Showing 78001 words to 81000 words out of 144591 words

Chapter 27 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2342

zamu yi? Ko gidan yaya zamu je?"

Nanma shiru yayi kansa a kasa, cike da tunani da jimami da rashin madafa, yaya? To yayan nasa fa a raye, kuma da rufin asiri, Ama shi da kansa rabonsa da ya leko shi irin a tsaitsayen nan ma an fi shekara, tun wani kaishi asibiti da yayi ya dawo da shi ya yar saboda makudan kudadan da akace za'a zuba a masa aikin bayansa saboda likita ya tabbatar idan har aka yi zai iya samun lafiya a hankali a hankali, tunda ya dawo da shi ya ajiye yace kawai a yi hakuri shi bashi da halin nema masa lafiya da kudaden nan, abinda kila wa kala ne ana iya zuba kudin kuma a zo a mutu ko aikin ya ki yi Shikenan an yi asara? Gwara kawai a yi hakuri , tun daga lokacin ko shi ko iyalinsa bai kuma ganin kowa a nan ba

A raunane yace" Tashi ki bata maganin, ki shafeta da man zafi, ki rufo gidan ku shige ciki ku rufe ku kwonta, idan har Allah ya sa mun waye lafiya basu shigo mana cikin dare ba sai ki SAKANI a baron mu je inda ya dace, domin na tabbata idan muka je za'a shiga tsakaninmu da su koda kuwa yarinyar nan karya take yi za'a yi mata uzuri a duba lalurar kunnenta sannan a mana tsakani da su, Allah ya shiga tsakaninmu da su"

Inna ta mike ta je ta rufo gidan jikinta na rawa, ta dawo ta dauki ruwa a kwanon shan ruwa na roba da suke da shi, ta gyara masa kwonciyarsa ta kula masa gidan sauronsa da komai da komai sannan ta bashi fitilar hannunsa da makamin da yake sakawa kusan kanshi tamkar wanda zai iya tashi ya bige wani, rayuwa kenan du irin yadda yake cikin halin ciwo a kullum yana iya kokarinsa dan kawo tsari ga iyalinsa........,

Jiki a mace ta ce" Baffansu, ina ne zamu je? Ko wajen polisawa?"

Ya girgiza kansa a hankali ya ce" Haba, ina muka ga kudin shigar da kara, in takardar da za'a kirawo wanda muka kawo karar ce aka kai, ya zamo ana ganin tufafin jikinsu da namu za'a ce hasada ce ko zafin talauci zai kai mu yi musu Shari?, ai kafin a gama bincike a gane muna da gaskiya aikin gama ya riga da ya gama saboda kamar na san duk tsiya a yau ba za'a yita ta kare ba....., inarsu wajen da kafin a ji abinda yake faruwar mai faruwa ta faru? Ke dai ki bari mu je inda koda bamu da sisin shigar da karan ake iya jin matsalarmu , sannan a tura a zo da kai koda baka shirya zuwan ba, Zamu je ne gidan da za'a zaunar da kowa a lokacin da aka zo da damuwa a ba kowa hakinsa, in sha Allah zamu je wajen MAI DAMAGARAN ne Allah ya sa mu samu ganinsa "

Kai Inna ta gyada, a haka ta mike ta shige dakin , sai dai ta kasa saka sakata gaba daya hankalinta a kansa , tausayinsa ya fi komai damunta, bayan ta ba kurma maganin ta bata sauran kokon da suka sha ta haye salaya ta shiga gabatar da Sallah tana ta fadawa Allah damuwarta....., da ta ji wani motsin kuwa sai ta ji gabanta ya fadi a haka har asubahi ta yi ba tare da ta rintsa ba, kuma wani ikon Allah bata jin barcin ko kadan domin idanuwanta sun gama kekyashewa .

Tun da safiya ta yi, ta dake bale sauran maganin ta ba kurma ta sha, zuwa yanzu gefen bakin kurma har ya zumgume, gaba daya bata cikin hayacinta, haka dai mamansu ta samu ta kunna ciyayi ta dake dama musu sauran gasarar da take da ita ta zubawa kowa

Kafin suke gama sha ta samu ta goge mijinta bayan ta kai shi yayi duk wata bukata tashi ta saka masa jalabiyarsa dake ajiye wace rabonsa da sakata tunda yayansa ya kai shi asibitin nan

Takardu ta zuba a karamin baron nasu ta gyara ta Wora tsohon bargonta a ninke sannan ta kuma kamawa ta dora shi ta yada ya dan dago saboda filo din da ta saka masa shima ta bashi kokon sannan ta sake dukawa a gefe tana jira su gama

Tausayinta yake ji, yana yin kuka fiye da sau uku a wuni idan ya dubeta, har tsufan dole ya kamata, shi dama ba'a magana jikinsa sai fata da abinda ba za'a rasa ba, a lokacin da aka zo da maganar aikatau din y'arsu da kyar ya amince, sai gashi da albashinta ne mamanta take samu tana yar sana'ar kayan miya harma ta sama musu kwaki da abinda ba za'a rasa ba na ci, domin sun jima da nema dan kyalkyali sai dan a samu a rayu, Ama kuma sun sani bakin da Allah ya tsaga ba zai Hanna masa abinci ba.


