Showing 45001 words to 48000 words out of 144591 words

Chapter 16 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2349

sai an dawo daga rakiyarku kuma ku dawo ku nuna an tsane ku?.... Najeeba yawancin lokuta rashin hakuri, saurin fushi, tsayaya da miji, a nuna masa bai isa ba ko makamancin haka din nan na sakawa ka fita daga ran namiji, ke kin san mijinki yana son ki, Ama shine daga yin dan fada kin kirayemu kin daga mana hankali kin yanke jiki kin fadi, athmarki ta tashi, Allah Jiya da kin ga fuskar Mai DAMAGARAN sai kin tausaya masa, yana falon nan hannaye hade , magana ma da kyar yake yi, ki fa guji tayarwa da kanki hankali a kan maganar aure......, idan ma aure yace zai yi a kanki zata zauna ne? Bana tunanin zai auro wace zata zo ta shiga gabanki, meye to na daga hankalin?????"


Kusan hada baki sauran matan suka yi wajen furta" Aure kuma????"

Ya bi su da harare harda A'isha, ya nuna musu hannu ya ce" Bana son shashanci fa, ku kiyayeni, idan ban yiwa NAJEEBA wuji wuji ba , ba zata dawo hayacinta ba, auren, nace auren, a kanta zata zauna ne?????"

NAJEEBA da kanta ke kasa ta dago idannuwanta da suka cika da kwallah a hankali ta ce" Ama, ai ka bani dama ka ji ta bakina ko?"

Dayabu ya gala mata harara ya ce" Ina sauraron ki!"

NAJEEBA ta lumshe idanuwanta a sanyaye ta ce" Yaya, aure? Aurensa bai daga min hankali ba kamar yadda ya jingina da maganar da ba haka ba yake son nuna min lalle nice na janyo harma zai min kishiya!"

Muryarta da ta fara rawa ya sa A'isha saukowa ta rike hannunta tana kallon ta,

A hankali ta ce" Yaya, shekara takwas da aure ai ko yayane ka san ba zamu rasa yan fadace fadace na yau da kullum ba, wa'inda suke faruwa a duk wani zaman da ba munafurci, yaya na taba kiranka saboda wani abin makamancin haka na tayar maka da hankali?????, bari ka ji yaya akoy lokacin da matarsa ta min habaici a kan haihuwa....., a lokacin da na rama sai ya nuna ai ba haka take nufi ba, yaya za'a yi ta ce min haka.....a gabana a gabanta ya min sumul na kuwa bada hakuri aka ci gaba da rayuwa......., ta rike ?a?anta ina ji ina gani sai da kyar suka ci gaba da shigowa nan....karshe ko sati biyu ba'a yi ba da ta sake yi min wani abin a kan Aliyu......., Ama na yi shiru saboda ko na fada ya riga ya sakawa ransa nice mai fada, Ni ce mai rigima Bama ya tsayawa ya gane, nice abar harinsa, sai daga baya yake iya min sassaucin murya a lokacin da ya gama kona min zuciyata........"

Ta yi shiru hawaye na zubowa a gurbin idanuwanta ta Dube shi a sanyaye ta ce" duk me ake gani? Najeeba ce fa, ba'a tabbata Bama ta yi rigima bale an tabbata, Najeeba ce fa, ai nata da hakuri, Najeeba ce fa, du abinda aka fada ta gama aikatawa.....wannan dalilin ya sa shi SHAHEED, baya saurara min a duk lokacin da abinda ya faru ya kai kunnensa.....shi yasa na iya zama da shi nima nake kare mutuncin kaina bana yarda in daga murya dan na riga na san SHAHEED fa karfen kafata ne, tunda Allah ya jarabceni da auren Wan uwana jinina to kuwa sakamakon rashin jin da na yi ne zai fito a nan.....na kuma yarda na amince , a wajen Allah nake neman sauki ba mutun ba, shi yasa nake ci gaba da walwala duk da tarin kalubalen da Ni matar da ake yiwa kallon na gama dacewa nake haduwa da shi Wan kawai na zama matar da ta gama dacewa....."

