannan aiki?"
A gaskiya tun a ƙasar mu Nigeria ya kamata ka amince da aka ce maka ba wata matsala a tare da ita, ƙwaƙwalwar yarinyar nan lafiya lau take ."
"Ba lafiya take ba!"
Ya faɗa a tsawace.
Jin furucin Asad ya sa Doctor Isma'il ya san cewa ransa a ɓace yake.
"Calm down yallaɓai. Yanzu ya kake so ayi?"
" Gwada kai ta wat ƙasar , ina ganin a kai ta ƙasar larabawa. Su na su gwada yin na su kokarin ko kuma a kai ta Germany."
Shiru Dr Isma'il ya yi don yana da yakinin duk in da za su ce ƙashe kudi kawai za'ayi, amma duk sakamakon iri daya zai kasance.
"Ya na ji ka yi shiru?"
"Ba shiru na yi ba, ina tunanin in da ya dace a kai ta."
"To ina kake ganin ya dace a kai ta?"
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce.
"Akwai abokina mai suna Kamal Jamil Balaraben kasar Egypt ne, tare da shi muka yi karatu a ƙasar Madina. Mahaifinsa cikakken likitan ƙwaƙwalwa ne, yanzu haka yana da Asibiti a Abu Dhabi Ina ha a kai ta can ƙasar ko Allah zai sa a dace."
Har cikin zuciyarsa ya ji daɗin shawarar da Doctor Isma'il ya bayar, godiya ya yi masa sannan ya ce anijma zai kira shi sai su tsara yadda tafiyar zai kasance."
Sallama suka yi sannan ya kashe kiran wayar.
_Zahrah_
Kwance take a gadon asibiti an saka mata ruwa. Barci take yi yayin da Umminta ke zaune saman gadon wajen saitin ƙafarta.
Abbi na zaune a kan kujerar yayin da Yaa Mahmud ke tsaye ya jingina da bangon ɗakin.
Dukkansu zuba mata idanu suka yi suna kallonta.
Dada da Papa ne suka fito ƙofar dakin suka shigo da sallama a bakinsu. Sai direban da ya kawo su wanda shi ne yake sanar wa Papa halin da suka ga Zahrah a ciki an kai ta asibiti.
Babu ɓata lokaci kuwa sai suka ce ya kawo su tun da sun san asibitin da suke zuwa dole nan za su kai ta.
Bayan sun amsa sallamar su Papa ne suka shigo .
"Abbi ya ba Papa kujerar da yake zaune ya zauna, yayin da Dada ta zuba saman wani kujerar dake kusa da na Papa.
"Ya aka yi ciwon na ta ya tashi na ga yanzu ba lokacin yawan tashinsa ba ne?"
Mahmud ne ya ce.
"Wallahi Papa ban san dalilin rashin ciwon na ta ba, sai dai kawai na dawo na ganta kwance a ba ya motsi, kuma da dukkan alamu karatu take yi, don na ga takardar da take karantawa a gefenta."
Shiru Ummi ta yi kafin ta ce.
"Na yi mamakin halin da ka ce ma Ni ka same ta, saboda yanzu ba lokacin sanyi ba ne, ciwon na ta ya fi tashi a lokacin sanyi. Kuma yanzu ciwon na ta bai cika tsananta haka idan tana gida, don idan tana gida ta zaran ta ji alamar ciwonta zai tashi take take neman magani, shi ya sa kwanan nan baya mata tsanani, saboda tana kiyaye wa sosai."
Shiru suka suka yi kowa da tunanin da yake yi a ransa. Yaa Sadik ne ya shigo kamar an jefo shi daga sama.
Ƙarasawa ya yi wajan gadon yana kallonta.
"Ammi harin ya hakan ta faru?"
"Wallahi ban Sani ba Sadik, Yayanka ne y kawo ta rungume a hannunsa wai ya ganta a gidan ta sunfi."
"Anya ba wani abu aka yi mata kuwa? Ta yaya har za ta kai ga suma bayan..."
