Showing 90001 words to 93000 words out of 154779 words

Chapter 31 - GABAR CIKIN GIDA Complete Hausa Novels Book.txt

NIl   

26 Feb 2026

6290

akan belt ɗin wandonsa. Ganin haka ya saka ta kalli fuskarsa da sauri. Fuskarsa ɗaure tamau Babu sassauci ko kaɗan.

Hannunsa ya dora a saman lips ɗin sa alamar ta yi shiru.

Haɗiye kukan ta yi sai ajiyar zuciya take saukewa, ga numfashinta ya fara fita sama-sama alamar ciwonta zai iya tashi.

Suna cikin wannan halin ne sai su Papa suka fito suna ta yaba kyawun gidan tare da masa fatan alkahiri da samun mace tagari.


_Jidderh_

Ko da ta fito daga bathroom ɗaure da towel kamar yadda ya nuna mata.

Ya shigo ya ajiye mata wasu kayan. Ya ganta tsaye .

"Akwai matsala."

Ya faɗa yana ƙarasowa wajen.

"To idan mutum ma ya yi ya rasa tunaninsa sai ya rasa komai a ƙwaƙwalwa? Har wanka da shirya kanta ma ba za ta san yadda za ta yi ba.?"

Ya ƙarasa maganar tamkar wanda zai yi kuka.ledar ya duba ya ga har da pant. Ɗaukar daya ya yi ya nuna mata yadda za ta yi sannan ya ɗauki doguwar rigar ya karasa in da take ɗure da towel, sai da Allah ya sa towel ɗin mai girma ne ya sauka mata. Bayan ya zira mata rigar ne ya nuna mata yadda za ta sake pant ya fice yana jinjina lamarin a zuciyarsa cikin damuwa.

Yana fita ya tarar da Dr Isma'il ya karaso. Nan suka gaida ya tamabaye shi jiki ya amsa da Alhamdulillah.

Bayanin lamarin Jidderh ya bashi da yadda take . Shiru Dr Isma'il ya yi kafin ya ce.

"Maganar gaskiya dole sai an kai ta asibiti."

Jinjina kai Asad ya yi tare da cewa.

"Sulaiman sai dai ku tafi tare da ita."

"Okay Sir "

Sulaiman ya faɗa yana miƙewa.

Asad ya koma dakin ta bar su nan tsaye.ba jimawa suka fito tana sanye da Hijabi ya masu jagora suka fita.

Sai da ya ga wucewarsu sannan ya dawo ciki zuciyarsa fal tausayin yarinyar.


_Maryam_

Suna shiga dakin Hilal kamar yadda ya basu umarnin su je su gyara masa part ɗin sa.

Suna shiga falon nasa wani daddaɗen ƙamshi ya ziyarci hancin na su. Nabeela ta ce.

"Yanzu wata rana fa nan ne falona ni da Yaa Hilal har na hango ni ina zuba masa shagwaɓa yana ta lallaɓani muna zaune s wancan kujerar."

Ta yi maganar tana nuna kujerar mai zaman mutum uku dake falon. Gabadaya suka saka mata dariya wanda hakan ya saka Nabeela ƙuluwa da haushi.

"Kin san Allah idan ma kina mafarkin cewa ko kin auri Yaya Hilal za ki masa shagwaɓa ta ɗauka kin yi kuskure. Domin shi bai san rarrashi ba ballantana lallaɓa mutum Abu guda ya sani shi ne hukunci a duk lokacin da kika masa ba daidai ba."

Maryam ta yi maganar tana dariya.

Kausar ta taɓe baki tana cewa.

"Ni zan yi daidai da shi don na iya zama da shi kuma zan koya na jure."

Nadeeya dai zama ta yi tana cewa

"Kanku ake ji ƴan wahala kawai."

Hotonsa dake manne a bango ne Kausar ta kalla.

Sanye take da kakinsa ya yi kyau sosai.

Shafa hoton ta yi tana murmushi.

Madadin su yi aikin da ya saka su sai suka zauna suka ɓige da yin fira.

Kusan mintuna talatin suna a haka suna fira kafin Maryam ta ce.

