Showing 96001 words to 99000 words out of 144591 words

Chapter 33 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2336

ya kuma gama gane cewar da wahala maganar nisa Ni da shi ta samu duk rintsi, sai yake anfani da damarsa yake aikata din karfi da dane na kusa da shi yana ba na nesa da shi damamaki masu yawa......, ya taba tabbatar min cewar ko yayane dole ya ringa ba nadiya gaskiya saboda idan ya zamo kaf dangi nawa ne, ita kuma ta kama wa ta ji sanyi? Nadiya matarsa ce, dole zai yi mata adalci!"


Ta kausasa muryarta ta ce" Ai sai ya ci gaba da yi musu adalci su da suke da wannan damar a wajensa, nima a bani dama in samo mai min adalcin!"

Yaya Dayabu na kalonta har ta dire maganar ta dauke kai tana girgiza kaffafuwanta

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce" Kin daina sonsa kenan? Kina nufin dan kawai ya bata maki rai kina iya rabuwa da shi ma kenan?"

NAJEEBA ta Dube shi ta ce" Dama sonsa na yi? Ai dama ra'ayi kuka yi, ku kuka so kuka hada, yanzu kuma nace na gaji du Wanda ya ga zai iya shi ya zauna da shi mana!"

"Najeeba zan ci ubanki!" Yaya Dayabu ya fada yana nuna mata yatsa

Kai ya sada tana alamun zata fashe da kuka, hakan ya sa ya dubeta a sanyaye ya ce" Ama kin san ai ina da manya a gabana ko? Ko so kike yi su rufeni da duka su ga laifina har su yi fushi da Ni? Najeeba mutumen nan da kike yiwa kallon sako mu ba sa'anmu bane, ke kin san cewa ya fi karfin mu, dan Allah ki saka zuciyarki a ruwan sanyi mu yi maganar da zata fishemu "

Najeeba ta zuba masa ido,

Yaya Dayabu ya dora da fadin" Yanzu zan yi shiru ki kara kwana biyu, a ci gaba da neman ki harda Ni, idan kika huta sosai sai mu je wajen Anmy, kin san da tace idan aka ganki abinda kike so za'a yi babu wanda ya isa ta takuraki???"

Wani tausayin Anmyn ya sake ratsa zuciyarta ......,

A shekarunta ta kai mizanin da zata ji irin soyayar d'a da uwa......ba abu ne da ake iya haWawa da komai ba....., Ama cikin ikon Allah a haka Anmy take daukan manyan d?cision din da ba lalle kowace mace ta iya dauka a tsakanin d'anta da wata ba koda kuwa d'an zumunta ne....., Ama a duniyar Anmy ta gama sanin abinda ake cewa soyayar kanwar uba , wato soyayar dangin iyaye bata da Mahadi idan an hadu da na kirki, su kam Anmy itace duniyarsu, sun yarda da soyayyar da take yi musu dari bisa dari

Sake kalamamayeta yayi har ta amince da maganar cewa idan an kwana biyu sa je, sannan ya mike ya sa ta fito falo ta fadi abinda zata ci mai aiki ta shiga girka mata suka dora fira

A cikin ransa ya san cewa idan Sultan ya kara 2 days yana neman Najeeba zai sake daukan fushinta da mahimmanci fiye da yadda ya dauka a yanzu harma zai daina abinda yake yi mata, .....sannan yayi niyar idan ya je fada in an jima zai sanar da Anmy inda Najeeba take dan ta kwontar da hankalinta , sannan su ci gaba da nemanta har su Abiey din domin kuwa hatta Abiey ba wani daukan lamarinta yake yi da kyau ba, shima yana kallo ake son mayar da ita baya haka kawai dan ana takamar an aura mata d'an uwanta.....