Ta ja hanci sosai ta fuskanceshi ta ce" Yaya....., ban fa rasa ci , sha , sutura ba, ban rasa soyaya ba, ban rasa daraja ba, ban rasa girma ba, ban rasa sarauta ba.......sai dai Ni ce matakin takewar SHAHEED, Ni ce wace idan wani ya cewa SHAHEED na yi laifi yake bashi hakuri ya fatatakeni, Ni ce wace duk irin girman laifin da za'a cewa SHAHEED na aikata ba zai taba dubana ba sai ya fara duban wanda ya fada harma ya gaskata shi.....yaya,....YAYA , yaya za'a ce SHAHEED ya fake da wannan ya nuna min dalilin wannan zai yi aure?????, yaya za'a yi SHAHEED ya ci gaba da musguna min dan kawai ya san ya gama samun power da yake so a kaina????? "

Dayabu dake dubanta ya ce" Najeeba, kin san bana son koke koken nan ko?????, to wai har yanzu dai maganar auren kamar ita ta fi damunki.........., wacece zai aura? Har akoy macen da zata daga maki hankali ne dan yaya zai aureta?????"

NAJEEBA ta dage kafadu ta ce" Na fada maka ba a kan aurensa bane......., babu abinda ya shafeni da wace zai aura, na fi damuwa da damuwar dake gabana a yanzu wace wallahi ba zan yarda ba, ......yaya Dayabu tunda aka rikeni a asibiti da ya zo ya fice daga asibiti bamu kara samun zaman lafiya ba!"

Zahra'u dake kallon ta ta ce" Ban gane ba"

NAJEEBA ta dubeta ta ce" Tunda ya je, likita ta ganshi a kan ciwona bai kuma bi ta kaina ba ya dawo gida..... Tun daga lokacin maganar kirki bata shiga tsakanina da shi ba, wai an ce masa maganin mata da nake anfani da shi ya zubar masa da ciki....., yana cikin wannan fadan kuma ya sake shigo min da maganar nace zan dauko likita dan kishina.....yaya gaba daya ma sai tunanina ya raja'a kan, niya yayi zai yi aurensa shine yake neman laifina ido rufe......, to wallahi sai dai ya ci kansa dan kuwa ta nan ba zai samu abinda yake so ba, nice nan zan dauko masa matar idan ma zinariyar ce Ni zan dauko masa ita in kawota......, wani irin wulakancinsa ne ban gani ba a kan aure? Ni ce farkon abar harinsa a duniyar aure......, dan na zamo a tsakiyar farin cikinsa ba zai dame Ni ba!, abu daya ne ba zan yarda ba, maganar cewa Ni na zubar da cikina....., yaya wallahi a tsakanin DOCTER MUHSEEN da DOCTER IZRANE sai an fitar min da wanda yayi bayanin nan ya fito da takardun da aka auna Ni ya nuna min sawun maganin da ya gani an ba wani likitan ya duba....., tabasss sai an gano min wanda ya zubar min da ciki na, sannan sai Malami ya min bayanin dalilin da ya sa aka yi min raini mai girman da har zan yi aike a sanarwa da mai martaba bayan ba aiken kisa na yi ba, ba na sata ba, ba na maita ba, ba kuma na kwartanci ba!"

Umi dake dan murkususu da dan karfi ta ce" ke, wai wani dan balaja'un ne zai ce ke kika zubar da ciki.....?"

Gaba daya suka kaleta saboda yadda ta yi magana tana jan harufa

NAJEEBA ta watsa hannaye ta ce" shi ne mana!"