"Mu tashi fa kada ya zo ya same mu ba mu yi masa aikin da ya saka mu ba."

Nan suka tashi in da suka yanke shawarar mutane biyu su shiga su gyara bedroom su wanke toilet, sai mutane biyu su zauna su gyara falo.

Da wannan shawarar suka yi amfani. Nabeela da Nadiya suka shiga don gyara masa bedroom. Maryam da Kausar suka tsaya gyara masa Falo.


Nan ma suna shiga bedroom ɗin Nabeela ta zube a gadon tana shaƙar daddaɗen ƙamshisa.

Nadiya ta ta shiga don wanke toilet. Tana shiga ta ga toilet ɗin tsaf .

"Ni ban ga abinda za'a wanke a anan ba komai tas yake."

Nabeela ta taso ta gani ta ji kamshi ne ma a ciki. Don haka ta ce.

"Watsa ruwa kawai ki fito."

Haka kuwa aka yi tana watsa ruwa ta fito.

Suka dawo suna dube-dube a wajen madubi.

"Kalli duk waɗan nan maiyuka da turaruka duk na mutum ɗaya ne, sai ka ce mace, duk nan fa mayukan jiki ne da ba gashi, sai turaren jiki da na jiki. Komai na sa disigner ne.

Nadiya ta faɗa tana dudduba su yayin da Nabeela ma ke dubawa tana cewa.

"Bari na fesa turaren masoyi."

"Kada ki fesa kin san dai tutarensa ba gamagarin turere yake amfani da shi ba, sai an gane ki idan kika fita ko shi idan ya shigo zai gane ne kin san halinsa ."

Jin haka ya saka ta ajiye tana cewa su gyara gadon.

Duk da ba yamutsewa ya yi ba zanin gadon ma a gyare yake. Sai suka yaye bargon da zanin gadon suka hau kici-kicin gyarawa.

Amma sai suka kasa shimfida zanin gadon da kyau, sun yi iya iyawarsu don ganin sun gyara gadon sun kasa.

Sai haki suke yi duk sun gaji amma sun kasa shimfida zanin gado.

Cikin ƙosawa Nabeela ta ce.

"Wallahi Nadiya na gaji, ke ma kin san ba iya gyara ɗaki muka yi ba saboda masu aiki ke gyara muna ɗaki ta ya ya za mu iya wannan aikin tun da ba mu taba yi ba."

"Gaskiya ne to yanzu ya za mu yi yanzu?"

"Mu kira su Kasar ko za su iya gyaran."

Fita suka yi nan suka same su a falo suna kuciniya su su ma ba iya aikin suka iya yi ba.

Maryam ta jika towel da ruwa ta zuba omo sai kuma yake yi haka take ta laptawa Tv da duk wani abu dake wajen. Da suka abinda ya shafi glass dake wajen.

Kausar kuwa ita ma ta sai mofin take tana goge tiles ɗin sai kumfa yake yi sosai ta zuba detergent.

Suna cikin wannan halin suka zo suka same su, nan suka ce sun gama na su suka ɗunguma bedroom ɗin .

Nan ma suka hadu su hudu suna kokarin gyara wajen amma sun kasa.

Haka suka lulluɓa zanin gadon suka ɗora bargo akai.

Irin mopping stick 🏒 suka ɗauko nan ma suka jiƙa masa ɗakin suka fice.

Maryam ce ta ce

"Kun san ba iya aiki muka yi ba tunda masu aiki ke gyara mana ɗaki ba za mu kira su nan su shigo su gyara masa ba?"

"Ke ma kin san baya yarda mai aiki ta shigo masa part ɗin sa. Ko girkinsu kina ganin bai cika ci ba sai dai ya sha tea. Ko kuma ya tafi part ɗin Dada saboda ba ƴar aiki ke mata girki ba."

"Wai ba Yaa Faisal ke gyara masa ɗaki ba, me ya saka yau bai yi masa ba?"

"Yau da wuri ya fita kasuwa ."

