Showing 24001 words to 27000 words out of 144591 words

Chapter 9 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2326

cewa lafafen cikinta take tsoron ya taso
Ya yarda cewa rakaduwa take gudu
Ya yarda cewa kofar biyowarsu take gudun ta karu
Ya yarda cewar bata son damuwa na kukan jariri
Ya yarda cewar ba zata so tara ya'yan da zasu ringa bi ta gabanta ana cewa ita NAJEEBA itace ta kawo su duniya ba!, lalle zai nuna mata bata isa ba, tabas koda rashin ta a kusa da shi da gangar jikinsa zai ilatashi ne sai ya hukunta ta, ta yadda zata gane cewar rashin ta ba tsiyar da zai haifar masa!, idan ta nemi sulhu kuwa suka samu sulhu zai yi zama da ita na mamaki, domin haihuwar nan da take gudu sai ta zo tana zuba masa su du shekara, ...........

A lokacin da Muhammad ya shigo fuskarsa dauke da rawani ya karaso inda mahaifinsa ke tsaye rike da sandar sarautarsa ya zubawa waje daya ido, har ya tsaya ya dan dago fuskarsa yana kallonsa, a hankali ya furta" Abiey"

Dubansa ya sado kan fuskar yaron, irin kallon da Muhammad ke yi masa sai da ya ji wani wani irin har cikin zuciyarsa

A hankali ya dauke dubansa saman lebensa ya furta" Yau rawani ka yi asarki???"

Muhammad yayi murmushin da kumatunsa suka lotsa, hakan ya sa mahaifinsa lumshe idannuwansa yana ayyana ' ire irensa nawa take takewa kar su zo?, dole ka jure, dole ka jajirce SHAHEED!"

Juyawa yayi ya nufi dakinsa a hankali ya furta" Yau bana fita fada "

Daga haka ya shige baban dakinsa ya shiga warware nadin rawaninsa da yake jin yana neman hadasa masa jin zafi sosai da sosai din nan

Da ido Muhammad ya raka mahaifin nasa kafin ya juya a hankali ya koma baban falo ya dana NUMBAR dakin karatu

Malami ne ya daga bayan ya zube kasa ya fara sauke gaisuwa da girmamawa

Da sauri Muhammad ya tare shi Wan ya tabbata ya zata mahaifinsa ne ya furta" Barka da safiya kaka , Nine Muhammad"

Malami yayi murmushi ya furta" Ja gaba baban manya, mai baban sunna mai kafa tarihi, ina fata kana cikin aminci"

Muhammad yayi yar dariya, domin sosai jinninsu ya hadu da na Malami, yakan zaunar da su ya ringa basu tarihin damagaran harma da wasu garuruwan Nijar, yakan sanar musu su waye kakaninsu, yana nuna musu girman sarauta da hatsarin dake tare da ita, yana sauraron tambayoyinsu na yarinta da shirme irin na yaro harma ya taya su dariya irin ta yara, yana Wora musu karatun islamiyya idan ba ranar da malamin islamiyarsu zai zo bane, sosai suke zama da shi, haka kuma a zaman da suke yi da shi ne idan ya fuskanci wani abin da yake da bukatar gyara ko ya ji wani abin da yake da bukatar bincike a kan tsaron lafiyarsu yake mikewa ya kai gaban mahaifinsu wanda yake matukar taka tsantsan da lamarinsu, domin ana kai yan uwansu yan matan wani waje hutu banda su, su sai dai su yi hutunsu a nan wajen Anmy..............................

A tausashe Muhammad da girmamawa ya ce" Kaka malami, dan in sanar maka ne yau Abiey ba zai fito da wuri ba "

Malami yayi dan tsai, a nutse ya ce" Ai kuwa takarda bata iso min ba asarki"

Muhammad ya ce" Kafin ta iso makan ne na sanar maka dan kar ka yi ta jiran isowarta, na ga sai sun ga 12 ta yi bai fita bane suke sanar maka"

Malami ya ce" Ka kyauta, ama gaba ka bari a sanar ka ji elhajina?"

