Showing 132001 words to 135000 words out of 154779 words
lura da kowa ba Jidderh kawai ka sani da ita ka damu."
Ta yi magana cike da takaicin share ta da ya yi.
"Afuwa Anisa na bari ne mu je gidan sai mu gaisa da kyau ko?"
Murmushi ta yi tare da cewa.
"Ya kake ya lokaci, sau tari ina tura maka message ba reply, kuma na ga kana amfani da social media."
Bai ce komai ba illa iyaka ya mayar da hankalinsa ga tuƙi, ya kalli Jidderh yana cewa .
"Kina lafiya?"
Ta jikin madubi ya kalli Dr Isma'il ya ce.
"Ya jikin na ta?"
"Da sauƙi."
"Alhamdulillah."
Ya faɗa yana kallon titin yayin da yake driving, abubuwa da yawa ne suke yawo a cikin ransa.
A bakin gate ɗin gidan ya yi horn maigadi ya leƙo, ganin uban gidansa ya saka ya wangale masa gate ɗin gidan ya shiga cikin gidan.
A parking space ya yi parking ɗin motar, fitowa suka yi yayin da shi da kansa ya bude wa Jidderh murfin motar ta fito cikin sanyin jikinta.
Maigadi ne ya taya su ɗaukar trolley bag ɗin da suka dawo da su.
Ciki suka shiga dukkansu suka zube a Falo, Jidderh ta zauna kusa da Anisa.
Kuku ne ya kawo masu abun sha, bisa umarnin uban gidansa.
Dr Isma'il ya mike yana cewa.
"Zan je gida na ga iyalina zan dawo mu yi magana, daga baya."
"Yanzu Doctor har yanzu tunanin na ta bai dawo daidai ba, gaskiya da sauki kam."
Cikin damuwa Asadullah ya ce.
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un, ta ina zan fara neman iyayen yarinyar nan ballantana har na damƙa ta a hannunsu."
"Kada ka damu in sha Allah za'a gane in da suke, bari na dawo mu yi magana."
Ya karasa maganar yana ficewa don zuwa gidansa ga iyalansa.
Jinjina kai Anisa ta yi jin ta samu amsar da take nema, wato sanin shin Asad na da alaƙa ta jini da Jidderh ne ko a'a. Hakan ya saka ta gane wato bai ma san su waye iyayenta ba."
Murmushi ta saki tare da ayyana abubuwa da yawa a zuciyarta.
"Za ku ci abinci ne ko sai kun yi wanka kun fito?"
"Sai mum yi wanka mun fito."
Cewar Anisa tana nufar ɗakin da aka sauke su ita da Jidderh.
Kallonta da mamaki ya yi kafin ya ce.
"Ita kuma fa me ya saka kika tafi kika bar ta a tsaye."
A fakaice ta harara Jidderh sannan ta ƙaƙalo murmushi wanda iya fatar bakinta ya tsaya ta ce.
"Oh sorry ƙanwata ba ki biyo ni ba."
Ta fada tana jan hannunta suka bar wajen zuwa cikin bedroom ɗin su.
Da ido ya bi su kafin ya haura upstairs zuwa ɗakinsa.
Suna shiga Jidderh ta kalli Anisa da ta murɗe mata hannu da karfi wanda sai da ta ji zafi ta kalle ta.
"A gidan uban wa ba ya samo ki da kika zo kika tare masa a gida, ga shi ya bi ya damu dake, duk in da kike idanunsa na kanki sai dai idan baya wajen, ta zan yi da ke ne, duk yadda zan yi sai na yi na fitar dake daga cikin gidan nan, idan ya tambaye ni zan ce ban san in da kike ba ina barci, sai na tabbatar na nisanta ki da gidan nan yadda ba za ki iya dawo wa ba kafin na dawo. Don na ga alamar kece katangar da za ki yi Mani shamaki da abun so na."
Jan hannunta ta yi da karfi suka shiga bedroom ɗin dake cikin ɗakin.