Abbi ne ya ya dakatar da shi ta hanyar cewa
"Ya isa haka Sadik, ba na son jin wata magana kuma. Na san halinka kada ka janyo mani wani tashin hankali ka bar mu mu ji da halin da take ciki."
Shiru kawai ya yi ba don ransa ya so ba, sai dai zancen sa ya sanya Mahmud cikin tunani, saboda lokacin da Mahmud ya ɗauki zabarah zai kai ta asibiti ya ji sautin dariya kafin ya fita daga falon gidan, bayan ya juya dai ya ga Kausar da Nabeela suna dariya. Da a lokacin Sadik na wajen ko kuma shi ya dauko Zaharah to ba makawa sai ya ajiye Zaharah ya ci ubansu ko sama da ƙasa za ta haɗe, don shi ba tsoron tashin hankali yake yi ba. Shiru Mahmud ya yi don idan ya faɗa Sadik ya ji ya san zai iya komawa gidan kuma ya tuhume su don ko shi bai da tabbas
Kuma Abbi ba zai ji dadin hakan ba ko kusa. Don haka ya yi shiru don samun zaman lafiya a cikin wannan zuri'ar.
Wayar Papa ce ya yi ruri ya fita waje ɗin dubawa. Har zuwa lokacin Sa'idu direba na jiran su Papa da ya kawo.
Bawan ya matsa ya ba Papa hanya ya fita ne shi ma ya samu wata kujera ya zauna.
Daga cikin ɗakin kuwa wayar Zaharah ke ruri, don kuwa lokacin da Mahmud ya ɗauko ta ya ga wayarta a wajen ya ɗauka.
Har sau uku ana kira kafin Sadik ya ce .
"Wai waye ke samun mutane ne yanzu haka, ga mai wayar na kwance a karfe wayar gabaɗaya mana."
"Ammar ne ke kiranta."
Daga Dada har Ummi suka kalli wayar. Kafin Sadik ya ce .
"A fada masa halin da take ciki ba ta laflya mana."
Dada ta mika masa hannu alamar ya bata wayar. Mika mata wayar ya yi bayan ya yi picking zalla ɗin.
Cikin wayar ta ji ya ce.
"Masoyiya ta laflya kuwa ina ta kira shiru?"
"Ba ita ba ce Ammar, tana kwance a gadon asibiti ne yanzu haka tun a gida aka ɗauki ta a sumammiya.'
Cikin tashin hankali Ammar ya ce.
"Subhanallah Dada me ya same ta ne?"
"Ciwonta ne ya tashi."
"Subhanallah lallai zan zo Nigeria gobe in sha Allah."
Cikin mamaki Dada ta ce.
"Wani irin za ka zo gobe kuma, ka kwantar da hankalinka Ammar, ciwonta ne ya tashi ba wani bakon al'amari ba ne ya same ta, in sha Allah za'a sallame ta yau ko gobe."
"Allah ya sa haka Dada, kuma Allah ya bata lafiya, amma hankali na ya dawo Nigeria ba zan iya haƙura ban zo na hanta ba."
Duk yadda Dada ta so ta hana Ammar zuwa ki ya yi , don haka ma ta bar shi dole ganin ya kafe akan abu guda.
Addu'ar Allah ya kawo shi lafiya ta yi masa. Kafin suka yi sallama ta ajiye wayar daman Drawar na yi gadon mara lafiya. Kallon Abb da Ummi ta yi kafin ta ce.
"Ammar ne wai zai zo gobe ya sun jikin Zajrah."
"
Ummi ta ce
"Da dai ya yi zamansa Dada mutum ya taso tun daga London ya zo duba ta akan Meye, mun yafe ya yi zamansa kawai."
"Ni ma haka na ce masa amma ya daga kan cewa sai ya zo duba ta, wai masoyiyarsa ba lafiya."
Da mamaki Abbi ke kallon Dada yana cewa.
"Soyayya suke yi ne?"
