Showing 15001 words to 18000 words out of 144591 words

Chapter 6 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2335

Sai dai in bani da farar rigar nan a jikina, ko wancen da ta haifi d'anta na farko namiji ai na ji dadin mutuwar da yayi a gidansu, yaya matan da ta haifa kuwa basa daga min hankali , wannan na yanzu kuwa ai Bama na saka shi a lisafina, wadannan biyun sun fi tsole min ido, kuma daga su uwarsu ta gama haihuwar wasu!"

Da tarin mamaki har tana kame baki ta ce" Wai kina nufin cikin ya samu matsala?"

Cike da tabbatarwa ta ce" Kwarai, na zubar da shi, dama dan blding ta fara, na idasa tunkude shi, danma y'ar masifar jakadiyar nan Tata na jikinta like? Ai da na tsokalo wani gagarumin ciwon da zai sa in kaita dakin tiyata in cire mahaifar gaba daya kowama ya huta!"

Hajiya ta mike tana tafa hannu sama sama ta ce" Wannan kin fi Ni masifa, iyeah, wannan kin fi Ni balaki, wai Allah da gaske kike? Lalle zaki rama min wulakancin da Najeeba ta min, kece zaki rama min dukan da mijina ya min saboda ita, iyeah....."

DOCTER IZRANE ta yi murmushi tana bin mai aikin hajiyar da kallo da ta fito ta kawo mata ruwa ta juya

Kasa kasa ta ce" Wannan fa kar dai aje ta ji mu?"

Hajiya ta yi murmushi ta ce" wai wace wanann? Bata ji da kyau fa, kurma kurma ce, sannan gyadi gyadi ce, ko a gabanta kika fadi abu bata ganewa bale in ta bada baya"

Docter IZRANE ta yi murmushi ta ce" Abinda ya kawo Ni yanzu tashin hankalin da ya fi wannan ne, Hajiya gaba daya karra tsorata nake yi da bawan Allahn nan, gashi sonsa sai karra shiga zuciyata yake yi, kin san da na yi masa bayanin cewa ita ta yi sanadiyar zubewar cikin nan yau na kusa amsar hukuncin duka daga wajen Sarkin bulala?"

Hajiya ta zarro ido tana kallonta ta ce" Kina nufin shi din kika fadawa laifin NAJEEBA? Kin kuwa san irin yadda ake fadin tsakaninsa da NAJEEBAr nan? Ai yarinyar nan an yi Y'ar balaki, kin san lokacin da baban yaran nan ya so ta a kofar gidansu ya ringa kwana ? Idan tace abu a lokacin yake yi mata, mota fa ya cenja mata, har mamaki take bani da tsoro, na sha tunanin asiri ta masa, to gani na yi wa ta fi kyau ne? Me ta fi Ni ne? Ama yarinyar nan ta sa ya ringa zane banza, dan kuwa sai dai in ban zageta ba, kamar na zagi mamansa haka yake sakani a gaba ya zane banza"

DOCTER IZRANE ta dubeta, irin yadda take rusasa a zaune ba tsari , kanta kamar an ci goriba da wuka take ikirarin da me Najeeba ta fi ta? Hum

Da kula ta ce" Kin san idan hurumin aikina za'a bi ai ina da damar yi masa bayanin nan, Shikenan mutumen nan ya hade fuska, karshema na duka in bashi hakuri Sarkin bulala ya kusa zane Ni, da ace da tazara tsakanina da shi da tabas yau sai bulalar nan ta hau kaina"

Hajiya ta yi dariya tana tafa hannu ta ce" Wallahi da kin zanu, Cabdijan "

Itama ta yi murmushi ta ce" Yanzu menene mafita? Yaya zan yi KENNAN?"

Hajiya ta yi shiru, kafin ta ce" Kin san su manyan mutanen nan, ba'a yi musu shigar saurin nan, saboda in har aka yi musu kamar an musu rashin kunya ne, haka din kuwa matsala ne baba, Ama ba kin ce kin saba yi masa bayanin abinda ke damun matansa ba?"