_Dada_
Shirya amaren gidan take yi babu kama hannun yaro, kasancewar sati ɗaya za su yi a gidan kafin su tare, wato bayan daura auren da sati ɗaya kenan za su tare. Dada ka cewa ta yi duk da ba lokaci za ta ɗan yi masu gyaran da ba zai cutar da su ba, wanda ko ba mu'almar aure suka yi a farkon auren ba to amaren ba za su shiga wani hali ba. Don gyaran amarya take yi masu Sai dai ba wanda zai basu matsala ba, bisa la'akari da yanayin yadda auren na su ya zo, ba na soyayya ba ne.
Duk da ba su don gyaran da take yi masu amma ba yadda suka iya, dole kowane safiya dai sun zo da yamma ma sai sun zo. Don idan ba su zo ba Dada da kanta take zuwa part ɗin kowa ta yi wa uwar yarinyar tas, dole yarjnya ta biyo ta.
Zahrah dai dama tana na nan part ɗin, kuma har yanzu jikin na ta bai warware ba, amma duk da haka Dada ba ta ƙyale ta ba cewa ta yi rashin son auren ta saka ki sakin jiki ballantana ta warware.
Kasancewar sun yi hutun school daman Islamiya kawai take zuwa.
Papa ya kira Daddy da Abba, da Abbi ya sanar da su ranar juma'a kowace ƴa za ta tare a gidan mijinta, don haka kowane uba ya yi wa ƴarsa kayan ɗaki a kai a jera mata a gidanta kafin ranar juma'a. Ya sanar da su cewa ya riga ya siye wa kowane yaro gida Hilal ne bai karba ba, don haka su je su siye kayan daki a kai a jera. Kafin ranar juma'a.
Ba yadda suka iya da to suka amsa masa kafin suka yi masa sallama.
Sannan ya nemi ganin angwaye don so yake ya mallaka wa kowa takardun gidan da ya bashi da makullin gidan.
Zahrah dai tana ɗan shan wahala wajen gyaran da Dada ke masu, sakamakon dukan da Hilal ya yi mata jikin na ta akwai raunin ciwon saboda belt ɗin ya ɗan fasa mata jiki, ga shi da ruwan lalle da wasu hadin take masu wanka, hakan ke saka tana jin zafi a wajen ciwon.
Kamar yadda Papa ya ce haka kuwa ya damƙa masu makullayen gidajen da takardun. Dukkansu huɗu, Mahmud, Mansur, Sadik da Faisal. Godiya suka yi masa, duk da cewar dukkanin su suna da gini da suka fara ba su mayar da hankali ne ba kawai ba su yi ba ganin ba saka auren nan kusa suka yi ba.
Haka suka je kowa ya nufi gidan da ka bashi bisa umarnin Papa, kowane gidansa Madaidaici ne, mai ɗauke da babban falo, da ɗakunan barci uku, kowane da toilet a cikin ɗakin, sai kitchen da dinning area.
Kasancewar sabbin gidaje me dukkansu ba wanda aka shiga, fenti ne kawai za su yi.
Duk da cewar ransu s jagule yake sakamakon auren dolen da Papa ya yi masa, amma ganin kyautar da ya yi masu sai suka ji kaso ashirin na haushin sa da suke ji ya ragu.
Zahrah da wayarta kwana biyu kenan tana kashe sai yau ta kunna ta, messages ta gani da yawa musamman na Ammar.
Duk ya damu akan rashin jin daga gare ta, kamar za ta kira shi sai ta fasa, ajiye wayar ta yi tana kuka.
Kamar yana jira sai ga kiransa ya shigo cikin wayarta. Ba suna da emoji ta yi served ɗin sunansa.
Har ya katse ba ta ɗaga ba, yayin da kuka sosai da tausayin rayuwar da za ta yi a gidan Hilal take yi.
Kasancewar yau sauran kwana huɗu tarewarsu, kuma ranar da za'a tare za su yi taron biki, hakan ya saka Papa ya ce ma kowace ta je ta samu mijinta a ɗakinsa su yi shawarar yadda za su tsara bikinsu ko akwai wani dinner da za su yi ko wani shagali dai.
Dan haka da kansa ya saka Dada ta tabbatar kowacce cikinsu ta tafi ta samu mijinta sun yi magana.