Maryam ta faɗa suka janyo masa kofar suka sauko Downstairs. Ba kowa don haka Kausar da Maryam suka nufi part ɗin su. Yayin da kuma Maryam da Nadiya kowace ta nufi part ɗin mahaifiyarta.


_Sulaiman_

Yana nan zaune a asibitin yayin da Likitoci ke kan Jidderh don gano matsalar dake damunta.

Yana nan zaune sai ga wayar Mom ya shigo cikin wayarsa. Ɗauka ya yi bayan sun gaisa daga can ɓangaren Mom ta ce.

"Sulaiman ina ka shiga ne daga maganar CCTV Camera aka neme ka aka rasa?"

"Mom na ɗan fit ne yanzu zan dawo."

Kashe wayar ya yi yana fita da sauri don sanar da uban gidansa.

Motarsa ya shiga ya yi mata key ya bar wajen .

A falo ya samu Asad wanda ganin shigowarsa ya ce.

"Ya aka yi ne ina take?"

"Ban sanar da kai ba ne wallahi Mom ta kira ni akan bincike da za mu yi na gobarar da ya tashi to zan bincik..."

"Kada ka yi wannan bincike ka ɓatar da komai da y faru."

Kallonsa Sulaiman yake cikin mamakinsa. Jinjina masa kai Asad ya yi alamar tabbatar wa.

Jinjina kai ya yi cikin girmamawa ya fice daha gidan.


_Zahrah_

Tana nan tsaye a wajen da take sai haɗiyar kuka take yi , yayin da Hilal ke aika mata wani kallo. Har lokacin numfashinta baya fita daidai.

Fita suka yi gabaɗaya don Zahra ta ce ba za ta shiga ba.

A motar ne Dada ke cewa Zahrah za su biya gidan abokin Papa ɗansu ya rasu. Ko za ki je mu mu tafi tare?"

Girgiza kai ta yi alamar a'a don tana don tana ji. Yadda numfashinta ke fita ba ta don Dada ta sani.


Sai da Hilal ya fara ajiye Papa da Dada gidan rasuwa Sannan suka fita.

Zabarah na bayan motar y dskata bai tayar da motar ba ya yi shiru.

"Waye Direban ki da za ki zauna Mani a bayan mota?"

Fitowa ta yi ta zo ta shiga gaban motar wajen me zaman banza. Gajeren tsuki ya ja sannan ya ja motar suka bar wajen.

Har suka isa gidan ba wanda ya yi magana sai sanyin AC da ƙamshin dake tashi a motar.

Bayan sun isa gidan ne ta fito da sauri don neman magani.

Tana zauna kofar falo ta tura kofar tare da sallama. Mummy ce da Umma sai Aunty Laila.

Ba su amsa ba kuma ba ta saka ran za su amsa ba . Sai da ta zo daidai in da suke har ta gifta Aunty Laila ta daka mata tsawa.

"Ke!"

Tsayawa ta yi ta juyo tafe da zuwa in da suke.

Wani kallo Ne Mummy ta yi mata tana cewa.

"Ya na ji ƙamshin turaren Hilal a jikinki?"

Gabanta ya fadi tuna lokacin da ta tuna tsorata da ta yi ta rungume shi .

"Ba komai."

Ta fada da daƙyar.

"Iskancin da kike yi da maza a waje yau ya zo kan Ɗana?"

Umma ce ta ce.

"Wannan mkirar yarinyar ba za ta fada ba, ya aka yi turaren rigarsa ya shafi rigarki?"

Daidai lokacin ya shigo fuksar nan kamar kullun a murtuƙe.

Kallonsa suka yi Aunty Laila ta taso da sauri tana duba gabar rigarsa in da shape ɗin laɓɓan Zahrah ya fito a rigarsa sakamakon fadawa jikinsa da ta yi da karfi lokacin da ya janyo ta . Maiƙon ne ya fito a a rigarsa kamar an zana.

Zahrah tuni ta nufi part ɗin Umminta. Wani kallo Mummy ke yi masa.

Aunty Laila ta ce

"Son daga ina kake yanzu ?"

"Sabon gidana da na kammala."

Wani kallo suka masa kafin ta ce .

