Showing 132001 words to 135000 words out of 144591 words

Chapter 45 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2336

ta ce" Dan Allah wai da gaske kike? Kan uba, Najeeba kece?......, koda yake ba abinda ya gagareki kin ga, kika kuma kirana kina min ihun ya tabaki sai na kara maki Allah!"

Najeeba ta turo baki tana basu baya hadi da kwontawa kasa kasa ta ce" Aikin banza idan nace sai ya sakeni ai sai ku bani hakuri, to ya sakeni wa ya iya da Ni? Ai sai ku yi!"

Karshe dai ukun ne suka ringa masifa sunna karawa, aunty zahra'u kuwa ta tare haba da hannaye bibiyu tana ta tunanin duniya, Najeeba kuwa tana jan carbn nan barci ya dauke ta Wan so take yi safiyar nan ta yi ta yi ta tabbatarwa Anmy ba wani asiri a hayacinta take.



SULTAN.

Sai da dare ya tsala sosai sannan ya iya Mikewa daga saman salaya ya nufi wayarsa karama dake ta ruri

Dagawa yayi a dakile ya ce" Wai kai meye? Issuhu ka bani lafiya baka ga dare yayi bane?"

Sultan Yusuf yayi dariya ya ce" Wa ya tabaka kake kirana da sunan issuhu? Me yasa kai baka gudun balaki ne?, YUSUF, YUSUF ne sunan ko kace YUSEF ka ji ?"


SULTAN SHAHEED ya ja jalabiyarsa ya cire ya kwonta saman gadonsa a hankali ya ce" Gy ina cikin wani hali, ana so a sa in fita a hayacina sosai da sosai"

SULTAN Yusuf ya ce" Subahanalah, me yake faruwa haka?, "


Sai da SULTAN ya ja numfashi, a hankali ya ce" Basu san irin abinda nake ji a duk abinda ya shafeta ba......, ba zasu gane ba lokacin a ja min rai da abinda ya shafeta bane....., ka san da cikina na nan man....?"


Sultan Yusuf ya tashi zaune yana furta" Masha Allah, alhamdulilah, to ba Shikenan fushin ya kare ba? Sai ka daina fushin ko?"

A hankali SULTAN ya ce" Dama na jima da daina fushin, itace ta yi, kuma yanzu ita din ma ta hakura Anmy ce ke son shiga tsakanin mata da mijinta "

YUSUF yayi dariya yana shafa kansa, a hankali ya ce" Bana tunanin Anmy zata yi haka dan cutarwa, a bata dama da dan lokaci a gani in sha Allah zata yi hakurin itama tunda giwarka ma ta sauko"

Sultan yayi dan murmushi yana lumshe kdannuwansa cen kasa ya furta" Allah ya aminta"

Fitar tasu bata yi tsayi ba saboda yadda SULTAN hankalinsa je rarrabe, a haka suka yi Salama , ya kwanta idannuwansa da zuciyarsa na hasaso masa Giwarsa......, ya Allah macen da ta san kanta duniya ce Elhaji, Allah ya karawa mata lafiya......a hankali ya sake yin murmushi yana tunanin inama ace tana nan a yanzu haka? Kai Allah sarki beebah.....cen cikin zuciyarsa ya ayyana 'Allah mun gode maka fa ka halicci mata, kuma ka bamu damar samun mata a matsayin abokan rayuwarmu......Ubangiji ka dada mana lafiyar da zamu amshi ganimar mata muma, Allah ka da muna da rabon samun na aljanna '.......
Sai kuma yayi wani murmushin yana lumshe idannuwansa cike da bege.




Washe gari da wuri wuri gidan ya ringa watsewa saboda du jirgi suka bi, wa'inda suke gari kuwa zuwa karfe goma suma du sun watse , ya rage baby da maman baby da mutanen gidan



Tunda safiya ta yi Najeeba ke zirga zirgar da za'a gane cewar a hayacinta take fa, sai dai wani tashin hankalin da ta gani Anmy ta saka ky ta datse hanyar da zata iya yin satar hanya ta je bangaren nata ma bale har su hadu, saboda tana kulewa ta rike ky din a hannunta sannan ta mugu mugun saka mata ido daga ita har shi, domin shima a lokacin da ya ga wannan lamari hankalinsa ya Wan tashi harma ya sake bada wani hakurin Ama sai Anmy ta yi masa birisss



A hankali a hankali bulalar Anmy ta fara neman gigitashi, saboda Yadda kiri kiri take kara dauko maganar a ba yarta takardar saki bayan ta san abu ne dake iya girgiza duniyar sa, dan kuwa yau kwana hudu kenan sunna cikin wannan dauki ba dadin su da ita, ta yi kememe ta kame ta nuna bata san zancen ba, hakan ya fara neman taba lafiyarsa shi, saboda du yadda zata bi dan ta hana Najeeba dogon tunani a kan lamarin ta bi , bata barinta zama da yinwa, bata barinta yin dogon Zama ita daya, idan ta samu ta gudu dakinsu ta kule sun kama vidio call kennan ita da shi tamkar sababin aure.