Dayabu ya ja kira ya salamce ya nuno su da yatsa ya ce" kun ga, du abinda za'a yi ku kiyayi fadin maganganu irin wadinan a kanshi, ko ba komai baban yaya uba ne, kar ku yarda ku ce a fadar shi zaku ringa maganganun nan, dan wallahi bana jin za'a iya amsar mu....., bayan wannan ke Najeeba ki min Magana yadda zan gane, wani shegen ne ya ce ke kika zubar da ciki???"

NAJEEBA ta gyara zama tana duban yaya Dayabu ta ce" Shine fa, shi SHAHEED din!!!"

Da sauri yaya Dayabu ya ce" Astagfrullah, Astagfrullah, ke ba zaki daina Shari ba? Ba yaya SHAHEED nake nufi da maganata ba, wanda ya fada masa nake son ji Bana son iya shege! "

NAJEEBA ta ce" to yaya Dayabu Ni ai shi ya fada min, kuma ya ki yarda in bincika, abinda na sani shine in a ina ya ji maganar nan a asibiti ne, kuma harta Jakadiya tana tune da wani magani da likitar nan ta bani"

Ummukulsum ta ce" Wai wace likita? To a kan me ba za'a kirawo su , su zo a zauna a yi magana ba? Haba, ai ko mahaukaci ya san Najeeba na son haihuwa ba zata taba zubar da cikinta ba!"

NAJEEBA ta ce" Ummu, ai ya ki a zauna din, du yadda na so na ganar da shi cewa ban zubar ba ya nuna na zubar kuma sai na yarda cewar na zubar sannan zamu shirya, kenan so yake yi a wannan karron ma dan kawai ya nuna karfinsa a kaina, in yarda da laifin da ba nawa ba kamar yadda yake min wasu lokutan a kan wannan maganar mai girma??? Na rantse in na yarda ubana goma!"

Zahra'u ta murguda baki ta ce" Ke ji wani rainin hankali a wajen likitocin nan, to wallahi ba zai yiwu ba, tashi zaki yi mu je asibitin, kamar yaya ki yarda cewa kin zubar da ciki? To shi yaya a me ya dauke ki? Mutun mai fada daban, makashin rai daban ai, ba za'a taba hada su ba, to wai ina girman sani irin na yaya ne? Cabdijan zuwa zamu yi a bamu komai a bayyane idan ya so in ta kama mu daukaka kara sai mu daukaka, wallahi harta vidion cctv sai an bamu, a girman asibitin da kuke zuwa ta fi karfin cctv Camera, ai yanzu da ilimi ake abu wallahi ba fa zamu yarda ba"

Dayabu zai yi magana ANMY ta shigo tana gana, ummulkhair na biye da ita kanta a kasa sumui sumui......

Sunna shigowa ANMY ta ja ta tsaya tana bin su da kallo

Da sauri Dayabu ya mike yana fadin" Kun dai ji, ku wuce in mayar da kowace dakinta!"

ANMY ta bi shi da kallo kafin ta girgiza kai ta ce" yaushe ka zama munafiki kuma? Ka dawo ka zauna ko in tsinke darajar fuskarka yanzun nan......, kai me yake faruwa a nan......., yanzu nake son ji!"

Gaba daya suka shiga kame kame................

Wanda hakan ya hasala Anmy, ta juya zata yi tafiyarta

Da sauri Dayabu ya riko hannunta, hakama Najeeba ta mike ta kamo hannun ANMY tana kokarin fashewa da kuka, ANMY ranta bace ta ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




15


Alhamdulilah, karshen free page........sai mu hade a gidan yan gata=??>?#?>??





Jikin Najeeba ya kara yin sanyi......., hakama na yan uwanta...., du yadda suka so ficewa a gidan abin ya gagaresu, karshema ummi na jin cewa sun zo ta zo gidan ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har sai da ta gaji dan kanta ta kyale saboda du yadda ANMY ta so ta kyale kiyawa ta yi sai da ta musu wankin baban bargo sannan ta yi shiru.......