Docter IZRANE ta gyada kai tana duban ta

Ta yi murmushi ta ce" Ai inaga, dabara zaki yi, ki rike wannan damar, ki Wan ?ara kusanta kanki da shi........a hankali a hankali har ki samu ki kai ga ci........, Ama fa gaba gaba sai kin sa mahaifinki a maganar , a samu ya je ya kai gaisuwa, a hankali a hankali sai ku nuna manufar ku, in dai an dace zaki ga burinmu ya cika"

Docter IZRANE ta dafe gaban goshinta cike da tashin hankalin dake damunta ta ce" Idan ba'a dace din ba fa? Yaya zan yi KENNAN? A yanzu ina ji a raina girman bawan Allahn nan nawa ne Ni kadai, ina ji a raina cewar nice na fi dacewa da duniyarsa, da shinfidarsa, da fannin fuskarsa."

Hajiya ta gyada kai tana sake girmama lamarin ta ce" To kuwa ya zama wajibi ki dage, sosai sai kin dage, haka kuma ki fake da aikin ki ki ringa saka masa jin haushinta a ransa....., hakace kawai zai sa ya Dube ki Wan kuma Ni ba zan taba yarda da cewar wai tsabar so har sarki ya kasa karra aure bayan matarsa bata haihuwa, ke gidan sarauta fa hudu reras din nan sai an jera su, zan so ace kece ta ukun nan ki je ki jera da yan kutumar uban matansa!"

DOCTER IZRANE ta dauke kai cike da isa tana girgiza kafa ta ce" Matarsa dai, ita dayan nan, saboda bana daukan nadiyar nan a cikakkiyar macen da zan yi kishi da ita........., koda yake, itama ta min shigar sauri dole zan bi da ita, lokaci dai"

Haka suka yi ta sakawa sunna kuncewa har dare ya tsala sosai, dole a nan ta yi kwonciyarta saboda a gidansu an san tana wajen aiki babu wanda zai damu, safiya na yi sai ta wuce gida kawai.




SULTAN SHAHEED


Sai da dare ya tsala ya nufi coridor din dakin Nadiya

A nutse ya bude bangaren nata ya shiga ya nufi dakin ta kai tsaye ya dakata ya dan buga sannan ya ja ya tsaya yana jiran a bude masa

Sai da yayi bugawa hudu sannan ta jiyo, a tsorace ta ringa tambayar waye tana duba agogon dakinta

Jin yannayin Muryarta kamar ta tsorata ya saka shi yin gyaran murya mai dan karfi sannan yayi shiru

Tasowa ta yi da sauri ta bude dakin tana kallonsa da yannayin tsoratar ta ce" Allah ya taimake ka, kai ne? Me yake faruwa? Ko jikin NAJEEBAN ne?"

SHAHEED ya dan kautar da kansa saboda kai tsaye take magana , ga abin barci da ta yi odora dinta bashi da dadi

Bai bata amsa ba ya shige ciki ya zauna bakin gadonta ya hade hannayensa waje guda yana kallon kasa

Shigowa ta yi itama ta duka daf da shi tana kallon kasa ta ce" Allah dai ya sa lafiya ranka ya dade, na ga yannayinka ba dadi, ko laifi na yi?"

SHAHEED ya dago idannuwansa yana kallonta, a hankali ya ce" Kina tune cewar, na taba yi muku kwakwaran kashedin shaye shayen magungunnan Hausa???"

Gaban Nadiya ya kwonci kwonci ya fadi, innalilahi Shikenan asirinta ya tonu, yaya aka yi ya san tana sha? Ita da take boyewa ta sha abinta, to wai yaya za'a yi yace ba zasu sha maganin mata ba? Wani irin zaman aure ne mace zata yi ba gyara? Ita matarsa menene bata sha? Ta tabbata Najeeba babu abinda bata sha, Shikenan ita sai a hannata? To komai ma so ake yi NAJEEBAN ta fita kenan?