Kwonci tashi har lokacin awonta ya kawo , Anmy ta sanar mata cewar ya shirya bayan magariba zata je wajen likita a aunata kamar yadda likita tace zuwa lokacin abin cikin ya kai kusan wata hudu in sha Allah.

Tunda ta ji wannan batu sai ta kule a daki ta dauki wayar ta ta tura masa da sako dan ta san a lokacin ta yiwu yana tare da baki

Sakon na shigowa ya duba , bayan ya karanta ya samu kansa da sauke sansanyan ajiyar zuciya ya maida mata da amsar cewar shine zai kaita kafin a tausashe ya sake duban Abiey ya ce" da gaske Abiey, Anmy tace wai sai an bata bayan mu mun ce Bama so a yi maganar ma, PLZ do anfng Abiey"

Abiey da mamaki ya ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




48



Da mamaki Abiey ya ce" Ikon Allah, lafiyarta kalau kuwa? Ai ban san abinda ake ciki kenan ba, yaya za'a yi kai baba ka shiga cikin fadan yara? , hum barni da ita kai zan sameta"

SULTAN ya sauke boyayiyar ajiyar zuciya.........., a hankali ya ce" Na gode Abiey, Allah ya saka da alkhairi"

Abiey yayi murmushi kawai, tabas wata nutsuwa ta sake ratsa zuciyarsa da kwonciyar hankali, haka kuma zai sake zage dantse wajen bin yaran da addu'a, zai bi su da addu'ar fatan alkhairi duniya da kiyama......., shi fa da akace SULTAN ne ya karaso sai da ya Tsorata kar aje wani tashin hankali ne ya faru .............................

Sultan na duba lokaci ya mike a tausashe ya ce" Abiey, zan koma"

Abiey da ya mike shima ya ce" Mu je , nima ai fadar zan je, mamansu? Kina ina?"

Ummi ta fito tana amsawa fuskarta yalwace da murmushi

Abiey ya ce" Zan je in dawo, yauwa bani takardun odar nan da aka yi ta shagon kayan kicin din yarinyar nan in je in gama clrng din komai, kai Najeeba? Wai ka san rabonta da ta bi ta kan shagunan nan an kusa wata? Ko kira bata yi bale ta leka, dama lekawar nema take ta gagara dan ba lekawa take yi ba"

Yayi dan murmushi a tausashe ya ce" Abin ne ya mata yawa Abiey, zata leka a hankali in sha Allah , shi yasa ma ai ta raba muku ky din kai da Ummi da Dayabu "

Ummi ta yi yar dariya ta ce" Wai abu ya mata yawa, matarka dai sai ta sha bulala idan ta yi wasa, dan bata jin magana"

Murmushi yayi yana sada kai, kafin su fice Ummi na bin su da addu'a

Da mota daya jal suka zo dama, kuma motar ma irin mai bada sawun nan ce dan ko rawanin dake fuskarsa sasauka ne , shima ya dora ne kawai dan dare bai gama rufawa ba saboda madubin motar irin mai baki sidik din nan ne ba za'a iya gano wanda ke cikin motar Ba in ba yarda mutun yayi a ganshi ba ta hanyar sauke madubin

Abiey ya shige gaba yana duba takardun nan, sanyi kuwa na ratsa jikinsa da kanshin da motar ke dauke da shi, a haka amintacensa ya ja suka dauki hanyar fada.


Ta baya suka shige, kuma sunna shiga sai suka daura alwallah saboda sallah.

Bayan sun fito daga masallaci shi Abiey sai ya zauna tare da su malami sunna dan tattaunawa, shi kuwa sai ya shige cikin dan hanzari ya shirya ya fito ya nufi bangaren Anmy.


A bangaren Anmy kuwa, tunda ta shirya take duban Najeeba dake jan kafa, har sai da ta zarro mata ido sannan ta je ta shirya ta Wora katon hijabinta da nikaf din ta da su safarta bayan ta sake bin jikinta da turaruka kamar zata yiwa kanta wanka da su , tana ta duban wayarsa, sai dai ganin bai kirayeta ba sai kawai ta share ta bar wayar a nan ta fito da nufin su yi tafiyarsu kawai da Anmy

Sai dai tana fitowa ta samu abinda ya tsinka mata zuciya, sakamakon samun Abiey a zaune saman kujera, Anmy a zaunen itama, sai dai shi SULTAN da bata san shigowarsa ba yana duke daf da ?afafuwan Anmy kansa a kasa ya dafa kaffafuwan nata............