Ya san zai fuskanci fushi daga wajen iyayensu, Ama kuma ya yi niyar kwatowa kanwarsa yancinta har sai inda karfinsa ya kare

Najeeba kuwa, ji take yi zuciyarta ta saku da nauyin da ta yi mata, haka kuma ta ringa ji a zuciyarta idan aka fadawa Anmy zata kwontar da hankalinta Shikenan , su Muhammad ne kawai suke cikin ranta, tun Jiya kuwa idan ta ji abin ya dameta kamar zarariya take budar baki ta nuna kanta a gaban madubi tace "ke Najeeba, yaushema kika san dadin ya'yan da har zaki wani sako su a rai dan wani salamamen munafurci?, ya'yan da suka kamo ki a tsayi goya su zaki yi? Bama wannan ba to da mutuwa kika yi ba zasu rayu ba akace maki? Dilla ki cire shirmen ya'ya a rai dan kuwa koda jarirai ne zasu rayu ne da karfin ikon Allah bale samarin ya'yan da suka iya yiwa kansu komai kuma a gefen kakarsu da take yi musu soyaya irin ta wanke hannu ka taba? Ke mema ya haWaki da ya'yan mutumen nan ne? Aikin banza ai sai ki yi....."

Da wannan take samu zungoy zungoy ta bar gaban madubin harma ta samu sukuni a zuciyarta da tunanin ta kwabi kanta ba zata ci gaba da yada rashin kunyar nuna son ya'ya ba........

A hankali ta hade kafafuwanta cikin dabara ta dafe saitin kirjinta dake bugawa sakamakon tuna Anmy da ta yi da kuma tuna yaranta da ta yi..........



"Ummi, gayanan bari in bashi wayar"
Aunty A'isha ta fada tana nufo yaya Dayabu da wayarta, domin ummi ce ta yi ta nemansa a layinsa Ama itama bata samu, domin tun Dazu Abiey ma yace ta yi kiransa ta ji yaya ake ciki dan rabonsu da shi tun jiyan nan, Ama kuma sun kasa samunsa, du a tunaninsu fushi yake da su, du a tarin tsoronsu ko bashi da lafiya ne? Domin waye bai san irin shakuwar ya'yan nan ba?, yanzu haka Sarkin agadaz da kansa sai da yayi kira ya kai sau uku yana tambayar yaya ake ciki? An samu Najeeban ne? Saboda matar ta daga masa hankali, sunna cen sun hade kai, haushin kowa suke ji, kadan suke jira kamar jarirai su fashewa mutun da kuka, wannan takaicin ya sa ta fattatakesu da yi musu alkawarin korar kowace dakinta idan har basu bata lafiya ba!......

A tausashe Anmy ta ce" Yayansu....., ina ka ajiye wayar taka ne muke ta nemanka?"

Yaya Dayabu Muryarsa a sake sosai , wace sam ya manta hakan na iya saka mamaki a zuciyar Ummi ya wani gyara zama ya ce" Wayar na daki, kasheta na yi na yi barci ummi, Barka da warhaka"

Shiru ummi ta yi na lokaci kadan, domin tarin mamakin yanayin maganarsa, uwa uba fadar da yayi cewar kashe waya yayi yayi barci sai ta ji wani irin mamaki ya kamata, dan haka ta ce"......
https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3
*Kayan kitchen kike nema?* *Laces ko atamfa ko* *materials?? Yar uwa muna da takalma ,jaka akwatuna d kayan parlor* *nd toiletries, d sauran* *abubuwa d dama kuma* *delivery nationwide In* *sha ALLAH=?
? sannan* *muna bada kaya a* *farashi mai sauqi domin masu siya su siyar kiyi* *joining domin ki amfana* >??>??






>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




33





Shiru ummi ta yi na lokaci kadan, domin tarin mamakin yanayin maganarsa, uwa uba fadar da yayi cewar kashe waya yayi yayi barci sai ta ji wani irin mamaki ya kamata, dan haka ta ce" Ah, ga dukan alamu ka ga kanwar taka ko Elhaji?"