Hakan kuwa aka yi kowacce Dada ta tura ta ta je su yi shawara da mijinta.
_Mansur_
Yana zaune a falonsa yana kallon wani program da gidan TV da yake aiki suka saka. Maryam ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Ɗagowa ya yi ya kalle ta ba tare da ya amsa mata ba. Kallon banza ya yi mata kafin ya ce.
"Lafiya?"
Ganin kallon da yake yi mata da yanayin yadda ya yi magana ya ɓata mata rai, duk da cewar ita ba ta da masifa amma ba ta daukar raini da wulaƙanci, kuma ta san Mansur ɗan wulakanci ne da rainin hankali. Shi ya sa baya jituwa da mutane da yawa.
Ganin ta masa shiru ya ce.
"Kin matsu ki tare ne shi ya saka kika kawo Mani kanki da kanki ko ya aka yi, idan ma kina tunanin zan kalle ki a matsayin macen aurena kin yi kuskure. Don wallahi sai kin yi nadamar wannan ..."
"Ya ishe ni haka nan Yaa Mansur, ka ɗauka sonka nake yi ne ko kuma da son raina na zo ɗakinka, yadda kake gani an yi maka dole ni ma haka aka yi mani, ba sonka nake yi ba ballantana ka wulakanta ni."
"Ku je ku fadawa Papa bakya so na."
"Kai da kake namiji ka je ka same shi mana."
Tsawa ya daka mata tare da cewa
"Fita a ɗakin nan kafin na yi maki shegen duka."
Da gudu ta fita tana gunguni.
_Mahmud_
Dawowarsa kenan daga aiki a gajiye yake, yana shirin rage kayan jikinsa kenan sai aka turo ƙofar aka shigo cikin ɗakin . Juyawa ya yi yana kallon ƙofar sai ya ga Nabeela ce ta shigo cikin ɗakin.
Harararsa take yi a wulakanci, shi ko kallonta kawai yake yi cikin da mamakin abun da ya kawo ta.
"Ba alkhairi ne ya kawo ni ɗakinka ba, Hakazalika babu abin alkhairi da zan yi tarayya da kai akansa. Ina mai maka albishir da cewa daga ranar da aka kai ni gidanka daga ranar ka yi bankwana da farin ciki. Sai ka ɗanɗani kuncin rayuwa wallahi sai ka yi nadamar kasance wa ta a matsayin matarka."
Tana gama fadar haka ta fice daga ɗakin, karo ta yi da Ummi a falo, ɗauke kai ta yi tare da sakin tsuki ta fice daga ɗakin, don dama Aunty Laila ta zugo ta akan ta yi masu rashin mutunci daga shi har uwarsa.
Cikin sanyin jiki Ummi ta zauna kan kujera tana tausaya wa ɗanta Mahmud. Domin ta san shi da sanyin hali da wuya ya yi magana akan abu. Ballantana wannan auren ta san sai Mahmud ya ji jiki a wajen Nabeela. Da a ce ƙaninsa Sadik ne to da za su yi daidai da juna. Don shi m kansa ba kanwar lasa ba ne, don ma Ummi da Abbi na taka masa burki, amma karya ne a taka shi ko a taka iyauensa ya ƙyale mutum ko waye kuwa.
_Faisal_
Yana zaune a falonsa yana lissafin kuɗi, kasancewar sa ɗan kasuwa. Kausar ta shigo ɗakin ba sallama. Kallonta ya yi sannan ya ɗauke kansa lissafi da ya cigaba da yi. Harararsa take yi ta ƙasan idanu, shi ko kallon banza ma ba ta ishe shi ba.
Tsawon mintinan ashirin ta gaji ta yi ficewarta, don ita dama Aunty Laila ba ta yi mata hudubar ta yi wa Faisal rashin kunya ba, saboda shi ɗan Mummy ne, kuma akwai mutunci tsakaninsu. Amma Mahmud kasancewar ɗan Ummj ne ya saka Aunty Laila ta zuga Nabeela ta yi masu rashin mutunci.