A tsorace ta Wan ja baya kirjinta na wata irin dokawa sannan ta saurara

Abiey a tausashe ya ce" Ki yi hakuri kanwata kin ji?, in dai ba kin san kina da wata hujjar da ta wuce dan kawai sun samu yar matsala a tsakaninsu bane to ina neman alfarmar a yi hakuri a barsu su yi tafiyarsu bangarensu su rayu da juna, kuskuren da ba'a so wanda za'a yi ne kuma a nuna a kan hanyar daidai ake babu wanda ya isa ya ce ba haka ba, ina ganin a duba a yi hakurin hakanan idan kuwa da wani dalili da yasa kike so zaman nasu ya tsaya iya nan PLZ Tell me"

A tsorace NAJEEBA ta dafe kirjinta, saboda ita bata taba tunanin cewar wani dalili ne zai sa Anmy tace kar su rayu da juna da ya wuce fushin da take yi da abinda ya faru, sai dai yanzu Abiey ya daga mata hankali ainun da maganar nan ta fito daga bakinsa, a hankali SULTAN ya dago idannuwansa da suke hargitse a hankali ya kalli fuskar Anmy ya ce" Anmy PLZ, i bg U, i'm so sorry, Anmy i lv yr Daughter, PLZ Anmy ki yafe min abinda na yi , in sha Allah zan kiyaye , PLZ Anmy"
Ya karashe yana dan rabar kansa da kafarta

ANMY ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" To ita ai saki take so, saboda irin yada kake abubuwanka kai sake......., wannan yaron wai ka gane dalilin da ya sa matarka ta yi fushin kuwa? Ko kuma ka dauki hakan sama sama irin yadda wasu mazan ke cewa mace kuwa, har sai an yi mata wani abu take haushi? Mace kuwa, har wani abin fada gareta? Wai Macen? ai bata da wata isa a duniya sama da ta yi biyayya wa abinda aka dorata ko menene, fada min ka fahimta?"

A hankali ya gyada kansa, a tausashe ya ce" Ni na fahimta Anmy, tana fushi ne saboda irin yadda da an fada min wani abin da ya shafeta na bacin rai nake hawa sama ba tare da bincike ko bata damar kare kanta ba sai in yarda da maganar da wani ya fada in yi ta daga mata hankali, Anmy ina yin haka ne dan a tunanina itace zata dauki kowani irin halina , itace kadai ta fi kusanci da kirjina , itace ta fi gane yarena koda ban bude baki na fada ba, ........a tunani a cikin launin fadana zata iya ware kalaman rarashina....., a tunani zata iya gane yanayin kaka naka yi a cikin furucina........, Anmy likitanta ce, tana da damar yi min bayanin abinda yake damunta idan ta ga kamar abin zai daga muku hankali, a haka na dauki lamarin , shi yasa a lokacin da ta min bayanin ma sai na yarda har hankalina ya tashi.."

Ya Wan saurara ya dubi Abiey a hankali ya ce" Abiey, kai ka san menene hukuncin zubar da ciki ko?, ba hukunci bane na barin mace a gidanta a tsarin masarautarmu, bayan horo mai tsanani na kurkuku za'a Salama mace ne...."

A hankali ya dubi Anmy ya ce" But, a cen kasan zuciyata na kasa........, tunda na baro asibiti barci ya gagareni, bale da na je wajen Nadiya ta idasa tabbatar min cewar eh sunna shan abinda na hana su sha din, sai na ji tamkar kirjina zai fashe dan tashin hankali.................., Anmy na zata zaki fi kowa gane abinda ya faru????????????"

Ya sauke ajiyar zuciya ya kai sau biyu sannan ya dora da fadin" kuma da na tarbeta da maganar sai ranta ya bace......., abinda ya kara dagula mana lamarin kenan saboda itama dole ranta zai bace, yaya za'a yi Ni da ya dace ace na fi kowa sanin matata Nine zan yarda da maganar ta zubar da cikin da muka fi kowa burin samu???????"

A hankali ya lumshe idannuwansa dan sassautawa kansa tashin hankali ya ce" idan abu ya zo a haden nan, Allah ne ke kawo saukinsa......, Ni abu daya na yi jira ta bude baki tace ta yarda ta zubar ta bani hakurin haka shikenan, ita kuma ta gama gane cewar idan a wannan karon ma ta amshi laifin da bata aikata ba ta ginawa kanta ramin ramin da zai zamo mata matsala saboda da wahala in kuma yarda da ita a duk wani abin da ya shafi lafiyarta ko ta yaranmu......., kamar yadda Malami ya kwatanta min"

Ya sake duban Abiey a hankali ya ce" Shi yasa na so ace, an bani dama na hukunta likitar nan yadda ya dace ta yada gobe idan wani ya tuna abinda ya faru zai ja baya da nufin shiga hurumin cikin gidana!"