Bai sake yin magana ba amsar ta yake jira, yannayinta kuwa gaba daya ya sa ya zuba mata ido da wani tunanin daban, shi ya gaza rintsa ido ne da tunanin to ko shine yake tunanin ya hane su wannan dabi'a ta matan yanzu da suka dauki shaye shayen maganin nan abin yi ba dare ba rana sai an dauki shekaru a hadi da rashin lafiya kala kala kuma a zo a yi ta fama, shi bai Hanna su hade haden fruits ba, da nau'ikan abubuwan da aka sansu aka yarda da su, ba abubuwan da baka san me suka kunsa ba , Ama shine yake ganin kamar bai musu maganar ba

Ta sosa kai ya fi a irga kamar mai kwarwata a kan tsabar gigicewa, murya a raunane ta ce" Dan Allah ka yi hakuri ranka ya dade, wallahi in ba ranar girkina ba bana sha, kuma idan na sha din ba abinda zai cutar da Ni bane, in dan Wanda na sha yau ne wani ya sanar maka ka ganshi....."

Sai kawai ta mike ta dauko wata roba fara mai dauke da wani gari lukwui ruwan yelow carrrr ta duka ta bude ta ce" Ka ganshi nan, siyansa na yi, irin yadda yake da tsada Bama zai cutar da Ni ba, kuma cokali daya ne jal ake sakawa a madara a sha , dan Allah ka yi hakuri ranka ya dade"

Ikon Allah kawai yake kallo, a'a, KENNAN dai maganar Docter gaskiya ce? KENNAN dai NAJEEBA har maganin da ya zubar mata da ciki ta sha? Lahaula wala kuwata Ila bilah, ransa idan yayi dubu sai da ya bace, da kakkausar murya ya ce" Na hane ku shaye shayen nan ko ban hane ku ba?"

Murya na rawa Nadiya ta ce" Ka Hanna mu"

Ya rintse udannuwansa cike da bacin rai kafin ya mike ya nufi hanyar fita

Hankali tashe Nadiya ta duka tana fadin" Dan Allah ka yi hakuri, ba zam......"

Rai bace ya juyo ya dora kausasan idannuwansa a kanta ya ce" Kul, kar ki yarda ki sake sako wanda nake yin alfarma dominsa a lamarin da kika san kin cuce Ni!, wato Ni zan saka muku doka ku nuna min ban isa ba......? Ku sha maganin sai ku nemi mai amsar sakamakon maganin naku!, sai dai baku isa in ringa zuba muku y'ayana kunna salwantarwa ba, baku isa ba!"

Daga haka ya fice a dakin ya nufi bangarensa, Nadiya kuwa da gudu ta yi bayi saboda tsabar tashin hankali da firgici ta haye salga cikinta na murdawa, zufa na keto mata, anya ta taSa ganninsa da bacin haka kuwa? Ita dai bata taba gani ba, baban tashin hankalinta itace sila? Yanzu ina zata sa ranta kennan? Yaya za'a yi ta bashi hakuri da alkawarin ba zata kuma ba? Yaya aka yi ya san tana shan maganin hadin nan? Ama ai yace in abu ba zai cutar da su ba, maganinta sanannen magani ne a wajen sananiyar mace mai hada magungunnan mata na Hausa kasa da kasa, gari da gari, ta yi sunna an Santa , dan yanzu haka maganin nan dazu ne tace bari ta gwada in ya karbeta gobe sai ta sha na kirki dan ta je ta nuna bajintarta itama, dan kadan ne ta sha Ama sai da ta ji ni'ima a jikinta, bayan ita mutun ce mai wahalar kama magani, sai ta sha magani kala goma bata samu daya da ya amsheta ba, sai gashi ya zo da tsautsayi? Innalilahi gashi dare ne bale ta yi kira gida a bata shawarar yadda zata yi? Ya zama wajibi ta je asibiti tunda safe dan kuwa tana da yakinin Najeeba ce zata je kanta tsaye gabansa da maganar ta musu sulhu, in sha Allah ita sai ta daina shan maganin ma gaba daya in dai har haka zai saka musu rigima ita da shi

( Hum baki san barat da baki kika yi ba ke rigayi liman zuwa Masallaci ko?)