_Sadik_
Yana zaune saman kujerar yana nazarin wani Shari'a da za su yi a kotu. Wasu takardu yaje dubawa wanda yake karanta muhimman abinda wanda ke kara ya sanar masa .
Da sallama Nadeeya ta shigo ɗakin. Amsa mata Sallamar ya yi sannan ya ɗago suka hada Idanu. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai ya cigaba da abinda yake yi.
Ƙarasowa ta yi idanunta akansa ta ce.
"Ina wuni Yaa Sadik."
Ba tare da ya kalle ta b y ce.
"Lafiya lau ya kike?"
Ba ta san lokacin da Murmushi ya suɓuce mata ba
, don ba ta yi tunanin zai kula ta ba, musamman da iyayen su ba jituwa suke yi ba. Duk da ta san shi iyayensa ba sa da matsala kowa ta sani ba ruwan Abbi haka Ummi ma, haka Mahmud da Zahrah. Dama shi Sadik ɗin ne ya fita daban kamar ba su suka haife shi ba.
'Gaskiya ba zan yi wa kaina sagegeduwa ba, tabbas Yaa Sadik haɗaɗɗen namiji ne, duk da cewar na san zan fuskanci ƙalubale daga wajen Abba da Umma da kuma Yaa Mansur. Amma ba zan yi sake na rasa wannan kyakkyawan saurayin a matsayin mijina. Walau dole na rungumi mijina in dai har zai so ni.'
Haka ta dinga magana a zuciyarta.
Shagala ta yi da kallonsa, ba ta san yana da kyau ba sai yau, ga shi yana matukar Kama da Zahra. Ji ya yi a jikinsa ana kallonsa don haka ya ɗago manyan idanunsa ya kalle ta, da sauri ta kau da kai cikin jin kunya.
Shi kansa bai yi zaton za ta kalle shi da idanun rahama ba, sanida a gaban idanunta kwanakin baya ya yi wa Abba mahaifinta rashin kunya har don ya nemi zargin Abinsa, kuma sun sha dambe da Yayanta Mansura ba sa jituwa gara kowa da shi a wajen Mansur.
"Lafiya dai ko?"
Sunkuyar da kai ta yi tana addu'a Allah ya sa kada ya kore ta. Ga mamakin ta sau ta ga ya nuna mata gefensa kusa da shi ya ce.
"Ki zauna."
Kamar jira take ta zauna.
"Make ke tafe da ke?."
"Am fama Papa da Dada ne suka ce ki za mu shirya dinner party."
"Ba na bukata."
"Am to ko wani reception ba za mu yi ba?"
"To ba auren soyayya ba ne to me za mu je yi wa wani reception ba shiri ba komai."
Da sauri ta kalle shi tare da cewa.
"Kenan kai ba ka so na?"
"Ke kina so na ne?"
Murmushi ta yi tare da cewa.
Rufe fuskarta da tarin hannunta.
Murmushi shi ma ya yi tare da cewa.
"Yanzu ina tsaka da aiki gobe za mu yi magana kin ji?"
Tashi ta yi tare da cewa.
"Sai da safe."
"Okay Allah ya bamu alkhairi."
Har ta bude kofar za ta fita ta juyo ta kalle shi, ta ga ita yake kallo, da sauri ta fice, murmushi ya yi ya cigaba da abin da yake yi.
_Zahrah_
Tana kwance kan gado sanye da wandon Pallazo purple colour top fara, gashin kanta tufke da ribbon ya ɗauka har gadon bayanta.
Dada ke ta fama da ita akan ta tashi ta je part ɗin Hilal su yi magana, ƙi ta yi sai da Papa ya shigo sannan ta saka dogon Hijabinta fari ta nufi part ɗin sa. A hankali take tafiya tana taka step ɗin saboda ƙafarsa na yi mata ciwo bai gama warke wa ba don ba karamin duka ta sha ba
Ta jima a kofar kafin ta sami ƙarin guiwar yin knocking.
Jin shiru ya saka ta shiga falon, ba kowa dai sanyin A.C ke tashi da ƙamshin air freshener.
