Showing 90001 words to 93000 words out of 144591 words

Chapter 31 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2354

mahaifinta bane Aban Abdallah, kai mijinta ne......"

"Aban Abdallah ka san kuwa irin karfin kusancin zuciya biyu?, ka san menene ribar ace ana son mace? Ka san macen da ta isa a wajen mijinta ba daya take da Macen da bata isa da komai ba?, ka kuwa san cewa kudi, mulki, ko kyau ba sunne kaWai gishirin zaman aure ba?, du irin yadda mace zata yiwa namiji biyayya, du irin yadda namiji yake tunanin ya isa da mace idan har ya zamo macen nan na tunanin babu wata isa da take da shi a wajensa, a hankali a hankali sai an wayi gari yace miko min hula tace dauko abinka mana, saboda a tsayin tafiyarsu har yau da gobe ta cin musu bai ankara ba, har sai an je inda ba za'a iya gyarawa ba, kuma ace ta lalace har a yi mata kirarin ta raina mijinta......?, Aban Abdallah zumuncin dake tsakaninka da ita ne ko kuma kai salon taka soyayar ce haka ya zamo kowa na iya fada ka yarda banda ita......????"
Anmy ta karashe tana jefo masa tambayar muryarta na zafafa harma da fara yin tari saboda irin yadda kirjinta yayi zafi sosai

A hankali Sultan ya sada kansa, Muryarsa a shake sosai ya ce" Allah ya huci zuciyarki ANMY"

A hankali su Dayabu suka ringa fada su ma

Ummi ta mike ta dauko mata ruwa ta kawo ta mika mata

Anmy ta ki karbar ruwan a hankali ta ce" Kowa ya zama sheda, idan yarinyana ta fito abinda ta zaba zan yi mata, dama mun hada auren nan ai ba tare da kana so ba ko? Tunda har ka haWa da aminiyarta tun farko, yanzu kuma zaka karo likitar da tace maka ita ta zubar da cikinka , wato ita ta zo ta haihu ko? Ba laifi, kana iya kara aure ba zan hanaka ba, sai dai ka sani, idan ta bayyana in tace sai ka salameta sai ka salameta, babu wanda zai hana ka bata lafiya, na tabbata ba zata rasa wanda zai so ta soyayar da zai bata darajar da ta cencenta ba "

A wannan karon kam kan nasa ma kasa dagowa yayi, sai Abiey ne ya ringa neman yin wa'azi da nuna a yi hakuri shi ya fi dacewa da wannan tashin tashina, kuma kar a yanke hukuncin komai tsakanin mace da miji a barsu su shirya kansu

Kiraye kirayen sallar isha'i ya sa mazan mikewa suka wuce masallacin cikin fada...................., suma matan suka shige dan gabatar da Sallah

Bayan sallar isha'i su uku suka tsaya suka yanke ta inda zasu fara, ya zamo tun a lokacin Sultan ya shige bangarensa ya shirya ya kuma gama magana da duk wani mahalukin dake karkashin sa, suka fice su biyu kawai daga shi sai sarkin bulala a motarsa ta sports suka fantsama cikin gari, a nasa tunanin yana iya samunta a wajen da takan je kafin a yi aurensu, wajen hutunta, wajen basket ball dinta ne, kai harta wajen da take siyan abinci yayi niyar sai ?afarsa ta taka a daren nan, Sarkin bulala kuwa dama a shirye yake su zaga du inda kafarsu zata shiga dan sami GIWAR uban gidansa.


Yaya Dayabu ya koma ya sanar da su Anmy cewar zai je ya duduba gidajen motoci, zai wuce gidajen kawayenta a sirance da dabara, uwa uba zai samu AIDA saboda itace abokiyar tayata wasu abubuwan.


Daga nan shima ya fice, Abiey kuwa dama bai shiga gidan ba, ya je ne ya samu mutanensa dan a sa ADU'A, a duk inda take Allah ya karkato da hankalinta gida ya tsareta.