Muhammad ya gyada kai sannan ya ajiye shima ya shiga cuje nadinsa domin gaba ta kai shi shi dama yau ba son fitar yake yi ba, yana son yin karatu ne an kusa komawa makaranta.


Malami ya jima zaune yana tunanin mafita, domin jira yake yi idan dan masani ya fito ya saka hannu a takardar kirawo likitocin nan a ba Sarkin dogarai da Sarkin bulala ne, sai ga bayanin Muhammad ya same shi, idan kuwa mai martaba ba zai fito ba yau shi yake saka hannu a dukkan abinda ya shafi saka hannu dan kuwa dan masanin ma ba zai samu fitowar ba zai wuni ne a kofar mai martaba , sai kawai ya shige ciki ya shiga saka hannun sannan ya fito ya nemi layin Sarkin dogarai da Sarkin bulala dan ba zasu wuce sunna fada ba ya sanar musu akoy sakon mai baban daki, sakon zasu kai shi da yama ne, kuma kafarsu kafar wanda take son gani.


A bangaren Anmy kuwa a lokacin da take kokarin zuwa inda Najeeba take , Najeebar ce ta sameta a dakinta

Du irin yadda ta yi dan ta boye damuwar da take ciki kuwa bata boyu ba a idannuwan Anmy

Tana daf da fara kokarin n???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?una mata ta cire komai NAJEEBAN ta nuna mata zata je bangarenta akoy abubuwan da take son yi sai ta dawo

Anmy na dubanta a rausashe ta ce" Zo nan babyna, zo nan"

NAJEEBA ta dubi fuskar Anmy, sarai ta san ko ta boyewa kowa abinda take ciki banda Anmy dinta

Dan haka ta karasa a sanyaye ta zauna daf da Anmy tana mai sada kanta

Anmy ta yi murmushi a tausashe ta ce" Ni na yarda cewa ba zaki aikata haka ba, Ni na san cewa idan akoy wanda ke son ki sake samun rabo bayanki zai biyo a duniya koda uban d'an ne!, ki yi hakuri ki cire komai daga ranki, kar ki saka a matsayin damuwar da zata dame ki ko ta haifar maki da wani ciwon kin ji?"

Tabas wannan din uwa ce ke magana a gabanta, kwarai uwa ce wace ta rike ta tun a lokacin da Tata mahaifiyar ta yi nisa da ita, kwarai wannan din itace uwar da take da yakinin zata bada shedar ta koda a cikin lakafani take , tana son Anmy, tana matukar kaunar Anmy, tana fatan Allah ya ci gaba da bata damar kyautatawa Anmy har karshen rayuwarsu

A sanyaye ta ce" In sha Allah anmy, zan kiyaye "

Anmy ta gyada kanta ta ce" Ki je ki gama abinda zaki yi ki dawo, Ama kar in ji kin je inda yake, kin ji Ni da kyau?"

NAJEEBA ta gyada kanta sannan ta mike ta nufi hanyar coridor ta shige ta yi ta bangarenta bayan ta sanar da Andiya ta yi zamanta zata kirayeta

Sai da ta shige falonta ta kunna wutace sannan ta kai zaune tana cire hijabin dake jikinta ta ajiye shi gefe sannan ta shiga murza gaban goshinta...........