Kasa sha yayi shi din ma, yana kallon yaran yadda suke sha kamar sun samu wani abin dadi, ga kurma itama da kyar take turawa, har suka gama suka saka hijabansu, namijin ya ya koma daga gaba yana jan igiyar, mahaifiyarsu na turawa, su kuma suka daure fuskokinsu da dan kwali, bale kurma dan duk a tsorace suke, suka bi lunguna dan saduwa da Fadar DAMAGARAN!






Kaka kara kaka>??>??>??>??>??
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




26





A lokacin da suka karaso hanyar da jama'a ke bi dan shiga fada aka fara tare su a Babar kofar nan suka sanar cewa sun zo kawo kara ne, hakan ya sa aka basu damar shiga bayan sun cire takalman su a nan kofa sun ajiye suka ci gaba da tura shi suka nufi ciki da shi

A kofar da ake shigar da karan sai da suka jima a tsaye kafin ake basu damar shiga, a nan din ma takarda ce suka karba ta ganin Malami sannan suka sake zuwa suka yi zugum zugum sunna jiran lokacin da zasu samu ganin Malami domin sai ya gama da su shamaki yake fitowa, adadin mutanen da shamaki ya dauka kamar yadda bukatar sarki take na shari'ar da Sarki ne zai gabatar idan ya zauna ya fara cira takardar da zai ba mutane ta samun Shari'a a yau har sai ya gama, a cikin takardun kuwa Akoy wa'inda suke jira a gama tasu Shari'ar da wa'inda sun yi zuwa hudu ma basu samu ba saboda mutane, ana duba girman abinda ya kawoka ne, idan har kana da bukatarta yanzu yanzu sai a baka dama, sannan a cikin ake ware ta Sarki sannan a bar wace zasu gabatar su saboda daga yanayin girman munin abu ne ake gabatar da Shari'ar.

Cen kusan karfe goma sha biyu Shamaki ya zo ya samu Malami dan ya sanar da shi cewar a yau fa Mai DAMAGARAN yace ba zai yi Shari'a ba, dan haka ya dauki kowace su gabatar

Malami ya amsa da girmamawa sannan ya soke takardar da ake cirawa mai son gannin Mai Martaba, yana tunanin yau Mai WUKAR YANKA yana da bukatar hutawa ne.

Kofar da yake samun baki ya karasa ya bude ya shige sannan dogarai suka shiga nasu aikin suma sunna saka tsari, ana saka mutane da daidaya, har aka yi sallar azahar ya fito du suka je suka gabatar suka dawo sannan ya dora da karba dan yau mutanen ba laifi da yawansu, a haka har aka zo kan su kurma da babanta da innarta

Sai da dogari ya kama suka saka baron babanta ana ta yi musu addu'ar samun sauki sannan suka samu ganin Malami

Kasancewar babanta baya iya daga murya, Inna ce aka umarta ta yi bayanin abinda yake tafe da su.........

Bayan ta nuna kurma ta fadi iya abinda ta sani wanda kurmar ce ta fada musu sannan ta Wora da fadin" Allah ya karra maka lafiya, mu bamu da kowa bamu da komai sai Allah, ba zamu iya da rigimar masu kuWi ba, dan Allah mun nufo nan ne ba dan mun gaskata bayanan yarinyar nan ba, a'a sai dan a taimaka a yi mana tsakani da iyayen gidanta ko ma samu hankalinmu ya KWONTA , domin tunda ta zo Jiya take zabura tana ihun wai Hajiya Turai tace sai ta kasheta idan bata yi aiki ba, tsoro muke yi kar a biyo mu a ilatamu cikin duhu"

Tunda suka koro da bayanin nan shamaki yayi tsam yana duban su, yana rubuta takardar dake gabansa yana sake nazartarsu,

Tabas yannayinsu bai masa kama da wa'inda za'a iya siya su zo su aikata haka ba, to ko yana tunanin ana iya siyan nasu wa kenan zai siye su dan su yiwa matar da ake cikin rigima da ita Shari? Ai itace masharanciya dan nan jiya ta sa aka gurfanar da mai baban daki, karshe dai nan suka bar abin magana a fada domin haka ake ta mamakin ina hadin wannan mata da SULTAN? Gaba daya zancen da ace zasu samu damar daga shi da sun jima da dagawa, dan sun san ba wannan fuskar ne kowa sai dai yayi jajensa da abokin jajantawarsa