A lokacin da ya koma dakinsa ya tarar da wayarsa dake kunne wify a bude sai shigo da kira take yi , wato vidio callll da sunnan Beebah.......

Kallon kiran yayi kafin ya katse shi ya kashe wayar gaba daya ya wurgar da ita saman bed sannan ya nufi bayi ya dauro alwallah ya zo ya tayar da sallar nafila, dan baya tunanin bacin ran nan in zai barshi rintsawa yau.


Najeeba rike da waya ta zata da aka katse kiran kiranta ne zai yi dan har ta Wan gyara tana murmushi sai ta ji shiru, hakan ya sa ta dake tura kira, Ama baya nuna alamun yana shiga irin na dazu da alamun da yake nunawa ya sa ta gane yana online

Da sauri ta fita ta shiga tura masa kira, sai dai abin takaicin wayar a kashe take gaba daya

Gaba daya layikansa babu wanda bata kira ba, Ama amsar daya ce, sweet of, hakan ya sa ranta bacewa ta rike wayar cike da sukar rai tana tunanin kenan zuwan da yayi gidan zuwa yayi ya samu Nadiya ya runguma shi yasa ya ki daga kiranta ko? Wannan ai cin amana kenan, in har hakane daga ita har shi sai ta fada musu ba zata yafe musu darenta ba, ita fa bata so ana daukan ta shashasha wallahi haba dai!
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




6



Gaba daya layikansa babu wanda bata kira ba, Ama amsar daya ce, sweet of, hakan ya sa ranta bacewa ta rike wayar cike da sukar rai tana tunanin kenan zuwan da yayi gidan zuwa yayi ya samu Nadiya ya runguma shi yasa ya ki daga kiranta ko? Wannan ai cin amana kenan, in har hakane daga ita har shi sai ta fada musu ba zata yafe musu darenta ba, ita fa bata so ana daukan ta shashasha wallahi haba dai!

Bacin ran nan da kyar ya barta ta rintsa bayan an saka mata maganin dauke zafin ciwon marar da kuma na barci a ciki, hakan ya sa washe gari sai kusan karfe takwas ta buda idannuwanta cike da abin barci

Bayi kawai ta shiga ta yi bruch hadi da wanke jikinta sosai da ruwan dumi, Ama ta kasa yin wanka ta fito da hijabinta a jikinta ta sanarwa matar yaya Dayabu cewar ita fa gida take so kuma

A'isha ta yi murmushi ta ce" Ai Docter dama yace a barki har ki farka da kanki, sai a kirawo shi ya bamu salama, dan har na kira su Anmy nace kar su zo muma gamunan zuwa, gwara mu yi mu koma kar a gane kina asibiti a fara damun mararsa lafiya da baki"

NAJEEBA ta yi murmushin itama ta dauko wayarta da tunanin zata tarar da tarin miss call dinsa, da msg dinsa, da kuma tarin msg a whatsup, sai dai abin mamaki du inda ta duba babu wani alamun ya tuna da ita a duniyar, hakan ya sa hankalinta ya fara tashi da tunanin ko ba lafiya yake ba?.......

Kwarai dole zata yi tunanin ko ba lafiya yake ba, domin a zamantakewarta da mijinta sunna da shakuwa mai ban mamaki
Ya zamo basa jimawa basu nemi junna ba ko lafiya kalau suke bale ace bata da lafiya......
To ko ciwon kai ya san tana fama da shi shima sai ya shiga yannayin rashin jin dadi bale bari.