Ashe da ake cewa, idan ran namiji ya bace babu abinda baya fadi hakane? Ashe dama gyaran da take yi dan jin dadinsa da nata na iya zame mata matsala? A ina ta sha abinda zai barar mata da ciki? Ita fa ba jahila bace, kuma bata yi son duniyar da har wai zata zubar da cikinta da gangan ba, ta yaya zai kasa yi mata uzuri ya kasa dubanta a irin wannan lokacin? Ashe du adalcin namiji yana iya muzanta Mace ya munana mata idan har aka yi rashin Sa'a macen nan ta biyo ta hanyar da bata yi masa ba?, yaya za'a yi ace ita NAJEEBA da har take bada salahu a kan mijinta da kyakkyawar mu'amalarsu haka na faruwa da ita?, ashe du ginnin da zaka bata lokaci kana yi a kan d'a namiji kawai ka yi domin Allah sai kuma dan samun aljanna gobe kiyama? Ashe du jimawar da sabo da kaza ba zai Hanna a yankata ba????, gaba daya jikinta yayi sanyi, gaba daya hankalinta a tashe yake, ji take yi inama ace tana tsaye lokacin da aka masa bayanin wai itace ta sha wani abin da yayi sanadiyar gudan jinninsu????? Tabas akoy wata a kasa, kuma zata zauna da likitan da likitar da suka ganta gaba daya, zasu zauna ne su sanar mata me suka gani a takardun da suka yi mata bincike?, zasu sanar mata me da me ya sa suka iya budar baki su sanarwa mijinta cutar da suka gani a jikinta Ama ita har suka saketa daga asibitin basu sanar mata ba?, ita ba jahila bace, ba zata dage sai ta ji dan ta tabbatar masa bane, a'a, tana son tabbatarwa kanta sannan ta cire shakun abinda asibitin a ranta, idan har bata samu gamsashiyar amsa ba bata tunanin ko mutuwa take yi in har zata koma asibitin nan, SHAHEED kuwa ita ta fi kowa sannin hanyar da zata bi dan su shirya, zata je din, zata duka din, zata bashi hakurin, zata bari idan ya huce daga fushin da yake yi su zauna, zata bashi hakurin, zata sanar masa gyara ba ila bane, zata nuna masa abubuwan da take sha tun daga na itace har zuwa na fruits, zata tabbatar masa cewa haihuwar nan da yake tunanin yana so shi, bai kama kafar yatsarta ba, saboda shi ai yanada wata da zata bashi, ita kuma fa? Ta yiwu daga su Abdallah bakin rabonta kenan, ta fi shi tsayuwar dare kan samun haihuwa, ta yiwu shi a cikin bukatun da yake roka a wajen Allah baya sako na samun rabon haihuwa a ciki, ita kuma fa? Shine abinda ta fi roka zata iya cewa.


Gannin ta samu mafita a zuciyarta sai kawai ta shige dakin ta ta rufe ta kwonta dan ta samu barci ko zata iya zama da su, domin barci take ji sosai, rabonta da ta yi dare cir bata rintsa ba har ta manta.


Sai kusan sallar la'asar ta farka, ta shige ta kula sosai da jikinta ta fito ta saka rigarta marar nauyi sannan ta kunna Babar wayarta dan ta tabbata yan uwanta sun wuni neman layinta,

Tana kunnuwa ta shige grup dinsu na familly ta yi msg sannan suka shige fira da du Wanda yake online sai sakin murmushi take saboda in dai zaka shiga MUTALAB grup ba zaka hadu da ciwon kai ba sai nishadi., ta yi zamanta tana jira a sanar mata da zuwan bakin sannan ta saka kaya ta same su........


A lokacin da aka fito daga sallar la'asar Docter muhseen suka sake gaisawa da Sarkin dogarai sannan ya mika masa takardar gayata hadi da Worawa da fadin" Yanzu yanzu ake da bukatar zuwanka falon baki na uwar gidan mu, da kai da Docter IZRANE, an ce ko me kuke yi ku amsa kira"

Hankalin Docter muhseen ya so tashi, da kula ya ce" Sarkin dogarai, ina fata ba laifi muka yi ba?"