Murmushi Dada ta yi irin ta su ta manya, kafin ta ce.
"Idan Allah ya ba ta lafiya sai ku ji daga bakinta."
Don shi Abbi bai san da zancen ba, ya dai san Ammar ya taba zuwa gaishe su kar part ɗin su, wanda hakan ya ba su mamaki ganin abokin Hilal ne kuma shi Hilal bai taba zuwa gaishe su ba ballantana abokinsa ya zo, ashe soyayya suke da Zahrah.
Cikin sanyin murya Ummi ta ce.
"Ba na son alakar soyayyar Zajrah da yaron nan, saboda kun san irin zaman da muke yi da su a cikin gidan nan, tsabar aminta dake tsakanin Hilal da Ammar har ya sa iyayensu mata suka zama ƙawaye suna zumunci da juna. Wanda har ya kai ko ƙasar suka je a gidan su Ammar suke sauka. Ko kun mance rashin lafiya da Papa ya yi a ƙasar yana jinya. Lokacin da muka shirya gabaɗaya zuwa gidan su Ammar suka sauka a ƙasar London ɗin, amma ni da Abbi ya samar Mana hotel a ƙasar. Na tabbatar ba za su bari ɗan su ya auri Zahrah ba saboda sai mahaifiyar Hilal da Laila sun ɓata lamarin. Hakan ya saka na ba wa Zahrah shawara akan cewa ta fita harkar yaron kada sai ta yi zuri a cikin son sa sannan su yi mata yankan ƙauna ta zo ta shiga cikin wani hali."
"Kar ki damu in dai suna son juna zan yi wa Papa magana akan lamarin bayan mun ji ta bakin Zahrah, na san zai saka hukunci mai tsanani akan lamarin akan ita Laila da Maimuna, wato Mummy.
Shiru ta yi amna dai hankalin ta bai kwanta da al'amarin ba.
Daidai lokacin aka shigo ɗakin da sallama. Papa ne tare da abokinsa Alhaji Modibbo, mahaifin UmmI.
(Idan masu karatu ba ku manta ba dama na fada maku a baya cewa da Mahaifin Abbi da mahaifin Ummi abokan juna ne, lokacin da Abbi ya gana karatunsa ya dawo Nigeria Papa ya tura shi ya je ya ga Ummi idan ta yi masa su daidaita. Daga nan suka daidaita aka masu aure)
Alhaji Modibbo ya kalli gadon da jikar ta sa take kwance idanu a lumshe. Sai yake kallonta kamar Ummi lokacin da take da shekarunta.
"Barka da zuwa."
Kamilalliyar fuskarsa ya ɗauke daga kallon jikar ta sa ya maida ita zuwa ga kallon ƴar ta sa wacce kullum yake jin tausayinta a zuciyarsa fiye da sauran ƴaƴansa, saboda yanayin zaman da take yi da sauran jama'ar gidan.
"Lafiya lau ya jikin Amaryar ta wa."
Murmushi ta saki tana cewa
" jiki da sauki."
Daga nan su Sadik da Mahmud ma suka gaishe da kakan na su. Sadik ya ce .
"Modibbo ina tsohuwar matar taka ce ka zo kai kaɗai"
"Ina hanya ne kakanku ke sanar da ni, abin da ke faruwa sai na zo nan kawai."
Amma ina hanya na sanar da su na san suna nan zuwa ita da ƙanwar mahaifiyar ku Bilkisu sai ƴar da ƴarta Amal.
Nan suka gaisa da kowa ya zauna akan kujerar da aka ba shi ya zauna.
Bayan mintuna goma sai ga Didi mahaifiyar Ummin Zajrah tare de ƙanwar Ummin sai ƴar ƙanwar Ummin buduwarwa wacce ba za ta wuce sa'ar Zahrah ba. Kuma suna ɗiban kamanni da Zahrah sai dai ba ta kai kyawun Zahrah ba. Su biyu ne Allah ya mallaka wa Modibbo Daga A'isha wato Ummin Zahrah sai Bilkisu mahaifiyar Amal.