A lokacin sallar magariba ne ta karaso, du suka shige tsohon dakinsu na gidan dan su gabatar da Sallah , haka suma su ANMY suka shige dakin ANMY dan su gabatar da sallar


Sunna shiga daki Najeeba ta kai zaune tana rintse ido saboda juwar dake dibanta, a hankali ta ce" Ku shirya ku juya gobe dan Allah, bana son abinda zai sa mu bata musu rai"

Umi karama ta dubeta ta ce" Kin san Allah, tunda nakudata ta kwonta hankalina ya dawo jikina, sai mun san abinda yake faruwa zamu tafi, to wai ke yaushe kika zama shashasha irin haka????"

Ummulkhair ta ce" Ke yayarki ce kar ki zageta "

Zahra'u da takaici ta ce " Ni da kaina da ake yiwa kallon mai sanyi a cikinku ba zan dauki laifin da ban yi ba sai ke? Me ya same ki? Yaushe kika zube haka????, Nadiya? Kenan har Nadiya take gasa maki aya a hannu kina kallon ta ba zaki dirtse yar buro'uba ki sakata a hayacinta ba????"

Najeeba ta lumshe idanuwanta tana girgiza kai, wato ba zasu taba gane halin da take ciki ba a yanzu......, sai dai da sun san irin abinda ke ranta a yanzu da sun tsorata, tabas da sun ji tsoro, Ama ba komai......gaba daya ya fice mata a rai, gaba daya wani irin haushinsa take ji

Ummulkhair ta sassauta murya sosai ta ce" Ba fa kyalewa zamu yi ba, wallahi ko da hannun uban waye a wannan abin sai inda karfin mu ya kare, dan kuwa ba zai yiwu ba, Ni maganar likitar nan da ta baki magani ya fi damuna, wai har ta isa ta ringa magana da yaya? A kan abinda ya shafi lafiyarki????, yaushe kuka yarda ta samu wannan wajen a cikin gidan aurenku? Akoy wanda ya isa ya samu kusanci da kijinku sama da ku ne????"

Najeeba da dan karfi ta ce" Wai yaya kuke so in yi? Likitar nan da kuke magana a kanta tunda nake bata taba dubani mai sunan dubawa ba sai sanadiyar zubar da jinin Nan da na yi, likitar Nadiya ce, ita ke amsar haihuwar Nadiya, kuma du wani abinda ya damu nadiyar shi take fadawa, inaga shi yasa nima ta min wannan gangancin, Ama na rantse koda an gane cewar ba a asibitin su aka min sanadiyar cikina ba na kare da asibitin nan da kuma likitocin cikinsa! Dan babu wanda zai min iko da rayuwa ina ji ina gani!"

Ummukulsum ta ce" Ban gane ba, bayan su kina zargin wani da zubar da cikin ne???"

Najeeba ta dubeta, a hankali ta dauke kanta, ta musu alamun lokacin sallah sannan ta ce" Shi uban cikin nake zarginsa da haka, saboda daga Sangarensa na fito da ciwon cikin"

Zahra'u ta zarro ido ta ce " Ke ubanki, shi zaki ma Shari? Yaya za'a yi ya zubar da cikinsa?"

Najeeba ta dafe haba, ta ce" Ba zaki gane ba, aikin banza kawai, wallahi ku kiyayeni idan ba haka ba mu daku da ku a dakin nan"

Ummukulsum ta sakar mata harara ta ce" Sai ku maida hankali, dama ai mu kin gama raina mana wayo, ga cen wa'inda ya dace ki shaka ama kina nan kina faman yi musu kuka....., ba laifi,sai dai ki sani, ko maganar auren da zai karra ba kyalewa zamu yi ba, ko yar gidan uban waye muna nan sai an kawota mun ga kalar takunta kafin mu bar gidan dan na kula ke kam baki iya so ba, sai kace ba nan kike sakamu da ihun Bakya sonsa ba, Shikenan ya saka ki a daki ya gama yi maki wayo yanzu har kin fi shi iya soyayar.......aikin banza, soyayar nan taki ai bana kaunar irinta gaskiya saboda tana tafe da rashin sannin ciwon kai"

Da ido kawai ta bita a lokacin da zahra'u ta fito daure da alwallah ita kuma ta shige

Ajiyar zuciya ta sauke tana zaune har suka gama shiga da fitar sannan ta mike itama ta shiga ta dauro alwallar ta dawo saman salaya ta kabbarta sallar.......