Sarkin dogarai ya ce" Babu abinda na sani sama da tana son ganninku yanzu yanzu"

DOCTER muhseen ya sauke ajiyar zuciya ya ce" To Shikenan, Allah ya sa Docter dinma ta shigo dazu zata duba kawar mamanta , bari in sameta yanzu mu fito sai mu zo a motarta ko a mota ta"

Har Sarkin bulala zai yi magana Sarkin dogarai ya Hanna shi ta hanyar cewa" Ka yi hakuri a yi haka din, ka ga ba tsagerun gari bane bale mu saka su a kejin MAI WUKAR YANKA"

DOCTER MUHSEEN da sauri ya nufi ciki yana jin da gaske hankalinsa kam yanzu ya tashi

Direct ofice din Docter IZRANE ya nufa, yana zuwa ya dakata ya buga sannan ya shiga

Ta mike ne tana shan Lipton , tana kokarin gamawa sannan ta wuce gida dan ta ga marar lafiyar, ganin Docter muhseen ya sa ta Wan yi takwaf takwaf da fuska ta ce" Docter, ba dai aiki zaka bani ba, Ni dai na gaji ka ga banda lafiya fa, zuwa dai na yi na ga kawar mamanmu"

Docter muhseen ya mika mata takardar da yanayin damuwa ya dan huda hannayensa ya ce" A'a Docter, Bama wannan bane, shin me yake faruwa ne da FADAR DAMAGARAN?"

Da sauri ta daga tana kallonsa ta ce" Wani abin aka yi?"

Docter muhseen ya ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




9



Docter muhseen ya ce " Eh, wai Gimbiya ke kiran mu Ni da ke yanzu yanzu, shine hankalina ke son tashi, ina fata babu wani abinda kika yi Docter da zai sa a neme mu? Kin san karfin sarautar DAMAGARAN, kuma kin san wacece ita Gimbiyar, matarsa ce ta farko kusan tunda ta farkon bata nan, kuma y'ar uwarsa ce ta jinni, bayan wannan y'a ce a wajen MUTALAB Balarabe, duk wani abinda zai sa ka guji wata mu'amala in ba ta dadi bace da su kawai ka kiyaye, harda Sarkin bulala aka zo tafiya da mu wai"

Cikinta wani irin juyawa da yayi sai da ta ji kamar juwa zata kifata da kas, Muryarta na dan rawa ta ce" To, to, aa aa me zamu yi mu kuma na laifi? Mu fa likitocinsu ne, ko dai bata da lafiya take so mu dubata a gida, duba da miscag ne ta yi jiyan"

Docter muhseen ya dan yi jim, sai kuma ya juya yana fadin" Bana tunanin haka, bari in je ofice dina in dauko abin bukata in rufe, ki sa hijab dinki na sallah mu wuce tunda kin ga har falonta na amsar baki zamu je, kenan ciki zamu shiga, Ni dai bari in sanar da maman Mumina cewar zamu shige in ta ga shiru ta nemi gannin mai Martabar kawai"

Yana fita ta zarro ido jikinta na daukan rawa, cike da tsoro da firgici

Da sauri ta rarumi babbar wayarta hannunta na rawa ta zauna tana sake maimaita shawarar da ta yanke a zuciyarta

Jikinta na rawa ta dana NUMBAR SHAHEED, wace aka basu damar kira kowani lokaci saboda idan sunna tafe da maganar da ta shafi lafiyar matan gidan ko shi din da kansa ko Aliyu da sauran yan uwansa, ya sa aka basu NUMBAR

A lokacin sun fito daga masallacin sallar la'asar har sun zauna sun ci abinci ne shi da yan samarin sa sun gama, yana ayyana cewar zai sa a dauko masa ya'yansa ne hutun ya isa hakanan makaranta ta kusa tashi kira ya shigo wayar

Haka kawai da ya ga kiran sai da ya dan yi tunanin to lafiya?, sai dai tunawa da yayi likitar Najeeba ce sai ya daga yana mika hannunsa dake rike da tissu fari yana dan gogewa Abdallah gefen bakinsa da abin miya ya dan gogu a hankali ya furta" Wa alaiki Salam"

Sannan yayi shiru yana sauraron irin yadda take fitar da dan kuka kasa kasa da kuma barin jiki, wanda ke tabbatar masa cewar akoy wata damuwa