"Waccen yarinyar Zaharah fa ina ka haɗu da ita?"

"Tare muke tafi "

Cikin yanayin rashin damuwa da yanayin da suke kallonsa ya nufi upstairs Yana cewa .

"Bari na yi wanka."

Daskarewa suka yi suna kallonsa.Yana shiga falonsa ya ɗauke idanunsa akan TV Wanda ya yi jirwayen fari-fari saboda kumafa. Haka duk abinda suka goge suka yi Centre table ma haka duk jirwayen. Ga tiles ma dake me duhu ne duk ya yi ya jirwayen wani wajen kuma ga ruwa nan kwance.

Ransa ne ya yi mugun ɓaci ya taka zuwa bedroom. Ya ga sanin gadon an ɗan yafa ne har da bargon ga pillow duk a karkace. Toilet ya shiga nan ma ya sake ganin wani ɓacin ran.Turarrukansa ma da alama sun yi masa wasa da su

Zuciyarsa har tafarfasa take yi ya nufi downstairs.

Daidai lokacin da Faisal ke dawowa kallo ɗaya ya yi wa Yayan nasa a zuciyarsa ya ce .

'Tau fa waye ya taɓo wannan birkitaccen?'

"Ka kira mani yaran nan dukkansu!."

Ya faɗa yana zuba idanunsa da suka canza launi zuwa ja.

"Yaa Hilal wasu yaran?"

Hararar da ya jefa masa ne ya saka ya nufi part ɗin ƴan matan gidan don kiransu, a zuciyarsa kuma yana tausaya masu.



*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z



*GABAR CIKIN GIDA*


*NA*

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)






*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect

*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*



*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*



Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.


Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.



Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩


1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more



Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.


*YAR GIDAN TAFIDA*


Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.



*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.

Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯

Page4️⃣5️⃣


Hararar da ya jefa masa ne ya nufi part ɗin ƴan matan gidan don kiransu, a zuciyarsa kuma ya tausaya masu.


_Sulaiman_

Ko da ya koma Asadullah mansion ba kowa a wajen da abun ya faru, da alama kowa ya koma ɓangarensa.

Kai tsaye ɓangaren su Mom ya nufa.

Tana zaune a falo ita da Fauziyya. Wacce ke kallon Mom cikin damuwa take cewa.

"Yanzu Mom waye zai aikata irin wannan aika-aikar?"

"Sulaiman nake jira ya zo mu tabbatar da ko waye."

Knocking aka yi suka bayar da izinin shigowa, Sulaiman ne ya gaida Mom. Ta amsa tana bashi izinin shiga part ɗin Asadullah ya bincika.

Kasancewar Sulaiman amintaccen bodyguard ɗin Asadullah ne, ko lokacin da Asadullah kenan yana shiga part ɗin kai tsaye har cikin bedroom ɗinsa.

Bayan ya shiga don tabbatar da wanda ya haddasa wannan gobarar ne ya janyo computer a gabansa bayan ya zauna kan kujerar dake gaban computer ɗin.

Binciken abinda ya faru juya ya soma yi har zuwa yau .

Ya girgiza matuƙa lokacin da ya ga Jidder ta nufi wata hanyar da abu a cikin hijabinta sai waige-waige take yi alamar ba ta da gaskiya.

Sai dai bayan ta nufi bayan part ɗin ba ya iya hango ta, Don ba'a dasa cctv Camera ta bayan ba

Sai dai ɓacewarta ba jimawa ya ga ta bar wajen a guje yayin da wuta da hayaƙi ke tashi daga can baya.

Bayan Jama'a sun taru ga motar kashe gobara ta ƙaraso ne ta koma wancan hanyar a guje.

Sai ta dawo tare da wani ya rufe rabin fuskarsa da hula sannan ga Facemask. Yana biye da ita.

Duk da ba ganin fuskarsa ya yi ba amma ya tafiyarsa ya kalla da kyau ya gane cewa ubangidansa ne.

Abin da ya girgiza shi kenan yana mamakin abun da idanunsa suka gani.

Danne-danne yake yi yana sarrafa computer cikin ƙwarewa.