Yana duban kurma da irin yadda fuskarta ta yi ya dubi mahaifiyarta da mahaifinta , kanenta kuwa dama a kofa suka zauna
Ya ce" Kun san cewa maganar da kuke tafe da ita magana ce mai girma da daraja da mahimmanci ko? Magana ce da idan aka tsayar da ku a duk inda ya dace zaku fadeta? Kun tabbata baku hada baki da wani dan kawo wannan zancen ba? Ku kula, Bama abu kai sake, ko menene zamu bincika bale abinda ya shafi mai baban daki ake magana"

Inna ta sada kai, a raunane ta ce" Allah ya kara maka lafiya, mu dai bamu san likitar da wannan yarinyar take magana a kanta ba, hasalima uwar dakin nata kanta bamu da sabon da zamu iya cewa ga halinta...., sai dai ita yarinyar tamu muna da yakinin da wahala ta zo a irin yanayin da ta zo kuma ace karya take fada, sai dai muna neman alfarma, idan har karyar ce a yafe mata, mu burinmu kawai a shiga tsakaninmu da uwar dakin nata"

Malami ya mike ya ce" Ina zuwa"

Ciki ya shige ya ciro wayarsa yayi kiran layin shamaki

Bugu biyu ya daga, cikin nutsuwa ya sanarwa shamaki abinda yake faruwa

Shamaki ya mike tsaye yana fitar da ido ya ce" sunna nan dakin amsar baki?"

Malami ya tabbatar masa cewa sunna nan

Shamaki ya ce" A zaunar da su, yanzu zan iso maka da sakon abinda mai baban daki zata yanke"

Daga haka suka yi salama, Malami ya fito ya bada umarnin a sanyo musu kujeru da ?a?ansu su zauna

Hakama shamaki a lokacin ya mike ya nufi bangaren Anmy ya nemi ganinta

Bai sha wahala ba Anmy ta bada damar ya shigo, ya zauna cike da girmamawa ya sanar mata abinda yake faruwa......

ANMY zuciyarta dai da ta buga, tana dubansa ta ce" Idan aka fito daga sallar la'asar a zo da su nan lalle a tabbatar an zo da su"

Shamaki ya amsa sannan ya fice

Anmy ta mike jikin ta har neman yi rawa yake yi, ta je ta dauki wayarta ta yi kiran layin SULTAN wanda su ne kawai ke samunsa da NUMBAR

Bata jima tana RINGIN ba ya daga

Anmy ta sanar da shi bayan sallar la'asar ya zo falonta direct

Ba tare da ya Musa ba ya amsata sannan suka ajiye zuciyarsa cike da tunanin ko lafiya?

Anmy bata yi kasa da gwuiwa ba ta nemi layin Abiey ta sanar masa shima ya zo din, sai dai Abiey ya titsiyeta da tambayar ko lafiya? Ta kuwa sanar masa abinda yake faruwa, hakan ya sa yayi murmushi kawai ya ce" Balkissa, tunda so kike yi lalle sai an wanke y'arki ba zan hana ba, Ama menene na sai mun zo an yi a gaban mu?"

Anmy ta ce" Ina so ne ku zama shaida sannan kowa ya bata hakuri, saboda an gigita min yarinya , an ci zalinta, an wulakantata a kan laifin da bata aikata ba, "

Abiey ya ce" Waye zai bata hakurin to a cikinmu? Ai kawai ita zata bada hakurin ma gaskiya idan na zo wajen"

Ganin ba fa zai bata hadin kai ba ta kashe tana fushi ta ajiye wayar sannan ta karasa dakin ya'yan nata ta bude ta shiga ta same su sunna fira

Murmushi ta yi saboda yada ta samu Najeeba kwonce saman kansu ta Worawa kowa kafa wani hannu , sunna fira , ga Muhammad cen kasa yana buga game, shi kuwa Abdallah yana ringeshe yana karanta litafi , sai kuma su Andiya dake yiwa Auta kitso

Gaba daya suke gaishe da Anmy din kamar wa'inda suka wuni basu hadu ba

Tana murmushi cike da farin cikin ganin ya'yan gaba daya cikin walwala ta ce" Najeeba, idan an fito sallar la'asar ki zo falo zamu zauna "

Najeeba ta dago ta dubi Anmy zuciyarta na neman sake cinkushewa a ranta tana ayyana ' Me kuma na yi Ni Najeeba na shiga uku da yawan karana da ake kawowa Anmy baiwar Allah, ya dace in sama mata lafiya itama ta huta ace kullum sai an sakata gaba an ce na yi???"