Daren nan babu wanda ya rintsa sai yara, tun daga WA'INDA ke cikin n fada har WA'INDA suka bazama nemanta, wani abin da ya dauki hankalin yaya Dayabu shine tunda ya ringa bin gidajen motocin nan ko kiran A'ishah bai yi ya sanar mata abinda yake ciki ba, hasalima bai san cewa lokaci ya ja ba har sai da sallar asubahi ta riske shi a cikin gari sannan ya dauki hanyar gidansa, a mugun gajiye, jikinsa ba karfi, zuciyarsa ba karfi, hankalinsa a rabe gida gida, bale da Ummi ta yi kiransa a Dazu ta sanar masa cewa Anmy bata da lafiya, kirjinta ke ciwo da kanta, wannan tashin hankali ya fi daga masa hankali, domin a yanzu yake kara tabbatarwa cewar da wahala zukata su samu sukuni in dai ba sannin inda take suka yi ba.........., dan kuwa shi Sultan babu wanda yake da labarin tasa wayar domin baya dagawa yana tare da Sarkin bulala a inda su ne kawai suka san inda suke sai mahaliccin su.......tabasss koda sun dauki zafi da gaggawa suke sakewa saboda su din sheda ne, bawan Allahn nan yana son matarsa, laifi ne kowani bawa na iya yi, dama duk girman shekaru da ilimin da ake gannin mutun yana da shi yana iya zamowa ta wani fanin yana aikata laifin da sai an tunatar da shi, wani kuwa haka zai yi ta aikatawa da tunanin daidai kenan har a koma ga Allah, shi kam maganganun Dayabu da na mahaifiyarsa hada da wanda ita din ta yi sun gama rikita duniyarsa da tunaninsa......., bashi da lafiyar zuciya da ta gangar jiki, a yanzu haka a tsaye yake kan kafafuwansa ba tare da ya zauna ba, Sarkin bulala ne kawai ke ankare da motsinsa, Ama kam yana da bukatar hutu koda na minti talatin ne.



Yaya Dayabu ya shigo gidansa kusan karfe shida na da rabi na safiya, mai gadi ya gaishe shi da tambayar ko lafiya ? Domin shi bai rintsa ba tunda uban gidansa bai dawo ba, ya kuma tabbatar masa cewa kalau kafin yake nufa Falon gidansa da tunanin ta yiwu A'isha bata rintsa ba.


A lokacin da ya shigo falonsa ya samu A'isha rike da plate din abinci a hannunta tana duban wajen d?ner ta ce" Najeeba, ga wainar kwai na soya maki, rufe abin nan tunda Bakya so, taso nan ki ci Please"

Wani irin ja yayi ya tsaya ya ce" Najeeba????"

Lokaci daya suka juyo, Najeeba ta mike tsaye da sauri tana kallonsa ta ce" Lah yaya, daga ina kake ka ga jikin ka kuwa?"

Yaya Dayabu ya tatare riga ya nufota yana fadin" Daga gidan ubanki nake, Najeeba yau mai rabani da ke sai Allah a gidan nan!"

Ihu ta saka ta ja hijabinta ta nade wandon dake jikinta zata yanka da gudu A'isha ta je da sauri ta shiga tsakani tana hade hannayen ta ta ce"
https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3
*Kayan kitchen kike nema?* *Laces ko atamfa ko* *materials?? Yar uwa muna da takalma ,jaka akwatuna d kayan parlor* *nd toiletries, d sauran* *abubuwa d dama kuma* *delivery nationwide In* *sha ALLAH=?
? sannan* *muna bada kaya a* *farashi mai sauqi domin masu siya su siyar kiyi* *joining domin ki amfana* >??>??