Babu abinda ya haWa da ita na jini, hakama bashi da wani kusanci da ita da ya zame masa dole ya ji dalilin kukanta , sai dai baban dalilin ba zai wuce kasantuwa wanda Allah ya nada dan ya jagoranceta ba, sai kuma dayan dalilin da ya zamo ita din ma'aikaciya ce a wajensa, dan haka ya dan dagawa su Muhammad hannu hadi da musu nunin su fita

Basu wani jinkirta ba suka mike suka fice sunna shawarar ina zasu nufa? Suka nufi wajen Dawaki

Gyaran murya ya fara yi , sai kuma ya furta" lafiya?"

IZRANE ta dukar da kanta, Muryarta na rawa ta ce" Dan Allah ka yafe min, idan har na yi wani laifin, ban san cewa a kasata bani da ikon fitar da abinda yake zuciyata ba sai yau, jiya na yi waya da kanwata a wajen hutunmu na aiki, nake sanar mata halin da nake ciki ina kuka, na fada mata cewar ina iya rasa raina, na sanar mata cewar lalle ina da bukatar addu'ar ta, na fada mata zan sanarwa mahaifinmu dan ya sakani a ADU'A, hakama zan fadawa mamanmu, na yi kuka sosai saboda damuwar tana da karfin da take iya kasheni, ban san cewa an ji maganar ba, inaga shine ya sa aka kai maganar wajen Gimbiya NAJEEBA......"
Ta ajiye zancen tana sake saka dan kuka a hankali ta kai dubanta inda ake bugawa wato ofice din ta

Har ga Allah yana daf da katse kiranta saboda irin yadda take masa kuka, kuma ya fahimci kiran da ta masa ba abinda ya shafi iyalinsa bane, ya so ne kawai yace da ita ta zo fada ta shigar da kara abinda yake damunta za'a duba zata samu mafita in sha Allah sai kawai ya ji karshen maganar ta, hakan ya sa ya dan dubi wayar kafin ya maida a kunnensa ya ce" Wa kika ce??"


DOCTER IZRANE ta ce" Gimbiya NAJEEBA"

SHAHEED yayi dan tsai, a hankali ya ce" Menene hadinki da Gimbiya?"

DOCTER IZRANE ta ce" Hadina da ita girmamawa ce, daragantawa ce, tsakanina da ita bayan girmamawa babu komai, a yanzu ne nake tsoron amsa kiran ta, ina tsoron ko an sanar mata ne, domin yanzu haka Sarkin bulala ne ke jirana zai kai Ni inda take"

........'ikon Allah' ya ayyana a zuciyarsa

A fili kuwa ya ce" Menene kika ce din?"

Docter IZRANE ta ringa dan dawurwuri kafin ta ce" Na sanarwa kanwata damuwata, da burina na son zamowa daya daga cikin iyalan mai garina, burina na son auren da na tabbata ya fi karfina, ina kyautata zaton shine ta ji, dan Allah a taimakeni tsoron Sarkin bulala nake ji, a Hanna shi tisa keyata ya kai Ni, zan kawo kaina da kaina, dan Allah a fara bata hakuri a sanar mata, da ace inada ikon hukunta zuciyata da tuni na yi mata mummunan hukuncin dauko min abinda ya fi karfina, Ni na san sarkina ya fi karfina......Ni na san ko hanyar da ta bi ta fi karfina, ba zan ja rigima da ita ba, ta gama kayar da ni, dan Allah a yafe min"........ Ta idasa tana sake sada kai, a hankali ta sake sakin dan kuka tana kama sunnan Allah

SHAHEED ya gama fasara abinda take nufi kafin ya katse kiran ya ajiye wayar ya dan zubawa waje daya ido cike da mamakin mene?, NAJEEBA ce ta tura a dauko mata Docter?, ta yi mata me? Wato ga abinda yake gabanta mai mahimmanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login