Yaya Dayabu ya gyara zama da sauri yana kallon NAJEEBA wace ta zuba masa ido da mamakin yadda ya Hakimce yake fadin barci ya shahara shi da yake nemanta

Murya ya gyara har sau uku, ya wani matse murya kafin ya ce" Ai jiki na yanke na fadi a cikin anguwa da safe Ummi, shine da aka kwasoni aka kawo gida suka kashe wayar barci yayi gaba da Ni, yanzu ma zan fita da na yi sallar magariba in ci gaba da nema, Jiya a tasha ma na kwana ai dan koda Za yi rashin Sa'a ta zo daukan mota in lakada mata dukan mutuwa kafin in kawota wajenki"

A bayyane ummi ke gane rashin gaskiya a cikin bayanan yaron nata, ....to Yayama za'a yi ta kasa gane bayanansa koda da ido yayi? Bayan wannan shi da yake fadan kar a saki a shiga hakin kanwarsa kuma shine yanzu da maganar idan ya ganta zai zaneta? Anya kuwa?

Ta gyada kai tana tabe baki ta ce" Ka tabbata baka san inda take ba?"

Yaya Dayabu ya mike tsaye yana fadin" Kai, haba dai ummi da na ganta da na fada ai"

Ummi ta girgiza kai ta ce" to Shikenan, dama mai kula da yara ne tace Rislan yana ta rigima, ka tura a dauko su a kawo su wajen mamansu idan na koma gida sai a kawo min abina, saboda ban san yaushe zamu koma ba, ga dare yana neman tsalawa, kuma likita bai sake mu ba"

Yaya Dayabu yayi shiru kafin ya ce" Likita? Waye ba lafiya?"

Ummi ta ce" Anmynku ce, Ama da sauki dai, har dai in ji bayanan likitan"

A sanyaye ya ce" Subahanalah, zazabi ne ko menene?"

Ummi ta ce" Ba zazabi bane, ka san ai hawan jini ga shekaru , ba zasu hadu da damuwa ba sai sun tayar da kayar baya, sai da na danganata da asibiti dai , saboda ko abinci fa ta ki ci"

Yaya Dayabu ya kalli Najeeba dake kallonsa da wani irin yannayi a kwance a fuskarta na tashin hankali

A sanyaye ya ce" Aya, Ummi kuna wani asibitin ne dan Allah?"

Ummi ta sanar da shi sunan asibitin sannan ta Wora da fadin" Idan zuwa zaka yi sa A'isha ta hada min madara mai dumi da Lipton ka zo min da shi PLZ, sannan ka ga ka rabani da kanenka, zan yi maganinsu , ka fada musu su hana mazansu kirana, bana son iya shege kun dai ji na fada muku"

Yaya Dayabu ya gyada kai a hankali ya ce" To ummi sai na zo, Allah ya bata lafiya "

Ummi ta kashe kiran, yaya Dayabu ya mike fuuuuuu ya nufi dakinsa saboda tunda ummi ta yi maganar abinda za'a hada mata A'isha ta yi wajen d?ner dan haWawa domin ta san yadda ummi ke shan su ,ya zamo sun bar Najeeba kadai zaune hannayanta na san daukan rawa, harda wata mijirya mijirya ta tashin hankali

Ya dan jima a dakin sai da ya cenza tufafi ya saka na fita sannan ya fito a shirye da shirin koda zai jima a cen din nan

Yana fitowa Najeeba ta mike tana dubansa ta ce" Yaya, Anmy ce ba lafiya? Me yake damunta? Ko ciwon kanta ne ya motsa?"