ANMY ta yi murmushi a tausashe ta ce" Ba haka bane zai sa a kiyayi gidanka Aban Muhammadu, abinda zai sa a kiyayi gidanka kaine zaka rufe wannan kofar..., ba wai likita cen ba, ko Ni nan idan na zamo mai fitina da kawo maka sukar matanka a kan rashin gaskiya da son tayar da fitina sai dai ka saurareni dan baka da yada zaka yi da Ni ka yi murmushi kawai ka bani hakuri, Ama ka ga du wani na waje bashi da damar kawo maka hada zaka yi da gidanka........., babu mai wannan ikon, idan ba haka ba kuwa zaka ringa haduwa da bacin rai irin wannan, in ya zamo wani ne zai fada maka laifin matarka ka yarda? Za'a hadasa maka fitina ne a Barka da ita fa"

Kansa a kasa yana sauraron Anmy

Anmy ta Wora da fadin" Ka ga, zan fada a gaban babanka........, Ni gaskiya ban baka ita dan ta zama itace wace zaka kashe ka ba wasu damar jin dadinka ba, eh kwarai itace wace zata dubeka Ama kuma ba a abinda yake gaggawar tabamu mu mata ba, saboda bari ka ji in dire maka maganar nan gaba dayanta, idan kana yi mata irin haka zata ga to ita fa? Kenan ita ba mutun bace? Kenan ka fi son yar uwarta a kanta? Kenan ka fi yarda da maganar wace ba komai dinka ba a kan Tata, kenan tsabar rashin so da tsana ce suka sa bata da wani fada a ji a gaban ka? Kenan du wahalar da take yi dan ta birge ka , dan ta gyara zamanta na aure da kai, du a banza suke tafiya saboda abu kadan na iya sakawa ka wulakantata a gaban du wanda ya kama?........irin wannan abin kuwa na sakawa mu tsani zama da mutun ko wanene! Wallahi du tsananin son da muke masa sai mu hakura da shi........, PLZ ka saka wannan a kwakwaluwarka!"

Sultan ya daga kansa bayanan na shiga kansa sunna zaunawa da kyau da kyau

ANMY ta Wan yi shiru kafin ta ce " sai maganar maganin gyara"

Najeeba ta Wan leko a ranta ta ayyana ' na shiga uku '

ANMY ta ce " wannan yaron ina so ka gane cewar gyaran nan ba ila bane, Akoy wanda mace mai junna biyu ma zata yi anfani da shi bale kuma in bata da komai ......, Ama idan har kace zaka yi tsaye a kansu ka hana su gyara jikinsu matsala ce gagaruma, saboda ita Macen da take haihuwa, take rayuwa a gidan mijinta dole sai ana yi ana gyara wasu abubuwan dan a ci gaba da samun fahimtar juna a tsakani.......ka fahimta?"

Abiey ya girgiza kai a ransa yace" To ai Shikenan, shi damuwarsa kenan? Allah sarki shima zai nemi na gyaran gaba gaba in dai yana so ya ci gaba da daga murya a yi gaggawar dukawa a dakinsa, yau da gobe ne ai, Allah na tuba Ni da uwar yara ke dakawa ta gurmaza min in kafa kai? To yaya zamu yi da ranmu tunda dai an diga lamarin a rai dole an taya , idan an taya kuwa a yaba shi ya fi alkhairi..... Allah dai ya bada lafiya kawai.'

A tausashe SULTAN ya ce" Anmy, to ba ance yana haifar da Cancer ba?, an ce yana zubar da ciki, yana haifar da ciwon koda , an ce ma idan mace ta saba anfani da su wai......wai.......wai ba zata iya wata mu'amala ba sai da su, to in shekaru suka ja fa Anmy?"

Abiey ya talabe haba a ransa ya sake ayyana ' Ga abin fade ba halin in baje masa komai? Kai innalilahi, yaron nan baka san duniyar dadin kenan ba? To wani lokacin in ba kanshi kanshi danshi danshi, matsewar kam ba ai gayan tuwo aka baka, in aka kai shekarun da ba za'a anfana da abin ba kuwa ai Shikenan an sha dadi a baya......, Ni daga nan ma sai na samowa uwar yara kashin rakumin da ake iya dakawa na je mata da shi Wan na ga ta sayi zumar, da turaran salwa, lemun tsamin kuwa dama bata rabo da shi, in je mata da su mu hade hadin mu zartar da yada akace .........wannan abu da ba lada ma da mun yi mu kam, bale da lada? ALLAH ya sa ladansa ya kai mu aljana '

Anmy kuwa du yada take jin kunya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login