>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




31




A tausashe ta ce" Haba bb, dan Allah kar ka taba lafiyar jikinta, ka san fa halin da take ciki"

Kanshin soyayan kwon nan gaba daya sai ya zama kamar wani duniyar abinci a hancinsa, ya saka hannu ya karbe , a gajiye tibis ya yi zamansa nan saman tiles ya nemi saka hannu ya ci a haka

Da gudu matar ta je ta dauko ruwa a kwano ta kawo masa hadi da madara mai sanyi ta ajiye masa suka Wan ja baya sunna kallon yadda yake cusa wainar kwan nan

Sai da yayi kamar loma hudu ya ci karfin kwan a hankali ya ce" Kya karo min???"

Kai A'isha ta gyada ta yi ciki da sauri , dama tuni ta yi harda nasa ta rufe dan ta tabbata duk tsiya in dai yana numfashi kuma a cikin hayacinsa yake zai leko gida da safe

Dawowa ta yi da shi ta juye masa duka harda nata hade da hankalin turawa soyaye ta koma kusan Najeeban suka yi zuru sunna kalonsa

Ci yayi sosai, sai da ya kusan koshi ya Dube su, ya ce" Ni zaku cuta ko? A'isha harda ke za'a hada baki a cuceni? Tun yaushe ta zo gidan nan? Karfe nawa ta zo gidan nan"

A'isha a sanyaye ta ce" Kusan magariba ta karaso , bab dan Allah ka tsaya ka sauraremu, ai muna nan zaune muna jiranka har karfe goman dare baka shigo ba, na so kiran naka Najeeba ta Kiya, Ama na bar maka msg ka duba WHATSUP dinka, tunda na yi kiran zahra'u ta tabbatar min du kunna tare sai na yi hakuri har Allah ya kawo ka"

"Ashe mata du hankalinku da tunaninku iri daya ne?, a kan me zaki biye mata ku kyale? Bakwa tunanin halin da za'a shiga? Bakwa tuna halin da iyayenmu zasu shiga da mijinta da mutanen dake zagaye da mu? A fitowarta da ace wani abu ya sameta sai a ce me? Shikenan ku idan zuciyarku ta Saci komai sai ku yi bakwa tuna WA'INDA ke zagaye da ku? Ke Najeeba dan ubanki idan kika ce sai an zauna ba za'a zauna a saurareki bane Shikenan sai ki tashi ki fita daga gidanki harda ikirarin a sake ki? Kina da hankali kuwa????" Ya katse su yana fada sama sama hadi da lalubo wayarsa

Da sauri Najeeban ta karasa ta rike hannunsa mai dauke da wayar, idanuwanta suka cika da kwallah, a raunane ta ce " Ba zaka yi kiran kowa ba, ba zaka sanarwa kowa inda nake ba, idan kuwa ka yi haka ko ta garu ne sai na haura na bar gidan nan ta yadda zan daga muku hankalin mai sunan hankali, idan ka kula a yanzu Ban so dagawa kowa hankali ba saboda na san ba a ko'ina nake iya shiga in fita lafiya ba, Ama idan har ka yarda ka nuna min a gidanka bani da mafaka idan rana ta min zafi zan kara gaba Allah!" Sai kawai ta fashe da kuka ta Wora kanta a hannun nasa , cikin rizgin kuka ta ce" Haba dan Allah, yaya kake so in yi to? Dama ina zan je in ji sanyi? Ka san ban isa in tunkari Ummi ba, ban isa in yarda a san na fito ba, zaman da kake magana nawa aka yi? Du ba tsoronsa kuke ji ba? Idan aka so zaman in magana zaka yi sai ka fara cewa Allah ya huci zuciyarsa maimakun ka dubi idannuwansa kace kai SHAHEED baka isa ka wulakanta min kanwata ba, du ba shi yasa yake ganin shi din wata tsiyar da ba zai taku bane?, to na ji, gaba dayanku tsoronsa kuke ji, Ni sai ku barni da shi, idan bai sakeni ba sai na daukaka kara daga Nijar har kasar makotan Nijar an gurfanar da shi an nuna masa shi karamin kwaro ne, na gaji, na gaji na gaji, kuma idan har aka sanar musu cewa ga inda nake guduwa zan yi, dan kuwa ina iya saka ku barcin kwana uku daga kai har matarka da mai gadinka in dauki motarka in yi tafiyarta ka san da na iya aikatawa ko?"