Yaya Dayabu ya dauketa da harara yana dauke kai ya ce" Inma me din ta ne ya motsa ai inaga yanzu ke ba zai dame ki na tunda kin ce Bakya sonta "

Da sauri Najeeba ta dubi A'isha, sannan ta dubi yaya Dayabu ta ce" Aya yayana, aya kamar wace na yi maka wani laifin bayan yanzu muka gama magana da kai?, dan Allah fada min mana yaya jikin ANMYNA "

Yaya Dayabu ya karbe sakon ummi yana duban ta ya ce" Anmy ai tana asibiti likita na kokowa da numfashinta, Allah ya sa ta yafe maki kaunar da take maki ke kina kin ta, Ni na tafi in kun ga karfe daya na dare yayi ku yi kwonciyarku saboda ai dole za'a ci gaba da neman wace ke gabana da Ni , Allah dai shi kyauta wanda ba zai iya yiwa mai sonsa uzuri ba ai butulu ne...., koda yake in ban fada Bama ai A'isha barcinta zata yi tunda ta fara hada kai da wasu ana MANTAWA da Ni a Duniya, sai an jimanku!"

Yayi gaba abinsa hankali kwonce, ya barsu tsaye baki bude sunna kalonsa

Kai kawo Najeeba ta ringa yi hankalinta tashe, ta duba screen din wayarta ya fi a irga, sai ta yi kamar zata kunna sai ta kiya, karshema ta doka wayar da kasa ta duke tana fashewa da kuka saboda irin yadda kirjinta ke bugawa da tsoro da tarin kaunar Anmy....

Da sauri A'isha ta karaso yana kamata ta mikar da ita ta zaunar da ita saman kujera tana rungumota kadan tana bubuga bayanta ta ce" Najeeba, ya dace ki sassauta kukan nan fa, zuwa yanzu ko Ni na san kina da juna biyu bale ke, ya dace ki rage damuwar nan kar ta shafi abinda yake cikinki Please"

Najeeba na kuka ta ce" Yaya zan iya dainawa? Ba zan iya dainawa ba, zuciyata bugawa take yi Aunty A'isha, kima ji Anmy ba lafiya wayo Allahna, ba zan iya jurewa ba, wallahi ba zan iya ba, wayo ANMYNA, an taba wajen da ba zan iya jurewa ba koda yankani ake yi zan je wajen ANMYNA ne kina ji abinda wannan masharancin mijin naki yake fadi a kaina Ama Bakya hana shi ko? Mutumen nan da ace lauya ne da an yi munafiki!"

Aunty A'isha ta dubeta tana harararta ta ce " To fa, mijin nawa?"

Najeeba ta mike ta yi dakinta tana fadin" Ai dama ba kowa ke son gaskiya ba yanzu, shi din da kansa marar tsoron Allah kawai mai fuska biyu!"

A'isha ta rafka tagumi tana kallon ta har ta shige,

Ta mike zata bi bayanta kiraye kirayen sallar magariba suka sa ta juya ta nufi dakin ta Wan gabatar da sallar kafin ta samu Najeeban ta sake rarashinta..............


Bayan sun gama sallah najeeba ta yi ta kiran layin yaya Dayabu da wayar A'isha, Ama yana kallo ya ki dagawa, sai da kyar ya daga da fada fada ya ce" Du wace ta kuma kirana sai na dauke fuskarta da mari du girmanta, Yan rainin wayo kai, so kuke yi a gane abinda nake ciki ne? To an dakatar da masu shigowa cat?gorie Kun san dai Sultan na daf da shigowa, du wace ta sa yayana ya dakeni babu mai hana Ni dukanta aikin banza kawai!" Kitttt ya katse kiran yana cika fuska

Najeeba ta mike ta yi dakinta ta cenza tufafi ta fito da katon hijab da nikaf ta zauna tana saka Safa

A'isha na dubanta ta ce" Wai me kike yi? Ina zaki je?"

NAJEEBA ta dubeta tana dauke kai ta ce" Ba zan iya zama ba bayan zan san halin da take ciki ba, zan je daga nesa in tsaya idan na ga da sauki in yi tafiyata!"

"Ama, ai yanzu kika ji ance Sultan zai je asibitin ko?" A'isha ta fada tana duban ta

Najeeba ta ce" To Ni ina ruwana da shi? Bayan wannan ai ba bari zan yi kowa ya gani ba bale har ace za'a min wani abu, kowa yayi ta kansa kawai zuwa zan yi in dawo "

A'isha ta sauke ajiyar zuciya ta je ta dauko mata ky din motarta ta ce" In zo mu je ko Najeeba? Kar in barki ke kadai?"