Bayan sun gama gaba dayansu sunna saman darduma ne rike da carbi, har suka gabatar da sallar isha'i sannan suka sake baje kolin wata firar, ko ta kan cikinsu basa bi, kowace na fadin abinda ya taSa shiga tsakaninta da abokiyar zamanta ko wani wanda Allah ya haWa zamansu tare da irin yadda ta kwaci kanta....du dan su sake zaburar da Najeeba ne, wace ke kallonsu kawai....., a ranta cike da murmushi da tunanin tabasssss da ace sun san irin alwashin da ta daukarwa kanta a kan SHAHEED da duk wani wanda ya shafi damuwarta da sun tsorata da lamarin nan, sai dai ba komai idan har ta aikata kowa zai ji ya gani!


Sunna cikin firar nan Andiya ta shigo ta sanar da su akace su fito su duka falo

Kasa kasa zahra'u ta ce" Andiya su waye a falon? Kai na shiga uku da girmana kun ja min yau da wahala mu kubuta a hannun Aba"

Andiya ta ce" Aunty zahra'u su Dady ne, da su Aba, harda su yaya Dayabu"

Umi ta ja filo zata KWONTA , ummulkhair ta ce " Wallahi tashi zaki yi, ubanda ya kawo ki gidan nan sai an hade har ke an ci uba, ai ba mu kadai ne muka yi rashin jin ba, tashi Malama"

Du mikewa suka yi kowace na gyara zaman hijabinta, Najeeba na kallonsu sai kuma ta yi murmushi domin a duniya idan ta ga irin yadda suke tsoron SHAHEED sai ta ji wani dadi na rufeta....., shine kadai mutumen da su suke tsoro ita kuma bata tsoro.... Allah kenan .


Gaba dayan nasu suka nufi falon, sai dai sun samu falon ana ta kayaniyar magana tsakanin ANMY, da Yaya MUTALAB, da ummi baba, ya zamo sun saka ANMY a tsakiya idan ta fada sai su maida mata martanin maganarta, sunna zaune su duka a Babar kujerar 3str, shi kuwa yana zaune a kujera mai zaman mutun daya kansa a kasa....., Yaya Dayabu a zaune a saman kafet kansa a kasa yana sauraron rigimar da ake yi, domin tunda ya shigo tare da Aba ANMY ta rufe shi da fada inda take shiga ba ta nan take fita ba, fada take yi a kan wani dalili zai tsiro aure a yanzu da suke cikin rigima da matarsa? Ita ba zata yarda ba, sai sun ganewa junna sannan inma maganar auren ce sai a dauko maganar, Ama haka kawai ba zata taba zuba masa ido ya nemi daga hankalinsa da na iyalinsa uwa uba yayi abu a cikin fushi ya janyowa kansa wata fitinar....., shine fa ya dukar da kansa ya bata hakuri hadi da fadin zai yi yadda tace din, Ama sai ummi ta tare tace atafau ba za'a yiwa wannan magana biyaya ba saboda aure akace ai ba laifi ba, karma ta sakawa yarinyarta wanan abin a rai dan wallahi tsaf zata iya janyo mata wata fitinar...., shima Aba sai ya ga ai yaushema dan zai yi aure za'a saka shi a gaba da wannan maganar? Yau ko wanda bai kai shi daraja da matsayi ba yana iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login