Ta karashe tana saka idannuwanta cikin nasa kafin ta saki hannunsa ta yi dakin baki da sauri ta shige

Mikewa yayi wuuuu zai bi bayanta, da sauri A'isha ta riko hannunsa

Ya warci hannun nasa ya nunota da yatsa ya ce" Zan make ki a gidan nan idan kika kuma tabani, tunda da ke za'a hadu a daga min hankali ! Daina, daina daina kallona kamar wata ta Allah, baki ji kunya ba ban shigo gidan nan tun Jiya ba baki nemeni ba? Koda yake ba zaki neme Ni ba tunda kin san abinda kuka yarda a yi?"

A hankali A'isha ta sake riko hannun nasa tana kallonsa a sanyaye ta ja hannunsa suka nufi dakinsu

Sunna shiga ta shiga taya shi tubewa, tana yi yana buge hannun da masifa kala kala , duka ta yi shiru har suka yi bayi

Bata yi kasa da gwuiwa ba ta taya shi wankan da ruwa mai dumi sosai, suka gama suka fito ta nufi bed da shi

Bai yi gardama ba, domin sai da yayi wankan nan ya ji babu abinda ya rage masa irin ya bi lafiyar gado

A hankali ya ce" A'isha, bani wayata in sanar musu cewa gatanan tare da Ni kin ji?"

A'isha ta gyada kai , tana faman shafa damatsunan hannayensa , like da shi a hankali ta ce" Zan dauko maka , so nake yi ka dan huta wai"

Sosai yake son juyewa da ita dan ya dauko wayarsa, Ama wani irin nutsuwa ke ratsa shi wace barci ya ringa fuzgarsa har ya fuzge shi gaba daya

Ajiyar zuciya ta ringa saukewa a lokacin da ta ga yayi barci, ta mike a nutse ta cenza tufafin jikinta ta rufe masa dakin ta nufi wajen Najeeba

Samunta ta yi saman gado , ta karasa tana yar dariya ta ce" Kuka wai kike yi?"

NAJEEBA ta turo baki ta ce" yanzu ina zan nufa? Ki bani ky din gidan ku in je cen in buya tunda shima haka zai min"

A'isha ta yi yar dariya ta ce" Kin san dole zai ki sauraronki, ki bari ya huce ya huta idan ya fito sai mu yi yakin da zamu yi, abinda na sani shine babu wanda ya kaishi tausayinki, kuma duk hukuncin da ya yanke a kanki dole zaki bi, ko a haka aka tsaya kin girgiza kowa, kuma na tabbata idan ma zaman za'a yi a yanzu sai kin fi Wora abinda kike so kuma a maki, plz dear ki yi hakuri kin ji?"

Najeeba ta juya ta a sauka daga saman gadon ta shiga bale mabalin rigarta, ta juyo tana kallonta ta ce" Aunty, ba zaki gane ba, a yanzu bana son wata masalaha da shi, idan kuwa dangina suka SAKANI a tsakiya na san zasu cin Mani ne, ki fadawa MIJINKI idan yace zai tursasani zai neme Ni ya rasa ne!"

A'isha ta rasa me zata ce mata, tana kallon ta har ta shige bayi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta sada kanta........

Ba zata so ace zukata sun wahala a kan abinda zukatan suka riga suka san abinda yake jiransu ba, sai dai idan har aka yarda akace za'a bi da ita da karfi wannan karon ma ta kai matakin da take iya zuwa din Ama kuma a yi zaman da ba dadi..........