Najeeba ta girgiza kai ta ce" A'a, yi zamanki, kin ga mijinki baya raina abin a kwabe riga a daku, yi zamanki A'isha"

Aunty A'isha ta gyada kai ta rakata har kusan motar tana ta sake jaddada mata dan Allah ta kiyaye


Motar ta shige ta dauki hanya bayan ta saka wakar larabawa a motar tana tuki hankali kwance............




A fada


A lokacin da yan matan Anmy ke falo su dukansu , harda su andiya da su auta sunna ta zulumi da firar Y'ar uwarsu da irin yadda zasu tsaya mata sai an yi mata abinda take so, nadiya ta fado musu ta coridor da wani katon hijabinta da ya masheta kamar rumbu ta zo ta zauna cikinsu tana kallon Muhammad dake kwance a cinyar zahra'u kamar wani karamin yaro, ta tabe baki ta ce " Sannunku da fira sisters, wannan fa da yake kwance a nan kamar wani jariri?"

Ummukulsum ta tabe baki tana jin haushin Nadiya ta ce " Jariri ne mana, d'a a cinyar mamansa har an masa zancen jajirtaka???"

Nadiya ta Wan dubi yanayin ummukulsum din, ta ga kamar ranta a bace, ta tabe baki, a ranta tana ayyana' aikin banza ita wannan ba zata daina kishi da Ni ba? Ko yayar taki ai ta ba kanta lafiya tunda ba dan ita kadai aka halicci mijinmu ba bale ke tsigi taka!'

A bayyane kuwa sai ta ce" Wai ina Najeeba ne......"

"Gimbiya Please, Gimbiya NAJEEBA...., wai yaya aka yi kuke wasa da darajar da take wuyanku ne? Ita din Gimbiya ce koda da sama da kasan daje faruwa kar ki manta haka!"

Zahra'u ta tareta da wani haushi haushin itama, domin du a tunaninta ta san cewa Najeeban ta yi yaji ne ta zo zata raina musu wayo , to kuwa daidai suke da ita, su a yanzu daukan magana ai ta wanda ya ajiyeta basa shayi in dai ba gannin Y'ar uwarsu aka yi ba bale Tata ita tarwada wahainiyar cikin ruwa!

Ummulkhair ta ce" Ta tafi awo, au bata yi maki salama ba???"

Da sauri Nadiya ta dubeta, ta ce" Awo ko me? "

Ummulkhair ta gyada mata kai, dan kuwa itama ta zata ai ta san bata nan din ne ta zo ta musu iskanci a nan, to kuwa zasu lakada mata na jaki su bar banza kwonce, sai dai a rufe su su din ma...........

Nadiya na dubanta ta ce" Na zata awo daya ake yi, .....na ciki...., oh koda yake akoy awo na hawan jini ko? "

Ummukulsum ta tashi da kyau tana ajiye wayar ta ta gyara zama ta ce" Ke , wai Akoy wani abu da kike tafe da shi ko kuma so kike yi mu baza rashin mutunci da ke a falon nan? Nafiya ki daina tunanin wani abu dan kina auren yaya, wallahi ba shi zai hana in shiga fatar jikin ki ba a kan rainin wayo, oh awon hawan jinni? A bakinki Malama, Ni dama na san ke din nan Bakya wani tsoron Allah, to awo dai na ciki ta je, ta tafi a auna mata ciki cikin haihuwa!"

Muhammad ya dan motsa saboda barci ya fara daukansa, Ama hayaniyar da ummulkhulsum ta fara ya sa ya kusa tashi

Nadiya kuwa wata irin zufa ke son Wanke mata fuska......., ku gane mana, cikin nan ai shine akace ya zube, wanda Najeeban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login