Tana kokarin sake aika masa kira yaya Dayabu ya zo da kayan kari niki niki , haka kuma likitan a lokacin ya zo shima

Gaisawa suka yi sosai, sannan likitan ya basu takardar salama, da magungunnan da zata sha, sannan ya sanar mata idan komai ya tsaya da ya danganci jinni zata dawo a yi mata hoton cikin a ga in wankin cikin da aka yi mata yayi kuma in ba wata damuwar

Godiya suka yi masa shima ya musu sannan ta luluba alkyabarta da Sarkin bulala ya dawo ya kawo ya ba Jakadiya cikin dare bisa umarnin uban gidansa, ta saka takalmin ta plate ta shiga tsakiyar yayanta da matarsa suka fito a nutse, jakadiya na bin sawayenta tana ta faman sake lulubeta da alkyabar da ko fuskarta ba'a gani, haka kuma mutane na ta kawo gaisuwa Aunty A'isha da yaya Dayabu sunna amsawa har suka shige motar yaya Dayabu, ita kuwa Jakadiya ta shige motar da aka kawo su da ita jiya , dogarai suka shige motar sojawan da suka kwana nan suka dauki hanyar fadar garin DAMAGARAN.

Bayan sun isa suka dakata daga nan , ita kuwa sai da yaya Dayabu ya Kaita har wajen bangarenta sannan suka fita suka wuce ciki shi kuwa ya ja motarsa ya wuce wajen Anmy dan ya gaisheta kafin ya wuce harkar kasuwancinsa


Sunna shiga Najeeba ta cire alkyabar ta amshi ky din dakinta mai haWe da dan karamin ky din dake hadata da dakinsa a wajen Andiya bayan andiyar ta rungumeta tana murnar ganninta sannan ta wuce corridor din tana dan sinsina hijabin dake jikinta da tunanin kar aje tana wari wari hancinsa ya jiyo, sai dai ta kasa tsayawa ta yi wanka kafin ta je inda yake saboda tunanin kar aje ko bashi da lafiya ne ya sa bai nemeta ba.

Sai dai ga mamakinta a lokacin da ta saka dan makulin ta yi ta yi ya murdu ya ki murduwa, hakan ya sa gaba daya tunaninta ya karkata kan yaushe kuma abin nan ya lalace?, gannin ta kasa budewa ta nufo falon daidai tagwaye sun shigo suka nufota gaba dayansu da murnar ganninta suka rungumeta, Muhammad sai murmushi yake yi yana sinsinar hannunta, Abdallah kuwa sai kallon fuskarta yake yi kafin ya ce" Momy yaya jikin ki?, kin ga yau bamu je islamiyya ba, da malamin ya zo Muhammad yayi ta kuka sai malan yace mu dawo da yama a yi karatun idan aka kai shi ya ga jikin ki "

Muhammad da haushi haushi ya bige Abdallah yana fadin" Kai Dilla, Nine na yi kukan? Bana son raini fa"

Abdallah ya harareshi ya ce" Waye zai rainaka? Kar ka sake dukana dan ba kyale ka zan ba"

Ai kuwa Muhammad ya sake kawo masa duka da karfin gaske , shima ya ja zai dirka masa dukan Najeeba ta riko kunnayensu ta zarro ido ta ce" Ok, Na zo zaku daga min hankali ko? To maza ku wuce ku je ku dauki littafan ku ku yi tilawa bana son iya shege, ku kenan kullum cikin fada????"

Aunty A'isha da ta daga kiran Anmy ce ta zo ta amshe su, Abdallah ya waske abinsa, shi kuwa Sarkin yan zuciyar tuni ya haye sundum kamar zai fashe karshe ma ya wuce ya nufi falon abansa yana rike kukansa, dan kuwa ba abinda ya fi bashi haushi irin in zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login