A hankali ta mike ta koma KICIN dan ta sake musu wani abin karin zuciyarta cike da farin cikin irin yadda alamomin cikin Najeeba na nan suka bayyana, domin tun Jiya da ta zo ta zo da kwadayin cin kwai, a soye ne ko a dafe zata masa cin da ya wuce tunani har ta ringa fadin bata san cewa tana son kwai irin haka ba........, kwarai Allah ke yiwa bawa yaki, kuma ta tabbata yakin da Allah ya yiwa NAJEEBA ne ya bayyana a yanzu, fatanta a ci moriyar abin cikin kiyaye harshe, da zuciya, a jajirce da hakuri.



*SULTAN*


Anya Akoy abinda za'a iya duban magidanci, baban mutun, Basarake ace Akoy abinda bai gani ba a duniya wanda zai iya saka shi a wani hali? A tunaninsa a yanzu, babu abinda zai saka shi a cikin irin wannan yanayin ko menene, ciki kuwa harda mutuwar makusanta saboda ya riga yayi imanin gidan gaskiya kowa sai ya je a lokacin da bai shirya ba, saboda babu wanda mutuwa ke dauka a lokacin da ya gama wanka ya shirya tsaf ya daura likafaninsa, wannan dalilin ya sa ya gama sakawa zuciyarsa dangana da jiran nasa lokacin ko na makusanta .....
Sai dai wani ikon Allah, tun Jiya kafin magariba yake tsaye a kan kafafuwansa har yanzu karfe goma na safe ba tare da ya iya saka wani abin kirki a cikinsa ba sakamakon ciwon dake nukurkusar zuciyarsa mai haWe da fargaba da faduwar gaba, harma da wani wani irin boyayan launin tsoro mai saka bawa cikin firgici da fitar hayaci

Dama babu abinda yake da saurin kashe yannayin mutun kamar zulumi da shiga halin kila wa kala

Tabas ya samu kansa a ciki har ya zamo ya rasa inda zai dosa

Ina take? Me take yi? Yaya take?

Sunne tambayoyin da suka fi yi masa yawo a kwonya har zuwa wannan lokacin da Ummi ta gane cewar dole ta sada aminiyarta Y'ar uwarta da likita saboda shi ciwo irin na hawan jini ko ga yaro bashi da dadi bale baba, domin andiya ta gama aunata ta sanar cewa jininta ya hau, kuma abin tashin hankalin shine ya ki ya sauka saboda ko ta sha maganin hankalinta ba a kwance yake ba, a dole ta mike da kanta ta nufi bangaren SULTAN, wanda sai da tsoro ya kamata sakamakon irin yadda bangaren ke cike da dakarun Sa, tamkar zasu fita yaki , kowane fuskarsa a tamke take, sunna cikin halin bacin ran da basu san dalilinsa ba domin su dai basu san abinda yake faruwa ba, sai sarkin bulala, da malami da shamaki ne kawai suka san abinda yake faruwa

Da kyar ta samu shiga, ta same shi rike da carbi yana kai kawo da waya a hannunsa , sanye da bak'ar jalabiya sai farar safa

Tunda ta shigo ya dakatar da kai kawon ya zubawa fuskarta ido hade da sakin tasa fuskar daga daurewar da take

A lokacin da ta gama shigowa ya sada dubansa dan girmamawa ya furta" Umani"

Ummi ta Dube shi da kula, a tausashe ta ce" Baka kwonta ba, baka rintsa ba, baka ci abinci ba, ko?"

SULTAN ya dan lumshe idannuwansa, a hankali ya furta" Zan yi"

"Yaushe?"
Ta kashe shi

A hankali ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, bayan keyarsa na wani irin rikewa

Nufa wajen waya ta yi ta dauka ta shiga contact ta danna NUMBAR bangaren Nadiya

Bata jima tana RINGIN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login