Sallamar Mom ce ya ji ta shigo bayan ya amsa.

"Sulaiman akwai abinda ka gani ka ga ko waye ya haddasa mana wannan ta'asar ko? Don a gakskiya ba za mu taɓa barin ko waye ba, duk da ba wani daga waje ba ne don akwai matakan tsaro a nan ba wanda zai shigo daga waje dole na ciki ne."

"Mom a gaskiya tsawon kwanaki bakwai kenan da CCTV Camera ɗin nan ta daina aiki.

"Abinda ya faru daga kwanaki bakwai zuwa yau duk ba sa cikin nan."

Ya faɗa yana zuba mata idanu.

"To ta ya hakan za ta faru?"

Nan ya yi mata danne-danne yana nuna mata yana tabbatar mata da ba komai.

Shiru ta yi kafin ta ce.

"To ba hanyar da za'a gane ko waye?"

"Gakskiya yanzu babu komai a nan, amma ina da hanyoyi da yawa da zan iya gane abinda ta faru ki bani kwana biyu."

Jinjina masa kai ta yi cikin sanyin jiki tana cewa.

"Allah ya ya sa."

Da amin ya amsa sannan ya mata sallama ya fice.

Zuciyarsa cike da tarin tambayoyi, me hakan ke nufi, dama kenan ta tabbata Asad na cikin gidan nan kamar yadda ya dage bai ga fitarsa daga cikin gidan ba a gidan ba har Uncle Adam na ganin laifinsa.

Tsawon wannan lokaci ne hakan ke nufi kuma ya aka yi Jidderh ta san da zaman Asadullah a wajen. Sannan me ya sa Asad ya hana a sanar wa da Mom da Dad?

Wadannan tarin tambayoyi sune fal a zuciyarsa ba shi da mai amsa masa waɗan nan tambayoyi dole sai shi uban gidansa.


_Zahrah_

Tana shiga part ɗin Umminsu ta tarar ba kowa a falon, bedroom ɗin ta ta nufa cikin matsanancin sauri don ta ga numfashinta ya fara fita sama-sama.

Side drawer ta buɗe. Inhelar ta ɗauko ta yi saurin kai shi bakinta har hannunta na rawa.

Bayan ta shaƙa ne ta fara jin numfashinta ya na daidaita a hankali.

Kwanciya ta yi tare da lumshe. Daidai lokacin Ummi ta shigo tare da Sallama.

Ganin yamma ce kuma Zahrah in dai lafiya take ba ta kwanciya ta yi barci da yamma. Sanin haka ya saka ta ƙarasa gaban gadon da sauri.

"Auta me ya same ki ne, ko ciwon ki ne ya tashi?"

Gyaɗa mata kai kawai ta yi alamar eh, kafin ta sake lumshe Idanunta.

Mayafin abayar dake kanta ya zame Ummi ta shafa gashin kanta tana mata sannu. Ya kamata a ce duk in da za ki je kuna tare da Inhelar kullum sai na fada maki."

Ganin kamar Ummin ta shiga damuwa ya saka ta yi kokarin kawar da yanayin da take ciki, mumrmushi ta sakarwa Ummin sannan ta tashi tana cewa.

"Bari na tashi Annabi ya hane mu da barcin yamma."

Ta fada tana murmushi yayin da Ummin ma murmushin take sakar mata cikin so da ƙauna hadi da tausayin ƴarta.



_Faisal_

Ko da ya shiga part ɗin ƴan matan gidan a nan ya same su a falonsu. Duk da kasancewar ba su cika kwana a part ɗin ba sun fi kwana part ɗin iyayensu. Amma idan ba dare ba ne nan suka zauna su yi fira.

Sallama ya masu suka amsa suna masa sannu da dawowa har da tambayarsa tsarabar me ya kawo masu yau.

Mumrmushi ya yi sannan ya ce

"Tsarabarku na wajen Yaa Hilal."

Gabansu ne ya faɗi suka kalli juna. A tare suka hada baki wajen cewa.

"Ya dawo ne?"

Kai ya jinjina masu sannan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login