Kamar za ta koma dai ta tuna dole sai Papa ya tambaye ta ya suka yi, don haka ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta shiga bedroom ɗin sa.
Knocking ta yi daidai lokacin da ya fito daga wanka ɗaure da towel a ƙugunsa, izinin shigowa ya bayar a tunaninsa Faisal ne .
Tura ƙofar ta yi ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ƙaramin towel ne a hannunsa yana tsane ruwan kansa towel ɗin fari kamar yadda na ƙugunsa ma fari .
Gabanta ya faɗi ganinsa da ta yi ba riga sai towel dake ɗauke a ƙugunsa. Ya zuba mata rikitattun idanunsa masu firgitata. Da sauri ta juya za ta fice ta ji muryarsa ya ce .
"Wait."
*Ga mai bukatar karanta complete book 2 zai tura kudinsa Naira ɗari biyar ₦500. Za ku tura kudin ku ta wannan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank. Sai a tura shaidar ta wannan lambar 09065327995*
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE*
Page6️⃣4️⃣
Gabanta ne ya faɗi ganinsa da ta yi ba riga sai towel dake ɗaure a ƙugunsa. Ya zuba mata rikitattun idanunsa masu firgita ta. Da sauri ta juya za ta fice ta ji muryarsa ya ce.
"Wait."
Tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba, bayanta ya zuba wa idanu kafin ya ɗauke kansa daga kallonta.
A hankali ya tako zuwa gabanta fuskarsa a murtuƙe, gabanta ya tsaya yana kallon ta kanta a ƙasa, dama ta rintse Idanunta jin ya kira ta. Ƙamshin da ta ji ne ya saka ta bude idanunta. Ta sauke shi akan faffaɗan ƙirjinsa da gashi suka kwanta luf a ƙirjin na sa.
Da sauri ta rufe idanunta da rafin hannunta. Mamaki ne ya kama shi sau biyu kenan tana ganinsa ba kaya sai ta firgita, sai dai abun da ke ɗore masa kai shi ne. Yadda su Aunty Laila da Mummy da Umma suke cewa ƴar iska ce bin maza take yi, babban dalilinsa na yarda da cewa tana bin maza shi ne ranar da ya ganta kwance a falon tana murƙususu kayanta ya ɓaci da jini, Aunty Laila ta ce ciki ne ta zubar. Ga shi da ya ɗauke ta ya kai ta asibitin kuma Doctor ya tabbatar masa da cewa ciki ta zubar. A lokacin hankalinsa ya tashi sosai wanda har ya ba yi mata duka don ta fada masa wanda ya mata cikin ta ƙi faɗa.
To macen da ta san maza me zai saka idan ta kalle shi haka take firgita, ko dai wani sabon munafurci ne.
Ji ya yi ransa ya ƙara ɓaci kamar yanzu ne lokacin da abun ya faru.
'"Open your eyes."
A hankali ta buɗe idanunsa kanta a ƙasa.
Haka kawai ransa yake sosuwa idan ya tuna da abinda ake cewa tana aikatawa, ko da ya ƙaryata ba zai ƙaryata Doctor ɗin ba, tunda aikinsa ne, ya kasa magana zafi kawai yake ji zuciyarsa na masa tare da jin haushin ta.
Gajeren tsuki ya saki kafin ya ce.
"Me kika zo yi a ɗakin nan?"
Shiru ta yi masa kuma ba ta bude idanunta ta ba.
"Okay na gane, wato kin kasa haƙura zuwa ranar da za'a kai ki ga mijinki shi ne kika ɗebo ƙafa kika kawo Mani kanki da kanki ko, saboda tsabar jaraba ko, to ba na buƙatar jikin na ki sai ki juya ki koma in da kika fito.
Tsabar ɓacin rai da kalaman sa durkushe wa ta yi a wajen tana kuka, zuciyata na mata suya, wai me ya saka mutanen gidan nan suke yi mata kallon ƴar iska mai bin maza ne, yanzu har ta kai wanda aka aura mata yana yi mata wannan zargin.
Maganarsa sun soke ta amma dai ta dake ta miƙe ta kalle shi ta kau da kai.
"Zato zunubi ne ko da