Akwai kuma Yayan Amal mai suna Doctor Khalil, wanda yake shi likita ne bai daɗe da dawowa ƙasar ba.
Suna nan zaune Zahrah ta fara motsawa tana a hankali. Numfashi da ƙarfi ta bude idanunta wanda ta ji sun mata nauyi.
Amal da mahaifiyarta Amal ɗin Hajiya Bilkisu suka karasa wajen gadon yayin da Hajiya Bilkisu ta ke cewa.
"Daughter sannu ko."
Gyaɗa mata kai kawai ta yi yayin da Amal ta rike hannayenta tana sakar mata murmushi, ita ma murmushin ƙarfin hali ta sakar mata.
Kowa a dakin hamdala ga Allah suka yi, ganin ta dawo normal cikin farin ciki suka karasa wajan ta suna tambayar ta jikinta .
Doctor ne ya shigo duka bashi wuri ya duba ta, tambayoyi ya yi mata ta ba shi amsa. Magani ya bata tare de bata shawarin yadda za ta kiyaye tashin ciwon ta.
Sallama aka rubuta masu, don ba ta jin komai numfashinta ma t daidaita.
Kiran wayar Dr Khalil ne ya shigo cikin wayar mahaifiyarsu wato Hajiya Bilkisu. Wayar na ajiye a saman gadon yayin da Hajiya Bilkisu da ke sa wa Zahrah hijabinta. Zahrah ta kalli wayar ta ga sunan da ya bayyana LOVELY SON.
Zahrah ta ce
" Aunty wayarki."
"Okay yayanki ne maybe ya karaso asibitin."
Ɗaukar wayar ta yi bayan ta yi sallama.
"Eh nan ne ka shigo."
Ba jimawa ya turo ƙodar ya shigo, sanye yake da Suit black sai farin glass dake Idanunsa. Ƙamshin turaren da Zahrah ta ji ne ya saka ta kalli kofar ita shi ma Idanunsa akan ta suna kallon juna.
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un"
Kalmar da ya firgita su kenan ya saka suka juya suna kallonsa.
*Maman Ihsan ce*✍️
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
*Albishir! Albishir!! Albishir!!!*
Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku.
Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇
Flasks
Cups
Dinnerset
Kitchenware
Pot
Jugs
Food processor
bedsheet lamps
Second hand gas
Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887
Page5️⃣3️⃣
Kalmar da ya firgita su kenan ya saka suka juya suna kallonsa.
"Haka yarinyar nan ta girma ban sani ba, ina wace ƙasar ne hakan ta faru?"
Modibbo ya zo kawo masa duka da sanda ya kauce yana cewa
"Subhanallah za'ayi kisan kai."
Kowa dake dakin sai da ya yi dariya.
"Yanzu dama saboda girma da ka ga Zahrah ta yi maka ne ya saka ka tayar mana da hankali kamar wanda ya ga wani abu mara kyau ko aka fadawa sakon mutuwa?"
Murmushi ya yi tare da ya.
"Kawai n ji ne don hankalin kowa ya dawo kaina ku ga abun da nake kallo."
Gaida su Papa da Dada ya har da ƴar tsokanarsu ko da bai saba da su ba yana jin labarinsu wajen kakanninsu su Modibbo da suka kasance abokan juna. Daga nan y gaida Abbi da Ummi, sannan ya gaisa da Yaa Mahmud da Yaa Sadik bayan sun yi musabaha. Yaa Mahmud ne ya girme Dr Khalil amma Dr Khalil ya girmi Sadik da shekara ɗaya.
Zahrah ta gaishe shi cikin sanyin muryarta ta ce.
"Ya Khalil ina wuni?"
Don ta gane shi a hoto saboda Amal na yawan posting ɗin photonsa duk da baya ƙasar.
Madadin ya amsa sai ya fara tsokanarta.
"Wai mara lafiyar