A tausashe ta ce" To anmy Allah ya amince"

Daga haka anmy ta fice, ya zamo yan uwanta na kallon kallo cikinsu cike da magana Ama wanzuwar su Muhammad a wajen ya sa kowa ya rike abinsa a cikinsa , dan yaran kana fara maganar da ta shafi mahaifinsu suke nuna maka a ido da yanayin fuskarsu cewar ba zasu dauka ba, shi yasa ma ko mamansu bata wannan , haka suke yiwa mahaifinsu domin koda wasa ya dan nuna fushi a gabansu a kan mamansu sai su tsaya sunna kalonsa, wannan dalilin ya sa shima yayi waje gefe ya ajiye lokacin da yake iya yi mata fada ba tare da sun gani ba gudun kar su dauki wata dabi'a ko su tsane shi da tunanin ko ya tsani mamansu ne

Zahra'u ce ta fara mikewa ta fice tana yafito Najeeba

Najeeba ta mike ta ji bayanta a wayance, ta sameta a coridor

Tana fitowa ta ce" Najeeba kar dai zaman nan da za'a yi wannan yar balakin ce ta kuma kawo karar ki?"

Najeeba ta Wan langwabar da kai ta ce" Kila, ta yiwu na yi mata wani abin ne"

Zahra'u ta dubeta ta ce" Yaushe kika fita bale ki mata wani abin? Mtsss Ni wallahi yarinyar nan haushi take bani, saboda batama san kanta ba, haka ake yi ne? Ai sai ki fita daga ran mijin da zaki aura din, ace mace sai shegen kawo kara da dan banzan Shari??????"

Najeeba ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce " Irinsu sun fi birge shi, ba zai tsaneta ba, kina gannin yadda yake mata yaki, tsorona yake ji da ita, na san gudu yake kar in kashe masa ita"

Zahra'u ta dubeta da sauri ta ce" Ke fa wani lokacin kin iya shari, kuma yayan ne zai ce haka?"

Najeeba ta yi murmushi, ta girgiza kai kafin ta ce" Ba zaki gane ba, ina fatan idan aka zauna din nan in tace na mata wani laifin ya sake Ni Shikenan, kin ga na bashi lafiya kuma na ba matarsa lafiya, Shikenan sai hankalin kowa ya KWONTA, "

Zahra'u ta rike hannunta tana dubanta ta ce" ina so ki cire wannan tunanin a ranki, domin kin san dai duk rintsi ba za'a taba baki goyon bayan haka ba, ke in kamo maki tun daga kan manya har zuwa Auta babu wanda zai goyi bayan ki, shi din da kansa ba zai taba sakinki saboda wannan dan abin ba, to kuwa ki ba kanki lafiya shi ya fi alkhairi, "

Najeeba ta dubeta itama ta ce " Aunty, kenan ba zaku tayani yakin nan ba? Har ku ba zaku kama min ba???"

Zahra'u ta tabbatar mata maganar tana fadin" Wani yaki? Ai Bama zamu fara ba, idan ke MIJINKI ne kar ki manta mu yayanmu ne, Sarkin garin mu ne, muna da wani abu da muka isa mu masa ne ? Ke dai kawai a samu masalaha a yi hakuri, wannan mata da zai auro mu taya shi da addu'a kar aje ta watsa masa gida, idan an jima bayan sallah in sha Allah sai mu yi tafiyarmu a duba mana ke, idan aka tabbatar da cikin nan na tabbata zai daina fushi da ke, sai ki komawarki dakinki ba Shikenan ba?"

Najeeba ta zuba mata ido, a zuciyarta kuwa tana ayyana ' Shikenan idan aka ce masa da cikin sai ya fasa fushin ya dawo mu yi yaya! ? Shikenan kawai sai ya dawo in ci gaba da zuwa turaka mu ci gaba da mu'amalantar junna bayan na san a haka din ma ba tsira zan yi ba? Kowani lokaci wata na iya lakaba min wani sharin ya hau ya zauna? Shikenan sai in zauna in ci gaba da shirin amsar matar da ta bani maganin da ya jijiga min abinda yake cikina?, Shikenan sai in ci gaba da zama da mutumen da yake iya yiwa kowa uzuri banda Ni dan kawai yana sarki kuma yayanmu????, to ai ku yake yayanku Ama Ni a SHAHEED daga dinsa na san shi, .............hum, lalle kuwa idan lokacin in kwaci kan nawa ya zo zan san hanyar da zan bi in kwaci kan nawa, ba zan neme ku ba saboda ga haza na gani ku din nan ba zaku bani goyon baya ba, bale kuma yaya Dayabu, dan wajen Ummi idan ma na nufa Ni na san sai ta nada min duka kafin ta dawo da Ni inda yake, Shikenan shi auren zumuncin dama haka ne? Gaba daya komai a kanka yake karewa? Kuma ba damar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login